← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 157

Sashe 18

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daren Malamijo yace su shirya da wuri zasu wuce gobe. Mairama ta roke shi alfarmar zata je gidansu Zainab kafin su tafi. Jume tana zaune tare da Mairama bayan ta yiwa Zayyan karami wankan yamma tace mata "yanzu Mairama daga yau shikenan ko? Nasan da wuya ku rinka zuwa tunda kin san ba ni bace na haifi Zayyanu. Ga bakin kishi yasa ni ban san ta yadda za'ayi na sami dangin mahaifiyarsa ba balle su san halin da ake ciki ma "

"In sha Allahu zan rinka zuwa Jume. Idan basu zo ba wa zasu nuna a matsayin dangin uba?"

"To nagode Mairama. Sai kin daura dammarar hakuri da juriya. Yanzu sabuwar rayuwa ce zata bijiro miki da baki taba zato da tsammani ba." Hawaye ya zubo mata da ta tuna rasuwar Mal Muhammadu.

Washegari da wuri Mairama ta tafi gidansu Zainab. Allah Ya taimaketa bata mance hanyar ba. Mahaifiyar Zainab din ta samu wadda ta fada mata kwana hudu da suka wuce babanta ya kaita Kano gidansu Hadir. Duk da bata san kan garin Kanon sosai ta nemi tayi mata kwatance amma anyi rashin sa'a ko sunan unguwar bazata iya tunawa ba don wahala yake mata. Mairama tana kuka tace ta fada mata tazo itama zata koma garinsu.

"Kema mijin naki yaji rauni ne?"

"Rasuwa yayi."

Idanu ta zaro "idan Hadir yaji ban yaya zai ji ba. Allah Ya zama gatanku Mairama"

Sallama tayi mata ta koma gidan domin su karasa shirin tafiya. A daren jiya ta bude envelop din da Zayyan ya bar mata. Ashe gabadaya sauran kudin gadonsa ne ya bar mata da takardun gidansa na Kano. Dasu ta fita a jakarta idan ta koma zata fito dasu ta nunawa iyayen. Dama suna rayuwa ne bayan tafiyar mazan akan albashinsu da ake bawa matan. Kudi ne da bai wani taka kara ya karya ba. Wasikarta kuwa zuciyarta ta kasa bata kwarin gwiwar karantawa har lokacin. 

**********
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: BAYAN AWA TALATIN DA BIYU

Mutumin da ya kai rahoton karya ga rundunar su Zayyan shine durkushe a babban sansanin da su Major Mustapha suke. Kuka yake kamar karamin yaro ga sojoji sun tsare shi babu wasa a idanunsu.

"Ka tabbatar ba yaudararmu kazo sake yi ba?" Cewar Captain Jonah.

Mutumin ya daga idanunsa jajir ya sake maimaita musu cewa yan tawaye ne suka kamashi. Sunyi masa mugun duka sannan aka umarce shi da yaje ya san yadda yayi ya kawo sojojin Nigeria wannan wurin. Idan baiyi ba garinsu gabadaya zasu tasa. Tsoro ya sanya shi cika umarni. Amma suna zuwa da ya ga me ake yi ya gudu. Shine yazo nema musu agaji duk da yasan da wahala a samu mai rai cikinsu.

Yana rufe baki wani zuciya ta debe shi ya buga masa kasan bindiga a keya ya fadi sannan ya bishi ya rinka duka da kafcecen takalminsa. Da kyar aka rike shi kowa ya sani akwai kaninsa uwa daya uba daya a cikin wannan sansanin.

Motocinsu suka cika da makamai suka tafi tare da wannan mutumin. Daga nesa suke hango sauran hayaki ga kauri ya karade wurin. Dirgowa suka shiga yi daga motocin suna gudu har suka je wurin. Su din sojoji ne fa jaruman maza amma hankulansu sunyi mumminan tashi da ganin wannan kisan gilla da aka yiwa mutanensu. Binsu suka rinka yi daya bayan daya wadanda jikinsu yayi alamun harbi ne kawai likitocin cikinsu suna dubawa ko akwai masu rai. Basu yi dacen samun ko daya ba. Duk da haka shugaban tawagar yace su bazu cikin dajin babu mai tafiya sai sun tabbatar ba'a bar kowa ba.

Mutum biyu ne suka bi hanyar da su Zayyan suka wuce cikin sa'a sai gasu a bakin kwazazzabon da Major Mustapha da Lieutenant Hadir suka fada. Suna hangosu daya ya dira ciki dayan kuma yana daga waje ya fara kiran ga wasu gawarwarkin a nan. Sai dai me, yana juya Major Mustapha yaji yayi wani irin gurnani na azabar ciwo. Ya zubar da jini ba kadan ba wurin da kafar ta cire ya kumbura suntum ta soma yin kore. Ihu yasa yana kiran suyi sauri wannan yana da rai don bai ma gane shi ba.

Ya koma ya juya Hadir. Mamaki karo na biyu, shima da ransa saboda bugun zuciyarsa da yake a raunane amma baya motsa komai na jikinsa. Sauran sun zo an taru an fitar dasu cikin sauri suka isa sansanin inda aka wuce dasu bangaren kula da lafiya. Daki ne madaidaici da 'yan kayayyakin taimakon gaggawa da abinda ba'a rasa ba.

Komai cikin sauri ake gabatar dashi domin alamu sun nuna su biyun sun galabaita fiye da zato da tsammani. Anyi nasarar cirewa Hadir bullet a hannunsa sai dai buguwar da yayi wanda suke tsammani a kansa ne har yanzu bai motsa ko da yatsa ba. Babu kayan gwaje-gwaje sosai da zasu iya gano ainihin matsalarsa.

Major Mustapha shima an gyara wurin da kafarsa ta cire. Bayan allurai da ruwa da ake kara masa babban likitan Major Dalhatu ya tafi ofishin ogansu gaba daya a wurin. Izinin shiga ya nema ya tsaya a kame a gaban Colonel Fredrick Madueke.

"Sir they need medical attention more than we can provide"

Lt Col Madueke ya dago idanunsa sunyi ja kamar gauta. A yini daya sun rasa sojoji da dama wanda duka a karkashinsa suke a wannan tafiyar.

"I am trying to reach the HQ at Monrovia Captain . We need to fly them back to Lagos"

Captain Dalhatu ya juya ya fita bayan ya sara masa. Yasan Lt Col Madueke akwai tsantseni. Bazaiyi saken da rayuwar wadanda suka tsira zata salwanta ba a nashi bangaren.

Kwana daya, biyu, uku, hudu....shiru headquarter bata turo helicopter da suka roka domin a kai su Major airport din Monrovia ba. Lt Col Madueke kullum yana magana da headquarter sun ce suna jiran feedback daga Nigeria. Abu yaci tura suka debesu da kansu a motoci ga gargada da komai zuwa Monrovia din. Nan ma a basu dama ko izinin fitar dasu ya zama aiki. A haka sai da suka kwashe sati uku ana abu daya. Hadir yana nan jiya-e-yau. Major Mustapha kuwa ya farka amma azabar ciwon kafarsa tasa ya koma yana sumbatu. Dole yayi sambatu wurin ciwon nasa ya soma fitar da ruwa mai wari saboda kwayoyin cuta da suka shiga ga rashin kayan aiki. Anyi rigima harda nunawa juna bindiga tsakanin Capt Dalhatu da wani soja a headquarter din saboda rashin daukar patients dinsa da akayi. A haka sai manya masu mukami ko wanda yasan wani shine abin dubawa. Mu kasarmu har kullum wa ka sani wa ya sanka ce.

A rana ta ashirin da bakwai Allah Yayi aka dauki Major Mustapha da Lt Hadir zuwa Lagos. Yanayin da suke ciki suna bukatar taimako na gaggawa sosai. Kai tsaye aka wuce dasu 68 Nigerian Army Reference Hospital dake Yaba a Lagos. 

An yiwa Hadir gwaje gwaje karshe dai likitoci sunce kawai a jira ko dai ya tashi ko kuma rai yayi halinsa. Idan da hali ana bukatar 'yan uwansa domin jinya da kuma fara biyan kudaden asibiti idan ana son su cigaba da aiki a kansa. Buguwar da yayi a kansa sai ya farfado zasu san ainihin iya damejin da tayi masa. 

Major Mustapha kuwa aiki gagarumi yake bukata a rubabbiyar kafarsa. Ciwo wata guda ya ga izaya ra'ayil aini har yanzu bai san waye a kansa ba duk da ya farka. Dungulmin kafar ke fitar da tsutsa saboda rashin gatance musu da kasa tayi a lokacin da suke da bukata. Gasu da rauni ga rashin kayan aiki a inda suke. Anzo kasar tasu kuma asibiti na bukatar makudan kudade domin su yi masa aiki a yanke abinda yayi saura na kafar. Sojoji da basu kirguwa sun tafi da lafiya sun dawo gidajensu da nakasa ta har abada. Shima dai an bukaci a nemo nasa iyalin domin kulawa dashi da kuma kudin asibiti wanda gwamnati bazata iya daukar nauyi ba duk kuwa da cewa a kokarin bin umarninta suka riski kawunansu a wannan hali.

BOYAYYUN JARUMAI (NA SARAWA MATAN SOJOJI)

Jiniya ce irin wadda aka kunna ranar tafiyarsu yau ma aka saki. Motoci manya na sojoji suka rinka shigowa barrack din a guje zuwa bangaren ofisoshin manyansu. A can aka bada cikakken rahoto game da mutuwar gabadaya sojoji da aka dauka a ranar tafiyarsu Zayyan daga Giginya Barrack da kuma halin da Hadir da Major suke ciki. 

Wuri ba sai ya kaure da hayaniya ba, manyan sojoji ana ta shige da fice suna samun cikakkun bayanai. Tattaunawa ce tsakaninsu akan yadda ya kamata su bullowa lamarin. Masu aure cikin wadanda suka tafin wurin tara ne sauran duk samari. Wasu ma basu dade da zuwa barikin ba.

Matan wadanda suke asibiti dai babu yadda za'ayi a boye musu. Bisa wannan dalilin aka buga takarda mai dauke da bayanin halin da kowanne yake ciki za'a bawa matarsa.

***********

Mairama tana gidan Zainab taje kitso suna zaune daga bayan gidan wanda katanga ta karesu babu mai ganinsu. Sannan an dan zarta bangon gidajen ta barin hagu da dama domin ya zama kariya tsakaninsu da gidajen kusa dasu. Sai dai ba'a hade ginin ba zasu iya wucewa. Yawanci matan ke amfani da wannan wurin domin ayyukan da suka fi karfin cikin gidan kamar suya da babbar sallah.

Zainab tana yi mata kitson gefe Radhiya ce da Ibrahim an baza musu tarkacen wasa suna ta ihunsu irin na yara da duniya ta yiwa dadi.

"Ke yaushe zaki yi kitson ne?" Mairama ta tambayi Zainab

"Ai kallonki nake duk sati kitso, ni nan ina jiran muji kishin kishin din zasu dawo ne naje ayi min famin (perming ko saka relaxer). Ya tafi ya barni da kitson ya dawo ya tarar dashi. Hum'uhm"

Dariya Mairama tayi "nima da kika ga na nacewa kitson bana son haihuwa da kai a tsefe ne. Lokacin wannan yarinyar kan na kusa cizgewa don azaba"

Tafawa suka yi suna kyakyata dariya kowacce tana tuna nakuda da haihuwarta. 

"Kin gansu tafiya daga wata uku an shiga na biyar ga ki haihuwa ko yau ko gobe" cewar Zainab da 'yar damuwa a fuskarta.
Chapter 18 · 0% Book details