← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 157

Sashe 123

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta rissina tace "Allah Ya kara budi Daada Ya saka da alkhairi"

"Amin" su Excellency suka ce suna murmushi.

Wani dan karami sosai Zayyan ya mikawa Emzee "Soja dan sojoji kaima ga naka"

Godiya yayi sosai shima aka fara daukarsu a hotuna sannan kamar hadin baki aka shiga miko musu gifts kowa da abinda yake badawa. Family picture aka tashi dauka aka hada iyalan Zayyan, Daddy, Baba Hadir, Excellency duka wasu a tsaye wasu a durkushe. Zayyan ya dan gama waigensa ya hango Chibuzor ya kira shi da hannu shi da matarsa.

"Sir this is a family picture" yace yana sake ja da baya.

"You are my family Chibuzor" Zayyan yace yana yi masa murmushi tare da nuna masa inda zasu tsaya kusa da sauran yaran nasu.  Chibuzor bai taba tunanin karamcin Zayyan ya kai haka ba. Yana da masaniyar yadda addini da yare ke kawo tawayar kyakkyawar alaka a tsakanin 'yan Nigeria amma ga wani babban soja masoyi ga mutane da dama ya rungumi kowa hannu bibbiyu.

An gama hotuna aka fara cin abinci wanda yake serve yourself anyi shi a wadace kowa yaci ya koshi. Duk wannan abu da akeyi Salame tana rakube ko motsin kirki bata son yi saboda ko yaya ta ga giftawar Emzee sai cikinta ya duri ruwa. Yanzu idan ya bude baki a wurin nan ko kafin ta koma Sumaila ta kade har ganyenta don bata san me zasu yi mata ba. Ana yiwa Zayyan kallon mai kirki amma tana da yakinin cewa ba karamin mataki zai dauka akanta ba.

Kallon kowa take yi daidai ana ta shagali wannan na hira da wannan, wancan da waccan amma babu wanda ya rabeta...abin bakinciki shine harda 'ya'yan cikinta. Idan Rahima ta gudu saboda yadda take takura mata meye dalilin Halifa da Khadi? Shi dai bai tsaneta ba amma baya kaunar halayenta ko kadan. Khadi kuma yarinya ce da ta goge a rashin kunya amma yau fushin nata saboda ta doketa ne. Salame sai ta ji ta very, very lonely abin ya tabata fiye da zato da tsammani. Kamar ance ta daga kai su ka hada ido da Mairama. Tun dazu da take gaisawa da mutane hankalinta yake kan Addarta. Yadda ta zauna ita kadai a table din mutum takwas an wareta kamar babu ita a wurin itama sai taji babu dadi. Fushin da take yi na kudin Rahima da ta karba dazu ya gushe. Murmushi tayi da su ka hada ido a karo na biyu sannan da hannu ta nuna mata inda ake dibar abinci. Wai don kada a rainata sai ta dauke kai ta juya mata keya.

Ashe Mama na kallonsu ta tuntsire da dariya.

"Oh ni Zainabu Abu inama ina da 'yar uwa mace muma mu hau sama mu fado."

"Haka ma zaki ce?" Mami tace tana murmushi.

"Abin naku ne kamar hadin baki. Kina yi dasu Gambo gefe daya ga Salame suna bugawa da Mairama"

Ummi ta sake kallon Salame "babu abu mara dadi kamar ace kai da 'yan uwanka bakwa jituwa. Yawanci kuma duk sai ki ga hassada ta fi komai ruguza mana zumunci"

"Ni zan fada muku haka don ina da tabbacin Hussaina da tayi ta ingiza rikicinmu da Gambo ba wani abu bane ya tunzuruta sai ganin wai muna da kudi mun wareta" Mami tace tana tuno bacin ranta.

"Amma dai dan Adam babu godiyar Allah. Sai ki ga muyi ta takurawa kanmu domin mu kyautata musu amma basa gani" cewar Mama 

Mami ta mike "Yo ina kudin yake banda dai ana yiwa rogo kallon kitse. Kunga ni mijina bai ci komai ba yau tun safe kuma na ga mazajenku sun saka shi a gaba da hira ku taimaka kuyi musu signal ko su tashi ko na zuba masa shi kadai" 

Ummi da Mama suka sa dariya Mama tace "yayi matar Major Allah Ya bar mana ke. Ana kwasar jikokin ma ashe a gefe ana ta dabbaka kauna"

Dariya Zainab ta basu suka mike tare kowacce ta zubawa mijinta abinda tasan yana so. Ummi na kai wa Daada nasa ta koma ta zuba fried sphagetti da wani sauce din naman sa da albasa, attaruhu da koren tattasai an yanka su manya manya, naman kuma dogo a tsaye ta hada da potato salad ta tafi mazaunin Salame. Ajiye mata tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun. 

"Meye wannan za ki wani turo min abinci" ta sha kunu

Ummi ma daure fuska tayi ta ja plate din "idan ba kya so sai na dauke"

Da sauri Salame ta janye yawunta ya gama tsinkewa "barshi dai....kada kiyi zaton zanci da dadin rai ne don dai kawai ba kyau wulakanta abinci ne. Kuma ga bakinku ana kallonmu kada na kunyata uwar gayya Mairama matar Zayyan mai kudi"

Ummi gimtse dariya kawai tayi tana ganin yadda idanun Salame suke walainiya akan plate din. "Bari na baki wuri kici"

Wani iri Salame taji bata so ta tashi amma bazata nuna ba "haka kika iya dama naki bola wasu can bare sun fimu matsayi."

"In zauna kenan kike nufi?" Ummi tace a ranta kuwa dariya ce fal take dannewa.

Baki fal da taliya da nama Salame tace "In kin so tunda ai ba sai kin nunawa duniya bama shiri ba"

A zuci Ummi tace "da baki girmeni ba da nace baki da kunya ma...kina so kina kaiwa kasuwa"

A can kujerun karshe daga bari daya Yousuf ne da Awwab suke hira duk yawanci akan bikinsu ne da shirin da su ka tanadar masa. Dinner din da zasuyi basa bukatar taimakon iyaye da kudinsu suke son yi gasu duka babu wanda ya waye da harkar biki a Nigeria.

"Ka bari idan mun koma gida muyi maganar da Bilal tunda shi dan gari ne" inji Yousuf 

"To shikenan. Yanzu dai shawara nake nema. Ina tunanin sayen mota amma kuma Alheran da zan barwa idan na tafi aiki itama ba zama zata yi ba."

"Kawai ka barshi sai ta gama ta dawo nan din kunyi settling sai ka saya idan ba haka ba wa zaku barwa? Tunda akwai motocin nan a gida kawai ka bari"

Arifah su ka gani ta nufosu da plates biyu Yousuf yayi saurin tashi ya karbo suka koma wani table din yana yiwa Awwab gwalo wai ga inda ake kula da miji. Arifah kunya taji ta kai masa duka a hannu ya rike hannun yana kallonta kamar su bar wurin nan ya samu damar nuna mata soyayya.

"Ehemm da mutum a nan dai...albarkacin kanwata bari na baku wuri"

Tashi yayi ya fara tafiya Radhiya ta kira shi kamar tasan ita zai nema. Tambayarsa tayi ina yake ya fada mata sai gata da plate guda daya da robar maltina.

"I am starving Hammana"

"Me yasa kike zama da yunwa" yace yana gyara mata kujera ta zauna.

"To ba kaine nake ta nema ba muci" tace tare da turo baki.

Bakin yake kallo yana lumshe idanu "kici abincin ni kuma ki bani bakin cin abinci yunwarsa nake ji"

Kunya Radhiya taji har ta rasa inda zata sa kanta. Awwab kuwa yadda take yi ga dimple dinta yana ta shigewa ya burgeshi sai da yasa hannunsa a wurin.

"I love this...." kanta ta sunkuyar yasa hannu ya rike kunnuwansa "sorry baby ina takura miki ko? Lets eat amma kinsan bazan ci na bakinki ba ko" ya kashe mata ido.

Bata fuska tayi "Ewwwww ka zama kazami dai"

"Kinga laifina an aura min ke"

Hannuwa ta nade a kirji tana cika tana batsewa yana mata dariya. Kawu Zakari ta hango ai kuwa ta daga masa hannu tana dariya za ta rama.

"Kawu Zakari tun dazu nake ta nemanka"

Fuskar Awwab ba shiri ta sauya ya bata rai kamar wanda aka yiwa duka. Yau dai ya ga wannan Kawu Zakarin. Dan kyakkyawan bafillatani ya karaso ya mikawa Awwab hannu. Radhiya sai sakin murmushi take sai da ta ga Awwab ya koma abin tausayi ta dena jansa da hira.

"Me yasa baka zo Antyn tamu ba ne?"

"Tayi nauyi bana so ta wahala"

Ba kunya Awwab ya saki fuska "ashe kayi aure"

"Eh muna da yaro daya ma ga na biyu a hanya" Kawu Zakari yayi murmushi.

"Kai Madallah wannan abu yayi kyau Allah Ya bar kowa da masoyinsa" Awwab yayi maganar farinciki ya mamaye fuskarsa abin dariya.

Radhiya tana dariya harda hawaye don yanayin relief din da ta gani akan fuskar Awwab kamar wanda aka yiwa bushara. 

Kawu Zakari yayi murmushi "mijinki yana da barwanci Radhiya. Ana kirana bari na baku wuri"

Sai da ya tafi Awwab ya kalleta "to dai kinji yana da aure matarsa tana shirin haihuwa ta biyu"

"Dadin abin nima ina da auren nan and God knows I love my husband"

Wani irin kallo yayi mata sai kuma kunyar abinda yayi ta kama shi ya cire hularsa ya rufe fuska tana jin muryarsa sai ka rantse kuka zaiyi "did I just make a fool of myself a gaban crush dinki Alheran?"

"Eh mana" itama ta yi kamar kukan zata yi.

Hular ya cire ya ajiye a gefe yana murmushi "laifinki ne Schatzi yanzu duk inda na ganshi sai na tuna da wai likita kike so"

"Hamma Awwab" ta kira shi bata so ko kadan ya rinka tunanin akwai wani kafinsa ko bayansa don babu.

Hannuwanta ya kamo ya rike "na'am"

"Kai na fara so kuma kai kadai zan so har abada in sha Allah" tace da wani irin yanayi.

Zuciyar Awwab ta sake yi mata wani babban masaukin "Alheran ki sassautawa zuciyata kada sonki yayi mata illa"

Bata sake magana ba ta nuna masa abincin. Spoon biyu ta sako amma yaki yarda sai dai suci da daya duk da tana kunya ga iyayensu ko ina amma haka ya tilasta mata suka ci babu magana sai kallo mai cike da ma'anoni.

DJ ya soma nasa aikin ana sako wakoki wuri ya kaure sai rawa wurin masu jini a jika. Ana soma wakar Nura M Inuwa ta amarya 'yar amana jikin Radhiya ya fara mazari tana hango 'yan mata musamman na Nijar 'yan uwansu ga Zahra can da Raji ana ta nishadi ta mike tsaye.

"Ina zuwa?" Awwab yace jikinsa na bashi rawa zata yi.

Wurin rawar ta kalla da ka tayi masa alama.

Maltina ya cigaba da sha hankali kwance "zauna Schatzi please"
Chapter 123 · 0% Book details