← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 157

Sashe 27

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutane da dama suna zaton da ance ka fita waje watayawa kake. Aikatuwa take bilhakki mijinta yana kukan nakasa a gefe. A hankali masu gidan suka yaba da kwazonta sai aka basu wani dan bangare karami a gidan. 

Cikin shekarsu ta biyu Harun yaje gida abinda ta hada ta bayar aka dauko musu 'ya'yansu sauran kuma ta aika Sakkwato wurin sojan da Major ya rubutawa sako cewa a bawa su Mairama. Shekara guda cif cikin kudin aikin Mami ake dibarwa Mairama.

Sako ya riskesu daga karyar Maikudi cewa tayi aure sannan dan cikinta baizo da rai ba. Hoton Alheran Radhiya kuwa da suka bukata cikin dakin Jume ya dauko wani da aka yi musu da yaransu gidan wani zuwansu da sallah. Murna sosai ranar da suka amshi hoton. 

Cikin ikon Allah sai ga Mami da ciki. Allah Ya bata 'ya mace Major ya saka mata suna Zayyanatu. Dariya tayi da taji sunan yace idan haihuwa goma zata sake Zayyan da Zayyanatu zaiyi ta saka musu.

A yanzu Major ya sami aiki a wani kamfani shima sannan Awwab ya sami scholarship saboda kwazonsa a makaranta. Harun da Gambo sun koma Nigeria da 'ya'yansu uku Ghazalatu, Hafsa da Imam. Su Mami kuwa zaman jiran kammaluwar karatun Awwab suke su koma su ma. Sun sami rufin asiri daidai gwargwado kuma sai Major yayi watanni lalurarsa bata tashi ba sai anyi zancen Nigeria ranar zai kwana hankali a tashe yana tuna aikin da ya yiwa kasarsa ya kaishi ga wannan rayuwa

**********

HADUWAR ALKHAIRI
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: ***********

"Ke Radhiya, zo kije kantin sauki ki siyo min yis"

Shanyar kayansu da ta wanke take yi nata da na Emzee da Mairama. Kallon Binta tayi tace "ki aiki Emzee ko wani don Allah kinga ni bana fita saboda Ummi"

"Inda na aike kin har wani nisa ne dashi da zaki fara yi min felekenki na tsiya. Ko kuwa nace kije ki zauna ne?"

Zumburo baki tayi "Ummi wanka zata yi idan na gama shanya. Zaki kai mata ruwan ki ajiye mata soso da komai a kusa da ita inji miki aiken?"

Mairama tana daki ta jiyo su ta rinka shafa bango har ta fito.

"Ke!" Tace da tsawa

Radhiya ta juyo tana jira taji Mairama ta umarceta da zuwa kantin ta fada mata kai tsaye ba zuwa zata yi ba. Tunda mahaifiyarta ta makance ta kara hankali da bambance su waye masu kaunarsu da gaskiya. Malamijo ya gina gidansa da turbar nafsi nafsi kowa ta kansa yake yi. Babu wani jinkai na azo a gani saboda rashin wadata su da abubuwan da ya dace. Idan ka cire Yadikko babu wadda take leka Mairama balle ace mata yaya jiki. Dukkansu take kallo tana jin kanta daidai dasu. A duniya bata da sama da Umminta sai Emzee. Shi kuma haushinsa take ji saboda rashin magana. Gabadayansa bashi da walwala sosai yaron saboda tsangwama musamman daga Salame kafin ta bar gidan.

"Ki karba kije ki siyo mata ko ma meye idan kin dawo sai nayi wankan"

Radhiya yarinya 'yar kimanin shekara goma sha daya wadda ta gado zuciya ta mahaifiyarta, barkwanci da jarumtar mahaifinta da kuma jinkai da tausayi nasu su biyu ta kekashe idanu "Ummi ni bazani ba idan na tafi ma zubar da kudin zanyi a kwata ko na sayi danmalelen gidan Fadi. Haka kawai yau babu makaranta kowa yana nan taki aikensu sai ni saboda bata damu dake ba" ta kare maganar muryarta da alamun zata yi kuka.

Mairama ta daga hannu daga inda take tsaye kamar za ta dake ta "kizo ki karba kafin ranki ya baci"

Juya keya tayi ta mika hannu ta baya tana jira Binta ta ajiye mata kudin harda wani kada jiki. Emzee ne yazo ya karbe "ni zanje me za'a siyo miki?"

Binta ta warce kudin "bazaka je ba din, wannan fitsararriyar nake so inga uban da ya tsaya mata a cikin gidan nan. Har ni kike juyawa keya saboda baki da kunya"

Mairama daurewa kawai take yi saboda rashin ido. Itama ta sani an tsangwami 'ya'yanta an hanasu rawar gaban hantsi saboda an ga tana zaune. Amaren Malamijo Hanne da Binta sunfi kowa kaudi da takura musu. Kuncin zuciyarta ne ya taso ta tuna mijinta. Da yana raye waye duk gidan nan ya isa ya taka su? Yadda kowane uba ke kaunar 'ya'yan shima tasan zai so nasa kuma ya kyautata musu rayuwa.

"Karami janyo min hannun yayarka"

Da kanta ta karaso gaban Mairama ta kama hannunta don ta nuna mata ta iso. Hannunta ta shimfide mata a gadon baya, dukan ya shigeta amma ta dake. Mairama kanta ciwo take ji yana addabar zuciyarta "in ce kije aiken ki ce bazaki ba saboda ban isa ba? Ko saboda bani da ido sai yadda..."

Zubewa tayi a kasa tasa kuka "Ummi kiyi hakuri don Allah zanje."

Kudin ta karba daga hannun Emzee tana cewa ya mayar da Ummi daki kafin ta dawo. Rai a bace taje ta siyo yeast din naira hamsin maimakon na ashirin da aka aiketa. Da ta dawo daga bakin kofa ta tsaya ta zura hannu

"Gashi"

"Shigo ki bani" Binta tace da gadara tana fadawa yayarta "kinga fa irin jarabar da muke fama da ita. Uwa makauniya 'ya'ya marasa da'a"

"Mu ba jaraba bane" Radhiya ta maida mata da tsiwa.

Bintu bata bata lokaci ba ta kai mata lafiyayyen mari.

"Uwarki makauniyar nan ma bata isa ba wallahi"

Tana kuka baki bai mutu ba "ba dai uwata ba"

Ran Binta ya kara baci "sai ta wa?"

"Wanda ya tsargu dashi nake" Radhiya ta amsa kai tsaye. Kafin Binta ta ankara ta fice daga dakin. Da sauri ta kamo Radhiya a tsakar gidan tana shirin shiga dakinsu.

Mairama tana jinsu ta yi salati ta sake tashi "me kika sake yi kuma?"

Binta ke dukan Radhiya da zagi amma a hakan cewa take ba dai tata uwar ba. Hajjo ta taho kwatar Radhiya Binta ta sake tunzura ta daga hannu zata sake kai mata duka ga Mairama har ta soma hawaye suka ji sallama.

Amsa sallamar bakuwar suka yi Binta bata kula ba ta kuma daga hannu taji matar da ta shigo tace tayi hakuri kada ta sake dukanta yara sai da rarrashi.

Idanu a soye don itama Binta ba kunyar gareta ba tace "yau ko uban da ya haifi uwarta ne wallahi bai isa ya hanani dukanta ba"

Malamijo wanda motocin da ya gani a kofar gidansa suka saka shi tasowa daga majalisar da yake ko kallon mutanen wajen baiyi ba tunda ya ga daya ta shiga gidansa. Ya shigo kenan ya ji me Binta tace ya kuwa murtuke fuska.

"Ahhh lallai yarinya kwananki a gidana ne ya kare shiyasa kike zagina. To shiga ki kwaso tsiyarki kizo ki wuce na sakeki saki biyu"

Innawuro ta kalli Ali tana jin wani bacin rai. Wato duk tsayin shekarun nan yana nan da bakin halinsa na sakin mata. Ta sani wadda ya saka din tayi laifi amma a bainar jama'a haka ya dankara mata saki.

Shi kuwa ko a jikinsa sai ma binta da yayi da kallo yana son tuna a ina ya santa. Matan gidan da yara hankali ya koma wurin Binta da tayi dakinta tana kuka basu kula da Radhiya da take zaune a kasa ba ko bakuwar da take tsaye. Yadikko har kullum ita ce mai hankalin kuma bata gida a lokacin. 

Mairama ta duka tana mika hannu neman Radhiya da ta tabbatar tana wurin tana kuka.

Cikin kuka da ta gaji da laluben tace "ina kike ne?"

Muryarta kawai Innawuro taji ta saki baki tana kallonta. Babu tantama wannan ce Mairama diyar Mairo don banda kama ta fuska hatta muryarsu tayi shige sosai.

Kafadar Radhiyan tayi sa'ar dafawa ita kuma haushin aiken tun farko ta janye jikinta tana saka kuka mai sautin da bata yi ba a gaban wadda ta daketa.

"Ba ke kika ce sai naje mata aike ba"

"Allah Ya baki hakuri to tashi muje daki"

Mairama ta mikar da Radhiya a daidai lokacin da Innawuro tace "Mairama?"

Malamijo kuma yace "Innawuro?"

Mairama ta juya duk da bata ganinta ita kuma ta juya tana kallon Malamijo ashe tun dazu yana tsaye. Hankalinta duk yayi kan Mairama tace "muna da yawa sauran suna waje. Na shigo ne sanar da zuwan namu"

Yawun bakinsa ne ya kafe, lebbansa suka bushe sai harshe yake ta fitarwa yana lashesu. Duka motocin nan bus uku da canta daya 'yan uwan Mairo ne? Ya sani da kansa ya taba nemansu saboda tausayin Mairama. Amma tuni ya watsar musamman yanzu da rayuwarta take cikin garari.

Innawuro ta dawo dashi cikin hayyacinsa da yaji tana cewa Emzee ya fita ya cewa bakin waje su shigo. Yaron ya tafi yin abinda ta saka shi ta dawo da kallonta ga Radhiya da Mairama da suke tsaye kawai a wurin.

Gani tayi har yanzu Malamijo yaki magana ta cewa Mairama "muje dakinki kinji 'yata"

Mamaki ne fal cikinta bata san ko su waye ba. 

"Ke muje daki" ta ce da Radhiya

Hannunta cikin na Radhiya suka shiga dakin da komai ya kare masa yanzu sai katifa da shirgin kayansu. Rage tsayi Mairama tayi daidai kunnen Radhiya "ina bakuwar take? Kin taba ganinta?"

 Innawuro tana kusa dasu kuma taji tambayoyin da tayi mata. Radhiya sai ta dago kai tayi mata murmushi tana dan jin kunya. Mairama ta matsa mata hannu

"Ki bani amsa mana, idan rigima kika sake kwaso min zaneki zanyi wannan karon" 

Hayaniya ce ta cika tsakar gidan. Maza ne matasa da magidanta harda dattijai haka ma mata suka rinka tururuwar shigowa. Malamijo yayi tsamo dashi yana kallonsu zuciyarsa ta cika da firgici da ya ga cikin matasan harda masu sanduna. Sandarsu ce ta fulani da ado baya cika sai da ita, amma da yake ba gaskiya gareshi ba sai ya manta da wannan al'adar ya luluka tunanin ko dai duka zasu yi masa. Fulatanci suke ziryan baka jin komai sai sunan Mairama. To shima dai yaren gidansa kenan sai dai suna taba Hausa sosai.

Gaban Radhiya sai da ya fadi da ta hangosu q ta tabota  "Ummi sun kara yawa wallahi harda sanduna."

A kidime tace "dan gidan wa kika tabo kuma?"

Harda dan guntun hawayenta na tsoro tace "ni da bana fita wa zan taba?"
Chapter 27 · 0% Book details