← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 157

Sashe 78

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Halifa yaro ne sa'an su Ibrahim sai dai ya fisu duka girman jiki. Ga tsaho kuma da 'yar kibarsa daidai misali ta hutu da jindadi. Bashi da matsalar komai a rayuwa sai mahaifiyarsa Salame. Duk kudin babansa yafi ganewa ya saya masa abubuwan bukata ya bashi kadan kawai don kada ya kai mata. Ita kuma da zarar ta ganshi tamkar ta ga nama ta rinka bani bani kenan. Ga matsalar muguwar kazantar gidanta ko yawu baya iya hadiya idan yaje. Kannensa na gidan idan suka yanyame shi ya rinka yamutsa fuska kenan. Daya kanwar tasa wadda Salame ta auri babanta farkon mutuwar aurenta bai fi sau biyu ya taba ganinta ba. Itama nata baban sai a hankali babu kudi amma dai bata da roko, sunanta Rahima. A haka itama bata huta da bani banin Salame ba idan taje gidanta idan tace babu ta hadasu ita da mahaifin nata da danginsa ta zagesu su tas. Yarinyar da iyakarta secondary don ma tana sana'ar kunshi da abin sai ya fi haka mun.

Washegari Alh Salisu da 'ya'yansa suka sauka a gidansa na Abuja yace su huta ana magariba zasu je gidan abokinsa.

**********

A can Jos Excellency bai huta ba Chibuzor bai huta ba. Bincike da tambayoyi yasa ake ta yi masa sai yau ya gama samun duk wata shaida da zata tabbatar masa cewa Chibuzor ba dan aiken 'yan hamayya bane sannan ba wata damfara bace ta kawo shi. Hankalinsa in yayi miliyan to a tashe yake da yasa shi a gaba yana bashi labarin rayuwarsu a kurkuku. Abu dai sai da ya kai Gwamna da zubar hawaye. Duk wani aiki da yake gabansa yasa an dakatar dashi domin ya samu yayi aikin Zayyan kawai. A ka'ida Major Mustapha da Hadir ya kamata ya nema amma sai ya tuna cewa yadda suka yi zaton Zayyan ya rasu haka shima yayi wannan tunanin. Abinda yaga yafi dacewa shine yaje ya kawo Zayyan Nigeria ya dangana shi da iyalinsa. Shawarar tayi masa, shi kadai bayan sunyi waya da matarsa akan zuwan su Awwab gidan ya sake shawarar gara ya tafi dashi ayi komai a gabansa har zuwa dauko shi.

Da wannan shirin suka kwana gobe zasu tafi Abuja shi da Chibuzor hedikwatar sojoji dake unguwar Garki. Mukaminsa na Gwamna kuma tsohon soja yasa tun a daren da yayi waya ya nemi ganawa da Chief of Army Staff Lieutenant General Enejo Adaji mutumin Kogi aka saka masa appointment din karfe biyu da rabi na rana.

Dukkan wata kulawa da ta dace da bako mai mahimmanci ita ake yiwa Chibuzor. Emma tayi murna sosai da ya fada mata yadda komai ya kasance. Da safe suna tashi da wuri aka dangana su da filin jirgi. Convoy din Excellency dama a Abuja suka kwana. Arifah da Mamanta sai ganinsa suka yi da bako kuma ko minti talatin basuyi a gidan ba suka wuce Nigerian Army Headquarters.

Bayan 'yan gaishe gaishe irin na manyan mutane Rtd Col. Nasiruddeen ya gabatarwa da Lt.Gen Enejo da Chibuzor da bayanin da yazo dashi.

Hankali a tashe Chief din na army staff ya soma buge bugen waya aka hau bincike a bangaren aiki da na'ura mai kwakwalwa akan waye Chibuzor Kalu, asalinsa da sana'arsa domin a tabbatar da ingancin zancensa. Yaga tasku ranar duk da babu duka amma fa an kaishi dakin bincike ace wannan ace wancan duk don su ji ko zai chanja magana idan bashi da gaskiya. A bangare guda kuma an binciko files din sojojin da aka tura Liberia daga Giginya Army Barrack na Sokoto a shekarar 1993. Zancen gabadaya an saka shi a jerin CLASSIFIED INFORMATION ba kowa ya sani ba sai mutane kalilan. Sunci karfin bincikensu washegari zasu nemi sa hannun shugaban kasa domin ya bada izinin ganawa da gwamnatin kasar Liberia. Excellency dai yayi ta rokon a gaggauta komai don a matse yake da yaga an fiddo Zayyan Tureta daga kasar nan.

*********

Alh Musa ne ya kira Ibrahim ya fada masa bakin da zasu yi yace ya sanar da mahaifinsa. Gobe zasu taho shi da Emzee. Ya gama jarabawa da kwana biyu kenan ya tsaya jiran Emzee su taho. Bayan ya fada masa shine ya kira Mama ya fada mata. Mamaki kwarai kuwa ya kamata ta sanar da Baba Hadir. Shi din ma mamakin yake. Yaushe rabonsa da Salisu, har ya manta. Rubutawa Mama yayi cewa ta fadawa Ummi tunda a iya saninsa akwai haihuwa tsakanin yayarta Salame da Salisu.

Itama tayi mamaki sosai nan fa suka hau shirin tarbar baki tunda ance shi da yaransa ne. Mama da Ummi suka yi ta mamakin wai yau Salisun da ko ita Ummi da ya taba auren yayarta rabonta dashi tun gaisuwar Zayyan. Halifa kuwa zata iya kirga sau nawa yaje gidan Malamijo tun tana makauniyarta.

Sun shirya komai a gidan Mama suka tafi yin sallah. Awwab, Yousuf da Raji basu wuni a gida ba ya kaisu ganin gari suma sai magaribar suka dawo.

Motocin biyu su Alh Salisu suka yi shi da 'ya'yansa. Daddy yaje gidan Daddy Haroun sada zumunci da magana akan halin da Ghazalatu take ciki a gidan Nura da ya fada masa. Shawara yake nema akan yadda zasu fadawa Alh Baba kada rigimar ta wuce yadda take yanzu don Gambo da Hussaina harda zage zage tsakaninsu. Rufa rufa suke yi kowacce bata son fitar da maganar kada aji ayi musu dariya.

A kofar gida Baba Hadir ya taresu suka karasa ciki shi da yaran. Zayyana ta tafi bangaren Mami da Hibbah wata  uwar surutu da karadi irinta. Yanzu take SS3 saboda haka hirar ta 'yan mata ce masu tashen girma. Kanenta su Husna suna can suna fadan daukar Femi da Jawad suna ta musu wasa. Dukkansu son yara garesu kamar su daukesu suke ji. A falon gidan Mama su Zahra sun gaishe da Alh Salisu suka koma bangaren Ummi a falo suka dasa tasu hirar. 

Baby Zayyan Ummi ta mikawa Alh Salisu yace "Mairama ko ina da bakin wanke kaina a wurinki da Hadir? Duk wani rikicin gadonku bani mantawa anyi dani haka lalurar Hadir amma neman kudi ya hanani yin abinda ya kamata. Tabbas ba karamar kunyarku nake ji ba ko ban taba auren Salame ba a matsayinki na matar Zayyan baici ace na yanke zumunta daku ba"

"Komai ya riga ya wuce sai dai mu fuskanci gaba. Kurakuranmu sai muyi kokarin mun gyara saboda kada yara su tashi basu san juna ba"

Halifa ya kalla da yake zaune ya karbi babyn yana masa wasa "Halifa wadannan duka iyayenka ne saboda haka a rike zumunci"

"In sha Allahu"

"Ina Ibrahim ne da Zayyan?" Alh Salisu ya tambaya.

Mama ce ta masa bayanin suna makaranta amma zasu taho gobe. Sai Radhiya da ya gani cikin matan da suka shigo dazu.

Awwab dasu Yousuf da suka dawo sun shiga bayan sun gaisa dashi Mama tace ya nunawa Halifa bangaren Ummi ya gaishe da Nasara tunda can zasu koma cin abinci. 

Fadan su Farida akan daukar yara har waje Radhiya tana alkalanci. Jeans ne baki a jikinta da top sai da dora hijab mai hannu da ya wuce gwiwarta kadan. Suna shigowa ta koma tana sulhun daga zaune.

Halifa ya kalleta ya kara duka akan idon Awwab yana mamakin yadda ta zama. Da kuruciya basa shiri saboda Salame ta koya masa kinsu haka itama bata son shi tunda dan Gwaggo Salame ne wadda bata son Umminta.

 "Radhiya bazaki gaisheni ba" yace bayan ya zauna.

Murmushi tayi tace "Ka rainani Halifa ko don kana ganin ka zama basamude"

Yadda take magana ya sashi dariya "ance Emzee yana NDA ko, ke kuma me kike yi yanzu? By the way you look great and ...beautiful"

Turnuku, ya kai Awwab wuya Yousuf ya koma kallon Awwab din yana dariyar mugunta.

"Thanks" tace da murmushinta.

Bai da son hayaniya amma yaji yana son tsawaita hira da 'yar uwar tasa da ya jima basu hadu ba.

"Da gaske fa da a waje muka hadu bazan ganeki ba. Nafi gane wannan terror din abokiyar fadana...tsoronki fa nake ji da"

Fauziyya sai ta tattara 'yan matan da yaransu suka koma daki saboda kada Awwab ya fashe musu a wurin. Da Halifa zai ga irin kallon da yake masa kila da yayi shiru. Radhiya ta gani sarai ko zama ya kasa yi amma ta biye masa.

"Ta da dinma tana nan sai dai idan ba'a tabota ba"

"Halifa mu bazaka yi hirar damu bane sai 'yar uwarka?" Yousuf yace domin ya kawo karshen hirar. A fusace Awwab ya juya ya fita. Kalmar great and beautiful ta tsaya masa. Jikin mota yaje ya tsaya sai ya sami kansa da kiran layinta.

Su uku suka rage a falon saboda Zahra tana can dakin Awwab da mijinta tunda ya leko suka fice. Yanzu hirar da Yousuf ake yinta yawanci akan makarantar da ya gama a Dubai da kuma wadda take yi yanzu.

Allah Yasa wayar na gefenta ta ga kiran ta dauka.

"Fito" kawai yace mata ya kashe.

Tashi tayi tsam ta saka wasu flat shoes dinta masu kyau ta fito wajen ta hango shi zaune cikin mota. Kallo daya tayi masa tasan ransa ne a bace sai taji babu dadi kuma.

"Hamma" tace a dan tsorace.

"Get in" ya umarceta. Bata ce komai ba ta shiga gaban ya daga waya ya kira Ummi yace mata Alheran zata raka shi siyan magani ba jimawa zasu yi ba. 

"Hamma baka da lafiya ne?" Idonsa akan titi yaki kulata.

"Ko mu koma gida a taho da namiji ka ga idan lalurar tayi tsanani sai an daukeka ni ba karfi gareni ba Allah."

Bai san lokacin da ya soma dariya ba tun yana yi a hankali har ta fito.

"Yanzu fushin ma bazaki bari nayi ba?"

"Fushin me?" Tace kamar bata sani ba 

Murmushi yayi "Ya wuce" 

Daidai nan ya wuce wani kanti ta hango katan din lemuka an jere a waje harda na maltina.  Kwadayin ne ya motsa ta dube shi.

"Hammaaaa" muryarta ta doki kunnensa da shagwabarta da take bashi sha'awa yanzu.

"Uhmm"

"Ka saya min maltina don Allah yanzu ka wuce shop din a can" ta nuna da hannu.

"Kinyi dinner ne?"

"Sai anjima"

"Bazan saya ba, na kula ba kya son cin abinci kema"
Chapter 78 · 0% Book details