← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 157

Sashe 7

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar lahadi ya samu da babu training sosai ya fita yaje ya sanar da Mal Aminu da mutum biyu cikin ‘yan uwan mahaifinsa game da auren da yake nema. Sunyi farinciki da alkawarin bayan ya koma Kanon ya fadawa mahaifin yarinyar zasu je bayan sati daya da zuwan nasa. Godiya yayi musu ya nemi matar Mal Aminu mai suna Gwaggo Ladi matar da ta maye masa gurbin uwa wurin kulawa da bashi abinci da sauran abubuwa lokacin da kowa ya gane gashin kuman da Jume take yi masa. Kudade ya bata da yake so a fara siyayyar kayan aure ta yadda idan zasu tafi zasu je ne a shirye saboda nisa.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: F
Sai da ya nemi izinin fita na kwana biyar, da kyar kuwa bukatarsa ta biya saboda ba kasafai ake son suna yin nesa da barikin ba. Ranar da zai tafi sai da ya bi ya sallama da Captain Mustapha. Yanzu alakarsu tamkar wa da kani ga kuma yaransa sun mayar da Zayyan uba na biyu. Shi Captain Mustapha asalinsa da Katsina ne daga shi har matarsa don auren gida ma su ka yi.

Asubancin fita yayi ya shiga cikin gari gidajen dangin Mal Muhammadu. Daga can ya wuce tasha sai Kano.

Yayi sa’a masu kilishi sun fito ya sayawa Malamijo. Shi dai a dan zamansu na farko bai hango komai a tattare da shi ba sai barkwanci.

Kwanakin da suka gabata Salame ta dami Mairama wai me ya hana Zayyan dawowa saboda Salisu ya matsa lamba kuma Malamijo ya riga ya bashi. Ganin akwai kudi yaron ya kara shiga ransa. Salame so take ta tabbatar Zayyan bazai dawo ba sai ta amince masa ko babu komai zata huta. A haka tana tsoron saurin amincewa ya dawo a bashi Mairama ita kuma ta rasa. Akwai ranar da ta tambayi Mairaman ko ta fadawa Zayyan yanayin gidansu.

“Kinsan boye-boyen babu amfani gara yasan wa zai aura kada Malamijo ya nuna masa hali”

Bata rai Mairama tayi “yau da kanki Adda Salame kike cewa Malamijo zai nuna hali? Ni dai soyayya bazata sa na kwashe sirrin gidanmu na kaiwa saurayi ba. Idan bai aureni ba shikenan ya gama sanin komai nawa. Kuma ko yaya Malamijo yake ai babanmu ne dole mu so a mutunta shi”

Waskewa Salame tayi amma a ranta tana ganin ta sami hanyar rabasu “irin wannan sharhi ba wani abu nake nufi ba, abar maganr dai”

Yau kamar daga sama sai ga dan aike wai ana sallama da Mairama inji Zayyan.

Wanka take yi lokacin ta gama aikin fura Salame ce taji sakon. Jikinta har bari yake tsabagen murna ta fada dakinsu da sauri. Kaya ta sauya da sauri ta shafa hoda harda janbaki ta sako daya daga cikin kayan da Ta Madina ta dinka mata. Komai da azama take kada Mairama ta fito ta sameta. Tazo fita ta koma ta cire mukullin sif din kayansu bayan ta kwashe duk wani kayan sawa ta saka a ciki ta jefa a karkashin sif din ta fita tana dariyar mugunta.

Bata yiwa kowa sallama ba don basa tsakar gidan ta fice zaure. Dama niyarta da an tambayeta ina zuwa tace wurin Innarta zata je.

Kamshin turare wanda Salisu ya kawo mata zuwansa na karshe ya fara ji kafin ya ganta. Ta gumbuda turaren sosai kuwa a ransa yaji dadi ba Mairamansa bace take wannan aika-aikan. Fuska ya saki yana mata murmushi. Ta sunkuyar da kai tana ‘yar dariya don jin kanta take kamar yau take sallah saboda ganin Zayyan.

“Babban bakonmu barka da sauka, yaya hanya?”

“Lafiya kalau Saude ya mutanen gida”

Wani abu taji ya soki zuciyarta, wato ku sunanta bai rike ba. Bata nuna damuwar a fuska ba sai ma wani kasha murya da ta tsiri yi “Salame dai ko, baka ma rike sunana ba saboda baka damu dani ba”

Banbarakwai yaji zancen nata “Afuwan kada ki fadawa Mairama tace ta fasa na yiwa Addarta ko ince Addarmu laifi”

“Ba wani abu ai, ita ma bata soma fada ba yadda ta matsu tayi auren nan. Allah Ya dube mu, masu gudunmu saboda Malamijo zasu sha kunya”

Zayyan mutum ne mai saurin dago ina mutum ya dosa idan suna magana, yanzu ma tuni ya fahimci akwai abinda Salame take son fada masa tun hirar bata tsawaita ba.

“Ban gane masu gudunku saboda Malamijo ba, ba babanku bane?”

Hannu ta dora akan bakinta kamar gaske tana ware idanu “ba dai Mairama bata yi maka bayani ba? Irin haka ai da wuri ake fada saboda toshe matsala don kada kaji a waje. Idan na koma zan fada mata gara ta sanar da kai komai da wuri zai fi. Sai ka danyi hakuri ta gama aikin furar sayarwa ne ta shiga wanka”

Wai shi za ta jawa rai, kawar da kai yayi abinsa yana kallon waje. Haka nan bata yi masa ba tun haduwarsu ta farko a gidan Gwaggonta da akayi bikin yaranta. Sai tayi ta wani kifi-kifi da idanu amma sau goma idan zai dago kai sai sun hada ido.

Yanzu da ta ji bashi da niyar tambaya sai ta sake salo. Jan hanci yaji tana yi alamun tana kuka. Dawo da hankalinsa yayi gareta da sauri.

“Ya dai?”

Goge hawayen da ko digonsu babu tayi sannan ta dan tabe baki duk yana kallonta “gara kawai na fada maka don abin zai yiwa Mairama nauyi”

Halin Malamijo kaf da yanayin zamantakewar gidansu ta kwashe masa. Hatta dangin mahaifiyar Mairama sai da ta kwancewa zani. Jinjina kai kawai yake yi yana kara tausayin Mairama sosai. Yanayin rayuwarta kusan daya da tashi wato dukkansu basa jindadi a gidan iyayensu.

Salame sai ta dauki sauyin yanayinsa a matsayin tarkonta ne ya fara kamu ta dan murmusa “nasan rashin dangin uwa lokacin aure a kusa da ciwo…..” ta dan ciji labbanta “…uhmmm ni kaga dangin Innata suna garin nan kuma bikin da muka hadu ma nasu ne, Mairama kara kawai aka yi mata”

Yanzu ya gama gane manufar wannan dogon sharhin. Kaurara murya yayi ya hade rai “Salame!....”

Bai karasa maganar ba sai ga Mairama ta fito da sassarfa sanye da kayan da tayi aikin furar ta makale a bayan kyaure.

“Adda” ta kira Salame tana kunyar fitowa.

Zayyan ne ya amsa yana mai jindadin ganinta “Mairam yau a nan zamuyi tadin?”

Kai ta sunkuyar ta sake yafito Salame sai kawai tayi gaba abinta ta fice don tasan me take nema. Kusan minti goma tun bayan fitowarta take ta neman mukullin sif din bata gani ba. Baki ta saki ganin ta fice bayan tasan kiranta take. Duk sai taji ta muzanta saboda Zayyan ma ya gani kuma baiyi mamaki ba duk da bai san me take bukata a wurinta ba.

“Nima in zo bayan kyauren ne?”

“A’a ina zuwa don Allah kaya zan sauya”

Hannu ya daga ya dakatar da ita “dawo abinki nima nan kayan jikina sun sha wahala da kurar hanya amma na kasa hakuri ko masauki ban nema ba nayo nan”

Jikinta ta kalla musamman zanin taji babu dadi. Zayyan ya matsa mata akan ta fito ba zai dade ba sai dare zai dawo. Busu-busu haka ta fito kayan jikinta masu saurin nuna datti ne dama saboda haskensu.

Kanta ta sunkuyar tana kallon kasa ta gaisheshi ya amsa fuskarsa a sake. Lura yayi a takure take sai ya mika mata ledar kilishin Malamijo yace ta shiga gida sai anjima zai dawo.

Yana tafiya a hanya amma zuciyarsa ta fada kogin tunanin kalaman Salame da kuma yanayin da ya ga Mairama. Yana da yakinin Salame ko dai tana son sa ko kuma kawai bata son cigaban kanwarta ne. Ko ma meye zaiyi kokarin sanin wacece Mairama Ali kafin ya koma bakin aikinsa.

A cikin gidan kuma Mairama sake komawa tayi neman mukulli har ta hada gumi amma ta rasa ina ya fada.

Da ta gaji da nema ga rashin sanin ina Salame ta tafi sai kawai ta cire kayan jikinta taje ta wankesu. Dije ce ta kasa hakuri tace mata me take yi da daurin kirji ta fada mata bata ga mukulli bane.

“Kin tambayi Salame?”

“Ta fita”

“Taje gidan uban wa?” suka ji Malamijo ya daga murya yana fada.

Tsoro taji da tasan zai shigo gidan a lokacin bazata fada ba.

Tsawa ya sake yi mata “baki da baki ne?”

Da ya ga bata da niyyar amsawa saboda rashin sani da kuma kokarin rufa mata asiri sai ya mayar da akalar tambayar ga Dije.

Hannuwa ta yarfe “ina dakina ina zan sani, dama tunda yaron nan mai kudi ya fara zuwa daga birni naga take takenta so take tafi karfin kowa”

“Babu mai fin karfina a gidan nan, idan ta dawo a turo min ita inji da izinin wa ta fita”

Zai shiga dakinsa Mairama tayi saurin dauko masa kilishin “Malamijo gashi yace na baka”

Ledar ya karba da sauri yana lekawa. Ganin kilishi yayi gari guda ya soma dariya “soja yazo kenan Mairama”

Kanta ta kawar gefe tana murmushi ya bantaro mai dan girma kamar tafin hannunsa ya mika mata

“gashi kema ki taba, ko ya baki?”

Sai da ta karba din tace masa nasa ne kawai. Dije tuni yawu ya tsinke tayi kasake tana jiran ya bata amma sai ta ga bashi da niyya.

“Bani nawa mana zan fara aikin tuwo ne”

Harararta yayi yana kanne ido “iyayen kwadayi ungo kafin a tara min taragutsan nan su fara min kallon nama”

Wani dan guntu ya bata ta jefa a baki a kan idon Hajjo. Fitowa tayi itama tana bata rai “ko a bani ko na gayyato jama’ar gidan nan”

Bashi da zabi haka ya dangwara mata a tafin hannunta. Jefashi tayi duka a baki sannan ta daga murya tace kowa ya fito Malamijo yana rabon kilishi.

Ai kan kace kwabo sun soma taruwa mutum kadan ne basa nan. Malamijo kamar ya hadiyi zuciya haka ya rinka yafita musu yana badawa ba da zuciya daya ba.
Chapter 7 · 0% Book details