Sashe 45
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga haduwa dashi kwana daya kawai take neman matsayi fiye da abinda zai iya bata. To me ma take nema ta tambayi zuciyarta. Ranta taji ya cunkushe gabadaya taji ta tsani zaman da take yi tare dasu a motar. Dago kai tayi kamar ba ita bace zuciyarta take kai kawo a abinda ta kasa gane zahirinsa ta kalli Ghazalatu.
"Matar Hamma kiyi hakuri don Allah. Haushi naji da kika kirani house girl. Ke da kishiya sai dai mota in sha Allahu"
Awwab kallonta yayi yadda ta nutsu tana magana kamar ba ita ba. Suka hada ido tayi masa wani murmushi da ya tsaya masa a rai yaji kamar ya dora hannunsa a kumatunta da ya lotsa.
"Kaima kayi hakuri bazan kara ba"
Tana kaiwa nan ta kama kofar zata bude sai ya cire lock din ta fita tare da duka tunaninsa kamar ta zare masa duk wani kuzari da yake jikinsa. A katon soron gidan ta ya da zango jikin wani dan tudun siminti da akayi domin zama. Abinda ya bata mamaki bai wuce kukan da ta fashe dashi sosai ba. Ji take idan bata yi ba ma zuciyarta zata iya bugawa. Kukan na meye? Oho, itama bata sani ba. Abu daya ne kawai ya tsaya mata a rai kalmomin Hammanta na karshe wai Ghazalatu ta jira sai ta hadu da mai matsayi irin nata a wurinsa sannan tayi kishi. Tsaki taja tana jan hanci "Mtswwww in kun ga dama ku cinye juna karewarta, aikin banza. Dadinta dai nima Kawu Zakari ina komawa zai ce yana sona. Mu za'a yiwa burga da wata soyayya? Maza na fita filin yaki ko su je ceton rai a asibiti kai ka makale a jirgin sama kamar tsuntsu wa zai so ka idan ba wannan mai kwalakwalan idanun ba dama"
Hannu tasa ta share hawayenta bayan ta gama rarrashin kanta ta shiga gidan da sallama. A can mota kuwa Awwab da Ghazalatu an bude sabon shafi sai dai a wurinsa babu wannan dokin jikinsa kamar wanda aka yiwa duka haka yake ji. Su ma tana shiga suna shigowa.
Tabarmi ne aka shimfida daga can gefe inda inuwa take don dakunan gidan babu mai girman da zasu zauna a wadace da su da kuma tawagar Malamijo da suka zo kallon 'yan gayu. Akan abin sallah yake zaune ya mike kafafu dawowarsu kenan daga asibiti an zuke fitsarin an hadosu da tulin magunguna. Sallamar baki yasa aka kawo masa babbar riga ya saka ya rufe kasusuwan kirjinsa.
Radhiya ya hango zai fara tsokanarta sai da ta matso ya kula idanunta sunyi ja sosai.
"Kukan me kika yi ke kuma?"
Kamshin turaren Awwab kawai ta ji a bayanta ta gane ya shigo shima. Gashi ana ta kallonta idanunta sunyi ja haka saman hancinta.
"Ji nayi kamar ana kuka ance ka tafi shine na fara nawa nima. Ashe ashe kana nan."
"Kaniyarki" Malamijo yace ya yi mata dakuwa "Mairama ki rasa da wa zaki zo gidan nan sai da wannan aljanar 'yar taki, ko wancan hutun da kika turo su ni banji dadin zama da ita ba. Sau biyu tana yi min barna a gona"
Awwab sam hankalinsa kasa kwanciya yayi da aka ce tayi kuka. Bayan ya gaisa da mutanen gidan da suke wurin fuskarta ya rinka lalube yana son hada ido da ita amma fafur taki. Baya so ya zama sanadin kukanta ko kadan. Muryarta ya tsinkaya tana cewa "wai me ya sameka ne Malamijo, ciwon me kake?"
Hajjo ta soma dariya za ta tona masa asiri a gaban 'yan gayu yayi saurin cewa "zazzabi ne mai zafi ya damkeni kamar bazan kai labari ba. Ai naci wahala ba kadan ba. Yanzu ma daga asibiti nake"
Sannu da adduar samun sauki suka yi masa. Yadikko ta soma cigiyar Emzee shine Mairama tace ya tafi sayen gurasa da tsire wai yana sha'awa. Hakanan Malamijo ya tsargu ya daure ya cije yace a kira guda cikin samarin gidan ya yanka kaji uku ayi musu farfesu.
Mami ce tace " Kada ka damu Baba muna sallah zamu juya akwai tafiya a gabanmu. Ibrahim idan Karami ya dawo ku shigo da kayan nan ciki"
Nan fa hankalinsa ya tattara yayi waje. Ba dadewa Emzee ya dawo da ledoji a hannu. Ya sayo gurasar da nama a wadace harda lemuka irin su cway, lacasera da maltina masu sanyi. Ashe 'yan matan yunwa suke ji. Kafin Hajjo ta gama dafa shinkafar da Malamijo ya aunar mata bayan ya koma daki daga buhu daya cikin wanda su Mami suka kawo don kwarewa a tsiya har sun koshi.
Sallah kasaru suka gabatar azahar da la'asar sannan suka ce zasu koma. Idan sun isa da wuri ma Katsina zasu wuce kawai saboda kada su yiwa Zainab yawa a gida.
Da sauri Radhiya ta dago kai rike da gurasa a hannu sai lokacin take ci ta kalli Awwab. Hada ido su ka yi shima tun dazu ita yake kallo. Kin kula shi da take yi shine yake damunsa. Kwana biyar Mairama tace zasuyi a nan sannan su wuce Rugar Barkindo. Sai bikin su Zahra ya rage sati daya zasu koma Katsina.
"Wannan dan samarin baici komai ba zaku tafi. Radhiya ko saurayinki ne kika kawo baki gabatar min dashi ba?"
Malamijo yace yana kallon Awwab. Yaron da gani akwai maiko maiko zai so ya auri jikar tasa.
Murguda baki tayi da ta ga Ghazalatu ta sha kunu "idan ma kishi kake yi to ka dena Malamijo, ka jira sai na sami mai matsayi daidai da naka amma ba wannan ba."
Yanzu ya gano bakin zaren. Da gaske maganarsa ce ta bata mata rai harda kuka don sai da ya gano ja da kankancewar da idanun nata suka yi. Da ya juya kalaman a bakinsu sai ya ga rashin dacewarsu a dazun.
Mami haka nan ta fara zargin ko Awwab din ya yiwa Radhiya wani abin ne ya bata mata rai. Bazasu so ayi aure basa son juna ba. 'Yar dabarar manya ta kirkiro wadda bata baude da yanayin Awwab din ba a yadda ta san shi "haka yake baya son cin abinci, ga tuki a gabansa mai nisa"
"Ke zuba masa abinci ki kai masa wajen soro tunda babu kowa a wurin. Kila kunya yake ji ko dan Ummi" Mairama tace tana murmushi.
Hakan yayi masa daidai har ransa. Abincin da Hajjo ta dafa da wanda Emzee ya siyo ta zuba masa a plates biyu ta dora akan tray tayi gaba batare da tayi masa magana ba. Ghazalatu kamar ta bisu sai ta tuna bayan fitarta dazu daga motar yadda ya jaddada mata son da yake mata. Tayi ta gama iyayinta ta koma kauyensu kowa ma ya huta.
Wurin yana da fadi daga kan tudun dazu ta ajiye abincin ta koma daukar tabarma suka yi kicibus. Wai sai tayi masa murmushi a zuwan komai lafiya shima ya maida mata. Da ta kawo tabarmar yana zaune a gefen abincin ta shimfida ta sauke masa a kasa.
"Hamma sauko kaci kada kuyi dare"
Kura mata idanu yayi sai da taji kallon ya hanata motsi sannan ya sauko ya zauna a kan tabarmar ya tankwashe kafafunsa.
"Zauna mu ci"
"Na koshi"
"Ban isa da ke ba ko?" Taji yace a hankali yana daukar cokali.
Bata so yana magana irin haka sai ta taji zuciyarta tayi wani iri. Zama tayi a daya bangaren tray din ta tankwashe kafa yadda yayi. Cokali daya ne a ciki ya debi abincin yaci ya mika mata. Satar kallonsa tayi ya dage mata gira da ido yayi mata nuni da taci. Sai da ta sauke numfashi tana kunyar wannan abu ta rufe ido taci da cokalin da ya fito daga bakin Hamma Awwab.
Karba yayi ya sake ci ya kuma mika mata. Za tayi magana yasa hannunsa a kan lebensa sai ta hakura. Duk loma daya sai ya mika mata har suka cinye abincin gabadaya.
"Wannan gurasar dai bani da inda zan cusa ta ki mayar ciki"
Dama ta kagu ta tashi ta kinkimi tray din za ta gudu ya danne gefensa.
"Ban gama magana ba"
Komawa tayi ta zauna ba don taso ba taji yace "I am sorry Alheran. Nazo ina ta yi miki laifi ba da niyya ba"
Sake karyar mata da zuciya maganarsa tayi. Shi kam bashi da girman kai. Wai ita dinnan kanwar bayansa 'yar kauye yake bawa hakuri.
"An daure harshen ne? Talk"
Rufe ido tayi sai hawaye sharrr kamar famfo. Ta rasa gane irin emotions din da suke yawo a zuciyarta yau dinnan.
Hankali a tashe yace "Ya Allah, me nayi miki kuma?"
"Nima ban sani ba Hamma" tace tana kara fashewa da wani kukan. Me ya sami zuciyarta ne a cikin kankanin lokaci? Rabonta da kuka tun farkon zuwan su Mami rugarsu da ana bada labarin abinda kawunsu Maikudi yayi.
Kuka tayi harda shessheka Awwab bai hanata ba har ta gama don kanta ya bata tissue irin ya ledar nan karama ta goge idanunta.
"Feeling better?"
Ta gyada kai tana kallon kwanukan gabanta.
"Good, yanzu ki fada min tsakani da Allah me ya same ki? Nine ko?"
Rasa me za ta ce masa tayi ta kare da cewa "ba kaine kake murna zaka tafi ba"
"Ke kuma ba kya so na tafi?"
Kada fa ya fassarata ta soma tunani "dena fada kada budurwarka taji. Duk baka tambayeni labarin komai nawa ba zaka koma kila bazan kuma ganinka ba sai an dade. Shine naji raina ya baci"
"Sai nake ji kamar dai maganata ta dazu ce ta baki haushi. Amma nima bana son tafiyar ko sabawa bamu gama yi ba ko" yayi yar dariya.
"Eh, ko askina ban fada maka me yasa akayi min ba"
Sai da yayi dariya sosai yace "an gaya miki ni bana tsoron kiyi min balotellin ne? Ina sane naki tambaya kada na janyowa kaina"
"Ashe kai matsoraci ne" ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ta gama kuka ba.
Sweet ya dauko daga aljihunsa irin mai mint dinnan ya bare ya jefa a baki yana dariyar matsoracin da ta kira shi.
"Dazu ka raba abin leda baka bani ba yanzu ma a gabana ka shanye alawar? Kuma nice karama ni ya kamata ka bawa"
"Sorry gashi in kina so" ya cirota daga bakinsa dama niyyarsa kenan.