← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 157

Sashe 58

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daure idanun Ummi aka yi da farin bandeji likitan yace bazai bude ba sai gobe a wurin gwajin ido. Budewar idanun lokaci daya da yawaitar haske ne ya janyo mata wannan ciwon kan saboda haka tana bukatar hutu. Da an sabunta mata glass din ido komai zai daidaita in sha Allahu. 

Emzee fa rai bai so ba. Abinda aka fi gani wurin Radhiya yau sai gashi yana yi. Zama yayi kusa da ita a kan gadon yana rokonta wai ko dan yaya ta janye daurin idon ta kalle shi.

"Kayi hakuri mana Zayyanu gobe fa za'a bude mata."

"Nene shikenan sai ta kwana ni bata ganni ba." Yau abin nasa harda turo baki musamman da Radhiya take masa gwalo.

Ibrahim ya kalli yadda yake yi ya jinjina kai "yau kuma Zayyana ka koma? Ita ce bakinta kullum a tabe tsabar shagwaba"

"Kai kuma sarkin sa ido ko" inji Mama ta kalli Emzee tana bashi hakuri.

"Ka fita idona Surbajo" ya yi maganar yana nuna shi da dan yatsa.

"Sunan nan ya fita a bakinka fa"

"Kunga ku tashi mu tafi haka nan kafin ku cika mata kunne. Ummi bari mu gudu dare na kara yi"

Kwanukan da suka bata na abinci Radhiya ta hada zata kai mota Mama tace tayi musu sai da safe don tare zasu wuce Nene kadai ce zata kwana.

"Wayyo Mama nidai ki barni"

"Shagwababbun da yawa ashe, ai kuwa sai mun tafi don bazan bari ki zauna ki dameta ba"

Ibrahim da Emzee suka soma tsokanarta. A bangare daya kuma tasu rigimar su biyu bata kare ba. Mama dai kada su tayi duka suka fito wurin da ta ajiye motarta. Layin Awwab ta shiga nema don ya kusa awa daya baya dakin daga zuwa amsa waya.

Ghazalatu ce take kiransa dama shiyasa ya fita daga dakin. Mota ya koma suna waya. Ta sanar dashi cewa tana tunanin Daddy Haroun yau ya yiwa Alh Baba zancensu don ta ga ya tambayeta da safe. Hira yake da ita babu wannan irin dokin da yake ji akan Radhiya da ya hadu da ita kwanaki kadan da suka wuce. Har ga Allah sai yake jin babu dadi saboda baya son zama maci amana kuma baya son wulakanta kanwarsa. Biye mata yayi suna hirar kawai don ya faranta mata.

Wayar Mama da take ta shigo masa yace mata yana zuwa ya amsa kiran.

"Awwab ina kayi parking ne? Ka taho mu tafi gida don nasan bazaka gane hanya ba. Nima ba don Ibrahim ba bata zanyi"

"To Mama gani nan"

Zagayawa yayi inda suke Ibrahim da Emzee suna rige rigen shiga tasa motar saboda rigimarsu ta dazu tace Radhiya taje ta shiga su bisu a baya. Ibrahim da Emzee su shiga tata.

"Amma Mama ba mune maza ba sai mu bishi ki tafi da ita" cewar Ibrahim suna hada ido da Emzee suna dariyar shakiyanci.

"Ita tasan hanyar ne? Ko mu biyu kuke son mu bata?"

"Sai ku biyo mu a baya. Amma a haka kamar kinfi son ta bishi"

Ganin idon Mama kadai ya hana Radhiya kaiwa Emzee duka. Kunya ce ta kama ta sosai. Allah Ya taimaketa Mama ta kama kunnuwansu shi da Ibrahim ta gwara musu kai sannan tace su wuce itama tana murmushi.

Kwandon kayan abincin da ta dauko Awwab ya karba ya ajiye a baya sannan ya bude mata gaban. Ibrahim da Emzee kamar ba fada suke ba suka sake kwashewa da dariya harda tafawa.

"Shakiyai Allah Ya shirya min ku" Mama tace kawai tana tada mota.

Radhiya a kunyace ta shiga motar duk da cewa dazu tare suka zo a hakan daga Sumaila amma da Nene da Ummi. Yanzu kuwa su kadai duk bakin ma sai ya mutu.  Bangaren window ta karkata gabadayanta tana kallon waje.

Yatsantsa ya kada mata ta juyo amma taki kallonsa "tunanin me kike yi?"

"Babu komai"

"To in baki abin da zaki je kiyi tunani a kai?"

Da ka ta amsa masa yace "baki da wani course da kike sha'awar karantawa?"

"Duk ban sansu ba, soja kawai na sani"

"Sojan ma ai yana karatu"

"Training din kuma ayi yaushe? Na zata fada kawai ake koya musu da harbin bindiga"

"Sai kace wasu 'yan ta'adda? Kinga kamar Daddy da yayi soja amma computer engineer ne."

Dena kallon wajen tayi ta gyara zamanta yana mata bayani yadda zata gane. 

"Kin dami mutane da son zama soja bayan baki san komai akansu ba"

Baiyi tsammani ba kawai yaji tace "Hamma ka zaba min wanda kake so in karanta"

Kallonta da ya tsaya yi saura kiris motar Mama ta bace masa "kina son mass comm.?"

"Na 'yan jarida?"

"Yes"

Zata bashi amsa wayarsa ta hau ruri. Da yake a kusa da giya ya ajiyeta idonta ya kai inda hasken yake ta ga ansa My G. Wani irin abu taji ya soki zuciyarta ta dauke kai da sauri ta koma kallon waje. Awwab sai yaji gabadaya hankalinsa ya tashi. Wai haka ake yi da mata biyu dama? Shi tun kafin yayi auren kowacce yana kokarin ya ga ya kawar da abinda zai tuna mata da 'yar uwarta saboda alamun kishi da yake ganin suna dashi su duka. Wannan shine dauko ruwan dafa kai. Bai taba tunanin hada girlfriends biyu ba ma a lokaci daya balle mata. Shi irin mutanen nan ne da rigima ta taho ta hagu sai yabi dama babu karkace hanya. Duk abinda zai tada masa da hankali gudunsa yake. Shi kadai yake kwankwasar kansa da cewa sai ya jajirce ne fa komai zai tafi daidai. Yadda Alheran tasan ba ita kadai bace yana komawa Katsina gobe Ghazalatu ma zata sani. Kai iyayensa ma zasu sani don ya fara ji a ransa wannan shekarar da ya diba ko kadan bazai iya jira ba. Zamanta yanzu cikin motar ba karamin jinsa yake a ransa ba. Kiran ya katse wani ya sake shigowa ya dauka yace mata tuki yake zai kira idan ya tsaya.

Radhiya kuwa sai juya sunan take a ranta wai My G. Lokacin da ya gabatar mata da ita tun farko da haka ya ambaceta amma yanzu tafi jin abin a ranta. Har ya gama wayar bata kalle shi ba. Tunawa tayi da wayar da ya bata wadda bata samu nutsuwar dubawa ba ta dauko a hankali harda karewa da hijab don kada ya ga me take yi ta budo wurin sunaye. Suna daya tal ta gani a cikin contacts din. Hamma. To saura fatan akwai kudin kira. Satar kallonsa tayi idanunsa akan titi yana tunanin yadda zata kaya masa gobe a Katsina yaji waya ta sake kara. Ko kalla baiyi ba tunda yace zai kira yafi so ta kyale shi ya kira din.

Kamar ba wadda ranta yake a bace ba Radhiya tace cikin karamar murya "Hamma ana maka waya"

"Bari kawai zan kira idan na tsaya"

So take ta ga da wane suna yayi saving number dinta. Ko bai ma saka sunan ba. Gashi ya tura wayar a aljihu.

Da ta katse sai ta sake kira "Hamma ka dauka mana"

"Yadda kika bata rai dazu idan na dauka kila kuka zaki yi min" yace daidai lokacin da Emzee yake bude gate Mama tana shigar da motarta Ibrahim kuma ya shige ciki ya fadawa kawunsa kanin Baba da ya zauna dashi sun dawo.

Sake kiransa tayi na ukun ta turo baki "ni dai ka duba mana"

Bai taba kawowa ita ke kiran ba ya dauko wayar da saurinta kuwa ta leka. Shi yana mamakin kiran me take yi masa ita kuma tsabagen bakinciki tana mamakin wannan wane irin suna ne ya lakaba mata.

"Meye wannan Hamma? Nawa sunan kenan, meye sha...sha me ma?" Ta daga kai tana kara kallon rubutun wayar kuma ta katse bata gama hada harufan ta karanta ba.

Idanunta taf da kwalla ta dagosu ta zuba masa "sake nuna min nawa sunan" tace kamar me bashi umarni. Ya kuwa danno sunan nata ya bata wayar.

Kallon sunan ta sake yi ta ma kasa karantawa. Wata uwar harara ta doka masa ta kama kofar zata fita ya danna lock kafin ta bude.

Dukan kofar ta shiga yi "ka bude min in fita, kuma na fasa soja zanyi, kuma likita zan aura"

"Allah baki isa ba Awwab ne mijinki" 

"Ni na fasa ka bude min" sunan kawai take tunani ranta yana kara baci. Anya ma ba shashasha yake nufi ba. Kwafa tayi tana jinjina kai.

"Calm down Schatzi, me ya faru?"

Sai ga digon hawaye ya ziraro "nice shazi din? Ni ko? Ni ko?"

Dariya ta bashi yadda ta kwabe fuska da gaske wai ranta ne ya baci. Gyara motar yayi a cikin gidan suna kallo kowa ya shige ciki ya sake tambayarta ta fada masa laifinsa.

"To ba kaine..."

"Me nayi ni Hamman Alheran sarkin laifi"

Sai kuma taji nauyi amma dai dole ta fada ayita ta kare. Bazata yarda kawai don ita tana da hakuri ba a cewarta kuma yayi mata haka tun yanzu ba.

"Ita da ta kiraka ba my G ka saka mata ba...."

Ido ya lumshe yana dariyar kuruciyarta "shine kika kira ki ga me na saka miki?"

"Eh, kuma kiran yayi min amfani gashi ni nawa sunan ko ma'ana babu. Mu sake gani ma don na kasa karantawa"

"Schatzi" yace da wata irin siga da ta sauke mata tarkacen rigimar da ta debo ba shiri. Idanunta yake nema su hada da nasa taki dagawa "Schatzi yana nufin sweetie in german." Cusa kanta kawai tayi a tsakanin cinyoyinta saboda tsabar kunyar da ta dirar mata. Tana ji yana tambayarta "Idan kuma ba kya so sai na koma kiranki my A. Bari na chanja miki" ya fara danna wayar.

"Don Allah ka bari"

"Kina so?"

Ta wani rufe fuska tana dariya ya kada kai ya bude motar suka fito tare. A daidai bakin kofa zasu shiga ciki yace "rigimammiyar Awwab". Da dan gudu ta shige ciki ta barshi a nan yana jin kamar an bashi dukkan farincikin duniya.

**********

Washegari Awwab bai bar Kano ba sai da ya tabbatar an gama komai na gwajin da za'a yiwa Ummi. Ko kwandala basu biya ba shi yayi komai. Ummi da Nene sai addu'a kawai suke masa yayin da Radhiya take jin sonsa yana kara shigarta. Duk wanda zai mutunta maka iyaye hakika masoyi ne na kwarai.
Chapter 58 · 0% Book details