← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 157

Sashe 41

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ido daya ta karkace kai tana kallonsa "hmmm na gane wato ka gaji dani ko? Nasan komai idan ana yi min irin haka saurin fahimta nake yi. Kora da hali kake min irin na Ummi idan ta gani da hirata"

Hannu ya daga yana bata hakuri "ba haka nake nufi ba, yadda kike so haka za'ayi. A lokacin kowa ma sai a cire minti daya da rabi in kara miki"

Murmushi ta saki tayi masa gwalo "na maka wayau"

Girgiza kai kawai yayi yana jin nishadi da farinciki suna ratsa shi.

**********

Malamijo ke zaune a tsakar dakinsa akan filo yana sharba gumi. Zafi ya ishe shi daga shi sai dogon wando Hajjo da tayi karkon zama kamar Yadikko saboda bakinta dake kwatarta a wurinsa tana masa firfita.

"Ya kamata kaje asibiti fa, ka kwana ka tashi da abu daya ba'a zauna a gida ba" 

Daure fuska yayi ga azaba ta ishe shi da kyar yake magana "zaki biya min kudin asibitin ne?"

"Lallai ma Malamijo, to don Allah zauna kada kaje ka gani idan zan damu. Ka bar kudin kar ka tabasu idan ciwo ya karasa ka a raba mana gado. Nasan a lalace idan ban saka dogon buri ba zan tashi da a kalla shanu uku manya."

Ido ya ware yana jin kamar ya shakota amma jikinsa babu kwari. Ta turo dankwali gaba tana lissafi da yatsunta "kaga mafi girma a ciki in sa a danne a yanka min. In soya, in gasa, inyi miya. Kai har tafasasshe sai naci. Sauran biyun kuma in sayar nayi sababbin dinkuna kafin Allah Ya kawo bazawari"

"Mmmugguwa, saaai kin riga..rigani mutuwa"

"A hakan, karmai-kamai da kai kamar kazar mayu?"

"Akwai mayyyyyyar da ta wuccceki ne?" Yace yana cije lebe.

Yadikko ta dago labule ta shigo fuskarta da damuwa "Malamijo anya zaku cigaba da zaman nan kuwa haka? Use da Asabe fa suma irin lalurarka ta same su. Asabe sai kuka take da kyar na bata hakuri na fito"

Hajjo na jin haka ta tashi da sauri "Yadikko kice ciwon na ango ne da amarensa. Wannan abu shi ake kira guzurin masoya. To ni nayi nan. Kayan lefen can da aka gama gani zan je in killace kada ayi sibare inzo banci nanin ba nanin ta cinyeni ace don ba ni na haifesu ba ina musu bakinciki na bari an kwashe musu kaya"

Fita tayi tana rangaji da dariyar mugunta. Malamijo da amarensa duka sun kasa fitsari. Duka duka Asabe watanta uku a gidan ya cike gurbi da Use. Auren sati uku an wayi gari sun kasa fitsari. Shi tun jiya ya fara gashi yace a matse yake amma ko digo ya kasa yi.

Bata gama gyara kayan ba Yadikko ta shigo babu walwala a fuskarta saboda yadda ta kula yana jin jiki.

"Hajjo me ya kamata ayi ne, rashin fitsarin nan fa ba karamin abu bane. Malamijo sai zufa yaje yi yana numfarfashi"

"Sai kiyi ta damun kanki Yadikko. Akan me? Nan yayi auren nan fa ya soma mana wulakancin da ya saba. Saboda alhaki kwikuyo ne da yace mu dena girki wai ya bamu hutu kannenmu suyi ai ga sakamako nan ya samo. Banda kwadayi irin na namiji yaran da basu fi yayi jikoki dasu ba wai sune kannenmu"

"To dai a bar tone-tone mu kira su Habu yazo ko da motar da yake haya ne a kaisu asibiti. Zan tura a fadawa Salame ke kuma  ki kira Innawuro ta fadawa Mairama itama su zo babansu ba lafiya sannan ga karbar lefe ma da basu san anyi ba"

Ido Hajjo ta zaro "Ni shegiya inji dan daudu, da wane bakin zan fada musu mahaifinsu ya kamu da tagomashin soyayya? Kyaleni naji da aike gidan waccan mara mutumcin Salame. Amma Mairama ai akwai kunya taakaninmu, yarinyar mutumcinta yasa yanzu kunyarta ma nake ji"

"Meye kuma tagomashin soyayya ni Yadikko?"

"Sunan da ya dace da ciwon nasu kenan ai"

Yadikko ma dariya ce ta kama ta. Sai yamma aka samu biyu cikin mazan gidan suka dawo. Dama daga Mairama sai taron maza. Matan da suka taso kuma halin Malamijo ke korar musu manema. To yanzu anyi sa'a mutum hudu cikinsu abin yazo tare. An aikawa Salame dan aiken ko kallo bai isheta ba kamar ba kaninta ba. Mairama kuma Bature ne ya kira lambar Baffa Habubakari ya fada masa. A daren ya nemi layin Major ya sanar dashi cewa a fada mata.

**********

Hankalin Mairama ya tashi duk da bata san me ya sami Malamijo ba amma tunda aka fada mata tana ganin ba karamin abu bane. Major ya tsara musu tafiya washegari ganin duk ta tashi hankalinta. Dama motocin da yayi order biyu an riga an kawo su. Daya domin bukatarsa dayar kuma saboda Mami da kuma kai Zayyana makaranta da suke jiran a koma hutu ta fara SS1 sabon zangon karatu mai kamawa.

Jibi zai tafi Sakkwato kaninsa zaiyi masa rakiya su kuma yace washegari su tafi sai su tsaya a Kano su dauki yaran.

"Amma ina ganin motar zata yi muku kadan. Bus din da aka kai Awwab Kano kuma yace gobe zasu dawo. Dreban ya kamata ya huta haka shiyasa ba zan ce ya kwashe su ba"

"Awwab ya tuka ba sai ya bimu a baya ba" Mami tace su kuma dan gidan Hussainarta Abdallah ne zai tuka su.

"Bana son tukin Awwab a babbar hanya gudun nan nasa kamar yana iska".

Mairama ta fara musu godiya sannan tace "da kun barshi Daddy a hakan ma nagode sosai wallahi. Ba sai an sake wata wahalar daukarsu ba. Shima Awwab din yana bukatar hutu"

Mami ce mai kwantar mata da hankali tace "haba Ummin Awwab ki bar wannan godiyar mu dake duka daya ne. Babu matsala in sha Allah" 

Babban abinda zai kai Major wanda zasu hadu da Baffa Gide a Sakkwaton shine binciken dangin Zayyan na Nijar. Idan da gaske rashin idonsa a duniya yasa suka zare hannunsu daga kan iyalinsa ko kuma su ma karya Maikudi ya shara musu duk zai jiyo. Shi kanshi sojan da yake tura kudin zai baro bakin aikinsa ya taho don ransa ya baci fiye da ba Major akan rainin hankalin da Maikudi yayi masa. Idonsa idon Maikudi kawai yake jira.

**********

Tun dare anyiwa Zainab waya game da zuwa Sumaila duba Malamijo. Ita bazata sami zuwa ba saboda Hadir gashi asibiti zasu koma. Tunda ba kwana zasuyi ba Mairama da su Radhiya ne kadai zasu kwana sai ta yiwa Ibrahim izinin fita duk da shine karfin taimaka mata akan babansa sai Emzee da yake taya shi sosai.

"Yaya zakiyi da Baba"  ya fara cewa da tace yaje.

"Gara na fara sabawa, daga kai har Karami WEAC dinku ake jira a nema muku admission. In kana makaranta zanyi ta jiranka ne?"

Godiya yayi mata don yana son bin 'yan uwansa amma baya son kwana saboda kada aikin yayi mata yawa.

Dakin da aka sauki dreban gidansu Ghazalatu yaje ya tarar da Awwab ya karbi mukullin motar. Kudin mota da Zainab ta bayar a kai masa da zai koma Katsina yaje kai masa. Iyalan gidan su ma duka sati mai zuwa zasu taho Katsinan saboda bikin da yake na gida duka a garesu.

Shi kadai ya koma ciki Awwab ya zauna akan dan ginin da ya zagaye flowers din da aka shuka daga jikin bangon gidan. Waya yake son yi da Ghazalatu yau tun da ya taho tana fushi basu sake magana ba.

Da sauri ta dauka da ya kira sai kuma tayi shiru don ta nuna masa fushinta na kin kiranta da wuri.

"My G fushin ne ya tashi?" Nishadi yake ji sosai yadda suka rinka hira da Alheran kamar basu rabu ba. Kusan komai na rayuwarta da zata iya tunawa ta fada masa sai yake ga kamar a gabansa ta tashi. 

"Idan nayi magana kace na fiye kishi ko korafi. Tun yaushe ka isa amma ko text ban samu ba talkless of waya."

Sai yaji babu dadi don ya sani bai kyauta mata ba. Hakuri ya bata don bashi da girman kai ko kadan. Yayi mata laifi dole ya kwantar da kai ya rarrasheta. Kusan wayar minti talatin suka yi sai da yaji ana masa warning na karewar credit.

"Zan kiraki gobe in sha Allah, zamu je duba baban Ummi a garinsu. Dawowarmu sai wurin jibi kenan dasu Mami"

"Mami ba tana gida ba?"

"Zasu taho da Ummina gobe sai mu wuce tare"

"Yayana kace mata zani please. Da saasafe sai na koma gidan mu taho tare"

Yaji dadi sosai saboda shima ya soma kewarta. Suna gama wayar yace ta kira Mami din credit dinsa ya kare. Ta kirata ta wayance da cewa wurinsu Zahra take son zuwa. Mami tace to ta zauna su zasu biyo su dauketa.

Falon ya koma ya same su kowa na  cin abincin dare banda Radhiya da tasa plate a gaba tana kallonsu.

Akan doguwar kujera ya zauna ya kwantar da kansa baya. Alamun idanu yaji a kansa ya dago. Ai kuwa duka shi suke kallo har Radhiya

"What?" Yace yana kallon kansa.

Fauziyya ta nuna masa plate din gaban Radhiya. Taliya ce fara da sauce din ganyen alayyahu da ugu sai balangu mai dan karen dadi da Ibrahim da Emzee suka siyo. Dama yanzu sune 'yan zuwa aike.

"Me ya sami abincin Alheran?"

Kunya taji ta kasa fada masa bayan cika bakin da ta gama. Zayyana kuwa tace "kowa shaida ne Adda Radhiya zaki min gyaran akwatina tunda kin kasa"

"Dama akwai abinda zaki kasa?" Yayi tambayar yana kallonta.

Ta dai yi saranda inji bature kaudin nata bai kai nan ba ashe ta gama cika baki. Tana ganinsa taji ko da wasa bazata iya fada masa zaman me take yi ba.

"Emzee me ya kama bakin yayarka ne ta kasa magana?"

"Babu ruwana ni dai" ya cigaba da cin abincinsa yana murmushi.

"Ni bari na fada maka Hamma" Ibrahim yace yana kallo Radhiya ta daure fuska "Zayyana tace kafi sonta shine Radhiya tace don bata nan ne dama. To shine Zayyana tace mata ita fa ko me take so kana yi mata. Idan kana gida hatta abinci tare kuke ci. Shine Radhiya tace wai wannan na gaban nata kaine kace ta zuba muku tare kafin ka shigo. Betting su ka yi"
Chapter 41 · 0% Book details