Sashe 2
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Su biyun ne dai masu surutu dazu suka fara dariya. Ba komai ke basu dariyar ba kuwa sai cewa da suke idan aka kira su ladies wai sai su rinka hango kawunansu da sauran cikin kayan mata. Captain Mustapha ya gaji da halinsu don basa ji kwata kwata gashi a karkashin platoon dinsa suke. Sallamar sauran yayi dama duka a gajiye suke. Da yatsa ya yiwa samarin biyu alama da su cigaba da gudun sai sun sake zagaye uku zasu tafi.
Wanda ya fi fitinar ya dube shi hankali a tashe sannan ya kame cikin daga murya yadda suka fi yin magana da na gaba dasu ya roki alfarmar ya daga horon zuwa washegari.
Dayan Captain Mustapha ya yiwa kallon tambaya baiyi wata wata ba ya fadi uzurin abokin nasa, wato zance da zaije wurin sabuwar budurwarsa. Murmushi yayi don ya sami damar horasu yadda yake so.
“Zayyan Tureta”
“Sir” ya sake kamewa.
“Za ka sake yin zagayen nan sau biyar”
Baki ya bude sai kuma yayi saurin rufe shi don kada ya sake yin laifi. Yana kallo aka sallami abokin nasa don a bata masa rai tunda duka laifukan da suke aikatawa shine ja gaba. Hadir Murtala ya faki idon Captain Mustapaha ya yi masa gwalo sannan ya bar wurin.
Ko da zai kare da rarrafe ya sani bin umarni dole ne.
Juyawa yayi a matukar gajiye zai cigaba da gudun Captain yace yaje gidansa ya jira shi. Idan ya riga shi zuwa yana bukatar ya dawo ya ga a ina yake. Haka yake so yayi ta yi har sai ya iske shi a gidan.
A guje ya kwasa sai bangaren gidajen sojojin yaje ya dawo Captain yana nan inda ya barshi kuma yace ya sake tafiya. Sai da yayi haka sau hudu suna haduwa a kan hanya a wurare mabanbanta a na karshen suka hadu a kofar gidan. Zuwa lokacin Zayyan da kyar yake motsa gabbansa amma a haka ya kame a bayan Captain Mustapha.
Murmushi Captain din yayi masa. Yana kaunar yaron saboda kwazo da himma amma rashin jinsa yayi yawa.
“Kana jin yunwa na sani. Mu shiga ciki kaci abinci”
Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa don ba haka ya zata ba. Tunaninsa kullum Captain Mustapha shi yafi tsana duk cikin platoon dinsu. A waje ya jira shi ya fara shiga ya nemi iyalinsa su shirya zai shigo da bako.
Wani yaro ne da zaiyi kimanin shekaru bakwai ya fito a guje yana dariya yazo gabansa ya tsaya.
“Kaine Tureta?”
Sakin fuska yayi don akwai shi da son yara “nine”
Sai kawai yaron ya dane jikinsa har suka kusa faduwa yana kyalkyala dariya ya soma surutu
“kaine kayi karyar rashin lafiya don kada kaje training? Daddy yace rannan ka sakawa wani kunama a takalmi saboda ya shiga masallaci da takalminsa. Kuma wai ka iya karatu mai dadi amma baka jin magana”
Baki Zayyan ya rike yana kallon yaron yana ta zuba da bashi labarin abubuwan da yake na rashin ji tun zuwansa barrack din. Gyaran muryar Captain din suka ji yaron ya nutsu yana rike da hannun Zayyan.
“Awwab?”
Sunkuyar da kai yaron yayi yana kara matse masa hannu suka yi murmushi tare. Bayan Captain ya bi har cikin falon. Matarsa Hassana da ake kira Mami ta fito fuska a sake ta nuna masa wurin zama da dan tebur a gaban kujerar wanda ta dora tray din abinci da abin sha. Wuri suka bashi yana cin abinci Awwab na masa hira tamkar sun dade da sanin juna. Sai bayan rabin awa Captain ya sake fitowa sanye da jallabiya irin mai gajeren hannu da fadin nan. Zayyan ya dan gyara zama ya fusakance shi.
“Awwab ya dame ka da surutu ko? Halinku daya na fitina amma shi matsoraci ne”
Dariya Zayyan yayi yana kallon yaron da ya shiga ransa cikin kankanin lokaci. Basu dade suna hira ba Captain ya sallame shi bayan dogon gargadi akan halayyarsa idan ba yana da burin a kore shi tun kafin ya zama wani a cikin sojojin ba.
Har Hadir ya dawo Zayyan yana mamakin Captain Mustapha. Mutumin baya magana sosai idan ta wuce karbar umarni da badawa. Kuma baya nuna damuwarsa akan kowa amma ace wai banda sanin halinsa har labarinsa yake bawa iyalinsa. Hannun Hadir yaji akan kafadarsa yana jijjigawa.
“Zayyan lafiyarka kuwa? Inata magana kamar baka ji. Nace naje wurin Zainab mun daidaita kanmu”
“Na tayaku murna”
Cikin yanayin ko in kula yayi maganar hakan yasa Hadir taba wuyansa “zazzabi kake ko ciwon kai? Zainab fa nace mun hada kanmu. Da naje babanta ya fito yana yi min tambayoyi karshe yace in turo. Ina ta kokarin fahimtar dashi ba kai bane sai da ya tafi tace ta amince min itama. Nima kuma na gani ina so….”
“Wai kasan yau a gidan Captain naci abinci har muka yi hira? Ashe haka yake da kirki mune bamu fahimce shi ba. Kuma yana da da dan shekara bakwai abin mamaki yayi auren wuri inajin.”
Hadir ya kalli Zayyan ya tabbatar kalau yake sai ya rabu dashi. Washegari ne suka sake hirar bayan kowa ya dawo hayyacinsa. Hadir da gaske ya nuna yana son Zainab kamar yadda ta amince masa shi kuma Zayyan jin kansa yake ya kara girma saboda ya fahimci Captain baya kinsa. Kowa da nasa farincikin a haka abokan suka cigaba da zaman barikin suna horowa akan matakan kariya da tsaro. A gefe daya maganar su Hadir tayi nisa yana shirye shiryen idan sun sami hutu zaije Kano ya sanar da iyayensa su zo su nema masa aurenta. Zayyan kuma wata nutsuwa ce take sauko masa don ya burge Captain sannan ga shakuwa mai karfi tsakaninsa da Awwab da kannensa mata biyu.
Kimanin watanni biyar sun shude kafin aka basu hutun sallah wanda ba wasu kwanaki bane na azo a gani.
Duk da haka sun karba da godiya kowa yayi nasa wuri. Hadir mutumin Kano ne dan cikin gari unguwar Madungurun. Shi kuma Zayyan dan wata karamar hukuma ne a cikin Sakkwato, wato Tureta wadda ta zama inkiyarsa a barikin amma gidansu yana cikin garin Sakkwaton. Sun tafi gida da murna da abinda suka samu a matsayin albashi kasancewarsu a mukami mafi karanta a cikin sojojin Nigeria, Second Lieutenant. Su biyun da mafiya yawa daga cikinsu sun zabi shiga aikin soja ne domin zama ababen alfahari ga kasar da basu da kamarta. Nigeria kasar da manya manyan dattawa daga bangarori daban daban suka hadu suka hada karfi da karfe wurin kwato mata ‘yanci. Wadannan matasan sojoji zukatansu sun tafi ga ganin sun zama kariya ga al’ummar kasarsu batare da duba da bambancin yare, addini ko al’ada ba. Da wannan kyakkyawar manufa su Zayyan suka baro jindadi da kwanciyar hankalin da suke samu a gaban iyayensu suka sadaukar da kuruciyarsu don samarwa na baya kasar da zasuyi alfahari da ita.
**********
Tamkar ba soja ba tun da ya nufo gidansu yake jin faduwar gaba. Don ta shi a datse hutunsu saboda babu abinda yake tsinta a gidan nasu da ya wuce bacin rai da bakincikin matar uba da ya’yanta. Zayyan maraya ne ba uwa ba uba. Mahaifiyarsa mutuniyar Nijar ce ‘yar kabilar Tamasheq a cikin Agadas, mahaifinsa ne Basakkwace. Sun hadu a yawon fataucinsa na dabino da cukwi da yake zuwa sarowa. Soyayyar lokaci guda ce ta kamasu shi da Alheran bai kuma sha wahala ba babanta Alh Ghousman Agali ya amince masa kasancewarsa kwastomansa da aminci ya dade da wanzuwa a tsakaninsu. Mal Muhammadu Tureta a lokacin yana da matar aure guda daya Jume da yara shida, maza uku mata uku kuma shima kasuwanci yana damawa dashi kafin daga baya karayar arziki ta same shi. Wani mummunan zama akayi tsakanin Jume da Alheran. Da fari Alheran ta kwantar da kai sosai tana bin Jume sau da kafa duk da irin wulakanci da cin kashin da take yi mata ita da yaranta. Allah ma Ya taimaketa tana jin Hausa saboda cudanya da suke yi da Hausawan kasar tasu.
Bayan wani lokaci tana hadiyar bacin rai ita kadai ga gorin haihuwa ta ajiye kawaicin a gefe suke bugawa. Idan Jume ta shirya makircinta Alheran zata fidda kanta da kissar da wahala ta sanya ta koya karfi da yaji. A shekara ta uku da aurensu Allah Ya bata ciki. Sunyi murna ba kadan ba ita da maigidanta. Yadda yake matukar sonta haka yake son abinda yake cikin nata. Wata tara da kwanaki kadan Allah Ya sauketa lafiya aka sami Zayyan. Kafin suyi arba’in Alh Ghousman ya rasu. Alheran tasha kuka Mal Muhammadu ya dauketa suka tafi Nijar. A can ya barota bayan yayi kwana goma sai da ta shefe watanni biyu domin bayan anyi ar’bain aka zo rabon gado kanin Alh Ghousman yayi tsallan badake yace dukiyarsa ce kaf yayansa yake juyawa. Aka buga aka raya ya dauko shaidun karya harda barazanar kai iyalan dan uwan nasa kara. Rigima gagaruma akayi karshe suka hakura ya basu abinda yayi niyya cikin dukiyar mahaifinsu ya handame sauran. Da wannan bakincikin ta dawo Sakkwato sai mijinta ne yake ta kokarin kwantar mata da hankali.
Zayyan na da shekara uku ta sake samun ciki. Wannan karon tana laulayi mai wahalarwa wasu lokutan ko yatsa bata iya dagawa, amma duk da haka bata tsira daga kaidin Jume. A haka ta shiga wata tara.