← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 157

Sashe 136

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Labari yazo Zayyan ya mutu amma kika cigaba da nunawa Mairama kiyayya wadda har ta kaiki ga makanta ta. Abinda nake so ki gane Salame shine ba Mairama kika tsana ba kuma kiyayyarki ba gareta bane. KIYAYYAR SALAME GA SALAME TAKE. Rayuwarki ce gabadaya bata yi miki ba saboda kin ginata tun farko da hassada da bakinciki shiyasa komai baya burgeki sai abinda wani ya samu. Wanin ma wadda kika dauka kishiyarki baki son ta fiki da komai. Da ace kin kasance mai godiya ga Allah da karbar kaddara ina me tabbatar miki sai kin kwance zani kin baiwa Mairama kwance. Dubi irin dimbin arzikin tsohon mijinki yanzu. Ni fa banda kaddara babu wanda yayi tsammanin dawowata harda ni kaina. Dama kece babba a gidan nan amma da kin karbi rayuwarki ta farko da duk gidannan sai sunci arzikinki. Kin sake aure kin dauki karan tsana kin dorawa Rahima saboda ba auren bane a gabanki lokacin. Burinki ace kin yiwa Mairama zarra kuna zawarci ke kin rigata samun mijin aure saboda kin fita da komai. Nasan akwai kaddara da rabon haihuwa a kanki amma duk da haka yadda kike tafiyar da rayuwarki shine ya munanaki a gaban 'yan uwanki."

Mayar da hankalinsa yayi ga Malamijo da Ta Madina "ga iyayenki nan kowa cikinsu fushi yake da ke. Duk wanda kika raba kin zalince shi musamman 'ya'yanki kin bar musu abin fada wanda nake fata zancen ya mutu a gidan nan. Ki gyara rayuwarki wannan shawara nake baki idan kuma kinki ji to na tabbata jikinki yana kaikayi ne na son a taba lafiyarsa mu kuma zamu taba"

Shiru dakin yayi na wanu dan lokaci kafin Malamijo yayi gyaran murya ya soma magana "Zayyanu nasan Salame tayi ba daidai ba amma ina tuhumar kaina da zama silar komai. 'Ya'yana ban basu damar girma da iyayensu mata ba bare su samu ingantacciyar tarbiya. Babu wanda nasan damuwarsa a cikinsu hankalina yana kan dabbobina da yawan aure aure. Gashi an wayi gari ana ta sako min 'ya'yan bayan dogon jinkirin da suke samu kafin manema su fito. Nima ban rike Mairama da 'ya'yanta rikon da ya dace uba ya yiwa 'yarsa da take cikin halin bakincikin mutuwar miji ba ta yaya 'yar uwarta da ta bari shaidan yayi galaba a kanta zata yi. Ka yafe min do Allah do Annabi"

Kunya ce ta kama Zayyan yace masa dama daga shi har Mairama basu rike shi a rai ba.

"Ke kuma mutuniyar banza tashi zakiyi ki roki kowa gafara musamman Mairama da Rahima da kika rinka zalinta" cewar Ta Madina.

A sanyaye Salame ta fara cewa su iyayenta su yafe mata zuciyarta tana ta harbawa ta ma kasa gane wane hali take ciki. Bayan sun ce sun yafe ta koma ga Zayyan shi kuwa kofa ya nuna mata "kije ki sasanta da kanwarki sannan yanzu zan tura su Rahima su dawo ki daidaita tsakaninki dasu. Wannan magana bana so su sani kwatakwata burina kawai ki rungumi 'ya'yanki ki basu tarbiya mai kyau musamman wannan yarinyar da kika zo min gida da ita sai kin tashi tsaye." Yace yana tuna irin rashin kunyar da yaji Khadi tana yiwa Rahima watarana a Abuja.

Mikewa yayi zai fita ya dan dawo sai da gabanta ya doka "yauwa zanyi magana da shi baban Rahima yanzu sai dai ina son yi a gabanki so ki biyoni don ina sauri ne"

"To" tace da azama tana bin bayansa.

Suna zuwa soron su ka same su zaune akan tudun nan kowanne cikinsu ya mike da sauri. Zayyan hannu ya mika musu suka yi musabaha sannan ya kalli Baffan Rahima saboda kamanni da suka nuna shine baban nata.

"Ni sunana Zayyan" yace dashi.

"Idris nake" Baffan Rahima yayi masa murmushi.

"Ni kuma Alhaji Indararo aka fi sanina dashi" cewar maigirma miji na Salame.

"Mal Idris alfarma nake nemarwa kaima da iyalina Mairama"

"Haba Yallabai ni kuwa har wace irin alfarma kake tunanin zan iya yi maka?"

Zayyan ya kalli Salame sannan ya kuma kallonsa "Rahima nake so ka bamu idan babu takura. Dan zaman da mukayi da ita ta shiga ran kowa a gidan musamman ita Umminsu. Don Allah ka bamu ita kafin nan da Allah Ya kawo mata mijin aure ta sami soyayya da gatan da ta rasa na mahaifiya"

Baffan Rahima bai san lokacin da murmushi mai hade da dariya suka kwace masa ba "Yallabai Rahiman tawa ita ce kuke so?"

"Ta cancanci soyayyarmu kuma nayi maka alkawarin zamu riketa kamar 'yar cikinmu"

"To Yallabai za ku rinka kawota in ganta ko?" Yace a raunane harda 'yar kwallarsa.

"Wannan kuma dole ne" Zayyan yace yana dariya.

Mal.Idris ya kamo hannunsa "na baka Rahima amana Yallabai duk da nasan bata baki nake yi ba sai na fada ba. Nagode nagode sosai"

Juyawa Zayyan yayi ya tambayi Salame  "kina da abin fada game da hakan?"

Kada kai tayi a sanyaye. Alh Indararo ya murmusa "sannu da kokari Yallabai nima ina da yaran wallahi biyar ta haifa min duka mata. Bari na garzaya gidan na turo maka su sai ka zaba"

Dariya Zayyan ya danne a ransa kuwa yana tunanin ko ganinsa bazasuyi ba. Su ai 'ya'yan so ne basu da matsala. Ra hima kuwa ya fuskanci abinda Mairama keso kenan amma ta kasa fada masa saboda gudun kada yaki amincewa saboda halin Salame.

"Kina iya tafiya ki turo min matata idan kin shiga" Zayyan yace da Salame.

Ciki ta koma jiki a sanyaye yawancin kowa ya fito sun cigaba da harkokinsu  murya na rawa tace wane daki Mairama take. Da hannu Nene Marka ta nuna mata.

"Dama kiranta yake yi maigidan"

"To ni zanje in fada mata?" Cewar Nene.

"A'a" tace da sauri sannan ta shiga dakin yau harda sallama.

Mama ce ta amsa mata a fili Mairama kuwa a zuci ta amsa ta kawar da kanta gefe.

"Ana kira"

"Wa ake kira?" Mama ta tambayeta.

"Ita" Salame ta amsa tana nuna inda Mairama ta juya mata baya. Murmushi tayi duk da bata ganin fuskarta amma muryar Salamen tayi laushi a zuci tace kadan ma kika gani. Dama tayi kwalliyarta tayi kyau ta yafa mayafi a kafada ta fita ko kallon inda Addarta take bata yi ba.

Tana zuwa soron kamshin da yanzu mijin nata yafi amfani dashi ya doki hancinta ya mika mata hannu sai da ta waiga baya ta kuma kalli kofa ta girgiza kai.

"Za'a iya shigowa fa"

"Fillo rowa zaki min?"

Murmushi tayi ta taho gareshi ya rungumeta tsam yana jin wata nutsuwa tana ratsa shi. A kunnenta ya ce "Fillo ashe an sami karuwa? Allah Ya raya mana"

Gabanta ne yace das tsabar tsoro ta dago da sauri "rufa min asiri ni wallahi bani da komai"

Dungure mata kai yayi "matsoraciya kawai....barkar samun Rahima nake miki"

"Rahima kuma Sojana?"

"Mun gama magana da babanta yanzu ta zama 'yar Zayyan da Fillo"

Mairama bata san lokacin da ta kankame shi tana murna ba. Godiya take ta zuba masa cikin nutsuwa ya soma mayar da godiyar wani abu daban sai da taji kamar motsin ana tahowa tayi saurin matsawa gefe yana yi mata dariya.

"Ni yau zan koma amma Abuja zan tafi please ku dawo waahegarin bikin nan bana son zama babu ku a kusa. Sannan na kashe case dinnan ki bata dama ta gyara kuskurenta"

Dan jimm tayi kafin ta kada kai "shikenan, amma shine ka tsorata mutan gidannan da dakarunka ko"

"Bukatata zata biya nasan in sha Allahu zata gyara. Da farko tafiya naso yi da ita amma kinga amfanin shawara Major da Hadir suka kwabeni da hukunci cikin zafin rai. Tabbas na yarda Salame mai laifi ce sosai wadda bata cancanci a raga mata ba ko kadan. Amma ta bakin Major yace ku mata idan aka nemi a ci ku da wuta sai ku sake botsarewa baku ki ayi kan mai uwa da wabi ba. Muna iya hukuntata ta dawo yadda ta taba zuwa wurin boka yanzu ma ta sake iyaka dai a sake kamata wadda bazata damu ba indai bukatarta zata biya. Ina ganin mu bata wannan damar idan ta sake baudewa kuma to zan hadata da masu ladabtar da ita in and out"

Kwalla fal idon Mairama tace "nagode Sojana Allah Ya saka da alkhairi. Amma zaka jira yaran su dawo ko...idan ka tafi wannan yarinyar damuna zata yi ta hanani sukuni. Mutum ya girma sai sabuwar sangarta ke shigarta"

Murmushi Zayyan yayi "dole na jira. Ya batun abincin mutanen nan?"

Mairama tace masa an kusa saukewa. Waya ya dauko ya kira Emzee da suke tare da Awwab da yace su jira ko a gonar Malamijo ne sai ya kirasu. Mairama ce ta karba ta fada masa inda su Radhiya suke tace su daukosu su dawo gidan.

Zamanta tayi suna ta hira da Zayyan a ciki kuma Salame ta shige tsohon dakinsu da Mairama zuciyarta sai zafi take ta rasa inda za ta saka ranta taji dadi. Duka fadin gidannan kowa baya sonta tayi bakinjinin da ita da kanta ta rakitowa kanta.

***********

Mota bata karasawa kofar gidan saboda haka daga can nesa kadan Emzee yace Awwab yayi parking ya karasa a kafa. Ya shiga suna gaisa da mutane Radhiya da Rahima a tare suka ji muryarsa. Radhiya ce ta fara fitowa daga dakin da suke da sauri Emzee yayi kamo hannunta a dan birkice saboda fuskarta da ya gani tayi ja.

"Adda ina da ina ne yake miki ciwo? Kun koma asibitin? Sun baki magani?"

Murmushi tayi "kai Emzee irin wannan tambayoyi"

"Da kyar na wayi gari inata tunanin ko yaya kika kwana. Zo mu tafi tare muke da Hamma" yace yana kallon Rahima dake tsaye a bayanta ta janyo hijabinta ya rufe mata fuska.

Mamaki ya kama Radhiya duk da tasan  cewa dama zai damu saboda rashin wayarsu jiya. Yau kuma tun safe take gwada tasa wayar a kashe ashe yana sane. Murmushi tayi dimple dinta ya shige ciki sosai ta kamo hannun Rahima tana ce masa itama fa akwai ciwon a jikinta.

Tabe baki yayi "Allah Sarki"
Chapter 136 · 0% Book details