← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 157

Sashe 66

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kema G dinki ce ashe"

"A'a wallahi" tace da sauri, hakan ma yana kara bashi dariya har wani kada hannuwa take yi "taka ce kai dai"

"Yanzu dai kishin dreba kike yi" ya dage mata gira "Allah sarki kanwata ta kare miki gashi dreban nan bazai barki ba sai kin amsa sunan matarsa"

Tsuke baki tayi tana dariya kunya ta rufe ta. A hankali ta daga kanta suka hada ido tayi saurin rufe fuskarta da hannuwanta. Yatsun sun sha lalle kamar ya rikosu.

"Schatzi"

"Uhummm"

"I miss you"

"Zaka sa naji kunyarka Hamma"

"Kuma I love you"

Mayafi tasa ta rufe fuskar yanzu tana so ta tashi ta gudu tana gudun kada yace ya hanata.

Langabe kai yayi yace "Baki bani amsa ba ko daya. Kenan bakiyi missing dina ba kuma ba kya sona" 

Radhiya ba wayo yana fadin haka ta dago da sauri "ba fa kaji nace haka ba"

"Kina son nawa ne? Ba ni kadai nake abuna ba"

"Kai Hamma Allah bance ba" ta fada kamar tayi masa kuka.

Shi kuma ya sami na yi ya cigaba da cewa "do you love me?"

"Eh mana" 

Yadda maganar ta fito a bazata haka itama ta fita daga motar harda tuntube ta kutsa ta cikin mutane tana jin kunya ta barshi da yi mata dariya.

Wayarsa ce tayi ringing sai a lokacin ya kula ashe Mami ta kira shi sau biyar. Sunyi da ita suna zuwa zai hadata da Ummi tunda sun kasa samuta ya manta shaf. Bai yi tunanin amsawa ba yana gudun fada ya rufe motar ya koma ta bangaren da bakin suke don ya bawa Emzee ya kai mata. Ko da ya shiga ma sai yayi sa'a tana wurin dasu Nene tana basu labarin makantar da tayi da warakarta kwanaki kadan da suka wuce. Wayar ce ta sake shigowa ya mika mata yana cewa Mami ce.

Karba tayi ta kara a kunne da sallamarta sai dai maimakon muryar Mami sai taji Fauziyya tana kuka sosai tana cewa "Hamma ka dawo gida ba lafiya"

Ummi na jin haka ta mike tsam ta fita ta kofar waje saboda ko ina na gidan hayaniya akeyi ta sami gefen wani gida da bishiya a jikin gidansu ta tsaya. Hankalinta a tashe yake tace "Fauziyya me yake faruwa?"

Gabanta ne ya fadi. Da farko kamar bazata ce komai ba sai da Ummin ta soma yi mata fadan cewa itama babarsu ce.

"Ummi tun dazu Mami da Zahra suke kuka. Bansan me yake faruwa ba amma har Umma Hussaina da Mummy sunzo sunyi fada da Mami"

Zantukan Fauziyya sun daure mata kai matuka ta kasa fahimtar me yake faruwa kamar yadda itama Fauziyyan bata gama ganewa ba. Kwantar mata da hankali tayi tace mata gobe zasu taho in sha Allahu da Awwab.

Da ta koma su Mammee suka ce zasu tafi Kano su kwana biyu sannan su koma Nijar. Ummi bata ji dadi ba. Niyarsu matan su kwana a wurinta tun farko amma sun fuskanci hakan wahalarwa ne gareta saboda yanayin biki da ake yi a gidan babu masaka tsinke.

"Yara muka zo gani dake kuma Alhamdulillah mun gani duka kuna lafiya. Sai dai muna son muji yaushe ne zaiyi muku daidai mu turo ku taho Niger domin ku hadu da sauran 'yan uwa"

"Ba don bikin da zamuyi a Katsina na yara har biyu ba da tun yanzu zaku tafi dasu" Ummi tace tana kokarin boye damuwar da ta shiga tun bayan wayarsu da Fauziyya.

"Kema sai kinje Mairama ba yaran kadai ne namu ba" Mammee tace sauran suna dariya.

"In sha Allahu muna gama bikin zan sanar daku Mammee"

Sallamar Malamijo ce ta katse zancen nasu. Bai yarda ya zo wurinsu ba sai da ya shiga cikin gidan yaje ya chanja kaya. Kayan da zaisa gobe na daurin aure ya sako saboda motocin da ya gani sun tayar masa da hankali. Ya saka babbar riga yana ta baza hannuwa. Saboda karfin hali ya sami irin farin abin nan da akan gani malamai sun ninka sun daure hularsu dashi na ustazai shima haka yayi ya fito ko karya babbar rigar baiyi ba don ya kara cika ido.

Wurin bakin yaje ganinsu ya sake tayar da hankalinsa yasan lallai ba bakin rainawa bane.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: **********

Yau falon na Alh Baba ya cika sosai sakamakon yawan wadanda aka zauna dominsu. Jikokin da abin ya shafa suna cikin gida sai an gama da iyayensu za'a nemesu.

"Wace magana nake ji haka cewa jiya Gambo taje gidan Mustapha da Husaina yau kuma da Azumi ana rigima?"

Babu wadda ta iya yin ko da tari ne saboda kwarjinin iyayen nasu. Alh Baba ya kara hade rai yace Mami ta fada masa me ya faru. Kai a kasa ta zayyane masa komai. Gabadayansu sun nuna fushi akan abinda kannen nata suka yi mata tare da Azumi.

"Naga alama a kokarina na son inganta zumuncin zuri'ata al'amura suna kara tabarbarewa. A zamaninmu dai mace ko namiji sai dai ace ga wane za'a hadaku aure kuma ayi auren a zauna lafiya. To amma na kula daku da 'ya'yanku abin ba haka yake a wurinku ba"

Baba Karami ya kalli su Mummy "Gambo baku kyauta ba ko kadan abinda kuka yiwa Hassana har gida kuma a gaban 'ya'ya. Ko bata girme ku ba ai ta ci darajar auren yayanku"

Sun hadu sun yi musu fada akan abinda ya faru sannan Alh Baba yace to tunda abu ya koma kowa kanta ta sani da 'ya'yanta zai kira yaran ya sake tambayarsu. Duk abinda suka yanke shikenan.

Kana ganin yadda yake magana kasan akwai bacin rai sosai a tattare dashi

"Zabi ya rage tsakaninku da 'ya'yanku bazan sake saka muku baki ba balle inyi bakin jini"

"Alhaji kayi hakuri don Allah. Muma kaine ka aurar damu in sha Allahu duk yadda kace akansu haka za'ayi" Daddy yace sauran 'yan uwansa suka nuna amincewarsu.

Alh Baba sai kuma yaji nauyin yadda duk da yafi kowa sanin cewa son kansa ya nuna akan komai amma gabadaya yaran da iyayensu kai hatta kannensa kowa ya amince ne domin biyayya a gareshi. A tunaninsa wannan hadin kara dankon zumunci zaiyi amma zamani ya chanja. Bai manta ba daren jiya da Baban biyu yake ce masa auren hadi yanzu a cikin goma daya akan samu ana zaman lafiya. Biyu ayi zaman hakuri sauran bakwai din kuwa duk mutuwa suke yi wani lokacin ayi rabuwar da zata shafi har jikoki. Ya bashi shawara cewa idan jikokinsu sun hada kai a junansu a barsu suyi aure haka kuma masu nema a waje su ma a basu dama.

Haka suka shigo masa Zahra, Ghazalatu da Fauziyya idanunsu a kumbure suna kan kuka ma. Awwab kuwa kallo daya yayi masa ya dauke kansa. Damuwa da bacin rai sun rufe kyakkyawar fuskar yaro mai yawan fara'a da wasa da dariya. Anya ya yiwa 'ya'yan Hassana da Mustapha adalci kuwa? Yara har uku yana neman tauye musu hakki akan abinda ba addini ba. Don dai kawai Baban Biyu yana da kawaici amma ace jikokinsa har hudu duka ya nuna shine mai ta cewa akan makomar rayuwarsu kuma nasu kakan ya nade hannu ya kyale shi.

"Matso nan Fatima" ya yafito Zahra da hannu. A tsorace take ta tashi ta koma kusa da kafarsa ta zauna. Ya kira Fawaz shima yazo ya zauna daga daya gefen nasa.

"Kana son auren kanwarka?"

Shiru Fawaz yayi na 'yan dakiku kafin ya girgiza kai yace baya so. Haj Azumi tayi gajeren murmushi. Tun a gida tayi ta nanata masa idan yana son kansa da arziki kada ya yarda a aura masa yarinyar da bata sonsa. A nasa bangaren shi dai baya kin Zahra amma kuma ba soyayya bace tsakaninsu shiyasa bai ga amfanin aurenta ba.

Alh Baba ba haka yaso ba amma dole ya karba tunda a gaban iyayensu ake yi.

"Fatima waye shi wanda kike so din?"

Kasa magana tayi ya mayar da tambayar ga Major. Shi din ma bai wani san kan zancen sosai ba shiyasa Awwab ya fada masa yadda suka yi da ita dazu.

"Yanzu zuri'ata zan hada da kabilu?" Yace cikin wani irin yanayi.

Baba Karami yayi saurin gyara murya "Alhaji kada mu koyawa yaran nan kin 'yan uwansu musulmi saboda bambancin yare da al'ada. Mun sani cewa babu haramci a tarayya dasu sai ma kara karfin alakar dake tsakanin musulmi da dan uwansa."

"Haka ne, idan mun tashi daga nan a kira shi a waya yazo da magabatansa idan yana sonta. Daga yanzu na soke maganar aurenta da Fawaz."

Mami harda hawayen dadi. Lallai mai hakuri shi yake dafa dutse yasha romonsa. Bata taba tunanin zata sauyi irin wannan game da auren Zahra ba sai gashi ya samu cikin ruwan sanyi.

"Fauziyya da Bilal fa? Akwai wani korafi makamancin haka tsakaninsu?"

Bilal yaro mai tsananin kunya yace indai bata da wanda take so yana son aurenta. Fauziyya ma bata bashi kunya ba tace ta amince. Haka ya sanya farinciki a zukatansu.

"To uban gayya da aurensa ya janyo mana wannan tone-tone. Na baka izini Muhammad ka nemi amincewar Ghazalatu da waccan yarinyar ayi aurenku rana daya babu wadda zata jira wata"

Yana dire maganarsa Ghazalatu ta dago jajayen idanunta "Alhaji ina da magana"

"Ina jinki"

"Ni dai na hakura ko wani zaka zaba min zan amince amma banda Yaya Awwab"

Tsawa Daddy Haroun ya daka mata ta fashe da kuka. Tana da kishin da bata jin zata iya zama da Radhiya da take gani kamar wata kaskantacciyar yarinya. Amma ba wannan ne ya janyo mata kin amincewa ba sai zugar mahaifiyarta wadda itama Hussaina ce ta ingizata kan cewa su hada Ghazalatu da nata dan Nura. Hussaina gani take ta sami dama da zata dandali arzikin gidan Gambo yadda ya kamata. A zahiri Gambo da Mami sun fi ta rufin asiri. Sai dai bata sani ba Mami a nata gidan kafin Major ya sami lafiya har ya fara aiki guminta ake ci. Ita kawai gani take suna da kudi ne suke son hada nasu 'ya'yan ita ko oho. Mummy Gambo an hau dokin zuciya ba bata lokaci ta amince bayan sun bar gidan Mami a jiya.

"Saboda ance ya auri wadda mahaifinsa ya nema masa?" Baban Fawaz ya tambayeta.

"Ni dai kawai bana so ne yanzu"
Chapter 66 · 0% Book details