← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 157

Sashe 142

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari duk wasu masu zuwa daga wani garin sun gama isowa. Radhiya dasu Zahra da wuri suka tafi salon inda Arifah da wata cousin dinta suke jiransu. Gyaran hannu da kafa aka fara yi musu ga fatar jikinsu tana ta sheki anyi gyara har an gaji. Bayan sun gama  aka zo wankin kai. Radhiya na bude gashinta Arifah ta rike baki ganin yadda kasansa yayi wani irin ja mai duhu. 

"Dye kika saka?"

"Lalle ne" ta bata amsa kafin ta hau bayanin yadda ta kwana hudu tana kwana da lallen da take shafawa a a gashin kullum. Kimantawa tayi kamar daya bisa ukun gashin amma daga kasa take saka masa lallen shine yayi wannan kalar. Daga sama zuwa kafadunta baki yayin da kasan ya bada wata kala mai kyau. Ita da bata saka relaxer steaming da stretching aka yi mata ranar wuni guda a nan suka kwasheta.

Yau Laraba ranar da ake jira tayi. Karfe takwas mai lalle tazo dama jiya an yiwa kowa amarya kadai ta rage. Zama na musamman suka yi aka gama ja sannan aka dora baki. Karfe biyar Mama tayo waya don itama gidanta da baki haka na Mami. Su Hussaina, Nura da Hany wadda ta soma jin sauki sun taho. Gidan Mami tayi masauki sauran suna gidan Mummy Gambo.

A jikin katin an riga an rubuta tsarin events ciki harda zuwan baki daga bakwai da rabi tunda ana Magrib shida  da rabi ne zuwa takwas da kwata lokacin da za'a rufe hall a fara event. Mutanenmu da son biki babu mai son a rufe shi a waje shiyasa duk mai zuwa shiri yake da gasken gaske.

Wanka Radhiya ta silla tare da dauro alwalar magrib. Bayan ta shafa mai tayi sallah ta zura kaya don har ita Mama kira take akan idan suka bata lokaci zata saba musu ne. Riga da skirt ne na wani irin material pink da ya amsa sunansa. Rigar daidai da jikinta amma wuyan ya rufe mata baya sai daga gaba aka bude. Hannun dogo daga kasa an bude shi sosai. Shirt din ma sai daga kasan gwiwa aka saka net domin kara masa fadi. Kafin a fara kwalliya Emzee ya kwankwasa kofar dakin yana kiranta. 

Tana lekowa ya saki murmushi "my one and only Sis kinyi kyau"

Itama murmushin tayi "kai Emzee ba ayi kwalliyar ba fa."

"Duk da haka bani da ta biyunki" yace daidai fitowar Rahima ta kada kanta kawai don yanzu ta saba da halinsa. Dakin Daada ya nufa da Addarsa inda suka sami iyayensu suna jiransu. Baki yaran su ka saki suna kallon Ummi da Daada sunyi kyau kamar ranar tasu ce. Ummi lace ne baki a jikinta wanda ya amsa sunansa anyi masa wani irin adon cin baki da sky blue din zare da stones. Anyi mata kwalliya ta fito sosai tana haskawa abinka da mai yaron ciki. Mayafinta, takalmi da jaka duka sky blue ne, ga dankareriyar sarka da abin hannu. Daada kuma shaddarsa ce sky blue din aikin jikinta simple yet elegant. Yana sanye da hula zannabukar wadda ta dace da kayan. Ummi rike take da links tana kokarin balle masa a hannun rigar ta kasa. Shigowar Emzee shine ta bashi ya makala masa.

Daada yace a rufewa Radhiya ido kyauta zai bata. Emzee ne mai wannan aikin sai da Daada ya bude wata hadaddiyar sarka shigen ta Ummi sannan aka bude mata idon. Tsabar murna kuka ta saka masa ta fada jikinsa. Emzee sai ya koma gefe yana daukarsu hoto gashinta ya kwanta a bayanta. Saka mata dankunnen da sarka iyayenta suka yi tana ta musu addu'a da godiya.Kusan minti goma suna kashe selfie a tsakaninsu sannan Radhiya ta tafi aka fara zuba mata kwalliya tayi kyau karshe. Wasu kayan Fauziyya ta daukar mata a wata karamar jaka da kayan gyara kwalliya saboda idan anyi rabin taron an riga an kama musu daki da zasu chanja kaya a cikin Sheraton Hotel inda za'ayi event din.

Kowa ya gama shiri ana ta shiga mota masu tafiya da katinsu a hannu tunda card admit ne. Takwas da minti kadan Awwab ya shigo gidan ya bude wurin da wani irin kamshi mai ruda tunani da sanya shauki. Three piece tweed suit ce a jikinsa burgundy color da dark pink necktie da irin hankicin nan da ake leko dashi ta saman aljihun coat din. Yayi aski da gyaran fuska fuskarsa ta sake fitowa sosai. Yana shigowa daidai da Zayyana ta riko Radhiya saboda tsinin takalminta suna saukowa a hankali. 

Murmushi ya sakar mata ita ta mayar lokacin da zukatansu ke tsananta bugu ya karasa step na biyar inda suke tsaya ya mika mata hannu "shall we?"

Kai ta gyada a hankali tana ta murmushi ya riketa suka sauka. Su Zahra na biye dasu mazansu na waje suka je suka shiga motocin da mazansu ke jiransu. Ankonsu lace ne cream da head golden kowacce ka kalla kara. Zayyana kai tsaye motar Ibrahim ta wuce shi da Emzee su ma suit din ce jikinsu grey amma basu saka necktie ba sai maballin saman da suka bari a bude. Ba shi ba ba Emzee sai ka rasa wanda yafi yin kyau. Rahima tana biye da ita da dan glass dinta kamar a dauketa a boye Emzee ya kasa dena kallonta. Ibrahim da baisan dawan garin ba yace bari su dauki mota daya kawai suka tafi a tasa. Matan na baya suna gaba suna taba hira amma Emzee da Rahima sai uhm da uhmm.

Bakar Limousine ce ta dauki amare da angwayensu zuwa Sheraton Arifah da Radhiya suka zama bebayen karfi da yaji. Kayansu babu bambanci ko daya sai sarkarsu yayin da mazan su ma komai daya ne a jikinsu. 

Kofar hall din katuwar poster ce zaune a kasa gefen dama hoton Yousuf da Arifah wanda suka yi da shadda matan aka saka pin aka danne musu fafaren mayafansu ta tsakiyar daurin da suka sha. A bangaren hagu kuma Radhiya da Awwab sunyi tsayuwa iri daya. Matan na zaune akan kujera suna kallon fuskokin mazansu dake tsaye a gefensu sun dafa hannun kujerar. A tsakiyar hoton an rubuta sunayensu.

Kafin shigarsu iyayen taro suka taho. Kayansu saka iri daya bakin lace na Ummi da sky blue irin shaddar Daada, Mami Caramel irin shaddar Daddy, Mama light yellow irin ta Baba Hadir, Tante Brown irin na Alh Moussa sai kuma na Mom light green irin na Excellency. Idan ka cire iyayen Yousuf sauran hudun zaratan maza ne da suka dandani me ake kira bautar kasa da jiki da lafiya tare da matansu jarumai wurin hakuri da juriya. Taku suke ana daukarau hoto a cikin kayataccen hall din har zuwa mazauninsu. Bayan sun zauna be aka kira angwaye da amare abin gwanin ban sha'awa da burgewa. 

Taro ne na manyan mutane komai cikin nutsuwa da hankali ake gabatar dashi. Bayan an bude shi da addu'a aka gabatar da takaitaccen tarihin angwayen da amarensu.

Wani abin burgewa shine kiran Emzee da da MC Kdm yayi a matsayin babban abokin amarya saboda babu wanda yasan Alheran Radhiya Zayyan Tureta sama da shakikinta Muhammad Zayyan Tureta. Zahra ce ya bada tarihin Awwab sai kuma wani abokin Yousuf da kawar Arifah 'yar kanin babanta suka bada nasu. 

Can cikin taro akwai 'yan gidansu Zayyan da su Hussaina harda Mummy Gambo da yaranta. Ghazalatu ta shiga wani yanayi na tashin hankali ganin yadda Awwab ya fito yayi masifar kyau. Kallonsa take bata ko kiftawa saboda yadda take jinsa a ranta.

Ana tsaka da taron ne su ka ji wani dummm sai wanda ya sanya Awwab da Yousuf tashi lokaci guda kuma hall din yayi duhu sai haske ya koma bakin kofar shigowa. Radhiya dai taji Awwab ya matse mata hannu kadan sannan a daidai kunnenta yace mata yana zuwa. Idanu fa sai suka koma bakin kofa bayan kamar minti daya da rabi sai ga Yousuf da Awwab sun bullo ta katuwar kofar shigowa. Dukkansu sun cire coat dinsu sai ta cikin mai maballai ta gaba wadda suka dora akan farar shirt din mai dogon hannu sannan sun cire necktie sun bude maballai biyu na gaban shirts dinsu. Sanye suke da homburg hats kalar wandunansu an dan turo ta gaba a karkace.

Yousuf ne ya fara magana da mic a hannunsa daga can gefen amaren ta sama aka fara slide show inda hoton Arifah ya bayyana tana zaune cikin fulawoyi tana murmushi.

Sannu a hankali yake takowa zuwa gareta yana magana cikin harshen turanci duk da dai faransanci yafi zama sosai a bakinsa.

("Thank you Arifah Nasiruddeen for being a part of life. Thank you for accepting me to be the man in your life. You are my Queen the most beautiful woman I have ever seen. To the special you I say I love you")

Ba Arifah ba hatta Mom dinta sai da taji wata kwallar farinciki. Hannunta ya kamo zuwa tsakiyar filin idanunsu cikin na juna a lokacin da Awwab ya soma taku daidai zuwa wurin zaman Radhiya.

("Once upon a time an adorable Angel was born") hoton Radhiya ne ya bayyana ranar sunanta wanda aka daukesu tana hannun Awwab yana murmushi ya dan juyo da fuskarta yadda zata fito a camera ("You and I were always meant to be. I love you with all my heart...just so you know, it has always been Alheran Radhiya. The fearless 'Yar soja, my one and only")

Wannan karon Ummi ce da hawayen ta sunkunyar da kai Daada ya matsa mata hannu yana cewa suyi kusu addu'ar fatan zaman lafiya.

Awwab ma riko hannun matarsa yayi zuwa tsakiyar filin kusa da Arifah sannan ya yi mata murmushi shi da Yousuf suka ja baya. Kidan wakar da matasan wurin da dama suka sani ta Umar M Shareef JININ JIKINA ce ta karade wurin hasken wurin ta koma kan Awwab, Yousuf, Emzee, Ibrahim, Bilal da Raji duka sun ajiye coats dinsu kowa ya tsaya a inda ya dace suka fara takun wakar yayin da baitin farko ya cika wurin.

(Da ganinki sai na kamu.. gashi kin zamo jinin jikinaaaa)
Chapter 142 · 0% Book details