← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 157

Sashe 134

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan amma zan jira zuwa lokacin da za ka iya fada min idan wanda zan baka shawara ne sai na baka. A problem shared is half solved"

Ajiye wayar su ka yi bayan ya dan ja Emzee din da hira. Sam yaji hankalinsa ya kasa kwanciya ya yanke shawarar komawa wurin Mami ya kuma rokar arzikin ta kira Ummi shi dai burinsa ace kowa lafiya ko da baiyi magana da matarsa ba. Falon gidan ya nufa lokacin wurin takwas na dare. Tun kafin ya shiga yake jin murya kamar ta Ghazalatu da Mummy Gambo. Mamaki yake me suke a gidan a daren nan.

Yana shiga Mummy Gambo ta soma dariya "ango kasha kamshi"

A ladabce ya gaisheta yana tambayarta Daddy Haroun. Mami ya tambaya Daddy tace yana daki ya shiga.

Tunda ya shigo Ghazalatu ta kasa sukuni sai aukin murmushi tana fari da idanu sai da Mummy ta zungereta "baki gaishe da yayanki ba"

Ta turo baki "to ba shi bane kamar bai ganni ba"

Wucewa yayi abinsa duk da yana jin Mami tana cewa me yasa zai share mata 'ya. A ransa yace "Mami kenan, kema dai kin fada ne kawai don kada ace baki damu ba"

Mummy Gambo tace "jira kike yi ya fara gaisheki ko me da zaki ce kamar bai ganki ba? To ni dai bana son rashin kunya. Ku sulhunta ke da dan uwanki a cigaba da zumunci kamar da"

Murmushi Mami tayi don kada ta gwasale kanwarta a kokarinta na son farfado da zumuncinsu "kyalesu Gambo sun fi kusa ai, tashi Ghazalatu ki shiga wurin Zahra nasan tana daki tunda har yanzu Bilal da Raji basu dawo ba"

Tana tafiya Mami ta cewa Gambo gobe ta shirya su je gidan Hussaina.

"Babu inda zani Mami ki barta kawai. Tunda ita ta gina min gadar zaren nan na rufta sai ta kare kalau"

"Ba'a haka Gambo. Kada mu sake bari shaidan yayi galaba a kanmu. Ki duba sau nawa Umma tana kuka akan wannan sabanin. Indai ba so muke muma wata rana mu zubar da hawaye a dalilin faruwar irin haka ga namu 'ya'yan ba to mu bar komai ya wuce"

A can dakin Daddy kuma waya suke da Zayyan ya fada masa yadda su ka yi da Mairama.

"Ka bani shawara me ya kamata na yiwa matar nan. Idan banyi mata abinda za ta ji sosai ba komawa wurin boka ko wani tsibbu ba wahala zaiyi mata ba"

"Na rasa yadda akayi zumunci ya lalace haka wallahi. A fito tsatso daya ko ma ciki daya amma ka ga mun rufe ido muna neman ganin bayan juna. Hassada tayi mana mummunan kamu ita ce tushen komai" cewar Daddy cike da takaici.

"Akwai wanda zaiyi sama da abinda Maikudi yayi min kuwa? Banda kwashe komai ya kara da toshe hanyoyin da taimako zai iya samun Mairama...wani abin sai dai muyi kawai domin Allah ba don halin mutum ba"

Daddy tunawa yayi da yadda Maikudi ya jigata a hannuwansu saboda ba karamin bakinciki suka ji ba da abubuwan da ya yiwa iyalin Zayyan sannan ya auna da makantar shekara goma "daga shi har ita yayar Mairaman babu gwara. Makanta ko ta wuni daya ce fa ba abin mantawa bane"

Shawara Daddy ya bashi daidai da yadda yake ganin ko shine abinda zaiyi kenan. Yana dariya ya kara da cewa "ba don mun fara tara jikoki ba da mun kwashi 'yan kallo a garin Sumaila gobe."

Zayyan ma dariya yayi yana jin Daddy na cewa Awwab ya zauna ya jira shi ya gama waya.

"Ka fada masa abinda ya faru don nasan Alheran ba fada masa zata yi ba kuma hakkinsa ne ya sani."

"To sarkin taya bera bari"

"Zancen gaskiya fa kaga matarsa ce, don dai kawai mun biyewa mata ance sai anyi biki da tana gidansa babu mai shiga cikin case dinnan cikinmu duk wanda ya tabata da shi zasu gamu. Kace ya sameni a Kano kafin shabiyu goben kawai"

"So kake ku hana matar mutane kwanciyar hankali ne kake ta tara mata gayya?"

"Tsuntsun da yaja ruwa..." Zayyan yace yana shafa sajensa.

Suna gama wayar kuwa Daddy ya fadawa Awwab saboda duk a zatonsu duka sosai Salame ta yiwa Radhiya tunda da ta kira Daada kuka take yi fiye da yadda dukan yake mata zafi. Ita kuwa tayi ne kawai don yazo ya a kawo karshen mulkin Gwaggo Salame.  Ai kuwa Awwab ya shiga tashin hankali sosai bai iya bacci ba har garin Allah Ya waye yana tunanin wane irin duka ne aka yi mata. Ganin ba iya bacci zaiyi ba kawai karfe shida da rabi ya shirya cikin kananun kaya wandonsa chinos ruwan toka da polo shirt fara. Agogo yake daurawa lokacin da maganar Emzee ta fado masa da yace Rahima ba kanwarsa bace, ba mamaki dalilin faruwar wannan abu ne. Sai yaji ya kara tsorata da zumuncin yanzu. Kafin takwas yana hanya don shi bai dauki tuki a bakin komai ba.

Shima Zayyan jirgin bakwai da rabi ya biyo yana ta jujjuya maganganunsu da Hadir da Major na daren jiya. Kafin ya sauka Captain Onomza ya turo mota aka dauke shi zuwa Janguza barrak. Tara da rabi Emzee ya iso su ka jira Awwab shi ma goma da 'yan kai yana barrack din don ma bai san hanya ba da kwatance ya karasa.

Sun gama shirinsu motoci biyu cike da sojoji ta ukun Major General Zayyan Tureta ne da dreba da kuma escort dinsa da suke yawo tare sai kuma motar bayansu Emzee da Awwab.

Kafin su bar barrack din ya kira Mairama inda ya bata umarnin ta tabbatar gidan nan babu yara kafin ya iso.

"Ina nufin ko su Alheran bana son na tarar sannan kananun yaran gidan duka kowa ya fita."

"An gama ranka ya dade" tace tana kirkirar murmushi.

Kebewa tayi da su Yadikko ta fada musu su ka sanar da Malamijo. Nan yace su tattara duka yaran su tafi ainihin gidan iyayensa wanda yanzu sai 'yan uwa baya son kowa ya dawo saboda zasu yi taro na manya. Babu wanda ya kawo tangarda sai Halifa shima kuma hankalinsa ne a tashe saboda Salame da ba'a gani ba tun jiya Alh Indararo yana ta babatu. 

Ummi ta kira shi gefe ta kwantar masa da hankali sannan tace yaje gidan Ta Madina ya daukota. Gani tayi yana son yi mata tambaya ta dafa shi.

"Kada ka damu Malamijo ya gano inda ta kwana tun jiya kuma yana son shi da Ta Madina suyi mata magana ne."

Sai lokacin hankalinsa ya kwanta ya tafi. Bai dade ba ya kawo Ta Madina shima ya tafi inda su Radhiya suke. Yau dai bayanta yayi tsami a dan rankwafe take tafiya ita kuma Rahima sai dankwali tasa ta daure idonta saboda ko yaya ta motsa tana jin kamar kwayar idon fitowa zata yi. Ragowar shatin wayar kuwa yana nan kwance a fuskarta ba kyaun gani sai hijabi ta janyo ta rufe fuskarta sosai. Da Halifa ya shiga dakin da suke ya ganta kuka ta saka masa Radhiya sai ta fice kawai ta basu wuri. Itama kukan take yi tana tausaya musu. Babu dan da zai zo jin ana zagin iyayensa bare kuma a kai ga kowa yana jin haushinsu saboda wani abu da suke yi ba daidai ba.

**********

Tunda tazo gidan Mal. Kallamu abokin Malamijo Salame banda aikin kuka babu abinda take yi. Ta rasa me yake yi mata dadi kowa ganin laifinta yake yi. Duk abinda tayi ba karya aka yi mata ba amma babu mai fahimtarta. Duk wata rayuwa da take so da buri Mairama ta haye kai ita take yi. Rahima kuma ba komai ke dawainiya da ita akan yarinyar ba sai neman inda za ta sauke damuwarta. Ta rasa farinciki komai ba ya yi mata dadi gashi iyaye da 'yan uwa sun juya mata baya. Fuskar Mairama ta tuna lokacin da ta ke yi mata alkawarin bazasu sake haduwa ba taji wani iri a ranta. Wai shin mene ne takamaiman abinda ya rabata da Mairama idan ka cire auren Zayyan wanda ita Mairaman bata da masaniyar tana son shi. Kan nata ya toshe ta kasa tunanin kirki kawai sai ji tayi ana bubbuga kofofin gidan da karfi maza suna hayaniya ana kiran sunanta.

"Come out" taji wani ya doka kofa da karfi yana fada.

Ciwon ciki ne haka siddan taji ya kamata da tsananin bukatar zagawa bayan gida saboda tsabar firgici da tsoro. Kofa kofa sojojin suke budewa suna hargaginsu idan sun so tsorata mutane. Mal. Kallamu da matarsa duk da Malamijo ya kira ya fada musu yanzu sojoji zasu zo fitar da Salame amma bai hana shi shiga tashin hankali ba. Murdaddun maza ne majiya karfi babu tsoro babu rissina suke ta kiran Salame cikin wata irin murya. Dakin ta kalla babu wurin buya gashi muryoyinsu da bugun kofar yana ta matsowa kurkusa.

Jiki na kyarma ta tashi ta mikar da katifar dakin ta jinginata da bango sannan ta shige bayan ta buya a zuci tana cewa "sai nayi magana ace bani da hankali amma ta ina talauci yayi saboda Allah tashin hankali yazo wa mutum gida babu wurin buya. 'Yar kwabar nan ko gado da za'a iya shiga karkashi a labe duk babu"

Gidaje biyu ne tsakanin Malamijo da aminin nasa kuma har can gidan ana jin abinda sojojin suke yi shiyasa mutane kowa ya shige gida baka jin wani motsin kirki tamkar babu mutane. Dattijuwar matar Mal. Kallamu da tsoro ya isheta bata ci nanin ba nanin za ta ci ta tayi saurin nuna musu kofar dakin da Salame ta kwana. Gyada kai babban cikinsu yayi su ka yi shiru gabadayansu na dan lokaci har sai da ta soma sauke ajiyar zuciya a zatonta sun tafi.

"Allah Ya soni....amma bari na fito sai na nunawa Mairama har yanzu gaba nake da ita. Nice zasu turowa sojoji saboda........."

Haske ta gani wal daidai da faduwar katifar a kasa. Saura kiris ta saki fitsari ganin sojoji da kafta kaftan takalma kai kace filin daga zasu je suna nuna mata hanyar kofa wani ya daka mata tsawa.

"Get going my friend"
Chapter 134 · 0% Book details