← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 157

Sashe 74

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hotunan da suke ta tafiya akan screen din masu ban tausayi ne da taba zukata. Wani ka ganshi a gidan giya, wani fuska da jiki bab u gyara, wani ya zama manomi a kyauye, wani yana nan banda tuna lokutansa a filin yaki ko azabar da yasha a hannun abokan gaba babu abinda yake yi. Wasu ma karamin hauka suke dawowa dashi duka a dalilin bautawa kasarsu.

"Da wannan nake rokon ku bani dama in zaga in fito da rayuwar sojojin nan duniya ta sansu ta kuma san cewa ko yaya suka dawo duk abinda ya samesu ya faru ne a kokarinsu na kare dukiya da rayukan al'umma. Ina so sojoji da iyalan da suka bari duniya ta kasa dubansu su sani cewa har yau har gobe suna daga cikin mutane mafiya girman daraja a bainar al'umma saboda sadaukarwasu garemu. Nagode"

Fitilun hall din aka kunna gabadaya mutanen wurin suka mike tsaye ana tafawa Radhiya. Cikin matan kuwa harda masu zubar da hawaye saboda tausayi daga hotuna da video din da ta nuna musu. Sallamarta akayi akace ta jira tare da sauran da suka gabatar da nasu. Sai bayan kusan awa guda an gama sauraron kowa aka kirasu domin jin sakamako.

Tante Nasara tana nan a korido din ta kasa zaune ta kasa tsaye motsi kadan sai ta kira Ummi tace wallahi ta saka mata 'ya a addu'a. Ummi sai dai tayi dariya tace ai tana yi.

"Tanteeeee" taji muryar Radhiya kafin ta farga daga ina ne taji ta rungumeta tana murna.

"Nayi ta daya Tante, zanyi Military Voice a Nigeria da Nijar"

Nasara ta rungume Radhiya tana ta murna. Ita take tuka su zuwa gida  yayin da Radhiya take ta waya da mutanen gida. Ummi, Mama da Baba, Daddy da Mami, Mammee dasu Alh Sidi. Ibrahim da Emzee babu wanda bata kira ba tana sanar dasu cewa su fara shiri tana nan tahowa Nigeria nan da sati daya.

***********

Sai kai kawo Ummi da Mami suke yi a hanyar dakin theatre din da aka shiga da Mama. Ciki ya wuce kwanakin da ake sa ran haihuwarsa harda sati takwas yana cikin wata na goma sha daya yayi mugun girma. An so inducing dinta da wuri taki saboda tsoro ga dadewa bata haihu ba. Daga baya da kyar Baba Hadir ya lallabata sai da Ummansa da Mamanta suka sa baki ma. Shine aka yi inducing din nata kwana biyu tana fama da matsananciyar nakuda amma haihuwa shiru. Yammacin rana ta biyu ne aka yanke shawarar yi mata CS.

Baba Hadir yana mota hankalinsa ya tashi matuka. Shiyasa ya bar inda su Mami suke kada su ga shima namijin yayi rauni. Zainab dinsa bazai taba iya hada soyayyarta da ta kowa ba. Tayi masa abinda har ya mutu bazai taba iya biyanta ba. Inama cikin zai dawo jikinsa da ya hutar da ita. Text din Ibrahim ne ya shigo wanda tun safe yake yinsu ya kasa amsa masa. Sauran kwanakin tana daurewa ta dauki wayarsa su gaisa. Sauransa jarabawa biyu ya gama level 2. Ummi ta riga shi gamawa dama ba department dinsu daya ba amma tare suke tafiya a karatun. Kwana biyu taje tayi a Sumaila ta wuto Abuja saboda sanin halin da Mama ke ciki haihuwa ko yau ko gobe. Yau da ciwo yaci karfinta har aka shiga cs din Ibrahim bai sami kowa ya daga wayarsa ba shiyasa gabadaya ya kasa sukuni.

Baba Hadir yana kokonton amsar da zai turawa dan nasa Major ya kira shi ba wai don ya amsa masa da baki ba, ya dai san zaiji me yace.

"Hadir ka bar mata a ciki suna ta nemanka an fito da Zainab. Mun sami namiji"

Kabbara Baba Hadir ya shiga yi a zuci yana ta kokarin ya iya fitar da sauti da bakinsa ma. Waye zai karyata Kadaitar Allah a matsayin Ubangijin talikai? Shi Hadir da ya shafe shekaru yana kwance sai yadda akayi dashi. Fitsarinsa da kashinsa tun dansa Ibrahim yana da karancin shekaru yake wannan dawainiya shine a karo na biyu ya sake haihuwa da Zainab. A take ya turawa Ibrahim kyakkyawan reply sannan ya fita daga motar ya koma ciki.

Dakin da aka tura Zainab din aka nuna masa. Ummi na rumgume da baby din an nado shi da shudin shawl mai laushi sai raba idanu yake yi. Mami kuwa ta saka shi a gaba wai yasan yana son kallon duniya me ya zauna yiwa kanwarta a ciki.

Sai da ya dan kwankwasa sannan ya tura kofar ya shiga. Zainab baki ya mutu tana kwance allurar anasiziya bata gama sakinta ba. Sai dai da yake ta ido biyu ce tana jin me suke yi tana murmushin wahala. A kusa da ita ya zauna a gefen gadon Ummi ta dora masa jajirinsa a hannuwansa da ya bude.

"Zz..Zayyyyan" Baba Hadir yace da dukkan dagewar da zai iya yana rungumar yaron a jikinsa.

Idanun Ummi tuni sun ciko da kwalla har ta fara zuba Mami ta riko hannunta suka fita domin a basu wuri.

"Hadir magana kayi?" Mama tace tana kallon fuskarsa.

Murmushi yayi mata yana shafa kanta da hannu daya ya kuma cewa "Zayyan"

"Alhamdulillah...don Allah ka rinka kokarin magana kaji. Ina son jin muryarka Baban Ibrahim da Zayyan"

Kai ya gyada yana ta murmushi idanunsa na yawo tsakanin baby Zayyan da Zainab. Tun ranar da aka tabbatar mata da cewa namiji ne ta sani ko bai fada ba sunan yaronta Zayyan. Ko yana da rai tasan su biyun masu musayar sunayensu ga 'ya'yansu ne bare kuma daya baya nan ya bar musu wawakeken gibi a zukatansu.

Kafin gari ya waye duk wanda ya kamata yaji haihuwar nan yaji. Iyayen Mama da na Baba murna ba'a cewa komai. Har waya suka yi suna yiwa juna barka. Soyayyar nan daga Allah ce. Dubi shekarun da tayi a gidan Alh Musa sau daya tayi bari sai gashi daga samun lafiyar Hadir anyi ciki har an haife. Wannan shine dan soyayya inji Mami.

Radhiya kamar ta jawo tafiyarta da ta rage kwanaki uku. Wani babban mall ta shiga ta jidowa kanin nata kaya na ga na fada ta kara akan tsarabar da ta gama hadawa. Duk zuwa gida sai tayi wannan tsarabar saboda bata ga me zata yi da kudaden da suke jibge a account dinta ba. Mijin Nasara yayi daga Nijar kakaninta kamar masu gasa da juna wurin yi musu aike ita da Emzee. Ga uwa uba His Excellency ya mayar dasu kamar masu daukar albashi.

Kwananta Mama biyu a asibitin aka sallamota. Ummi ita ce uwar da tsakaninsa da Mama shayarwa ce sai kuma dare idan zata koma gidanta. Mami kuma duk wata bukatar maijego tana wuyanta. Baba Hadir gani yake sunfi kowa sa'ar zumunta a duniya. Babu ta inda jini ya hadasu amma dangantakarsu kullum kara karfi take yi.

Fauziyya ta matsawa Bilal da zaiyi tafiya Lagos wani aiki ya kaita Abuja ita da Jawad dinta da ya fara yawo ko ina. Zahra ma Radhiya tana sayen ticket ta fara yi mata famfo har yau bata taba ganin Femi a zahiri ba. Ba don yaso ba Raji yace zai kawota amma da sharadin idan ya kasa hakuri zata ganshi kuma dole su tafi. Shima yana son zuwa gaishe da yan uwan iyayensa ne a Osun state shine zasu fara zuwa kafin.ya dawo da ita Abuja.

Gidajen uku sun fara shiri duk da an dage suna ma sai sunyi sati biyu maijego ta kara samun sauki.

Yau da wuri Ummi taje ta yiwa baby wanka ta dawo gida. Dakuna uku ne a gidan daya nata sai na Emzee da Radhiya idan sun zo hutu. Rigima irin ta Radhiya wai dambun shinkafa take so taci shiyasa Ummi ta koma gida ta dora. Idan ba haka ba tunda da Nasara zasu zo tasan sai sun hanata sakat da mita. Hadi na musamman ta yiwa dambun nan da kayan lambu da hanta gida ya kaure da kamshi. A wadace tayi shi kuwa saboda dawowar Radhiyan rana dayane da Zahra. Dama shirya abinsu suka yi wai sun dade basu hadu ba ana kewar juna. Mami ta aiko mata da farfesun kayan ciki cikin flask wanda ta hada dasu da zata yiwa Mama saboda a nan duka zasu ci abinci bangaren Ummin. Fauziyya tuwo tayi musu Zayyana 'yan mata kuma salad da drinks ta hada aka jere komai a gidan Ummi. Su Zahra da azahar zasu sauka Radhiya kuma sai biyar na yamma.

 Major jiran zuwanta kawai yake yi saboda murnar nasarar da ta samu na project dinta. Ita da Zayyana da ta gama secondary bana ya tanadar musu wani babban surprise.

Duka suna wannan abu Mama ta kira Awwab kwanaki biyu da suka wuce ta tambayeshi yaushe zai dawo ne yace sai nan da sati uku. Yanzu haka ya koma Germany babbar hedikwatar kamfanin nasu akwai abubuwan da zai karasa ya taho gida.

"Babu yadda za'ayi ka dawo ranar Juma'a?"

"Mama so nayi na gama komai yadda idan na dawo sai na cike wata biyuna kafin na koma aiki" ya bata amsa.

"Ni dai idan da hali ka taho ina son ka taho iyayenka na bukatarka. Ka kusa shekara fa rabonka da gida duka ka barmu da kewa."

"To Mama zanyi kokarin tahowa tare da Zahra tace min jibi zata taho. Idan na kwana biyu sai na koma na karasa aikin"

"Allah Ya shi albarka Awwabun Ummi"

"Amin amma naki ne yanzu. Ummi ta dade da yayeni ai. Kada ma kice musu zanzo ita da da Mami ba murna zasu yi ba."

Mama sai murna ta dana tarko zata sha kallo. Ta san idan Radhiya ta iso baifi sati biyu zuwa uku zata yi ba zata fara aikin da ya dawo da ita. Shi kuma kullum yana sama kamar tsuntsu har sai yaushe zasu daidaita ta ga ta fara shirin bikinsu.
Chapter 74 · 0% Book details