← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 157

Sashe 104

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalamansa sunyiwa Jume dadi haka ma yayunsa. Tashi tayi da sauri tayi hanyar bangaren Maikudi. Yadda baije gidan gaisuwa ba haka ya hana matarsa da 'ya'ya suna zaune kowa rai a bace amma basu da yadda zasuyi dashi. Matarsa har tafi jindadin lokacin da aka tsareshi su ka sakata suka wataya son rai a gidan. Yana daga uwar dakinsa a kwance ya bararraje matarsa tana yi masa tausa. Daga bakin kofa take ta kwala masa kira ya taso a fusace.

"Jume ya haka zaki zo min har kofar daki. Wannan ai rashin tunani ne, waye yake zuwa kofar dakin mai aure. Gaisuwa ce dai nace bazanje ba ko ana dole ne inji"

"Ba wanan ya kawoni ba Maikudi kazo ga dan uwanka ya dawo"

Da yana da kudi bai ga dalilin da zaisa shi zaman gidan nan ba. Ya tsani ya farka ya ga kowa cikinsu saboda babu mai kaunarsa. Haka ya karaci zamansa da shan wahala a rufe sai sun bushi iska suke lekawa.

Zayyan da sauran suna jiyo yadda yake daga mata murya shiyasa ya tashi yabi bayanta.

"Ko ma waye dan uwan bai san inda nake bane da bazai karaso ya gaisheni ba sai kin taso da kanki? Wato gani matsiyaci nine zan fito gaida irin mutanen da kuke yiwa maula ke da su Badaru....."

Numfashinsa ne ya nemi daukewa a lokacin da Zayyan ya bullo tsakar gidansa inda ya tsare kofa ya hana Jume wucewa sai ma kukan bakinciki da take yi.

Zayyan yana shigowa bai tsaya ko ina ba sai a gabansa ya cire hannu ya kwada masa mari. Bude baki yayi yana neman hada kalma ko daya ce ya fada Zayyan ya kara masa wani. Marinsa ya rinka yi hagu da dama kumatunsa ya dauki radadi kamar garwashin wuta a take. Idanunsa a rufe suke da takaicin halin Maikudi. Banda bakincikin da yake ji na muguntar da ya yiwa iyalinsa kuma shine ya kara masa da rashin da'ar da yake yiwa Jume. Mahaifiyar da duk abinda tayi a baya mai kyau ko akasinsa tayi ne domin farincikin 'ya'yanta. Shi fa babu abinda zai dorar game da uwa sai labari. Wane irin farinciki zaiyi da za'a bashi damar kasancewa da tasa uwar ko da na rana daya ne. Shi wanda ya sami damar yana takewa ta hanyar cusa mata bacin rai.

Marin karshe da ya kai masa sai da bakinsa ya fashe. Mairama na ganin haka ta kama hannunsa "ya isa haka Sojana ban sanka da fushi ba, kamata mu koma dakinta"

Rungumo Jume yayi a jikinsa suka bar wurin bayan wani mugun kallo da ya yiwa Maikudin. 

Sawu na daukewa Maikudi ya kwalla kara yana riko matarsa ta zaro idanu a tsorace kada ya huce a kanta "kin ga abinda na gani yanzu? Kema kin ga fatalwar Zayyan?"

"Ni banga kowa ba" tace cikin halin ko in kula sai ma murnar marin da ya sha da take ganin rama mata akayi.

Kansa yaji yayi nauyi yasa hannu ya shafi jinin bakinsa ya tabbatar fa gaske an mare shi din ya fito zuwa dakin Jume. A zaune ya ga Zayyan din yana bata baki akan tayi hakuri da abinda Maikudi yayi mata.

Buguzum buguzum haka ya shiga dakin babu sallama ya sa hannu a kafadar Zayyan don ya tabbatar cewa mutum ne da gaske. Yadda idanun Zayyan din suka yi lokacin da ya dago kansa ya sa Maikudi yin baya da sauri jikinsa na bari.

"Baka mutu ba?"

"Ba haka kaso ba ko? Yadda ka tsara shine na mutu matata ta haifi da ba rai ita da 'yata suyi hatsari su mutu su ma kaci dukiyar da zata zame maka wuta ranar lahira"

Da borin kunyarsa ya kalli Mairama "sannu munaf...."

"MAIKUDI!!!" Zayyan ya daka masa tsawar da hatta Mairama sai da ta razana. Da dan allinsa ya nuna shi yana kada masa shi a gaban fuska "ko da wasa kada ka sake yunkurin yiwa matata magana balle kuma ka hadata da kalamai na batanci. Kai ba ita da Jume ba wani ma a gidan idan ya sake kuka da kai wallahi sai kayi mamakina. Abu na karshe daga yau har na bar gidannan kada ka bari ko inuwarka ce na sake ganin gilmawarta a gabana. Get out"

"Ni da gidan ubana kai ka isa kayi min turanci. Ba tsoronka nake ji ba" yace daga bakin kofa yana sauri kada Zayyan din ya biyo shi. Babu wanda ya sake saka shi a lissafi. Jume duk yadda yaso hanata da kanta tayi masa tuwon alkama da miyar karkashi akan wutar murhu. Zaman hira kuwa an raba dare ne ana bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa shima kuma ya fada musu nasa.

**********

Numfarfashi kawai Malamijo yake saki yana daga kwance a dakinsa ko zama baya iyawa sai an tada shi. Ga mutane cikin 'ya'yansa da jikoki ana ta yi masa sannu. Sallamar Nene Marka tare da Radhiya su ka shigo dakin. Ba arziki ya tashi yana nuna Radhiya.

Ba don kada a raina shi ba kuka zaiyi ko yaji sassauci a ransa "Wai da gaske so kike ki karasa ni ne? Dame kike so naji? Shanuna, shanuna shegen yaron nan Talle ya gudu dasu sannan kin kawo Marka wato tazo in biya musu kudin Hajji da yawun bakina ko"

Murmushi Radhiya tayi har ranta tana tausayinsa tace "duba ka tazo yi...ku taso mu basu wuri ko" Tace da su Emzee. Murmushi yayi yayar tasa ta fara daukan haske ta gane inda ya kamata ta rinka tashi musamman idan manya ne zasuyi magana. Nene Marka ma ta kalli bayanta har ta saki labulen da suka gama fita tayi dan murmushi. Radhiya fa tana da hankali idan aka tabota ne kawai bata da dadi. Daure fuska tayi lokaci guda tana kallon yayanta.

"Ali" tace da kaushin murya.

"Alin ma kai tsaye Marka, wato tunda na soma talaucewa an sace min shanu ga kaji ance suna murar tsuntsaye shine dan girman da kike bani ya kau. Kada ki manta dai sunan Malam ne kakanmu ehe. Idan kin kirani Ali kamar kin kira sunan Malam ne babu kara"

"Kaga dakata min ba wannan ya kawoni ba. Zumunci nazo yi zan duba ka nayi maka nasiha ta karshe don babu lallai na cigaba da hakurin zuwa gidanka"

Jikinsa ne yayi sanyi kuma. Gidansu ita kadai ce mai hakurin zumunci dashi sauran har wadanda ya hada uwa dasu sai abu ya kure suke zuwa. Ita kuwa 'yan dakinsu har gori suke yi mata wai tasa kwadayin abin hannunsa a rai shiyasa take like masa. Gashi dai shine babba amma sai aci a cinye a gidajen sauran babu shi babu 'ya'yansa saboda kawai kada ace yayi gudunmawa.

"Yanzu kuma me nayi?"

"Meye ma baka yi ba? Dubi yadda ka koma sai mokadewa kake yi kamar ragowar yunwa. Ni dinnan da bana takama da komai sai dan rufin asirin da Allah Ya yiwa mijina, ba da ba jika na fika kyaun gani da cika ido"

"Ku mata dama banda ci me kuka iya?"

Gyara zama tayi bata sake magana ba har yarinyar da ta kawo mata ruwa ta fita sannan ta cigaba "Malamijo wallahi ka guji haduwarka da Allah akan yadda kake rayuwa"

"To, tohhh zaki fara ko. Idan kina abu sai kace kin saki nono ne Hajjo ta kama. Kuyi ta zakulowa mutane laifuka kawai don a rubuta min zunubi to dai kowa mugun fatanta a kanta zai kare"

Girgiza kai tayi cike da takaici "kaga irin halin naka...ni ka saurareni don banzo da shirin kwana ba." Sassauta murya tayi ta kafe shi da ido don yasan zancen nata babu wasa a ciki.

"Malamijo ina tsammanin ko rantsuwa zanyi babu kaffara a kaina cewa duk garin nan babu mai arzikinka. Tunda Baffanmu ya raba mana shanu tun yana raye ba'a shekara biyu ba naka suka ninka abinda ya bamu. Ni ko wuka aka saka min a wuya bana ce ga abinda na tsinana da nawa ba. Amma kai kam ka sami albarkar kiwo. Nafi shekara arba'in a gidan miji ban taba batan wata ba sai gashi kai da kayi naka bayan ni yanzu a lissafina mutum talatin da daya ne naka masu rai banda biyar da suka rasu da masu bari"

"Hakkun" ya gyada kai maganar ta soma samun shigarsa.

"Wadannan 'ya'ya amanar Allah ne kuma kai dai kaci wannan amana. Ko kadan baka rikesu yadda musulunci ya tanada ba. Rashin wadatasu da abincin kirki ba shi yafi damuna ba kamar sakaci da zumuncinsu. Yawansu na banza ne saboda babu wanda ya damu da dan uwansa. Ka ga duk iskancin Salame....."

"Kyale wannan mara mutumcin ko ni kaza ta fini mutumci a idanunta"

"Kaga matsalar ai kayi ta aibatasu. Salame ko tana da mugun hali da sa hannunka a kara lalacewarta. Duk yadda duniya take wasan gare gare da ita a gidan miji bai sa tayi hankali ba har yau. Yadda ka banzatar dasu haka ta fita harkar Halifa da Rahima. Albarkacin kudin uban Halifa yanzu take jansa. Amma Rahima fa?"

Langabe kai yayi "ko a waje muka hadu bazan shaidata ba wannan"

"Shikenan so kake idan kasa ta rufe idanunka sun gama zumunci kenan sai a lahira idan an hadu a filin hisabi?"

"Kai Markajo ni dai fadi me kike so nayi duk kinbi kin tsorata ni. Kina kallo ba lafiya gareni ba."

"Ka hada kan zuri'arka. Kafin ka bar duniya ka dinke barakar dake tsakaninsu. Banda Mairama da Ayuba babu wanda yake nuna damuwarsa a kanka. Abu na biyu yau ka gani da kaki sharar masallaci ai kayi ta kasuwa. Wata can da bata da gadonka ta kwaso iyalinta suka tagayyara ka sai jikoki suka kwaceka. Da gidan nan a hade yake wadancan zaratan samain yaran naka ba ubanta zasu ci ba ta koma inda ta fito daren da ta tare. Wai ma shin auren bai isheka ba. Kayi lukuta, siririya, fara da baka, mai kyau da mummuna. Babu kalar da baka taba ajiyewa ba amma kaine har yau aure kake"

Jikin Malamijo yayi mugun sanyi domin kuwa ya soma ganin ishara. Marka ce kadai ya tabbatar zata fada masa gaskiya batare da sanya son zuciya ba. Ko Radhiya sai da ta hado da cewa a kai wasu hajji sai kace zuwa Zaria ne abin. 
Chapter 104 · 0% Book details