Sashe 111
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Harda masu ihun murna cikin kannen saboda tuni ta fara janyosu a jiki tun bayan yadda ta sake ganin rigimar Mami da kannenta.
Kallo na bakinciki da hassada Salame take wurga mata. Mairama dai atampa ta saka super itama amma duka wurin babu wanda ya kama kamar kyaun da suka yi ita da Radhiya. Fatar jiki ta nuna hutu da jindadi gami da kwanciyar hankali.
Radhiya ta tashi ta fadi sunanta itama sannan tace akwai kaninta yana makaranta bai sami zuwa ba. A sanyaye take magana saboda hawayen da take gani Rahima na zubarwa a boye. Komawa tayi ta zauna ta kama hannun Rahiman guda daya ta rike amma bata ce mata komai ba sai ma matsawa da tayi jikinta ta saka daya hannunta ta dan rungumota a jiki. Sai da tayi mai isarta a hankali nutsuwa ta rinka zuwar mata ta dago jajayen idanu ta kalli Radhiya.
"Abu ne ya fada min a ido fa kada ki zata kuka nayi"
"Mai karya" Radhiya tace tana kada kai.
"Ai dai baki ji na rantse ba"
Murmushi suka yi wa juna Radhiya taji kanwarta ta ta shiga ranta yayin da take tunanin hanyar da zata bi ta kartawa Gwaggo Salame rashin m ko dan kadan ne taji idan da dadi gwasale mutum a bainar jama'a.[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Sai da kowa ya gabatar da kansa aka kare akan jarirai Hassana da Usaina. Malamijo ya gyara babbar rigarsa yana kallonsu wai gabadaya tsatsonsa ne wannan. Bai taba tsayawa ya duba wannan babbar baiwa da Allah Yayi masa ta 'ya'ya ba. Kafin yanzu kallon nauyi da matsala kawai yake yi musu yana ganin matan da yake aura basa kyauta masa kowacce tana zuwa sai ciki. Babu wanda bai tara ba cikinsu da nagari da shakiyai. Akwai nutsatstsu ga kuma fitinannu. Biyu ma dai cikinsu kauraye ne 'yan chau-chau. Malamijo ya kusa shekara bai sasu a idanunsa ba kuma bai damu ba saboda sunfi zama a gidan kakaninsu na wurin uwa tunda babarsu daya. A can suka koma kaurayen saboda 'yan uwan babar tasu irin mafarautan nan ne masu yawo da karnuka. Ba'a tsaya nan ba duka dai cikin yaran nasa akwai rikakken dan jagaliyar siyasa wanda yayi suna akan rashin mutumci indai aka taba 'yan jama'iyyarsu. Ga dreban adaidaita sahu da karamin dan sanda mai mukamin kofur. Ga Mal Ayuba mafi rikon addinin cikinsu. Akwai mai sayar da kayan fruits a wheelbaro a cikin Kano. Bature shi da yake yayi NCE koyarwa yake yi, Habu kuma yana sayar da kayan masarufi. 'Ya'yan dai sai son barka kowa da inda yafi kauri.
A bangaren matan ma dai babu wata mai ilimin da ya wuce secondary sai Mairama da ta koma lokaci daya da 'ya'yanta. Da yawansu basu gama makaranta ba. Na gidan mijin kalilan ne ga zaurawa biyu. Akwai uku marasa jin magana daya saurayinta dan daba, biyun kuwa samari ke daukar nauyinsu. Ba dai yawon ta zubar suke yi ba amma ana kanwar ta zubar din kai na hayaki suna jinsu daidai da kowa.
Abinda Mal Ali Gidado Malamijon Sumaila bai saba ba kuma bai taba tunanin zaiyi ba ne yayi masa bazata. Hawaye ne masu zafi yake fitarwa saboda tun bayan wata nasiha mai nauyi da Ayuba ya cire kunyar mahaifinsa yayi masa jikinsa ya mutu murus. Duk wata guntuwar hayaniya sai ta dauke wurin yayi shiru. Mairama da bata hada son Malamijo da komai duk halinsa kuwa sai kuka.
Salame ta kalleta shekeke ta tabe baki "sabon salo"
Gyaran murya Malamijo yayi ya gama karya zukatan matansa musamman masoyiya Hajjo da Nene wadda yace dole tazo 'ya'ya nata ne itama "abinda zan fada muku ba yawa ne dashi ba, don Allah ku yafewa min"
Yaran nasa ma sai gashi daidai da daidai matan nan suna yarfe kwalla da wannan kalami nasa.
"Babu wani abu da nayi muku wanda zan bugi kirji dashi a gaban Allah game da rike amanarku. Haka Ayuba yace min jiya ko ba haka ba...Aradun Allah kasa bacci nayi duk ya tsoratani"
Wasu na dariya wasu na murmushi saboda yadda yake maganar bai dauketa da wasa ba.
"Nayi alkawari zan gyara sha Allahu kafin na mutu zanyi kokarin gyara laifina."
Radhiya don ta rage musu nauyin da ya saka musu a zuci ta dauko zancen da tasan baya so "dama ana cewa siituna aw saba'una tafiya tayi nisa"
"Don kaniyarki shekarata hamsin da bakwai watan azumin tsofaffi zanyi da takwas" yace fuska a tamke don yaki jinin zancen mutuwa.
Gabadaya wurin ya kaure da dariya da mugun tsakin da Salame take saki. Sarai Malamijo yaji kuma ya kudiri niyar saitawa 'yar tasa zama. Nasihar hadin kai ya dora musu da ita sai gashi sannu a hankali wadanda basu magana a da ko dai don rashin jituwa ko don rashin sabo da juna hira ta fara barkewa a tsakaninsu. Abinda Malamijo bai sani ba shine gabadaya 'ya'yan nasa ba kin junansu suke yi ba rashin tsayuwar uba a rayuwarsu ita ce babbar nakasun da suke fama da ita. Yau gashi zaune dasu babu hantara babu zagi kowa ransa wasai. Yadikko ganin haka tace me zai hana suna cin abinci yaran na zuwa gareshi yaji me kowa yake yi kuma ya bincike matsalolinsu. Abin yayi masa dadi matan cikinsu masu kuruciya suka tashi aka zubo abinci ga nama shar dasu. Hayaniya kuwa sai da Radhiya ta kira Emzee tace tana ta tausayinsa saboda yayi missing. Sun dan taba hira ta ajiye wayar.
Rahima ta kalleta a kunyace saboda ganin kanta take wata muguwar local akan Radhiyan tace "shine kanin naki da kika ce yana makaranta?"
"Eh bari ki ga hotonsa saboda kada ku hadu baku san juna ba" tace tana binciko mata hotonsa a wayarta. Wanda yake sanye da khakinsa yayi wani kyau ta nuna mata.
Shiru Rahima tayi tana kare masa kallo lokaci guda taji wata irin kunya saboda wani kallon kasa-kasa da Radhiya take yi mata "kema sojoji suna burgeki ko?"
"Uhm ni dai tsoronsu nake ji"
"Kice dai irin halin Fulanin zaki yi na tsoron duk mai uniform"
Dariya suka yi tare wata yarinya da bata fi shekara goma ba ta kawo musu tray shakare da shinkafa dafaduka taji kayan lambu tayi kyau. Karamar uwa ce dai tunda 'yar Malamijo ce suka karba su hudu da wasu matan kusan sa'annin Rahima duka 'ya'yan gidan suka fara ci. Radhiya duka burgesu take yi kana ganinta kaga wayayyiyar 'yar boko ga gayu amma da ta shiga cikinsu ajiye komai take yi ta koma daidai dasu kamar yadda Umminta take yi.
Abinci suka fara ci sauran matan suna yiwa Rahima korafin tana cikin garin amma bata son zuwa gidan duk ba'a saba da ita ba.
Murmushi tayi kanta a kasa ita kowa ma kunyarsa take ji "Zan rinka zuwa yanzu sai kun koreni"
Daga sama suka ji muryar Salame babu wanda ya kula da zuwanta sai hannunta da ta kama kunnen Rahima dashi da karfi "gani nazo tunda ke baki da hankalin idan kin shigo ki zo ki nemi uwarki ki gaisheta"
Kunnen zugi yake kamar zai tsinke ta soma hawaye idanu sun fara dawowa kansu anata bata hakuri ta wani hade rai ita me 'ya.
"Umma kiyi hakuri a makare nazo kuma bana son tsallake mutane na ga kinyi nisa"
"Tunda an samo abinda babu a gidan tsoho ai dole kice nayi nisa. Maza kici ki tashi ki koma"
"Umma!" Halifa yace a zafafe yana tahowa wurin ransa yayi mugun baci.
Kafin ya iso Mairama ta fizgo hannun Salame wadda bata sassauta rikon kunnen Rahiman ba sai da ta saki wata wahalalliyar kara.
"Ke wuce da ita dakin Yadikko ina zuwa" ta umarci Radhiya kafin ta finciki hannun Salame zuwa bangaren samarin gidan daga can gefe.
Kwace hannunta Salame tayi tana furzar da yawu da hura hanci. Maganar da zata yi ce ta makale saboda ido da suka hada da Mairama.
Borin kunya duk ya kama ta tace "ni kike yiwa wannan kallon Mairama?"
"Nayi miki Adda ko zaki dauki mataki ne?".
Bata ce komai ba ran Mairama a sama don zuciyarta wani irin tafasar bacin rai take yi saboda abinda Salame take yi. Ta gama kunyata kanta cikin kannenta sannan tazo ta matsantawa yarinya.
"Hantara ko kadan bata da dadi ya kamata ace ke da kika girma a gidan nan ki fi kowa dorarwa amma shine tun dazu kin saka yarinya a gaba kuma a cikin mutane. Ko me tayi miki ki bari ku kebe mana. Su wadanda kike fifitawar ai ba finta suka yi ba tunda yadda kika haifesu itama haihuwarta kika yi"
Cinya Salame ta buga "dadin abin dai baki isa ki fada min dadin haihuwarta ta ba bare kice ina cusgunawa 'yar wani. Ban shiga sabgar iyalinki ba kema ki tsame hannunki akan nawa. Halifa ma da kike wani jansa a jiki wallahi na hana daga yau a kyale min kayana"
"Nan kuma baki isa ba. Idan kinsa karfi kin shiga tsakanin zumuncinmu bazan yarda da na 'ya'ya ba."
"Mairama" tace da sigar warning tana kada yatsa "kada ki kaini bango"
"Allah Ya ganar dake don ban ga amfanin magana dake ba" Mairama tace tana juyawa.
Yadikko suka gani a gefensu "ke da nake yiwa kallon mai hankalin kuma ashe biye mata kika yi zakuyi rigima Mairama? Wai me ya sameku ne ku da kowa yasan kanku a hade yake kamar tagwaye"
Tsaki Salame ta buga tayi gaba tana harare harare. Yadikko da take matsayin uwa a garesu a gidan abin yayi mata zafi sai Mairama ke bata hakuri.
A can dakin da Radhiya ta kai Rahima kuwa yarinyar kuka take yi sosai abin tausayi. Radhiya taji wani irin haushin Gwaggon tasu ya dada shigarta. Maganar da Rahima tayi mata ne ya sake karyar mata da zuciya ita da Halifa da ya biyo su dakin.
"Me na yiwa Umma ta tsaneni? Don Allah ku tayani bata hakuri"