← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 157

Sashe 22

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk rashin halin Hajjo sai da tayi kukan tausayin Mairama. A haka suka tafi Kano Salisu yana ta mamakin halin Malamijo. Ashe Salame gado tayi na munin hali ba taka haye ba.

Tare suka sauka a tasha ya ja Mairama gefe ya fito da kudi masu tsoka ya damka mata sannan suka nemi motar Sumaila shi kuma ya shiga hayis zuwa gidansa. Dama ya riga ya gama shawararsa tun a hanya shiyasa yana ganin yadda Salame ta fito muzumuzu ita a dole tana cikin alhinin mutuwar masoyi ko sannu bata yi masa ba ya dakatar da ita zata tashi ta bar falon saboda ta ganshi.

"Salame ki hada kayanki ki tafi gida na sakeki saki daya"

Kiris...sauran kiris irin mai riss dinnan zawo ya tsinke mata. Tunda take bata taba jin fargaba da tsoro kamar wannan lokacin ba. Ya saketa ta tafi ina? Sumaila? Allah Ya kiyaye. A iya zurfin tunaninta Salisu yana mata son da zai iya hadiye kowane abu tazo dashi. Shiyasa take yadda taga dama iyaka yayi fada anjima ya dawo yana bibiyarta. To ko dai kunnenta baiji da kyau bane.

"Ni ka saka?"

"Halifa da muka haifa da ana komawa baya Salame bazan so hada jini dake da mahaifinki ba. 'Yar cikinsa tana cikin magagin rashin miji amma dukiya yake nema duk arzikinsa. Wallahi bazan iya ba. Kije Allah Ya baki daidai dake."

Kande ya kwalawa kira tazo ya cire naira goma yace ta wuce ta kaiwa mamansa Halifa yana tafe. Dayake daga can gidansu aka kawota ta riga tasan gidan.

Salame tana kame ta kasa motsawa ya wuceta ya shiga daki. Sai da abin ya sami wurin zama a kwanyarta ta shiga ta fara masa ihun masifa.

"Wato akan Mairama ka sakeni saboda Malamijo ya bata mata rai. Bazaka burgeni ba sai naga ta tare a gidan nan ranar asabar"

"Ki fita sawunki a likkafa kafin na tashi" yace daga kwance

Tafa hannuwa tayi " nima na huta da auren kaddara zama da mijin da baka so"

Duk inda zata cusa masa haushi ta rinka nema ko a jikinsa tunda ya rabu da kwallon mangwaro ya huta da kuda.

Gidansu ta koma ko ta kan Halifa bata bi ba. Awa uku tsakanin saukar su Malamijo da dawowarta gidan.

Yadikko ta tareta ganinta da akwati niki niki "ke kuma daga ina?"

"Sakoni yayi" ta fada cikin yanayin ko in kula.

Ashar Malamijo ya lailayo ya saki yana kara tunzura da yadda take magana ko a jikinta "wai nufinku duk kun dawo min gida kenan?"

"Ya son ranka? Ca nake mata biyu ka saki a dan tsukin lokaci guda, ai gara ka dana" Hajjo ta fada masa sannan ta saki labulen dakinta.

"To Al-Qur'an daga ke har Mairaman kowa taji da kanta bazan iya ba. Yara masu bakin hali kun fita a talauce kun dawo a tsiyace"

Dakinsu na da ta shige abinta ta barshi tsaye. Nan taci karo da Mairama da kyawawan 'ya'yanta. Kamar ta shareta sai ta fasa tace mata ya hakuri.

"Mungode Allah"

"Allah Ya jikan shi"

"Amin"

Daga haka babu wadda ta sake kula 'yar uwarta har suka yi shirin kwanciya. Ganin Mairama da yaranta ya tuna mata da Halifa sai taji wani iri gashi bata yaye shi ba dama. 

Kyandir Mairama ta kunna a gefen katifar da suke kwance ta kwanto wasikar Zayyan ta soma karantawa.

_(Na rubuta wannan takardar tun ranar da sunana ya fito a cikin masu tafiya Liberia. Sai nake ganin kamar jiya muka yi aure har zan tafi na barki. Mairam ban sani ba ko zan dawo ko shikenan tafiyar. Don Allah alfarma daya nake roko kada bakinki ya taba gajiyawa da sanyani a addu'a. Idan kewa ta isheki kinyi kukan rashina ki sani cewa nima ko a ina nake idan na tunoki sai na zubar da hawaye. Ina sonki Fillo Allah Ya sani amma ina son ki saka a ranki mijinki yayi alkawarin bautawa kasarsa ne. Zanfi kowa son son ace ina tare da iyalina kamar kowane magidanci. Sai gashi aikina yayi min tsakani da hakan. Lokaci zuwa lokaci zan rinka tafiyar da babu lallai na dawo. Duk da haka ina alfahari da aikina kema ki tayani kinji. Idan kin haihu kafin na dawo ki zabawa abinda muka samu suna. Ki kular min da 'Yar Soja Alheran innar Daadaa. Sauran kalaman da suka rage a kirjina sai na dawo gareki zaki ji su. Idan ban dawo ba na baki amanar kanki da ta 'ya'yana. Allah Yayi muku albarka. Lt Zayyan Muhammad Tureta)_

**********

BAYAN SHEKARA TAKWAS
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Ahayye nanaye, wallahi mutum ya yi min ba kyalewa zanyi ba don kaji in gaya maka yaro" tafa hannuwa tayi sannan ta rike kugu tana girgiza jiki a dole ranta ne a bace.

Abokin fadan nata wani sangamemen yaro ne don shima akwai kuruciya sai girman jiki.

"An fada din" yace sannan ya cigaba da wakar da ta hadasu fada "Malamijo Malamijo tsolon rake. Ga kwadayi ga rowa yaki yin gaba"

Wani kukan kura Radhiya tayi ta dire a gabansa ta nuna kasa "in ba tsoro ba dangwali" ta nuna masa kasar wurin. Dabi'arsu kenan 'yan makarantar wadda ta kasance firamare ta gwamnati idan ka yarda zaku dambace to kowa ya dangwali kasa. Daga nan sai a kaure karfinka ya kwace ka.

Dukawa yayi zai dangwala ga tsirarun abokansu da basu bar makarantar da wuri ba sun tsaya kallo. Sai da ta daidaici yayi kasa da fuskar nan kawai ta dauke shi da mari ta ranta a na kare. Kai tsaye staffroom ta wuce inda malamai suke wurin Umminta. 

Tana shiga ta cukwikuye jikin Mairama  tana kuka wai su Danmama ne suka dake ta. Tahowa suka yi Danmama ne a gaba kayansa duk kura saboda faduwar da yayi garin bin Radhiya. Kofar staffroom din taje ta saka su kneeldown har Radhiya sannan ta nemi jin ba'asi. Sai aka rasa me fada mata. Duk fitsarar Danmama yasan da kunya dai ya maimaita wakar a gabanta. Radhiya dama ko me zata yi mata bazata fada ba don kada ranta ya baci.

Daga bayanta taji wani malami yace "Anti barni dasu kiyi tafiyarki gida. Idan na gama zanesu zan taho da wannan mai kunnen kashin"

Mairama ta gyara zaman farin gilashinta tayi dan murmushinta da ta saba yanzu da wuya kake ganin bacin ranta ta koma ta dauko 'yan tarkacenta tayi hanyar fita daga makarantar don dama an riga an tashi.  Daga karkashin wata katuwar bishiyar marke take hango yara suna 'yan wasanninsu. Idanunta suka sauka akan Emzee yana zaune yayi shiru yadda ya saba yana jiranta.

"Karami zo mu tafi" tace da dan karfi don ta kula bai ganta ba sai gashi ya taso da saurinsa. 

Kayan hannunta zai karba tace ya barsu su tafi "Ummi ina Adda?"

"Kyale wannan yau ma fada tayi"

Sunyi gaba wasu 'yan ajinsu suka rinka kwalo masa kira suna Emzee sai an dawo hutu. Wannan suna da Mairama ta hakura da yakar sa dole shine sunan da yabi Muhammad Zayyan har gida. Mutane kalilan ke kiransa Zayyan ko Karami kamar yadda take fada. Yace wani malami da suka yi a firamare two ne yake kiransa MZ Tureta. Shikenan abu na yara ya koma Emzee.

A makaranta kuma gurfane gaban Uncle Idris su Radhiya ne da Danmama. Sai da Mairama ta tafi Radhiya ta fada masa sunan da suke kiran kakanta dashi. Uncle Idris ya tabbatar zasu aikata yayi musu bulala biyar biyar mai zafi da dorinarsa ita kuma biyu ladan biye musu. A waje ta jira shi shima ya dauko kayansa tunda yau take ranar hutu suka tafi yana mata nasihar fada da maza.

A cikin shekarun da suka gabata rayuwar Mairama sai dai godiyar Allah. Zamanta a gidan Malamijo tamkar zaman gidan haya ne. Iyakar gaskiyarsa shi nauyi ya masa yawa fitar da kudi kamar ana mintsininsa ne. Ya kara kudin cefane da kyar da sudin goshi amma daga nan fa ko me mutum ke bukata mace ko namiji cikin iyalinsa sai dai su nemawa kansu. 

Abu na farko da Mairama ta fara yi shine adana kudaden gadonsu a ranta tana tanadinsu ne domin karatun yaran a gaba. Sai da ta fuskanci sabulun wanka wannan idan bazata saya ba sai dai su watsa ruwa kawai ta fara taba kudin. A hankali kudi suka fara samun gibi dole ta fara neman sana'a. Tashin farko ta saro zobo tunda ta tsira da firig dinta ta soma yin zobo da lamurje na saidawa. TV da bidiyo da duka kayan gadonta banda katifar da ta ajiye kusu suke kwana da yaran duka suma saidawa tayi don ta kara jari. Allah Ya dubi halin da suke ciki ya buda mata kasuwa tana ciniki sosai.

Salame tana gefe kullum tana yawo tsakanin nan gidan nasu da wurin Ta Madina wadda da fari ta dauki fushi mai tsanani da ita sakamakon mutuwar aurenta. Har gida suka tura aka nemo Salisu ko zai maidata yace idan ta sami miji tayi aure shima auren zaiyi.

Zaman gaba, bakinciki da hassada ta dauka tana yi da Mairama. Kayan dakinta Ta Madina ta sayar ne ana bin malamai domin karkato hankalin Salisu. Shiya janyo ita bata da komai gashi jiki ya saba da jindadi an manta wanki, shara da wanke-wanke.

Wahalar gidansu a yanzu har tafi ta da tsanani ko don zawarci suke oho. Hankalin Mairama yana kan inganta rayuwar 'ya'yanta, na Salame yana kan me zata yi ta kere Mairama ko ta hanata cigaba. 'Ya'yanta musamman Radhiya sun tsole mata ido. Abu kadan ne zata yi ta kai mata hannu da duka amma Mairama bata taba tankawa ba. Lokuta da dama wurin Yadikko suke zama ko Hajjo idan 'yan mutumcin suna kusa.

Wata rana ta gama zobonta da lamurje ta kukkulle a leda santana suna cikin wani katon baho a nan bakin famfon tsakar gidan inda take aikinta ta tashi ta tafi jawo ruwa a rijiya zata wanke wurin. Salame tana ta fakonta don dama ta gane yanayin aikin nata. Idan ta gama kullewa sai ta janyo ruwa ta wanke wurin sannan ta dauka ta kai firig dinta ta jera. Su kan wuni da wuta amma da wuya ta kwana. 
Chapter 22 · 0% Book details