← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 157

Sashe 76

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan cije lebenta tayi tana tuno wani lokaci da abu makamancin haka ya taba faruwa dasu a Kano da Sumaila. Tana ji a jikinta ma mutanen falon kallonsu suke yi sai kawai ta dake ta karba. Idan bata basar ba zato zaiyi ta wani damu dashi ne har yanzu. Diban abincin tayi ta saka a bakinta cike da kunya. Kafin ta mika masa ya zura hannu ya sake karba ya ci sannan ya bata. Falon kamar anyi ruwa an dauke. Ita ta kasa kallon gefen da sauran suke shi kuma nasa idanun a kanta suke ba ma kallon plate din gabansa yake yi sosai ba. Yousuf yana ganin wannan abu yaji wani daci daci na taso masa dole ya tashi ya koma dakin Emzee. Awwab yayi wani murmushin gefen baki. Shi kuwa tunani yake wai dama Hamma din da take fada saurayinta ne ko me? Anya shakuwa zata sa Alheran cin abinci plate daya dashi kuwa? Ko da wasa duk zamansu bata taba kwatantawa ba. 

Sun cinye abincin dama ba wani yawa ne dashi ba Awwab ya janyo flask din "in kara miki?" Yace yana kallon zoben nan da ya bata har yanzu yana yatsanta

To a gaskiya ba koshi tayi ba ta langabe kai har yanzu taki yarda su hada ido "kadan"

Zubawa ta ga yana yi fiye da yadda take bukata ta kuma dago kai tana ware masa idanu "its ok"

Sai da ya zuba wanda yake ji zai ishesu su biyun ya sake mika mata spoon din taci ta bashi. Da za'a ce mata kyat a guje zata bar wurin saboda kunyar da take ji amma ita a dole sai ta basar kada ya rainata. Shi kam rabonsa da jin nishadi irin na yau ya manta. Ya kasa dena kallonta kamar ba Alheran dinsa ba. Tayi masa kyau sosai ga wata zazzafar soyayyarta tana fizgarsa kamar yadda ya kamu da sonta farkon haduwarsu. Ba don abinda tayi masa ba da yanzu kila suna da yara kamar nasu Zahra. Ba komai ya kawo shi gidan Ummi ba a lokacin sai zuwansa wurin Mama suka shigo da Tante Nasara. Mama da gayya ta dauko zancen Yousuf saboda yaji. Ai kuwa ta tayar masa da hankali.

"Haj Nasara wato kin mana kwacen 'ya sai munyi da gaske muke ganinta"

Dariya tayi tace "kuma ko na tafi wallahi a bar min yarinya ta sake. Ni da Yousuf duk mun shagwabata. Idan naji ba daidai ba ke zan fara kamawa"

"Bama zaki ji komai ba. Yaron nan naki akwai nutsuwa Nasara. Naji kamar Radhiya tace likita ne ko?"

Gaban Awwab sai da yayi wata rawa kamar ance masa anyi auren Radhiya ne. Likita??? Alheran da shegen son likitoci shikenan Ummi ta cuce shi wallahi. Wa ya sani ma ko sun fara soyayya an barshi a nan akan su Ghazalatu. Bai ko zauna ba ya wuce gidan Ummin sai yayi sa'ar ganin Yousuf din shine ya tsiri cin abinci tare da ita.

Juice din kankana mai sanyi ta zuba a glass cup bayan sun gama ci ta kurba sau biyu ta ajiye masa a kusa da hannunsa ta mike abinta ta koma wurinsu Zahra. Daukar cup din yayi ya shanye ya yi hanyar kofa tare da kiran Zayyana wai zai bata sako.

Wani shu'umin murmushi takeyi na abinda ta gama gani wanda dole ma ta labartawa 'yan uwanta Emzee da Ibrahim amma suna hada ido da ta ga kallon da yayi mata ta gyara fuskarta.

Radhiya na jin karar rufewar kofar ta tashi da sauri tana dafe kirji.

"Kuturin bala'i...wai... kunji kirjina kuwa? Har wani zazzabi zazzabi ne ya kamani fa" 

Zahra da Fauziyya suka kwashe da dariya harda kyakyatawa. Fauziyya ta karkace kai tana kallonta a tsaye hannuwa a kirji tace "shegiya Radhiya ashe kina nan baki mutu ba"

"Lallai ma Adda to wace wannan a gabanki?"

"Nufina Radhiyanmu dai mai balotelli ashe tana nan kin boyeta."

Dariya suke sosai su ukun Zahra tace "Fauziyya auren bakatsine ya koya miki zagi"

Juya idanu tayi tana dariya "Ke Radhiya auren Katsinawa akwai riba wallahi ku dena gulmar nan haka don naga take taken Hamma wata rana sai yayi hugging dinki a gaban mutane"

Kunya taji harda dora hannu a ka "haka kika koma maman Jawad?"

"Gaskiya ta fada miki ai, ni da wannan spoon exchange din da aure kuka yi kawai sai ayi wacce za'ayi ko Fauzi"

"Na shiga uku zasu bata yarinya" Radhiya tace tana dariya sosai.

"Wallahi balotelli na nan ashe kike disguising dinta da wannan hot chick din"

"Kinsan Allah Radhiya ki hana Hamma zaman lafiya...yarinya kill him with love sai ya dawo yana baki hakurin wannan fushin nasa mara dalili" cewar Fauziyya.

"Ni dai kiyi masa a hankali amma bance a sassauta ba" Zahra ta kawo tata shawarar.

"Ance muku son sa nake yi ne?" Ta basu amsa tana dage gira.

Fauziyya tace "Eh to gaskiya baki ce ba. Na fuskanci shi da Arifah kamar akwai wata a kasa don yarinyar tayi 100%. Kamar ance zata zo kuwa gobe zanyi kana confirming meye tsakaninsu"

Nan da nan fuskar Radhiya ta chanja  tana jin dan mutumcin da suka fara da Arifan ta waya yazo karshe. Zahra da Fauziyya sunyi dariya son ransu bayan ta fice zuwa gidan Mama.

**********

Washegari tsabar gajiya kasa tashi sukayi da wuri gashi sun raba dare suna hira. Ummi bata sauraresu ba ta shiga kitchen tare da Tante Nasara da ta biyota itama ta tashi da wurin. Cikinsu Fauziyya ce ta fara tashi taje ta karbi aikin kusan komai ita ta karasa shi kafin Ummi ta dawo daga yiwa Daadaa wanka don Radhiya ta lakaba masa daga zuwanta tace ita bata yarda a kira mata sunan baba ba.

Goma saura kowa ya tashi banda Radhiya. Tafi sati bata baccin kirki kullum yawon tsaraba da kuma kammala shirye shiryen project din ga tafiya a gabanta. Ummi tayi magana Tante tace a kyaleta ta gaji ne.

Sai shadaya ta tashi babu kowa a dakin. Wanka tayi ta gyara gadon sannan ta shirya cikin atampa blue da baki riga da zani wrapper. Tayi missing irinsu don bata cika sakawa ba a France. Ta gama daurinta mai kyau ta tuna ba zama zata yi ba sai kawai ta tuge shi ta tafi dakin Ummi. A can ta sami bakin mayafi mara nauyi ta yafa ta sake gyara fuskarta ta fito falo. Nan ma shiru, tana son magana da Yousuf amma bashi da sim din Nigeria. Ba ya nan yana wurinsu Awwab da Raji duk sun hadu dasu Daddy da Baba Hadir ana hira a gidan Mami.

Tasan basa wuce gidan Mama shiyasa ta tafi can. Ko neman abinci bata yi ba ta gaishe da iyayen nasu itama ta zauma zaman hira. Daadaa ta dauka ta shagala da yi masa wasa sai hamma yake.

"Kawo shi na goya shi bacci yake ji tunda akayi wanka bai koma ba" Ummi ta mika hannu za ta karbe shi.

"Don Allah goya min Ummi" tace tana ajiye mayafinta a gefe ta duka baya.

Ummi ta gyara tsayuwa "me? Rufa min asiri indai goyon ne ga masu karfi nan ki dauka"

"Tante" tace tana tura baki.

"Don Allah goya mata mana Mairama"

"Nasan halinta sarai. Dama can ba wani iya raino tayi ba bare yanzu da ta dade babu wani yaro a inda take. Da dai girki ne sai na sakar mata"

Zahra tace "Ummi ni zan bada labari. Cewa take fa na zunguri Femi don kawai taji muryarsa"

Dariya suke ta yi mata Tante na tarewa. Mama ma dai sai ta goyi baya "idan bata koya ba yanzu ba sai yaushe ni da nake fatan kafin shekara ta zagayo mun rike sabon jika"

"Yauwa Mama" tace tana murmushi ta sake dukawa.

Ummi tace babu ruwanta Mami ce ta goya mata shi aka daure shi sosai don Radhiya kam bata iya goyo ba. Ana goya mata shi kuwa ta mayar da mayafinta aka bude fuskarsa. Zama tayi akan kujera ko motsi bata son yi tana tsoron kada goyon ya kwance ya fadi. Tashi su Fauziyya suka yi zasu je suyi wanka Ummi tace bayan azahar su hadu duka da yaransu Awwab ya kaisu gidan Daddy Haroun su gaishe su. Bashi da labarin fitar tace Zayyana ta turo shi don tasan a waya bazaiyi yadda take so ba.

Can ya baro sauran mazan ya shigo falon da sallamar da ta tsinka zuciyar Radhiya.

Dauke kai tayi tana wasa da wayar hannunta ya shigo yana kamshi ya tsaya a bayan kujerar da take zaune. Na shiga uku tace a ranta tana jin kusancin dake tsakaninsu yana affecting dinta. Rikicewa tayi sosai amma bata so ta nuna shiyasa taki yarda ta dago kanta.

"Ummi gani"

"So nake bayan azahar ka hada kan kannenka ku je gidan mamanku Gambo ku gaishe su. Ga Raji da Yousuf ma duk ku tafi tare"

Shiru yayi amma yasan yanzun nan sai ta fara fada idan yaki amincewa ga mutane a wurin "to Ummi"

"Radhiya kun gaisa da yayanki ne?" Mama tace saboda dazu ya shigo sauran duka sun gaishe shi.

"Ina kwana" tace a hankali ko shi da yake bayanta baiji sosai ba. Kin amsawa yayi tunda dama baiji me tace da kyau ba.

"Nasara muje ki huta ko kin tashi da wuri ga gajiyar tafiya" Ummi tace suka tashi tare sai Mami da Mama. 

Mami ma sai tace zata tafi gida a turo mata Zayyana ta tayata girkin rana. Yana kallonsu duka suka fice Mama ma ciki tayi abinta dama duk hanyar barinsu tare nemanta take yi.

Dukuwa yayi da kansa gefen fuskarta taji tsigar jikinta na tashi abinda shi yaji fiye da haka "kin dena gaisuwa ne?" Taji yace muryarsa na dukan dodon kunnenta.

Muryarta ta sake ragewa tace "na gaisheka fa" 

"Sai a sake tunda banji ba"

Humm'umm bai san itama taci ganye bane yanzu ko. Kin magana tayi yana nan tsaye a bayanta har lokacin har ya soma amsa wayar Arifah tana masa barka da dawowa da sanar dashi zasu shigo gari da Mamanta kafin suna.
Chapter 76 · 0% Book details