← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 157

Sashe 119

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Radhiya ta rasa yadda zata yi sauran abinda basu gane ba ma sun gane don ba karamar kunya taji ba, shikenan Hammanta ya janyo mata. Turo baki tayi kamar za ta yi musu kuka "to ba...ba...uhmmm tissue na saka na goge"

Fauziyya ta saki fuska "ohhh irin makeup remover dinnan ko? Please nima bani nagoge don ni sanyi nake ji bazan iya wanka ba"

"Fauziyya ki kiyayeni ko in kira Ya Bilal yazo ya kwashe mana ke kowa ya huta. Mutum yana fama da kansa amma baki baya shiru" cewar Zahra amma daga ita har Fauziyyan dariyar tsokana suke yiwa Radhiya. Yau mai balotelli an dinke mata baki.

Cikin dariya Fauziyya tace "wai ma in tambayeki, makeup remover din baya goge fuska iyakarsa baki kawai?"

Sai yanzu Radhiya ta fahimci ina suka dosa da wannan tambayar da dariyar. Aka yiwa wani ma ta rama bare an shiga gonarta. 'Yar dariya tayi tana sunkuyar da kai tace "sauran yana bakin Hammana shi ya goge min"

Idanu Fauziyya ta zaro Zahra kuwa dariya harda rike ciki. Suna son juna idan an hado kamar kar a rabu saboda irin wannan dramar.

"Kika bashi ya shanye?" Fauziyya tace fuskarta kadai sai tasa mutum dariya.

Radhiya ta gimtse dariyarta ta zauna kan gado ta dora kafa daya kan daya tana daukar wayarta. Sunan da ta saka masa Mon Chèri (my sweetheart) ta nemo tana nunawa Fauziyya "In kira shi ki tabbatar?"

"Zahra ki fadawa su Mama tun wuri kada gobe labari ya wuce goge lipstick a bashi matarsa"

"Ba tambayata kika yi ba Adda Fauzinmu" tace da shakiyanci.

"Ah to matambayi baya bata gashi nan an dora ki akan hanya yadda zaki gane" cewar Zahra har lokacin dariya take yi sosai ita da Radhiya. Katse dariyar suka yi a dole da suka ji ance 

"Schatzi" daga cikin wayar hannunta.

Su duka ukun suka kalli wayar harda ita da ta kira bata sani ba kafin suka fice daga dakin a guje suna dariya sai ka rantse yara ne masu kananun shekaru. Awwab da yaji shiru sai ya kashe wayar yana tunanin kila bata san ta kira ba saboda dare yayi.

Da suka koma dakin ma suna kallon juna sai su kwashe da dariya Fauziyya na cewa dadin abin itama an goge mata nata janbakin yau da tayi kwanan tausayin kanta.

Komai nasu abin sha'awa musamman wannan hadin kan da ya samo asali daga jajircewar iyayensu.

**********

Washegari wuraren shadaya na safe a can gefe guda na katon falon gidan Zahra ce da kannen nata Fauziyya da Radhiya Rahima tana yi musu lalle iya yatsun hannu kawai banda kafa. Su na cikin yi Mami da Mama suka shigo Zayyana da tun daren jiya aka yi mata nata ta tashi da sauri tayi bakin kofa za ta karbi DK ta ga baya hannun Mama ko Mami.

Baki ta tura tana leka waje "Mama ina DK?"

Mami ta daure fuska tace "Meye haka babu gaisuwa ni matsa ki ban wuri yana wurin Ibrahim a mota"

Murmushi tayi kafin ta matsa tana gaishesu. Mama tace taje ta karbo shi kunya take tana ganin idan ta fita kowa zai gane meye tsakaninsu. Ganin Hibbah ta taso zata karbo shi yasa ta fita da sauri. Hibbah tayi dan murmushi suna hada ido da Rahima.

Fauziyya ta hararesu "gulmammu ko dai ku fasa mana kwan nan ko yau na danneku a daki ayi muku balotelli ko ya kike gani babbar yaya" ta kalli Radhiya.

Dariyarsu kadai ta isa tona asiri amma Zahra tace "ku bari ta dawo mu sakata a daki ta fada ko yau ayi taro tana gida"

Hibbah da Rahima dai sai dariya Fauziyya tace su din ma duk sai ta binciko nasu tunda Radhiya ta kauce su ne next.

Wata irin tafiya Zayyana ta rinka yi kamar bazata isa wurin motar ba saboda irin kallon da Ibrahim yake yi mata. Tana zuwa ya fito da DK a hannu yana murmushi.

"Kawo shi" tace tana mika hannu.

Kara makale shi yayi a jikinsa yana harararta "dama ba wurina kika zo ba?"

"Ni kanina nazo dauka"

Wani irin kallo ya bita dashi "Ya kina ganina amma ta wannan yaron kike yi. Tun wuri ki sani bazan yarda da wasan kanin miji ba."

Kamar gaske ya hade rai ita kuwa dariya ma take yi "Ka jira a haifi kanin mijin wannan dai twin dina ne ko ba ka ji sunansa ba...Zayyan da Zayyanatu" tayi masa gwalo.

Bata fuska Ibrahim yayi ya tale baki yadda take yi ta cigaba da dariya. Muryar kuka ya soma yi mata "idan ba kin janyo na rage masa matsayi ba tunda haka ne. Tun farko ni me yasa ba'a saka min Zayyan din ba shi a saka masa Ibrahim?"

"Saboda shi Zayyan kanina ne, shi kuma Ya Khaleel...." juya idanu tayi bata karasa ba ta kama hanya za ta gudu.

Ibrahim kamar wanda aka dora a gajimare yake yawo don dadi ya biyota ya mika mata shi. Tana karbarsa ta kai hancinta jikin nasa tana gogawa tare da yi masa murmushi "baby DK dinaaaa"

Jingina Ibrahim yayi da bango yana kallonta da jin sabuwar soyayya na dibansa "yaro kaji dadinka ko yaushe ni kuma zan sami arzikin ayi min haka wa ya sani"

Kai ta dago ya kashe mata ido bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta ji ta shige ciki ta barshi a tsaye yana ta murmushi.

Emzee ne ya shigo ta karamin gate da ledar mangaro masu kyau wanda ya sauka daga motar ya tsallaka siyowa da suna hanya kafin su shiga kwanar gidan. Yana karasowa motoci uku suka shigo manyan mata wayayyu suka rinka fitowa daga ciki. Mom Arifah kadai suka gane suka gaisa da ita da sauran matan tace Emzee ya kaisu wurin Mairama.

Yana gaba sauran duka suna bayansa da ita suka shigo. Su Radhiya suka gaishesu sannan Zayyana ta hau sama ta fadawa su Ummi. Gayyar lallen ce ta tashi dama sun saka wata leda a wurin basu bata ko ina ba suka tafi daki.

Dukkaninsu matan manya ne su takwas. Biyu matan gwamnoni, uku matan sanatoci, karamar ministan ilimi sai matar ministan ilimin wai sun zo sake yiwa Mairama murna ne zasu koma garuruwansa. Duka Mom Arifah ce ta gayyato su. Abubuwan ci da sha aka kawo musu Salame tana daga daki take jin muryoyin manya don su Yadikko bayan gidan suka tafi wurin aikin nama kafin isowar su Mama da Mami da zasu hadu ayi abinci da Tante. Ko da wasa bata hangi kanta tana taya aikin komai ba a gidan banda kwanan bakinciki da tayi jiya saboda yadda ganin Alh Salisu ya kara tada mata hankali shi da matarsa. Fitowa tayi tana hura hanci Mairama kuwa tace musu ga yayarta tana nunata.

A mutumce suke gaisawa da ita sai ta saki fuska ta samu ta zauna a kujerar da tafi kusa da Mom Arifah tana ta wangale baki.

Hannun Ummi da Mom Arifah ta gani ta yaba "gaskiya ina son lallen nan Mairama yaya zamuyi? A ina mai yi take? Yayi kyau sosai"

Dadi Ummu taji " 'yata ce tayi min sunanta Rahima"

Matar gwamnan Abia kasa hakuri tayi tana shafa hannun tare da kallon kafar gwanin sha'awa "ni dai a kirawo ta idan tana kusa tayi min inje dashi gida yarana su gani...nawa ake biyanta don basira irin wannan nasan da tsada"

Salame an dade ba'a shiga aji ba amma dai tana fahimta kan bai gama toshewa ba. Ji tayi jikinta ya soma rawa taji kudi hankalinta a tashe 'yarta zata yiwa matar gwamna lalle. Sauran ma kowa tace tana so saboda yadda zanen ya fito radau sannan kalar tayi maroon sosai. Bude baki tayi za ta ce ko dari uku ne ma su kawo sai Ummi ta riga ta.

"Ku da 'yarku ko nawa ne ma kuka bata sai dai muyi godiya"

Mugun kallo Salame ta watsa mata sai dai babu wanda a kula a zuci tace "shegiya 'yar bakin ciki"

"No, no please Ummin Alheran ki fada a biya don nima zanyi. Muna da yawa bare ace alakoro ne" Mom Arifah tace suna dariya.

"Yanzu kuke magana" Salame ta sake cewa a ranta.

Ummi dama ko kadan bata da niyar manyan matan nan suci bulus. Ta dai fadi haka ne don kada a ga kamar bata da kara. Amma wannan ai kofa ce da Rahima zata samu. Aunawa tayi ta ga a garin Abuja suke inda komai kudi ne.

"N2000 take yin hannu da kafa"

Wata Dr. Lara 'yar lukuta da ita karamar ministan ilimi tace "kirawota ta fara yi mana ko a gama da wuri tunda kuna da aiki a gabanku"

Matar gwamnan Abia kuwa jakarta ta balle ta dauko bandir din dubu daya ta mikawa Ummi "take this hundred k  sister Maryam for the eight of us."

Baki Ummi ta bude zata yi godiya Mama ta rigata a gayance don kada a rainasu "Thank you Madam"

Hannun Salame har wani kaikayi yake yi burinta Mairama ta miko mata tunda duniya ta shaida ita ta dau cikin Rahima ta haifeta ta shayar. Saboda haka tafi kowa hakki akan dukiyar 'yarta.

Gilmawar Emzee Mami ta gani yana dauke da plate da ya bawa mai aikinsu ta yanka masa mangwaron zasu sha shi da Ibrahim tace ya kirawo Rahima. Zuciyarsa har wani dan tsallen murna tayi ya hau sama ya kwankwasa musu kofa. Radhiya ce ta amsa ya dan daga murya don kofar a rufe take.

"Turo min Rahima ana kiranta"

Kululu haka cikin Rahima ya kada da taji muryar Emzee. Hannunta kasa rike ledar lallen nata tayi sosai saura yatsa daya ta gama yiwa kanwarta Khadi ta tashi bayan ta lallaba ta gama.

Hijabinta ta gyara ta bude kofar yana tsaye ya jingina da bango yana shan mangwaron da fork. Mika mata yayi ta girgiza kai cike da kunya. Kofar fita daga falon ta nufa yana tsaye har lokacin a inda ta ganshi da ta fito.

"Kawar soja"

Dakatawa tayi amma bata juyo ba har ya iso inda take ya tsaya a gefenta. A hankali yace "abinda muka yi jiya bai yi kyau ba ko?"

Sai lokacin ta kalle shi da idanuwan da suke narke masa zuciya cikin sanyinta tace "yayi kyau sosai"

"Amma kika kasa fada min?" Yace kamar yana fushi.
Chapter 119 · 0% Book details