← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 157

Sashe 12

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai hoto aka kira yazo akayi ta dauka. Gwaggon Zayyan tace suyi su uku zata kai hoton gida. Days suka dauka a tsakar gidan a tsaye tana rike da Radhiya shi kuma a gefenta. Dayan kuwa dakin Innarsa yace su shiga a kan tsohon gadonta ya zauna da 'yarsa a hannu ita kuma a kusa dashi. Daga nan ta kira danta Awwab ta dora masa kanwarsa tana tallabe da kanta daga bayansa ta dan duka aka yi musu sannan Zayyan ma ya shiga.

Ranar idan ka gansu dole su baka sha'awa. Mutan Agadas har irin abincinsu sun dafa duk na bikin dansu Zayyan da murnar haihuwar Alheran Radhiya.

A gidan maijego ta kwana ranar tare da danginsa ana ta bata labarin 'yan uwansu da irin yawan danginsu. Gwaggon Zayyan tace mata cikin gurbatacciyar hausarta da ace Zayyan ba soja bane gida Nijar suka so komawa dashi bayan rasuwar Mal Muhammadu.

"Idan ya sami saukin aiki ku kawo mana ziyara kinji Mairama. Zayyan dan gata ne saboda yana zagaye da dangi masu kaunarsa saboda maraicin uwa. Da mahaifinsa ya amince min naso tun rasuwar Alheran na dauke shi."

Hawaye ta ga dattijuwar tana gogewa shiyasa taji zuciyarta ta karye "In sha Allahu zamu zo"

"Allah Ya nuna mana"

Mairamu a ranar tayi kwanan farinciki da bakinciki duka lokaci guda. Soyayyar da ta samu daga wurin dangin mijinta ta tsaya mata a rai tayi matukar farinciki. Sai kuma tunanin dangin Innarta da babu wanda zata iya nunawa tace nata ne ta wannan bangaren. Sun manta da ita da shafin rayuwarta saboda rashin uwa da tsanar da suka yiwa Malamijo akan rikon sakainar kashin da ya yiwa 'yar uwarsu a gidansa.

Asubar fari aka fara tashi saboda masu shirin komawa. 'Yan Sumaila ne farkon tafiya aka bar Nene zata zauna wanka idan sunyi arba'in su tafi Sumailan tare. Mutan Agadas ma kaf sun gama shiri wai basa son dorawa Zayyan nauyi idan suka cigaba da kwanaki. Kawunnansa biyu ne a cikin tawagar Ghoumar da Sidi. Shatara ta arziki suka yi masa kyautar kudi da irin abin amfani nasu na can. Kamar kada su tafi haka Mairama taji har kofar gidan inda bus guda biyu zasu daukesu tayi musu rakiya.

Daga nan gidanta ta koma tare da Yadikko da Salame su ma a ranar zasu wuce.

Manya akwai kaifin tunani da hangen nesa. Cikin kankanin lokaci Nene ta gane manufar Salame akan Zayyan. Tasha mamaki ba kadan ba saboda a da tana yi mata kallon wadda zata iya sadaukar da komai domin farantawa kanwarta. Ashe abin ba haka yake ba. Ta ciki na ciki ne. Jan bakinta tayi ta tsuke bata tona ba sai dai ta jasu su biyun tayi musu fada akan sabon yanayin alakarsu.

"Nene gara da ki ka kula, ki tambayeta idan na mata laifi ne na bata hakuri"

Kallon Salame Nene tayi ta dauke fuska tare da janyo jakar kayanta tana shan kunu.

Nene tace "Salame idan ma da sabani na kula kece kike jansa. Tun zuwanki ina lura dake ko da wasa wallahi baki dauki Radhiya ba."

Saurin kallon Mairama tayi don kuwa hakan ne. Mairama tuni ta gane shiru kawai tayi.

"Nene bana jindadi tunda nazo garin nan shiyasa. Mairama Allah Ya baki hakuri...shikenan ko" tace a kagauce tana son fita daga dakin.

"Juna biyun shine zai sa ki kasa daukar 'yarki? Ki dai yiwa kanki fada don rayuwa bata da tabbas"

Mairama bata ma tanka ba ganin za ta rana musu wayo. Da zasu tafi Salisu ya kawo kudi ya bayar a sayawa Radhiya kaya harda cewa inji mamanta Salame. Godiya suka yi masa sun san kuma kara ce kawai yayi amma babu wani inji Salame.

Sun shiga gidan Nene ta goya Radhiya ta shige daki wai garin akwai sanyi. Ga gida mai daki daya tana rufo kofar Zayyan ya rungume Mairama harda ajiyar zuciya.

"Na wahala Mairam, na wahala sosai"

"Taron jama'a ko?" Tace tana kokarin kwace jikinta kada Yadikko ta fito.

"Wane jama'a, a kaina suke? Rashinki ne ya addabeni."

Murmushi tayi ta sunkuyar da kai ya dago habarta "dadina da mutum kunya. Yaci ace mun wuce wannan matakin fa, ga 'yar soja can kina gani"

"Ni dai kazo ka tafi kada ta fito ta sameka"

"Kin yarda zaki yi min irin kwalliyar jiya idan ta tafi?"

"Na yarda"

Rungumeta ya sake yi sosai "Ina sonki Mairam, shigowarki rayuwata ya sanyani farinciki mara misaltuwa. Karo na farko naga da dangin Innata su ka zo da yawa haka saboda ni. Kuma duk a dalilinki ne da kyautar Alheran da kika yi min. Nagode"

"Ina fatan Allah Ya bani ikon cigaba da kyatata maka Sojana. Kayi min komai a rayuwata. Ka rabani da kunci da bacin rai. Ka zame min miji, aboki kuma dan uwa"

Kashe mata ido yayi "ina ma daga ni sai ke a gidan nan kike wannan kalaman"

Ta gano manufarsa ta shiga dariya a hankali. Kofar dakin aka taba ya tashi a guje ya fice ita kuma ta dake fuska kada Yadikko tace me suke yi.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: ***********
Kyakkyawar kulawa da gyara Mairama take samu daga wurin Nene Marka. Ita da Zainab da Mami shakuwarsu sai gaba take kara yi. Idan kaga Awwab baya gidan to makaranta ce ta tsare shi ko dare ya tafi yayi bacci. Amma kullum yana wurin Mairama da kanwarsa Radhiya. Zahra da Fauziyya suna shan gori yayi ta cewa su Antinsu bata kawo baby ba har yanzu. Idan ya fadi haka Zahra sai tace ai nata cikin ya kusa fashewa ne su ma bazasu bari ya taba musu baby ba.

Zayyan ba karamin kewar matarsa yake ba. Ko yaya Nene ta dan bada wuri sai ya faki ido ya rungumeta yana fada mata yadda yake kewarta da matsuwa ayi arba'in dinnan kowa ya huta. Jaririyarsu Radhiya ta kara yin bulbul gwanin sha'awa. Idan kayi mata kallo daya sai ka rasa wa ta debo cikin iyayen. Bafillatanar mahaifiyarta ko sojan babanta da yake surki tsakanin mutanen Agadas da na Tureta. Yarinya ce mai matukar shiga rai musamman idan tayi murmushi gefen kumatunta na dama ya lotsa. Awwab har yatsa yake sakawa a wurin don kawai tayi masa murmushi.

Ranar da su ka cika wata biyu Zayyan ya kwashesu a motar haya sai Sumaila. Mairama bata taba tunanin zata yi kewar gidansu ba sai yanzu. Sun isa yamma likis 'yan uwa ana ta tururuwar ganinsu.

Malamijo yana jin isowarsu daga gona ya zari takalmansa ya yo gida. Fadi yake 'yarsa mai auren soja ce ta iso tare da jikarsa. Abin arziki kaza guda ya bayar irin 'yar sati goman nan aka yanka Yadikko ce da girki tayi musu shinkafa da miya.

Daki aka gyarawa Zayyan ya kwana. Da safe abin mamaki sai ga Salame wai bazata iya jiran su iso gidanta ba tana kewar Radhiya. Mairama taji dadi balle da ta ga yadda take haba haba da Radhiyan harda su goyo duk da ana hanata saboda nata cikin ya fara fitowa.

Zayyan dauke kai yayi saboda shige masa da take yi tana ta so ko magana yayi mata. Allah sai Ya dauke hankalin Mairama daga garesu bata kula ba.

Kwanansu biyu sannan su ka wuce Balan a karkashin karamar hukumar Gaya inda gidan Nene yake. Tana da kishiya guda daya mai yara shida. Maigidansu manomi ne babu wani kudi sai rufin asiri. Irin kyautar da Zayyan yayi mata Mairama kanta tayi mamaki. Nene Marka harda kuka tana masa godiya.

"Nene mune da godiya, Allah Ya saka da alkhairi. Idan ta sake haihuwa ke zaki dawo ko?"

Mairama ta tashi daga wurin da sauri saboda kunya. Nene tayi masa dakuwa tana murmushi "kuji min dan kaniya, wato a gaban nawa kake rashin kunya ko Zayyanu"

"Fada nayi fa saboda kada ace wata daban ce za ta zo." Tare su ka yi dariya don ta saba da barkwancin surikin nata.

Kofar dakin ta kalla ta tabbatar Mairama tana wurin kishiyarta sannan ta dan matso fuskarta babu alamun wasa "Zayyanu nasan kana sane da son da Salame take yi maka"

Gabansa ne ya fadi ya dago kai yana kallonta da kallon kofa "Nene ki bar zancen nan, yau ko Mairam zata fadi ta mutu bazan auri Salame ba. Matar da aure bai hanata nunawa mijin kanwarta soyayya ba"

"Tun yaushe ta fara son ka?"

"Kafin muyi aure...don Allah bana son kowa yaji. Ni dai babu abinda ya taba hadani da ita"

Hankalinta taji ya kwanta "nagode Zayyanu. Ka rike min amanar Mairama. Ga maraici ga rashin dangin uwa har yau mun rasa a wace rugar ma suke zaune. Duk tsiyar Malamijo yana ta kokarin nemansu domin ya faranta mata. Salame kuma ka barni da 'yar banza. Idan ta nemi tada muku hankali da kaina zan gyara mata zama don ba gagararmu tayi ba"

Kafin azahar sun koma Sumaila inda ta sake kwana biyu suka bar garin bayan ihsani mai tsoka da ya yiwa Malamijo da matan gidan. Mairama har mamakin ina ya sami kudi haka takeyi saboda ita tasan duka duka albashin nasu babu wata tsokar kirki.

Sun baro Sumaila tana sa ran za su wuce Sakkwato sai gani tayi sun shiga cikin Kano zuwa wata unguwa yana yiwa dreba kwatance. Gaban wani gida zubin zamani a wancan lokacin mai kyau da tsari tun a waje aka ajiye su. Mukulli ya dauko da ga aljihunsa ya bata yana dauke da Radhiya.

"Bude mana da sunan Allah"

Kallon tuhuma take masa yayi murmushi da ka yayi mata alamar ta bude. Ba musu ta bude yana cewa ta shiga da Bismillah. Farfajiyar gidan tana da dan girma daidai mota guda daya. Sai kuma ainihin ginin wanda flat ne gidan. Yana gaba tana biye dashi zuciyarta da tarin tambayoyi har ciki.

Wani korido su ka fara bi a karshensa kofa take inda suka tarar da katon falo ga kofofi a ciki. Daya bayan daya suke shiga yana mata bayanin. Kitchen, dakuna hudu, store da kuma bandakuna ko ina da fenti amma babu kaya. Daki daya ne aka shimfide da leda ga katifa sabuwa da filo biyu sai zanin gado a cikin ledarsa ko budewa ba'ayi ba.

"Sojana ina ne nan?"

"Mairam ga gidan mijinki na halak yau kin shigo"

"Gidanka ne nan?"
Chapter 12 · 0% Book details