← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 157

Sashe 154

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wankan yau na daban ne komai has to be extra special yadda Hammanta zaiyi ta tunaninta idan ya koma. Mimi skirt ta saka da wata top mai hannu three quarter ta bata lokaci tayi kwalliya ta gyara gashinta sannan ta fito tana kwas kwas da wani heel shoe dinta.

A tsakiyar falon Awwab ya tarota ta bata rai ganin bai ci ba. Kunnuwansa ya kama da hannu.

"So nayi ka fara cin abincin sai nayi presenting maka sabuwar member ta Awwab crew" ta kashe masa ido.

"Fully employed with all benefits baby...mu ci abincin nan kafin hankalina ya barshi gabadaya"

Daga cin abinci aka kwana ana sallama da kyar ya samu tayi bacci saboda kuka. Kuma da kukan ta tashi ta kasa sakin rai karshe yace ba zata bishi airport ba tunda haka ne. Sai da ta ga da gaske yake idan bata yi shiru ba bazai yarda ta bishi ba ta goge hawayen amma kana ganinta kasan kukan take yi a boye.

Da suka je yiwa su Mami da Mama sallama gabadaya tausayinta su ka rinka ji saboda fuskarta tayi ja alamun tayi kuka ta gode Allah. Ita da shi suna bayan mota sai dreba su ka tafi yana aikin rarrashi da kwantar mata da hankali. Da su ka dawo gidanta ta shige ta rushe da kuka ko abinci ta kasa ci a haka tayi bacci Zayyana tana dayan dakin za ta rinka tayata kwana.

Sai bayan kwana biyu ta saki ranta Awwab yana shan rigima da koke koke a waya dai. Shima dauriya yake yi tare da karfafa mata gwiwa. Kwanansa takwas da tafiya Daddy ya gama yi mata shirin tafiya Nijar ta karasa aikinta. Katsina suka tafi tare da Mami aka bar Zayyana da Rahima gidan Ummi. Kwanansu biyu ya hadata da 'yar kanwarsa matashiya da su ke kusan sa'anni Na'ima saboda kada tayi tafiya daga ita sai dreba da daracta Bigman da cameraman.

A can Nijar da connection din kakanni da iyaye aka samu aka hadata da wadanda ya dace cikin sauki tayi aikin sati biyu ta gama hada komai. Lokacin sati hudu ya rage mata ta koma France amma Awwab yace ko zai kara lokaci lallai ta jira shi yazo ya maidata.

[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: A Katsina su ka sauka Mami da Daddy su na nan amma bangarensu take zama saboda nauyinsu da take ji ga rashin 'yan hira. Gidan Fauziyya take wuni ko ita tazo. Cikinta ya fito ga Jawad ya kara wayo.

Sun zaga gidajen 'yan uwa saboda jan magana na Fauziyya ta kaita gidan Ghazalatu. Nura yana gida su ka zo ya rinka makalewa a jikin matarsa ba ta da damar motsi yana biye da ita. Duk haushi ya isheta wannan aure babu ranar rabuwa ta sake samun wani cikin. Ta kwantar da hankalinta amma rashin kunyarsa tana damunta. Duk wayewarta ta baya Nura kwararren dan duniya ne amma dai ya canja hali tunda yanzu da gaske son matarsa yake yi. Kadaran kadahan ta karbesu aka rabu lafiya.

Emzee yana nan yana takurawa Rahima da text idan ta ga dama tayi masa takaitacciyar amsa guda daya tace lafiya. Wannan abu yana damunsa amma ya san shi da fita daga makarantar nan da kyar idan ba sai ya gama ba. Jan ajin nata wani burge shi yake yi ma amma yaki yarda ya kirata a waya.

Cikin Ummi ma ya fito tana fama da karatu ga laulayi yaki sauki indai tana gida a kwance take. Yanzu an cigaba ta bangaren Salame tana yawan kiranta su gaisa.

Kwana hudu kafin dawowar Awwab saura kuma sati Radhiya ta koma makaranta Mama ta sa a gyara mata 'ya. Gyaran jiki na musamman aka yi mata tana ta saka lalle a kasan gashinta saboda sanin da tayi yana son hakan. Tun dare take jin cikinta a daure da safe ma daurewa kawai tayi tana girki Zayyana tana shara yau bata da lecture. Suna cikin yin breakfast ta ji ciwon cikin ya karu da kyar ta iya tashi tsaye ta ce "Zayyana kirawo min Mami cikina..."

Sai da ta taimaka mata ta kwanta akan doguwar kujera sannan ta fita da hanzari. Ko sallama bata yi ba ta fada gidan Daddy na tambayarta me ya sameta tace Adda Radhiya ke ciwon ciki. Cikin sauri Mami ta fito tana tunanin ko ciki ne da ita.

Nishi take a wahale Mami ta taimaka mata ta tashi "Zayyana dauko mata hijab ko mayafi mu tafi asibiti"

An gama saka mata hijabin jiri na kwasarta ta daga kafa Mami na rike da ita jini ya biyo kafafunta. Basu kula ba sai da ta daga daya kafar tare da zubewa a jikin Mami saboda wani matsanancin ciwo da bata taba jin irinsa ba da ya dirar mata lokaci guda da fitar gudan jini. Tana jin Mamin a rikice tana cewa Zayyana ta fadawa Mama da Daddy daga nan ciwo yaci karfinta jikinta ya saki.

Asibitin da suke zuwa na Sami Wadata su ka je jinin yaki tsayawa har lokacin aka shigar da ita emergency. Sai bayan minti talatin aka gangarota zuwa wani dakin likitan yace saidai suyi hakuri bari tayi kuma saboda yadda take zubar da jini sai da suka yi mata wankin ciki. Mami harda hawayenta saboda tausayi Radhiya tayi fayau da ita. Mama ce ta sanar da Ummi itama hankalinta ya tashi ta fadawa Daada shi kam nasa yafi na kowa ma. A asibitin su ka wuni har ta tashi daga bacci. 

"Mami cikina zafi" tace tana runtse idanu.

"Sannu kinji Radhiya zai dena in sha Allahu. Bari na hada miki tea ki sha"

So take ta tambayesu me ya sameta amma ganin iyayenta maza sai taji jikinta yayi sanyi a hankali take share kwalla duk da bata san me ya faru ba. Ta riko hannun Zayyana ta ce "me ya sameni ne?" 

Zayyana sai ta fashe da kuka Mama ta fara fadan za ta daga mata hankali. A tausashe ta dafa kafadar Radhiyan ta soma magana.

"Radhiya bari kika yi"

Gabanta ne ya fadi ta tuna cewa kwanaki sun shude da tayi missing period dinta tunda Awwab ya tafi shine ta siyo PT strip take ajiyarsa sai ya dawo su duba tare. Ashe ma ba mai zama bane. Iyakar daurewa ko don kada ta bawa Umminta kunya ta tattaro tayi da abin ya ci tura kukan ya matsota sai ta juya musu baya. Kowa na ganin yadda jikinta yake rawa alamun tana kuka Mami tace su fita a barta ta ji saukin zuciyarta saboda cikin fari akwai shiga rai. Kukanta tayi mai isarta bayan sun fita. Ta saka rai da cikin sosai saboda yadda Awwab bashi da aiki sai kwadaita mata haihuwa da irin son da yake yi ya ga 'ya'yansu.

A waje Daddy yace yaji shiru Awwab bai kira ba ga matarsa a kwance. Daada yace kada su fada masa tunda dai zai dawo nan kusa. Kuma bai kamata a tayar masa da hankali ba duba da yanayin aikinsa rayukan jama'a a wuyansa.

Shadayan daren Nigeria Awwab yayi landing jirgi a Canada. Kamar kullum yana isa masaukinsu ya kira Daddy da Mami sannan Radhiya. Yayi ta waya shiru ta na shiga ba'a dauka an manta ta a gidan. Mami ce za ta kwana da ita kuma ta riga ta yi bacci sai ya nemi Zayyana taki dauka saboda bata san me za ta ce masa ba. Lokaci ya duba ya san dare yayi amma Radhiya ta rike schedule dinsa sosai na satin ta san lokacin tashin jirginsa da sauka wani zubin kafin ya kira ta neme shi. Komai dare a Nigeria sai ta jira shi duk fadan da zaiyi ba ta ji.

Washegari da asuba yayi ta kira shiru ya kuma kiran Zayyana tace masa bacci take yi. Ya dai ji ne bai yarda ba . Mami ya kira da gari ya waye ya kusa tashi yace mata ya kasa samun Radhiya jikinsa na bashi babu lafiya kuma Zayyana na yi masa wasa da hankali. Hakuri ta bashi tace da kanta za ta kaiwa Radhiyan wayarta ce ta fadi. Shiru lokacin boarding yayi ya sake tashi back to Germany cike da damuwar da ake guje masa. Sai daren ranar aka kai mata wayar yana sauka ya kuma kira. Fada yayi niyar yi mata saboda ko faduwa wayarta tayi ya bar mata kudi da za ta iya sayen wata sannan ga wayoyinsu Mami. Amma yana jin weak voice dinta ya ajiye makaman yakin. Karyar mura tayi masa ya bi ta da toh ba don ya yarda ba.

Da yamma ranar aka sallameta Mami ta hanata komawa nata gidan tana kulawa da ita sosai. Karamin wankan jego ta yi mata ta rinka gasa mata jiki ga abinci mai gina jiki ita da Mama su yi Ummi da Rahima sai dai su zo dubiya.

Ranar da Awwab zai dawo taji karfin jikinta sosai tayi masa abinci. Naman sa ta yiwa yanka madaidaita ta tafasa da kayan kamshi su, citta, tafarnuwa, black pepper da albasa. Ruwan naman bayan ta tafasa shinkafa ta wanke ta juye shi ta karasa dafata da shi. Butter ta zuba a non-stick pan mai zurfi ta soya sausage da lawashi wanda ta yanka kananu juye shinkafar a kai batare da ta saka curry ba ta soyata. Naman shima soya shi tayi sannan ta hada attaruhu da albasa wadatacciya tayi grating ta soyasu da maggi da

 curry sannan ta hade da soyayyan naman. Sai kuma coleslaw da kunun aya. Gidan ya sha turaren wuta ga girkin amarya da sanyin AC Ba ta je airport din ba ta zauna kwalliya.
Chapter 154 · 0% Book details