Sashe 112
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwalla ce ta taru a idanun Halifa ya fice daga dakin don babu yadda za'ayi ya fada mata abinda ya fahimta wato talaucin mahaifinta yasa take kinta. Dreban da ya kawo shi ya kira dama ya zaga cikin gari ne yace yazo su tafi an gama taron. Babu wanda ya yiwa sallama yayi tafiyarsa yana ji inama inama....don dai kawai uwa uwace babu yadda mutum zaiyi da ita.
Radhiya rarrashin Rahima tayi ta yi tace mata idan babanta zai yarda tazo su koma Abuja tare.
"Baffa baya son kwadayi Adda Radhiya" tace tana dan murmushi.
"Zuwa gidana sunansa zumunci ba kwadayi ba kinji ko." Ummi tace tana shiga dakin da murmushi saboda yadda take jin son Rahima a zuciyarta. Hannunta ta kama ta mikar da ita "Tashi in hadaku da Habu ya biki gidan ya tambayeshi idan yaso kya dawo bayan bikin Addar taku"
Baki ta bude da murmushi "Adda aure zakiyi?"
Ganin idon Ummi yasa Radhiya jin kunya ta fita daga dakin. Ita kuwa zaunar da Rahima ta sake yi tana mata nasiha akan hakuri da mahaifiyarta.
"Gwaggo na ga ku ma duk kun tsaneta kuma a gidan nata ma Alhajin kullum idan yana nan naje fada suke yi. Bata son kowa sai su Ya Halifa kuma itama ba'a sonta"
Wani iri Ummi taji zuciyarta tayi nauyi. Wane da ne zai so ya ga kamar ba'a son iyayensa? To Salame haka kawai hassada da kyashi yasa ta bata da kowa nata kuma rainin da tayiwa baban Rahima yasa bata son 'yarsa bayan saboda soyayya ko auren fari baiyi ba ya aureta tana bazawara.
"Ba tsanarta muka yi ba...kinga ki cire komai a ranki zamu daidaita kanmu babu ruwanku. Ke da 'yan uwanki zumuncinku nake so yayi karfi"
Idan ba kakarta ba zata rantse bata taba doguwar magana da wata mace mai matsayin uwa ba a gareta sai yau. Ashe salihancin nan duka rashin samun wuri ne don samun fuska da ta gani wurin kanwar mahaifiyarta yasa ta saki jiki ta rinka fada mata matsalolinta da tambayoyi kala kala sai ga Ummi tana dariya sosai saboda sosai take ganin zallar kuruciya tare da Rahima. Irin abinnan ne dai wai ita kada a raina talaucinsu shine sai tayi ta daure fuska.
Salame a zatonta ta tafi sai ganinta tayi da Mairama sunyi wajen inda mazan suke tana magana da Habu. To su din ma kowa yaji takaicin yadda ta rinka yiwa Rahiman shiyasa ba musu shi da Bature suka tasata a gaba har gidansu suka roki arzikin a barta tabi kanwar mahaifiyarta saboda suna son a farfado da zumumcin da aka saki a baya. Kakarta Iya abin yayi mata dadi don tasan Rahiman tana bukatar dangin uwa. Babanta kuwa da farko ki yayi sai daga baya ya rinka kashedin don Allah a cewa Mairama amana kada su wulakanta masa 'ya kuma a dawo da ita kwana uku bayan an gama bikin zaiyi daidai da kwana biyu kafin a koma 3rd term lokacin da zata koma makaranta suyi jarabawar fita. Da zasu tafi kowanne ya samo dan canjinsa ya bata ta shige da murna Iya tace maza ta debo kayanta masu kyan ta wanke.
Duk bidirin nan Salame bata sani ba. Kuma tafiyar tasu washegari ne don da dreba aka hadosu. Tafiyarsu Rugar Barkindo ma Zayyan ya nace suyi kwana biyu kacal har Radhiyan su dawo saboda gaskiya shi an cuce shi ace sai ana baifi kwana biyu daurin aure ba Alheran dinsa zata dawo gida. Har yaushe suka gama hirar yaushe gamo. Sosai ya rufe idanunsa yace idan Mairama bazata iya fadawa Innawuro ba shi zai fada ai ba rashin kunya yayi ba kawai yana bukatar lokaci ne da 'yarsa kafin ta koma karkashin wani.
"Son 'ya'yanka yayi yawa Sojana" Ummi tace tana dariya.
"Kada ki ga laifina kinfi kowa sanin ni dasu muna bukatar juna"
"Ni kuma ba'a bukata ta ko?"
"Ke kuma matsayinki ai ba irin nasu bane. Idan kin dawo sai in kara jaddada miki cewa Tureta na Fillo ne ita daya"
Hirarsu suke yi gwanin sha'awa bayan sun gama ta koma wurin Malamijo suna zancen bikin Radhiya da ya gabato. Don Zayyan ya fada mata washegari Rayyan da Badaru zasu je Abuja saboda zuwan iyayen Awwab wadanda Daddy Haroun zai yiwa jagora neman auren Alheran Radhiya.
***********
Karfe goma na dare bayan Radhiya ta gama shirin bacci ta dauko wayarta ta ga missed calls din Awwab rututu. Turo baki tayi ta kira shi ya soma mita kuwa saboda rashin daukar wayarsa da ta tsiri yi.
Ya damu sosai ya kwantar da murya a hankali yace "Me yake faruwa ne Schatzi? Nayi laifi?"
"Hammana yaushe zaka dawo ne" yaji tace kamar za ta yi masa kuka. Yadda yake missing dinta ma baya jin ta kama kafarsa amma da yake ita ce mai bakin rigimar sam ta hana shi sakat.
"I am trying to finish up da wuri na taho."
"To" kawai tace ya dafe kai don ya sani ranta a bace yake da dadewarsa.
Komai na Alheran burgeshi yake yi zuciyarsa tana kara aminta da soyayyar dake tsakaninsu cikin wani yanayi yana jan kowace kalma yace "Do you love me that much?"
Kunya taji ta kalli gefenta da Rahima take kwance da sauran 'yan matan babu mai bacci sai kawai ta suri hijan ta fice. Shiru yaji bata yi magana ba sai da taje wurin dan tudun nan na soron gidan ta zauna.
"Kasan ina nake yanzu?"
Yadda ta iya yi masa shagwaba haka ya koyi yi mata shima "Baki bani amsata ba ni"
"I do"
Shiru suka yi kowannensu na begen dan uwansa. Shi yayi ta maza ya tambayeta ina take din.
"A soron gidan Malamijo"
Ai kuwa duk abinda yayi a soron nan ya tuna. Zamansu na cin abinci da suka rinka kama-kama da cokali daya sai kuma ranar da ya fara bata ragowar alawar bakinsa ta shanye sauran kadan din ya karba ya karasa. Kewarta sosai ta kama shi ya riga ya sabar mata da yasha ko yaci abu ya rage mata. Sau tari yanzu yana kai abu bakinsa ita ce take fado masa ya rinka tunani kenan.
"Kin tuna min da memories masu dadi a wurin na kara missing dinki fiye da yadda nayi few seconds back. Bari na fada miki su daya bayan daya"
Ita kadai take ta sakin murmushi yana fada mata din. Sai kuma ya koma rigimar wai ta kalli tsabar idonsa tace bata son aure. Wannan rigima taki wucewa a wurin Awwab sai dai idan bai tuna ba. Zancen gidan da zasu zauna ya yi mata idan bata da matsala dashi dazu iyayen nasu maza sun fada masa za'ayi musu gyara a bamgaren Ummi na da kenan zasu zauna kusa da Mami da Mama. Idan ta gama makaranta gabadaya sai ya nemi wani saboda bashi da ra'ayin zamansu a Germany duk da can yake aiki. Tunda aikin ba na zama bane babu amfanin ya ajiyeta can. Duk lokacin da yake off duty zai dawo Nigeria. Yana so ta cigaba da Military Voice ne amma babu inda zai fiye masa sama da ace tana yiwa kasar haihuwarta wannan aikin. Kare hirar tasu yayi da cewa ta turo masa sizes na duk abinda tasan cewa da size ake saya.
"Kamar me da me?"
"Seriously Schatzi? Nayi zaton zaki gane ba sai munzo muna jin kunya ni dake ba. Ai dai kinsan nasan size din takalminki"
"Kunya kuma? Banda takalmin akwai wani abu ne da za'aji kunyarsa?" Tace batare da ta kawo komai a ranta ba.
"Eh to kamar b...."
Ihu ta saka masa ta ma manta dare ne da kuma inda take "zan yi maka text sai anjima"
"Silly girl....call me kafin ku tafi goben kuma ina jiran size din b..."
Kit yaji ta kashe wayar yana imagining din yadda take yi da fuska saboda kunya.
Washegari suka wuce Rugar Barkindo harda Rahima. Tunda take bata taba fita daga Sumaila ba shiyasa ta kasa boye farincikinta. Ko me ta tambaya Ummi da Radhiya basa gajiyawa wurin bata amsa. Nan da nan ta zama lively kamar ba yarinyar nan mai boye kunci a zuciyarta ba. A irin shekarunta na tashen 'yan matanci babu abinda take bukata kamar uwa da zata sakata a hanya ko da ba ita ta tsuguna ta haifeta ba. Jin kanta take yi wata daban itama kamar kowa. Ummi har wani dokin isarsu Abuja take yi domin ta hadata da Zayyana kawance.
Sakon Zayyan na a koma masa da 'yarsa ya riski Innawuro a take Ardo yace baiga laifinsa ba domin da ya girma dasu bazai fadi haka ba. Amma tabbas bayan aikin da ta tafi tana yawon garuruwa kuma ta dawo ana shirin aure ta sake nisa dashi bai kamata ba. Innawuro bata ji haushi ba sai ma dadin cewa mijin Mairama tabbas dan halak ne ya dawo da dakon son 'yarta kuma yana kokarin samun kyakkyawar fahimta da 'ya'yansa. Sai dai bata so yadda bata samu ta gyara 'yarta Mairama ba a lokacin nata auren jikar ma ta rasa. Su ma suna da hanyoyinsu na gyara amarya na gargajiya wanda bata so Radhiyanta ta rasa. Da suka yi kwana biyunsu suka zaga 'yan uwa ta hada kayanta ta bisu tunda su Ardo zasu je wannan babban taro na dawowarsa ga daurin aure sa dawo tare.
Kafin su isa Ummi tayi waya a kai mata Zayyana gida ta taho mata da kanwa. Mami sai ta nemi Ibrahim tunda bai koma ba sai farkon February. Kadaici ne ya dame shi saboda rashin Emzee kullum baya gida kamar yaci kafar kare.
A hanya suna tafiya tayi shiru kamar ba ita ba. Tun ranar nan da yayi mata magana akan dena kula shi da tayi bata yarda su hadu su kadai sai ta gudu. Kunyarsa take ji sosai kamar wani surukinta. Gidan Mama ma ta dena sakewa saboda tsoron kada ya rutsata. Gefen titi ya samu kusa da masu fruits. A tunaninta wani abu zai saya amma kowa yazo tambayarsa me za'a kawo sai yace babu komai. Wurin minti shabiyar Zayyana ta gaji da dukar da kan nata ta dago a hankali tace "washh" saboda kagewar da yayi.
"Da baki dago ba nan zamuyi ta zama" yace yana tayar da motar.
"Me yasa" ta tambaye shi murya kasa tana faman shafa wuyanta.