← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 157

Sashe 141

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A asibitin tare suka shiga wurin likitan. Tambayoyi yayi mata game da yadda take jin idon ya haska ya gama bincikensa sannan yace ta rufe idon mai lafiyar ta karanto masa ABCD da aka hargitsa daga can karshen wani office inda ake gwajin ido. Zuciyar Emzee ta tsinke kuka ne kawai baiyi ba jin Rahima guda biyar kadai ta iya fada daidai sauran kuwa sai dai ta kalli Q tace O ko ta kira K da E. Abin gwanin ban tausayi sai da mutum yayi mata haka sau uku ya tabbatar abinda yake zargi ne ya sami idon. Ita kuwa ganin yana maimatawa har cewa tayi dashi tana gani fa. Sai dai sakamakon toshewar da jijiyoyi suka yi da jini aikinsu yayi matukar rauni duk da cewa an magance toshewar kumburin ya warke gabadaya. Ko idon zai yi lafiya da wahala ta sake gani sosai dashi. Yatsunsa ya shiga nuna mata yana cewa ta fadi ko nawa ne. Nan Rahima ta rikice inda bata tantance biyu da uku. Hawaye sosai ta soma yi da likitan ya soma bayani. Duk yadda Emzee yake kokarin nesanta kansa da ita ba karamin tausayinta bane hake bin ko ina a jikinsa. Wasu magungunan ya rubuta mata sannan ya auna karfin idon yace zaiyi mata glass ne su dawo nan da kwana uku.

"Babu yadda za'ayi mu samu gobe da safe saboda tafiya zamuyi a goben" cewar Emzee.

"Zaku iya samu amma sai ka kara kudi. Kayi magana da cashier din idan ka fita"

Nan suka gama komai ya biya kudi cikin wanda Ummi ta bashi. Maimakon su tafi gida wani babban shago ya wuce da ita ya sa salesgirl din tayata neman frame mai kyau. Wani round ta zaba ya dace da fuskarta babu dai me yiwa kowa magana ya biya kudin suka koma asibiti. A mota ya barta yace ya kai musu sannan suka tafi gida.

Zayyan na komawa gida ya sami Mairamansa a kwance Radhiya ta bata tea taki sha wai bacci kawai take son yi ta rabu da ita. 

"Jeki abinki Alheran ajiye min tea din" yace da ita.

Tana fita ya cire rigar khakinsa ya rage singlet da godon wando ya kwanta a kusa da ita tare da janyota jikinsa.

"Fillo me yake damunki ne kwanakin nan na lura kamar baki da lafiya."

"Stress ne Sojana kuma kaima kasan dole ne tunda kun dauko mana abinda yafi karfinmu."

Dariya yayi yana shafa kwantaccen gashin kanta da yake nadewa da kansa saboda laushi. Dinner ce angwaye suka tsara abarsu Baban Arifah yazo ya chanja komai. Abokansa 'yan siyasa da manyan mutane wasu ba zuwa Jos zasuyi ba shine suke ganin kawai gara ayi wata a Abujan. Sai kuma bangaren sojoji da suke yiwa Zayyan kallon wani celebrity suma kowa yana son zuwa bikin 'yarsa. Excellency yace bai ga amfanin ayi taro gutsi-gutsi ba alhalin mutane daya ne zasu zo. Kuma dama bikin ya rabu kashi kashi ayi ta tara gajiya da barnar kudi. Hakan da yayi ya kara masa kima a idanun su Baba Hadir da Daddy domin ya nuna yasan zafin nema ba kamar yadda yake a wurin 'yan siyasarmu ba ayi sati ana biki ana barin kudi. Shiyasa su Mama kullum suna tafe ana ta shiri domin suyi taron da zai kayatar ya fitar da mazajensu kunya.

A cikin kunneta Zayyan yace "ni kuwa sai nake ganin kamar na tureki ne Fillo"

Da saurinta ta tashi zaune "rufa min asiri da abin kunya Sojana. Muna bikin 'ya ka tureni da wane ido zan kalli mutane."

"Kin fiye tsoro kamar ba matar soja ba. Ina ruwanki da mutane. Iyaka ki goya namu ta goya nasu ba shikenan ba"

"Ni dai ka dena wannan fatan" tace tana sake narke masa.

"Yanzu ma na fara, kinsan irin farincikin da zanyi kuwa idan gaske ne? Hmmm Fillo kiyi fatan Allah Ya amsa domin ki ganewa idanunki babban matsayin da zaki kara takawa a zuciyata"

"Kana nufin akwai inda ba ni bace dama?"

"Ko daya, sai dai zan kara mata fadi ne domin a haka kinyi mata yawa" yace yana kara rungumeta tare da addu'ar cikar burinsa.

A nata bangaren itama hasashen cikin take yi amma kunyar kasancewarsa take. Ina zata boye kanta ace tayi ciki bayan ta aurar da 'ya. Ga tarin fargabar yadda Zainab ta haihu.

Sai dare ta iya saukowa Emzee yayi musu bayanin abinda likita yace. Mairama taji babu dadi sosai. Wata kiyayya ta banza da Salame ta dorawa kanta ta janyo ta makanta 'yarta da bata yi mata laifin komai ba. Kuka sosai Rahima take yi Zayyan yace kowa ya fita ya barsu da ita. Daga shi sai ita da Ummi ya rinka yi mata nasiha akan hakuri da karbar kaddara. A nutse yake janta karshe ya nemi jin me take son karantawa idan ta gama makaranta tace Nursing take so. Murmushi yayi yana yabawa zabinta sai dai wani hanzari ba gudu ba shine makarantar da aka sama mata sun ce sai sunyi mata gwaji kafin ta shiga SS3. Idan bata sami result irin wanda suke bukata ba sai ta maimaita ajin.

"Daada repeting fa kenan a wayance" tace a sanyaye da guntun hawayenta.

Ummi tayi dariya "kin ganni fa tare muke tafiya da yayyenki Ibrahim da Karami. Yanzu nan da sati biyu zan koma makaranta ina level 4 suna level 4"

Murmushi tayi kafin tace "Nasan ma sai sunyi min ko don English da Maths" 

Kwantar mata da hankali Daada ya cigaba da yi yace ko me ya faru kada ta damu. Ummi kuma tace za'a daukar mata lesson teacher a gida. Bayan ta koma wurin Radhiya wayar Malamijo Ummi ta kira ta fada masa.

Fada yayi kamar ya ari baki karshe yace "Mairama kinga hakkinki ko"

Hawaye ta soma yi "Malamijo ka dena fadin haka kaddararmu ce daga ni har Rahiman"

"Ai ko ban fada ba hakan ne. Salame ko kadan bata da hankali. A da bata damu da Rahima ba yanzu kuma hakkin yarinyar nan bibiyarta yake duk inda ta zauna bata da zance sai Rahima kamar wata sabon kamu. Tayi ta nunawa mutane kafarta wai ita tayi mata lalle..."

Dariya ce ta nemi kwacewa Mairama tace "Kayi hakuri ba da niyar bata maka rai na fada ba"

Albarka ya rinka saka mata yace ba da ita yake fushin ba yana dai jira ya gani ko wannan dalilin zai sa Salame ta dawo hayyacinta sosai. A yadda ya tsara Na'e da wasu ne cikin yaran zasu zo Abujan. Yadikko taje Sakkwato ita kuma Hajjo taje Nijar. Maman 'yan biyu dai banda ita a wannan yawon yaranta kananu ne ga zaman mota.

**********

Bikin kwana biyu suka halarta a Jos tare da su Tante Nasara da wasu daga Nijar da suka taho tare. Kudi dai yayi kuka to amma ba abin mamaki bane duba da cewa biki ne na 'ya daya tilo ga gwamnar jihar tasu.

Gabadaya aka dunguma suka koma Abuja wasu a mota wasu a jirgi. A hanya Ummi ta rinka amai kamar zata fitar da kayan cikinta don sosai ta galabaita. Mama tana sannu tana murmushi wanda ya janyo Ummi kai kararta wurin Mami. Hakuri Mami ta bata tana gargadin Mama da ido saboda birkici musu da Ummin tayi. Zuwa yanzu ta gama tabbatarwa ciki ne duk da bata je asibiti ba hankalinta duk ya tashi ina za ta kai abin kunya a cewarta. Da su ka isa gidan Daada su duka ukun suka sauka a nan ana lallaba patient. 'Ya'yan nasu basu san me yake damunta ba sai hawa suke ana mata sannu. Sai da ya rage su hudu a dakin da Tante Nasara sannan Mama ta kasa hakuri ta soma tambayarta.

Doki ne ya isheta tana dariya "Ummin Awwab anya baki harbu ba?" 

Ummi ta gama aika mata sakon harara kamar ido zai fado "kin manta bindigeni akayi"

Su duka ukun suka sa dariya ta sake hade rai lokacin da Tante tace "abar zancen wasa matar Yaya kamar fa ciki ne dake"

"Wannan ya wuce kama Nasara barka da zuwan Daada ne yake sakata amai. Sai dai muce Allah Ya inganta" cewar Mami.

"Wallahi...wallahi...." ta soma cewa sai kuma kuka sosai tana yi harda sheshsheka tace "ina zan kai wannan abin kunya don Allah. Ciki kamar wata yarinya?"

Mama ta galla mata harara "Allah Ya bamu hakuri" tana dauko DK da yake kwance akan gadon "kai taho kaji dan soyayya in yayeka in samo maka kani ko kanwa."

Fuska jajur Ummi take nunata da hannu ga hawaye yaki tsayawa "Ya isheki Zainab wannan ba abin wasa bane."

"Ni bansan ma me zan ce miki ba. Ki wayi gari bayan shekaru da dama da cikin Zayyan a jikinki abinda nasan ko a mafarki baki hangowa shine kike kuka? Mairama kyauta irin wannan ai sai sadaka da kyautata ibada. Uhmm Mami ga kanwarki nan bari na nemi Emzee ya kaini gida kada ta bata min rai" ta mike za ta fita Tante ta rikota tana cewa.

"Allah Ya shiryeku kuna abu kamar yara"

Mami ta sauke taguminta da tayi tana kallonsu suna aikin hararar juna "ni tunda nake ma na taba ganin matan da suka gagara girma kamar wadannan."

Mama tace "baki jinta ne da wani shirme wai kunya...wannan ba shine babbar shaidar Zayyan ya dawo da soyayyar Mairama ba"

Duk yadda jikin Ummi yake a mace bai hanata jifan Mama da pillow ba itama tana dariyar "Allah Ya shiryeki Zainab"

"Amin Ya shiryemu mu duka." Ta koma tana kallon Mami "saura ke fa ya kamata mu ga shaidar cewa har yau kina qalbin Major"

"Allah Ya tsareni da wannan abin kunya" tayi saurin cewa.

Ummi tace "ooooohhh da shine kuke yi min fata saboda rashin tausayi. Ni na manta yadda ake raino"

"Kin dai san yadda ake samun baby....."

Tante ta hangame baki "Haka kike Zainab?"

"Ta wuce nan Nasara ki kalleta kawai ki dauke kai" cewar Mami.

Tsokanar juna suka cigaba da yi ana cewa Ummi ta tabbatar taje asibiti duk da dai ko yanzu sun fara kirgin watanni. Babu ruwansu 'ya'ya suna shagalinsu suma suna nasu.
Chapter 141 · 0% Book details