← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 157

Sashe 15

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu gama da wannan firgicin da ya sanyasu daukan bindigoginsu cikin sauri ba kuma sai ga daya daga cikin masu patrol na wannan daren ya shigo bindigarsa tana kan saiti ya fada musu 'yan tawayen da su ka addabi wannan sansanin nasu sun kawo musu hari.

Idan da suna jin wai-wai, yau ga su zahiri a filin daga. Harbi ne yake tashi ko ta ina suka firfito kan kace meye wannan wurin ya kaure. Anyi musayar harsashi sosai duk da duhun dare sun sami damar fatattakar mutanen har da nasarar cafke mutum daya.

Wani bacci dama babu shi a lissafi maza suna filin daga. Kwana ukun farko sunyi su ne cikin rudani da tashin hankali. Da gasken gaske 'yan tawayen suke son korar sojojin Nigeria daga wurin. Akwai wuraren da suke tsammanin samun nasara su janyo mutanen garin domin a hadu a ture gwamnatin shugaba mai ci a lokacin. Rigima ta cikin gida a ganinsu mai zai kawo wasu baki da abin bai shafa ba a matsayin peacekeepers.

Kafin wani lokaci su Zayyan sun kara gogewa da halin da suka tsinci kansu yanzu. Shine ya koma yi musu limanci bayan tafiyar Abdulwahid Gbenga wanda ya kasance da shine limamin. Duk daren da babu gajiya sosai a tare dasu suna zaman hira a daki ko a waje. Su kunna wuta su zagaye wurin suna jin dumi saboda shigowar sanyi gadan gadan. Da safe kuma masu manyan mukami su ke jagorantar training dinsu don ba zama.

Watansu daya da kwanaki annobar cholera ta shigo kauyen da yafi kusa da inda suke. Garin kai taimako wurin fitar da marasa lafiyan zuwa asibiti a cikin gari wasunsu suka dauko ciwon suka kawo musu.

Cikin kwanaki bakwai mutum tara sun kamu. Amai suke yi sosai da gudawa. Suna ta kokarin neman agajin babban sansanin domin a kawo musu magunguna sannan a dauke marasa lafiyan cikinsu zuwa asibiti amma abu yaci tura. Ba wai sakon bai isa garesu bane, yaje amma su ma suna jiran command daga babbar headquarter saboda komai na soja bisa doka da oda ake yi.

Major Mustapha da ya ankara cewa sansanin su Zayyan ne ya matsa lamba sosai ranar da za'a kai musu maganin bayan kwanaki shadaya da fara cutar yabi bayan ma'aikatan lafiyan cikinsu. Su ma din sojoji ne amma hannuwan rigarsu daga dantse akwai wani farin abu da yake nuni da alamun cewa su likitoci ne.

Major Mustapha har yanzu bashi da magana sosai amma ya damu kwarai da kannen nasa Zayyan da Hadir. Motarsu ta iso sansanin a daidai lokacin da Zayyan yake limancin sallatar gawar Papa Dolapo wanda yayi ta fama da cutar ta amai da gudawa na kwana uku kafin rai yayi halinsa. Jikin Major yayi sanyi haka na likiticin da suke tare dasu. Zagaye sansanin nasu akayi da wasu irin wayoyi masu kaifi aka rubuta musu QUARANTINE da manyan harufa. Ma'ana an kebesu daga shiga ko fita har sai an sami kyakkyawan tabbacin cutar babu sauranta a tare dasu. Ana gudun su sanyawa wasu sojijin ko kuma su sakawa mutanen wani kauyen garin kai taimako.

Likitocin kadai aka bari suka shiga suma sun rufe jiki sosai da wasu kaya hatta fuskokinsu ba'a gani. Sunyiwa kowa allura sannan aka shiga bawa marasa lafiyan taimakon da ya dace. Ta bayan wayar suke magana da Major yana tambayarsu halin da suke ciki. Nuna masa suke yi babu wani abu lafiya kalau suke.

Ta'aziyar Papa Dolapo yayi musu wanda aka saka gawarsa a cikin motar da zasu koma da ita nasu sansanin. Idan sunyi sa'a za'a bari gawar ta koma Nigeria. Idan basuyi ba kuma to a nan za'a binne shi iyalinsa su dau hakuri.

"Shekaranjiya da aka toro wani troop din wannan wasikar tazo. Ta Lt Badmus ce"

Wasikar ya dago musu kowa jiki a sanyaye domin Papa Dolapo ne Lt Badmus.

Major Mustapha ya kara da cewa "duk da ban bude ba amma an fada min matarsa ce ta haihu. Zayyan makotanku ne ko?"

Kai ya gyada ya kasa cewa komai ya juya ya bar wurin zuciya tayi nauyi.

"Follow him Lieutenant" ya umarci Hadir.

Sai da ya ga sun shiga cikin wurin da yake mazaunin dakinsu ya koma motar da ta kawusu suka bar wurin.

**********

Rayuwar matan da mazajensu basa nan a barikin babu dadi. Ci da sha bai yanke ba tunda ana basu albashinsu to amma fa kowacce kullum kwanan duniya da fargaba take kwana matsawar ba mijinta ta gani ya dawo ba.

Mairama, Mami da Zainab dauriya suke yi kowacce tana son nuna ita ma jarumar kanta ce mai hakuri da juriya. A gefe daya basu fasa yiwa mazajensu addu'a da fatan alkhairi ba.

Awwab kusan ya dawo gidan Mairama da zama. A nan yake kwana idan ya dawo daga makaranta ya lalace wurin wasa da Radhiya. Sunyi shakuwar da har Mairama tana tabawa kyuya musamman idan zai fita. Kyalesu take yi tana fama da cikinta don ma laulayin yayi sauki yanzu.

Awwab ya fita da Radhiya sun tafi wurin Mami sai Mairama ita kadai a cikin gida. Hayaniya ta soma ji daga waje ta yafa mayafi ta leka. Can ta hango Zainab da wasu matan da suke tare sun zagaye wata. Fitowa tayi cikin sauri jin kamar ana kuka.

"Innolillahi wa inno ilaihi raji'oon....Oko mi tikú" kuka Maman Dolapo take tana tumani a kasa ga danyen jego.

Mairama ta tsorata da yanayin da ta ganta, ta taba wadda ta fi kusa da ita "what is wrong with her"

"Ahhh Mama Radhiya...Papa Dolapo don die oooo"

Ita ce amsar da ta doki kunnenta taji gabanta ya yanke ya fadi. Zainab ta matso kusa da ita tana fada mata wai yanzu aka sanar dasu rasuwar tasa. Cholera ce ta kashe shi Zayyan ne ma ya sallace shi, sannan anyi masa sutura a can kasar.

Kuka su ka taya Mama Dolapo aka kaita cikin gidanta. Bayan kwana biyu sai ga 'yan uwanta da yayan mijin suka zo daukansu ita da yaranta guda hudu zasu koma Akure. Ranar ma wani sabon kukan ne ya barke a tsakaninsu domin da yawa sun sani da wahala su sake sanya juna a ido har abada. Maman Dolapo ta tafi ta barsu da kewa da kuma fargabar labarin wa zasu sake samu kuma.

**********

Jaruman kasarmu suna can suna aiki tukuru bisa umarnin da kasa ta basu na wanzar da zaman lafiya a daya daga cikin kasashen gamayyar ECOWAS.

A yayin da magidanta suke tashi da safe su je ofishoshinsu yamma na yi su koma gida ga iyalansu, su ci, su sha mai kyau, su kalli matansu da 'ya'yansu su ji dadi wadannan sojoji suna cikin dokar daji suna fama da cizon sauro da wasu nau'in kwarin, rashin abinci mai gina jiki, karancin tsaftataccen ruwa balle ayi maganar wanka kullum da sauransu. Masu aure a cikinsu suna kewar matansu amma babu halin kasancewa dasu.

Yau da gobe kunnuwa sun saba da jin harbi da karar tashin bomb. Da idanunsu suke ganin 'yan uwansu, abokansu harsashi ya huda wani sassa na jikinsu sun mutu a take. Ko kuma bomb ya tashi dasu kana kallon mutumin da kuke tafiya kuna hira dashi ya tarwatse gabobin jikinsa sun watsu ko ta ina.

Jaruman nan sun yarda sun aminci su sadaukar da rayukansu a duk lokacin da kasa ta bukata domin zaman lafiya da kwanciyar hankanlin al'ummar kasarsu. Babu ruwansu da addini, kabila ko wata al'ada. Sun hadu akan abu daya ne wato TSARO na rayuka da dukiya.

A yayin da wahala tayi wahala, anga jiya anga yau a fanin rashin makusanta ko a kama mutum a sansanin abokan gaba a gana masa azaba domin ya fadi wani sirri da za'a iya cutar da nasa 'yan uwan sai ka ga zukatansu sun bushe ana yi musu kallon mutane marasa tausayi da imani. Sai dai abubuwan da idanunsu suka gani da wanda kunne yaji wani fa har ya bar duniya bazai taba kusantar abu makamancin wannan ba.

Jarumanmu ababen alfaharinmu, sadaukanmu da babu albashin da kasa zata basu da zai wanke ciwuka na zahiri da badini da suke dawowa dasu daga filin daga. Ga kuma iyalansu a yashe madogaran nasu, bangon jinginar nasu basa nan.

Wata hudu da tafiyarsu Zayyan sun fara jiyo kamshin komawa gida wata rana da yamma gari ya hade yayi bakikkirin ruwa zai iya saukowa a kowane lokaci wani mutum yazo wurin gaje gaje dashi da shiga irin ta mutanen wani kauye a kusa dasu. Jikinsa duk raunuka yace 'yan tawaye sun yiwa garinsu kawanya suna harbi kan mai uwa da wabi.

Sun riga sun san mutanen suna yin haka shiyasa su ka shiga motarsu ta yaki su ka durfafi kauyen da hanzari. A bakin wurin da yake kamar gate dinsu ne su ka hadu da motar su Major Mustapha. Ya fake da aiki ya taho ganin kannensa.

Duk da bambancin matsayi bai hana Zayyan zuwa ya rungume shi ba. Major yayi turus yana cewa.
"Stand at attention Lady"

Zayyan ya dago yana gyara rigarsa ya dan basar "Sorry Sir"

Major Mustapha sai yayi murmushi yana mikawa Hadir hannu.
"My Ladies are all grown up, sun dena dariya"

Zayyan ya kara gyara fuska sai dai dole dariya ta kwace masa. Karar bomb suka ji mutumin da ya kawo rahoton yace ‘yan tawayen sun kai mota shida. Su Major Mustapha sai kawai su ka bisu.

Sai da suka yi rabin tafiya kawai babu zato babu tsammani sai tashin bomb suka ji a gabansu ga ruwa ya fara sauka. Mutane ne suka fara bullowa ta tsakanin bishiyu da yawa ba na wasa ba sun zagayesu. Babu wata mafita sai fitowa suka yi suna musayar harsashi ga wuta motarsu ta kama saboda tankin mai da aka harba.

Bayan wani lokaci a cikin wannan yanayi ruwa mai karfi ya soma sauka kamar da bakin kwarya a cikin jejin gari yayi duhu baka ganin komai sai tashin kura, hayaki da wutar da ruwan bai gama kashewa ba. A gefe guda kuma Zayyan da Hadir ne suke gudun ceton rayukansu sakamakon bomaboman da suka tashi a wurin har uku ga harbin bindiga da bazasu iya tantance takamaimai daga ina yake fitowa ba.
Chapter 15 · 0% Book details