← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 157

Sashe 69

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga Kano Ummi sun taho da Mama, Baba Hadir, Ibrahim da kanwarta Laila da take tsarar Emzee. Daddy shi kadai ya taho daga Katsina saboda Zayyana ana makarantar kwana kuma satin Mami daya da tafiya Germany wurin Zahra haihuwa ko yau ko gobe. Fauziyya nata dan Amin watansa biyu. Ansan bahaushe da karamci da kawaici bisa ka'ida idan da hali da kuma lafiyar yi Hussaina ko Gambo ya kamata su tafi. Amma kowacce ta shafewa idonta toka har yau ana nan babu wani chanji. Ummansu tayi fadan har ta gaji yanzu maganar Hussaina kadai Mummy Gambo take ji. Bikin Nura da Ghazalatu watanni ya rage don ma an daga saboda korarsa da akayi daga wurin aiki sai da Daddy Haroun ya shiga ya fita ya sama masa wani. Tun a lokacin Mummy ta soma shan jinin jikinta game da auren amma tasan ko tasha giyar wake Alh Baba bazai saurari wata magana akasin wadda suke a kai ba.

Ummi tana tsaka da karatu Mama kuma dama dole ke dauketa daga gefen Baba Hadir. Sau daya taje China bayan dawowarsu ta saro kaya masu uban yawa. Da suka kusa karewa sai sako ta bada Ibrahim bashi da isasshen lokaci saboda karatu bare ta barsu tare ta tafi. Yanzu lafiya ta fara wadata gareshi magana ce dai har yanzu suke ta sa rai. Sai kuyi dogon zance dashi yanzu ta hanyar rubutu a takarda ko text a waya. Sai yayi awa guda da Radhiya suna musayar sakonni tace wannan tace wancan duka yana biye mata. Haka Emzee duk wata hira da uba yana yi da Babansa Hadir ne. Sunfi jin nauyin Major kasancewar shine babba.

Basu sami ganin Emzee ba yana tare da wadanda zasu yi marching din tare dasu. Sanye suke da kayan sojoji dalibai koraye kowannensu yana jin kansa wani ne saboda samun gurbin karatu a NDA sai anyi sa'a. Shima sai yanzu yake jin da baizo ba da ya cuci kansa. Har tsokanar Radhiya yake yi wai tana missing. 

Convey din babban bako na musamman gwamnan jihar Plateau Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu wanda tun lokacin kamfen jama'ar gari suke kira da Tsohon Soja ta shigo makarantar jiniya ta karade wurin. Watan shida kenan da rantsar dashi a matsayin sabon gwamna bayan zaben da aka gabatar a farkon shekara. Motar da yake ciki tare da Arifah sai da ta kawo shi kusa da inda aka tanada domin zamansa sannan aka bude masa ya fito. Kwarewa a siyasa da kuma tuna baya shima kayansa da suka dace da tsohon mukaminsa ya sanya sababbi fil sai ya fito a sojansa don ma dai ya fara ajiye tumbi. Arifah kuwa wani dankareren lace ta saka yellow da fari anyi mata dinki irin na zamani. Bata sa dankwali ba sai mayafi fari da ta yafa kashka mai matukar kyau da tsada. Komai na jikinta kudi ne tayi kyau sosai abinta. Commandant din NDA din wato shugaban makarantar gabadaya ya taso ya tare shi har mazauninsa. Sai da ya zauna sannan aka shiga gabatar da events din taron. 

Abubuwan da suke yi sun kayatar da Ummi da Mama, Ibrahim kuwa cewa yake ko dai shima zai taho ne ya kyale BUK. Major da Baba Hadir kowannensu sai ya sami kansa da tuna lokutan baya da suke training tare da Zayyan a Giginya barrack da irin zaman da suka yi har rabuwarsu. Suna ta sauraron jawabai daga manyan baki da kuma ganin abubuwan da sojojin suka tanada domin kawatar da taron Ummi ta kula motsi kadan Mama sai ta dauko wata danyar goba a jakarta ta gutsira ta mayar.

Suna hada ido Mama ta kawar da kai gefe tana dariya Ummi ta kusa yin ihu don murna.

"Kice Allah abinda nake zargi ne" ta riko hannun Zainab tana binta da kallo ko zata gane wani sauyi a jikinta.

"Bansan ki da sa ido ba Ummin Awwab" tace mata tana boye dariyarta.

"Harda hanci da baki babu abinda bazan saka miki ba. Taimaka ki fiddani duhu 'yar uwa. Shin da gaske ne?" Doki da murna sun kamata kai kace kananun yara ne.

Sai da Mama ta rage sautin muryarta ita kuwa ta kawo kunne ta kara mata "ban yi test ba amma jikina ya bani"

Hannunta Ummi ta damke tana murna sosai "yau Mami zata sha story, ahhh su Zainab an girma ashe ba'a girma ba"

Dariya tasa daga baya ta shiga nunsta da yatsa "Kinga Mairama ki kiyayeni, wallahi aure zan miki ko don na rama"

"Aure sai na 'ya'yanku idan sun shirya amma ni kam mijina yana jirana"

Murmushi Mama tayi ta gane wa Ummin take nufi. A hankali hirar ta koma ta Awwab da Radhiya.

"Kinci amanar soyayya da kika raba min su. Yaushe zata zo hutu ne in samu in hadasu a gidana. Dama anan aka fara..."

"Dandalin soyayya zaki ce, tunda ga babbar shaida na gani"

"Ya son ranki hajiyata, ai ko sati baiyi ba da fara motsa jikinsa aka..."

Duka Ummi ta kai mata a cinya saboda Ibrahim da ya taso da sauri yayo gaba. Zainab ba dai barin zance ba. Tun zamansu na baya haka take ta fadi magana ta barsu da kunya musamman Ummi. Shi kuwa ashe Emzee ya hango a cikin masu wani irin style din marching abin gwanin sha'awa da burgewa suna wasa da takubba amma na katako anyi musu fentin tutar Nigeria. Abin ya kayatar kuma Emzee shine yake jagorantar wasan nasu. Shi yake bada command sauran suna yin yadda yace. Karshen abinda suka yi shine hada kalar tutar Nigeria wato green white green. Jeruwa suka yi layi biyar kowannen layi mutum bakwai. Ukun da suke tsakiya a kowanne duka hulunansu farare sauran biyun na gefen hagu da dama nasu koraye. Sai suka durkusa a kan gwiwa daidai a haka aka fi ganin ma'anar abinda suka yi. Wurin ya kaure da tafi ga irin kidan band din sojiji ana yi musu suka tashi suna wani murda takobin hannuwansu a kan layi suna shirin barin wurin Ibrahim ya daddage yace "MUHAMMAD ZAYYAN TURETAAAAAA"

Mama ta kai masa dundu a baya kuwa "sai kasa yayi mistake ko"

"To nayi shiru"

"Ka daukarwa Radhiya a waya ko kuwa naka idanun kadai ka bawa abinci?"

"Na dauka fa Mama"

Kararar kade kaden baisa mutane sunji kiran da ya yiwa Emzee ba amma tabbas idan ba karya kunnuwansa suka ji ba His Excellency yaji kalmar Tureta kamar a iska. Bai sani ba ko yawan tunanin Zayyan da ya fado masa a wurin nan tunda yake ta ganin sojoji ne ya sa shi jin haka. An kira shi domin yin jawabi ya fara da taya daliban da suka gama murna kafin ya nusasshesu kalubalen da yake gabansu. Muryarsa ta karade ko ina saboda spikun da aka saka a wurin gashi harka da masu sanin doka da oda babu hargagi ko hayaniyar da zata hanaka jin me yake cewa. Cikin harshen turanci yake jawabinsa.

"Akwai kanina, abokina kuma saviour dina wanda ba don shi ba da bazan kasance tare daku ba yau. Wannan mutumi ban taba gani ko jin labarin mutumin da aka haife shi domin ya zama soja ba sai shi. Officer ne wanda ya san ma'anar sadaukarwa kuma ita ce nake baku shawara da ku runguma hannu bibbiyu. Kunga kowa a cikinmu akwai inda arzikinsa da abincinsa yake. Kamar yadda kanin nawa yake cewa sojoji ba yinsu akeyi ba...haifarsu ake domin domin su bada kariya. Saboda haka duk wanda yake tsaye a cikinku yanzu ina so ya sawa ransa cewa babu kudin da za'a biyaka ya maye gurbin iyalinka da zaka yi nesa dasu idan bukatar hakan ta taso. Babu wata karramawa da za'ayi muku ta fanshe hatsarurruka da zaku iya haduwa dasu domin kare rayukan al'umma. Ku din zababbu ne ku yarda da haka, kuyi aiki da haka ku tsira da mutumci da kimarku a ko ina cikin duniyar nan. KU RIKE KU SANI CEWA SOJA SHINE JARUMIN DA IDAN YA GA AN KAWOWA KASARSA HARI SAI YA DAUKI KOWACCE MACE A MATSAYIN MATARSA , 'YARSA KO BABARSA SANNAN KOWANE NAMIJI BABANSA KO DANSA YAYI KOKARIN CETON SU KAMAR NASA. Wannan shine zai sanya ku jajirce wurin taimako da kariya batare da tunanin bambancin addini, yare ko akida ba. Sadaukarwa irin wannan kuwa sai ga haifaffen soja jarumin kasata."

Tunda ya fara magana ya tafi da hankulan da dama daga cikin mutanen dake wurin. Sojojin kuwa ya kara musu wani karsashi da son aikin da suka zaba suna jin babu ranar yin nadama a shirye suke kodayaushe su bada rayuwarsu domin zaman lafiyar kasa. Sowa da tafi aka rinka yi bayan ya gama jawabin nasa ya koma mazauninsa. Arifah da ya gama burgeta tayi masa murmushi "I am proud of you Dad"

"Ba dadin baki ba saura anjima inji kin fara rokona wani abu" yace yana dariya.

Juyawa yayi ga Commandant din yace masa zai tafi yana so ya wuce Abuja a yau. Gwamnan Kaduna baya kasar a lokacin shiyasa ba'a gayyace shi ba balle yace zai kai masa ziyara tunda garinsa yazo. PA dinsa ne ya kira dreban ya kawo mota inda ya ajiye shi dazu domin su tafi. 

Sun kusa tashi kenan Commandant ya soma wani bayani da ya dauki hankalin His Excellency ya dan dagawa PA dinsa hannu cewar yana zuwa. 
Chapter 69 · 0% Book details