← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 157

Sashe 79

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake narke masa tayi sai da ya dage ya iya controlling kansa daga barin janyota jikinsa.

"Hamma manaaa..."

Bashi da zabin da ya wuce juya kan motar ya barta a mota yaje ya siyo. Katan uku aka saka masa a booth sai guda hudu masu sanyi a ledar hannunsa. Yana zama ya mika mata ta balle saman gwangwanin tana sha tana lumshe idanu.

Rabi tasha ta mika masa ya karba sai da ya kalleta ya dora bakinsa a kai ta kawar da kanta gefe.

"Tell me about your project tunda jira kike na roka"

Sun kusa gida lokacin ta soma yi masa bayani dalla dalla kamar ba Radhiyan da ya sani ba. Shirmen yana nan amma ta fannin karatun bata wasa. Wannan ita ce Alheran din da ya fada soyayyarta.

"Impressive. I am proud of you. Amma why mass comm? Meyasa baki zabi wani course din ba?" Ya tambayeta bayan yayi parking din motar. 

Gwangwani na biyu take shirin budewa ya karba ya bude mata. Kafin ta karba ta nuna masa wannan zoben nasa.

"Ka ga wanda ya zaba min nan. A hannuna sunansa Awwab shi yace yafi son nayi mass comm"

Duk kalma daya dake fita daga bakinta tana kara hura masa wutar soyayyarta ne. Bazai sake yarda da wasu dalilai ba da zasu sa yaki aurenta wannan karon. Baya ma tunanin komawarta school babu igiyoyinsa a kanta. So yake yaje ya kammala abinda Mama ta katse masa ya dawo ayi komai a gama kafin ya koma aiki.

Kwantar da kansa yayi baya a jikin seat yace "Kin shirya aurensa yanzu"

"A'a"

"Reason?"

"Sai ya dena fushi dani"

Gwangwanin hannunta da ya bude mata ta mika masa "rage min".

Kurba daya yayi ya bata ta dauki ledar ta fita batare da ta sake cewa komai ba. Yana kallonta har ta shiga gida ya fiddo wayarsa da niyar kiranta ya fallasa mata duka sirrukan zuciyarsa ya ga kira da bakuwar namba. Yana karawa a kunnensa ya gane muryar mai maganar mahaifin Arifah ne.

Tambayar farko da ya fara yi masa shine yana son sanin idan shi kadai ne a inda yake. Idan ba shi kadai bane kuma ya tashi ya kebe akwai maganar da yake so suyi.

Awwab ya tabbatar masa da cewa shi kadai ne sannan yace masa yana bukatar passport dinsa a daren saboda gobe da sassafe za'a zo a karba. Dakinsa yaje da sauri ya dauko yanayin muryar Excellency yasa shi jin cewa akwai abinda yake faruwa. Bai sanar da kowa ina ya tafi ba yaje gidan wanda kamar jiransa suke masu gadin aka bude masa gate.

Wani falo PA dinsa ya jagorance shi suka je ya same shi tare da bakon da bai sani ba. Duk da haka ya mika masa hannu suka gaisa bayan ya gaisa da gwamnan. Da turanci domin kowa ya fahimta ya soma magana.

"Awwab wannan sunansa Chibuzor Kalu"

Murmushi ya sake yiwa mutumin wanda ya dauke a lokacin da yaji Excellency ya fara fada masa abinda ya kawo Chibuzor garesu.

"Zayyan is alive and in prison"

Mikewa yayi tsaye yaji kansa ya kulle. Gaban Chibuzor yaje ta idanunsa suna nuni da rauni matuka "is this some kind of a joke?"
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Nima haka nayi tunani. Zauna Awwab. Duka wani protocol da ya kamata nabi domin sanin gaskiya nabi. Yanzu haka ina jiran kira daga Mr President ya bamu go ahead mu nemi ganawa da gwamnatin kasar domin a sake shi"

"Kana nufin Babana Zayyan yana da rai duka tsahon shekarun nan a prison" hawaye ne mai zafi ya zubo masa baiyi yunkurin dakatar dashi ba.

Dukkan bayanai Excellency da kansa yayi masa yaci kuka tamkar kankanin yaro. Zancen da girma kuma da nauyi. Gashi yace yayi shiru har su dawo saboda yana tsoron sakawa iyalinsa rai da abinda ba gaskiya ba.

"Ka samo min hotonsa, na matarsa dana 'ya'yansa. Idan da hali harda copy na national identity card dinsu ko international passport domin mu tabbatar musu bashi da alaka da Liberia"

Kamar anyi masa duka haka ya koma gida zuciyarsa tana ta bugu da karfi. Zahra bata dakinsa a nan ya kwana sai dai ko digo bai iya runtsawa ba. Kwana yayi yana tunanin ta yadda zai samo hotunan da ake bukata. Duk da yace kada kowa yaji dole ne ya nemi mai taya shi. Jira yayi sai da su Yousuf da Tante suka tafi airport zasu wuce Nijar, shi dai bai bisu ba su Radhiya ne suka tafi rakiya ya shiga bangaren Mama. Baba Hadir yana falo sai ya wayance da ganin Daadaa ya tafi. Mintu talatin bai cika ba ya kuma dawowa har yanzu yana falon ita ta tashi. Zama yayi kamar akan kaya yana jiran Baba Hadir ya fita ko ya koma daki shiru. Mama tun da ta dawo take karantarsa daga karshe tace wa mijinta ya basu wuri zasu gana da danta ta ga alama son aure yake yi.

Baba Hadir ya girgiza hannuwa wai babu ruwansa ya tashi ya shiga ciki. Sai kuma ya kasa cewa komai.

"Awwab ka fara bani tsoro. Akwai abinda ke damunka fa"

Siririn hawaye ta gani ya ziraro daga idonsa ta soma tafa hannuwa "Radhiya ta sake cewa bata shirya auren bane?"

"Ni ai na shirya so bana bukatar amincewarta" yace yana kakalo murmushi.

"Good, me kake boye min?"

Yanayin da ya shiga da Excellency yake masa bayani har tafi shi. Zainab kuka take rikewa Awwab yana bata baki da ta daure saboda kada a gane. Abubuwan da yake bukata ya zayyane mata tace zata yi masa kokari zuwa dare. Daurewa kawai ta rinka yi kada ayi saurin ganota musamman da Ibrahim da Emzee zasu dawo yau gidan zai kara cika. 

Dakinsu ta shiga cikin kayan Baba Hadir ta dukufa bincike. Bata yi mai yawa ba ta samo hotunan Zayyan da khakinsa shi da Hadir. Da wayo da dabara tasa Radhiya ta kawo mata passport dinta wai zata gani. Hadawa tayi da hotunan ta bawa Awwab cikin wata leda wai sako ne. Yana karba yaje yayi photocopy na passport din ya dawo mata dashi. Sauran hotunan ta waya ta tura masa duka yayi printing ya kaiwa Excellency. A hanyarsa ta komawa gida ya kira shi ya sanar dashi shugaban kasa da kansa ya nemi shugaban kasar Liberia zai bada umarnin a duba masa mai wannan suna a prison din. 

Wannan dare ma bacci barawo da kyar ya dauki Awwab, Mama Zainab da Col. Nasiruddeen. Dare ne mai tsayi a garesu wanda a safiyarsa ne zasu ji dahir. Ayi ba ayi ba sai gabanin magariba wayar Excellency ta shigowa Awwab.

"Karfe tara na safe zamu tashi gobe, Zayyan has been found"

"Alhamdulillah" Awwab yace idanunsa na cika da kwalla. Baya jin komai don yayi kuka saboda abin kukan ne ya same su.

A daren ya sanar da su Mami tafiyar gaggawa ta kama shi Lagos wai kamfanin jirgin da yake aiki zasu gabatar da wani shiri. Ita kadai ce karyar da ya iya nema ya fada musu. Rashin zamansa a gida yasa bashi da lokacin neman Radhiya abin har ya soma damunta. Tun daren da akayi masa wayar sai yau yaje wurin Ummi saboda yana gudun ta fahimci wani abu a tare dashi kamar yadda Mama tayi. Zancen tafiyar yayi mata tayi masa fatan alkhairi. Yaso ganin Radhiya sai dai tayi bacci da wuri period pain ya kwantar da ita. Da safe kafin ta tashi ya tafi sai labari taji wai ya tafi Lagos. Fada ta soma yiwa kanta na saurin bada kai da taso yi bata san babban aikin da yasa a gaba domin iyalansu gabadaya ba.

Da yaje airport yayi mamakin ganin official plane din shugaban kasa aka bayar dungurungum domin dauko Lt Zayyan Tureta. Su tara ne duka a tawagar. Shi, gwamnan Plateau, Deputy chief of army staff, Chibuzor da wasu sojoji guda biyar. Gani yake kamar da shi yake tuka jirgin sai yafi haka gudu amma sannu sannu bata hana zuwa sai gasu sun sauka a filin jirgin Monrovia babban birnin kasar.

Su ma sojoji suka turo domin daukarsu ana musu zancen tafiya hotel Excellency yace ko ruwa bazai iya sha ba sai ya ga Zayyan tare dasu.

**********

Kararrawa aka buga lokacin cin abincin dare yayi 'yan prison din suka soma fitowa daga dakunansu da aka bude. Kusan kullum cin abincin tamkar yaki ake yinsa kowa na sauri ya sami abin arziki.

Tafiyar nan tasa da dogayen kafafunsa yake yi cikin nutsuwa ya isa layin ya tsaya kenan wani kato yazo ya sha gabansa. Sai ya ja baya ya bashi wuri saboda gudun rigima. Sati uku da kwanaki da tafiyar Chibuzor dan guntun hope din da yake dashi gabadaya ya tafi. Fadawa kansa yake yi ya cigaba da hakuri da kaddarar rayuwarsa me yiwuwa shi da iyalinsa sai a lahira. Shi da kasarsa kuma sunyi bankwana kenan. Rikici ne ya kaure daga gaban inda ake rabon abincin garin dambe aka zubar da kulolin abincin a kasa. Mutane kuwa suka dira akansa suna wawaso ga gandirobobi suna ta kokarin raba su.

Yau ma bashi da abinci kenan zaiyi kwanan yunwa ya juya a nutse zai koma dakinsu. Da rana wani tsoho ya barwa nasa saboda ya taho zai zauna irin shakiyan nan wani yasa masa kafa yayi tuntube ya fadi. Yanzu kuma abincin duka an zubar. Ya kusa isa dakinsu yaji da karfi ance.

"LIEUTENANT ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"

Tunda ya shiga kurkukun nan sunansa 3810 sai ko mutanen da suka san sunansa kalilan amma su dinma  numbar tasa suke kira. Gabansa ne yayi mugun faduwa ya juyo da sauri. Babban prison Warden dinne da kansa ya shigo wurin. Wannan salon tafiyar tasa da shi kadai ya iya kayarsa yayi zuwa gaban mutumin. Ga mamakinsa sai ya ga ya cire hularsa ya maketa a kasan hannu daya sannan ya gyara tsayuwa ya sara masa. 

Habawa sai idanu suka tattaru a kansu shi ma sai yayi saluting mutumin yana jin idonsa ya soma ruwa domin hasken da ya fara hangowa na rayuwar 'yanci
Chapter 79 · 0% Book details