← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 157

Sashe 64

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Meye matsayina a gareki?" Mairama tace babu alamun wasa da ta bari a fuskarta duk kuwa da cewa abinda take niyar yi tamkar ana yankar zuciyarta ne. Iyalin Major Mustapha wani bangare ne na rayuwarsu da bazata taba mantawa da alkhairinsu ba. Daga dawowarsu sai fadi tashi yake a kansu musamman na hadasu da danginsu da yayi.

"Babata ce" cewar Radhiya gabanta na sake faduwa.

"Daga yau babu ke babu Awwab kina jina?" A gigice Radhiya ta dago kai Ummi ta cigaba da magana nata hawayen na zuba "bani ba ko mahaifinki bana jin akwai mutumin da zaiso bawa aurenki sama da Awwab amma daga ke har shi farincikinku yayi kadan ya haddasa husuma a tsakanin iyaye. Saboda soyayyarku Mami yau ta daga hannu ta mari kanwarta. Zaman da nayi dasu na kwanaki da kuna Kano babu ranar da Mami bazata ce Gambo ba saboda yadda take sonta ta amma yau akanki ta mareta"

Jiki na rawa Radhiya tace "Ummi kada ki rabani da Hamma don Allah. Ummi tunda na fada da bakina wallahi kinsan ina son shi....Ummi don Allah"

"Kina sha'awar aure a dangin da basa sonki? Ko an fada miki idan kika aure shi daga ke sai shi sai iyayensa? Bazaki yi mu'amala da sauran 'yan uwansa bane?"

Shiru tayi babu amsa sai kukan da take yi mai sauti tana gurfane a gaban mahaifiyarta.

"Gata nake son yi muku ke dashi. Aurenku a yanzu babu abinda zai kawo sai tashin hankali da rabuwar zumunci. Mu da muka tashi da karancin dangi ai kinga yadda abubuwa suka kasance mana kafin zuwansu Innawuro ko? Kina sha'awar ki mutu a rasa mai kula da 'ya'yanki saboda kiyayyar da ake yi miki ne?"

"A'a"

"Alheran Daddynku Major da Mami da 'ya'yansu duka suna son mu suna mutuntamu. Sakayyar da zamu yi musu kenan mu rabasu da da nasu 'yan uwan? Kina ganin zaki taba yafewa wata mace ta gida ko bare da zata yi kokarin rabaki da Karami misali? Ki tayani sakawa su Mami da alkhairi na tabbatar miki wallahi Allah bazai bari ki wulakanta ba. Ki taimaka kada ki zama sanadin datse igiyar zumunci ki gani idan Allah bai saka miki da alkhairi ba. Ana barin halal ko don kunya kinji. Kin girma ke ba wannan karamar yarinyar bace da take fita ayi dambe da ita. Kece kike da burin yin abin alkhairi domin a nuna ki ace 'yar Zayyan Tureta ce ga dama ta samu gareki."

Babu abinda Ummi ta fada mata wanda ba gaskiya ba. Baza ta taba yarda ta batawa Umminta ba bayan wahalar da tasha akansu kuma ta sani cewa rabuwarsu zata taimaka kwarai wurin daidaita lamura. Tana share hawaye saboda yadda take jin zafin zuciya har dafe kirjinta tayi tace "Ummi to yaya zanyi da son shi?" muryarta can kasa kamar ba Radhiya ba.

Tsantsar tausayi da soyayyar 'ya da uwa suka sa Mairama kuka itama. Rabuwa da masoyi akwai ciwo mai radadi. Bata taba mantawa da Zayyan ba haka nan har yanzu zuciyarta bata rabo da tasowar kunci lokaci zuwa lokaci idan ta tuna sun rabu kenan har abada. Soyayya ciwo ce da bata warkewa sai dai hakuri babu abinda ya bari.

"Kiyi hakuri a hankali zaki rinka jin sauki a zuciyarki. Da kaina zan fada musu cewa ba kya son auren. Ina ganin ma idan munje Nijar din in barki a can har komai ya lafa"

Duka zantukan da suka yi tun shigar Radhiya dakin zuwa yanzu a kunnuwan Umman su Mami ne. Ta taho gidan cikin fushi ne saboda a ganinta Mami ita ke neman raba zumunci tsakanin kannenta. Ko gaisuwar Emzee da Zayyana da suke falon bata amsa ba tace ta nuna mata dakin Mamin batare da ta saurari bayanin da take mata na cewa basa gidan ba. Juyawa tayi ta tafi batare da ta yiwa kowa magana ba.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Awwab yana tunanin yadda zai shiga gidan ya gabatar musu da bakin ga taron mata tun daga waje sai Allah Ya taimake shi ya hango Emzee yana tahowa tare da wasu samari sa'anninsa. Shadda ce a jikinsa light green irin wadda sai ka kula da kyau zaka gane kalarta saboda rashin turuwa da hular zanna bukar saka mai kyau. Yayi aski da gyaran fuska dan gemu da gashin bakin da ya fara tarawa an gyare su fuskarsa ta sake fitowa ga kamannin Zayyan karara. Muhammad Zayyan Tureta kenan yaro matashi da yake ganiyar kuruciya dan kimanin shekara goma sha takwas.

Kayataccen murmushi yayi da ya hango Awwab ya taho wurinsa da sauri.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Zayyan?" Mammee tace muryarta da jikinta na rawa.

"Na'am" yace lokacin da ya juya yana fuskantar mutanen. Idanu suka zuba masa suna mamakin irin wannan kamanni. To ai ko ba'a nemo su ba duk inda suka hado da yaron nan zasu rantse jininsu ne.

Babu wanda ya sani cikinsu amma yadda ya gansu yawanci dattijai ne masu kuruciyar basu da yawa yasa ya rissina da zumar gaishesu wannan mata da ta kira sunansa kanwa ga kakarsa marigayiya Alheran Ghousman ta rungume shi a bainar jama'a tana kuka tare da ambaton sunansa.

"Zayyan, Zayyannn, Zayyan kuyi hakuri"

Mutanen da suke wurin sai suka fara kallonsu. Emzee ya shiga kici kicin kwace jikinsa tana kara nanikarsa. Daga gefe Salame matsowa tayi ta kare musu kallo da kyau. Bata iya ganin fuskar Emzee shiyasa bata san ko waye ba ta kada tawagarta suka shige gidan.

Awwab ne ya riko hannunsa yana yi mata murmushi yaja shi gefe "nayi ta kokarin kiran Ummi ko Alheran bana samu. Daga Nijar suke"

"Da gaske?" Emzee yace yana zaro idanu da mamaki. Da sauri ya shige ciki Awwab yace musu zai je ya sanar da Ummi ne. Duk basu damu ba suka ce zasu jira.

A ciki mata musamman manya ne suke tsokanar Emzee wai ya shigo taron mata. Hankalinsa baya garesu yana ta wurga ido yana neman Umminsa. Radhiya ya hango ta fito daga daki da shadda kalar tasa anyi mata doguwar riga mai karamin hannu da bai kai gwiwar hannunta ba. A Kano akayi musu dinkin Mama ce ta bada. Kamar ba ita ba tayi kwalliya harda janbaki. Dauri akayi mata irin mai hawa hawan nan dayake dankwalin da girma babu mai gane yaya gashin yake. Ta sami mayafi dark green kalar zaren aikin rigar ta yafa ta bayanta iya kafada ya rufe mata hannuwa amma bata hade shi ta gaba ba. Da gudu gudu ta fito daga dakin tana mita saboda Ummi tace mata saura ta bata jikinta. Ta yaya za'ace kada ta bata jiki kamar yarinya. Ummin ta rinka dariya tace ta saba jin suna haka da Innawuro.

"Sai na zata kazama ce"

"Innawuro ai ba sona take ba. Ni da tayi min...."bata iya karasa me zata ce ba ta fito shine suka hadu da Emzee.

"Ina Ummi?"

"Tana ciki"

"Hamma Awwab yana waje" yace da ita tayi hanyar kofar da sauri.

Shiga yayi ya ganta tamkar ba Ummin da ya sani ba. Sanye take da irin kayansu dinkin da komai irin na Radhiya. Bata yi kitso ba amma ta tufke gashin ya wuce kafadarta yana ta kyalli. Mairama tayi matukar kyau babu yadda zaka ce ita ta haife su. Zamansu a ruga babu yunwa babu kishi sai dai kawai rashin wayewa wanda da karfin cin tuwo Mama Zainab take cusa musu. Tsallake matan dake zaune a dakin yayi ya karasa gefenta ya duka ya sanar da ita bakin da suka yi. 

Ummi bata san lokacin da taji kwalla ta taru a idanunta ba. Da gaske Major ya nemo dangin Awwab na Nijar har sun biyosu Sumaila? Da zafin nama ta tashi tunanin me ya kamata ta farayi domin karramasu ya darsu a ranta.

"Su nawa ne?" Ta tambayi Emzee a yayin da take fita daga dakin.

"Wallahi Ummi motocin da yawa"

Tana fita dakin Yadikko tayi inda suke ta fama da baki ciki harda Innawuro da Nene Marka. Sanar musu tayi kowacce ta tashi da sauri aka shiga kiran kannenta masu kuruciya su taho za'a gyara bangaren samari inda babu kowa. Wurin akwai dakuna uku da baranda mai dan girma. A barandar suke tunanin saukesu idan an share. Hajjo, Yadikko, Innawuro da Nene Marka kowa ta bazama ana kokarin hada abinda ya dace. Allah Yasa akwai kofa ta waje da za'a iya shiga wurin ba sai sun shigo cikin turmutsin 'yan biki ba. Sai da Ummi ta ga komai ya fara daukan saiti tace da Emzee yaje yace suyi hakuri tana kokarin samun wurin da za'a saukesu ne saboda 'yan biki gidan a cike yake.

 Ya juya zai tafi fadin sakon sai ga Salame da 'ya'yanta ta rasa dakin wa zata je. Yadikko da Hajjo duka ta leka basa nan. Asabe da Hanne ba saninsu tayi ba kuma ma dai ta rainasu. Bai kula da ita ba ya rabe abinsa ya wuce. Yarinyar da ta yaye ce ta shiga jan zaninta tana kuka tare da nuna wasu yaran da suke cin shinkafa dafaduka.

"Umma umfafa"

"Rufe min baki dalla can za'a zuba muku"

Na biyu a cikinsu shi kuma ya ja hannunta cikin tashin hankalin kuruciya ganin wadda yaran da suke kallo suke ci ta kusa karewa "Umma zasu wawashe bamu samu ba"

Dagewa tayi ta make bakinsa ya sa kuka kuwa da ta ga an fara kallonta ta rage murya "dan ubanka rufe min baki maye"

"Ya zaki kira shi maye? Haba kinsan yara sai hakuri ki zaunar dasu mana a zuba musu abincin"

Ummi Mairama ce tayi maganar saboda zata wuce ta hango Salamen. Wani farinciki taji a ranta duk da rashin jituwar dake tsakaninsu tana kallon yadda 'yar uwarta ta chanja. Rashin lokaci saboda shirin biki da kuma hani daga Nene Marka duk da bata san dalili ba ya hanata zuwa gidanta bayan idonta ya bude. Isowarta taji suna wannan rigima da yaran.

Batare da ta dago ba, har yanzu tana duke saboda bayanta da ya amsa garin saurin dukan yaron taji wani uban kamshi mai sanyi da ya mamaye wurin wanda ke fita daga jikin Ummi tace "barni da shegu basu da aiki sai cin abinci. Gudun kwadayi yau sukunbiya na saya musuuuuuu" bakin ya makale ta kasa shiru duk da ta kai karshen kalmar.
Chapter 64 · 0% Book details