Sashe 156
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lafiya dai kike min dage dage?" Cewar Ummi.
Sake baza hanci tayi da kyau tace "Ummi warin magani ko dai maganin Nasr ne ya zube a wani wuri?"
Daada na jin haka ya ajiye jaridar hannunsa yana kallonta "maganin kamar panadol yake Alheran?"
Ta tafa hannu "eh wallahi Daada ka canka..."
Ummi ya kalla ya soma dariya yana cewa "kina ji kamar ma ya rube ne?"
Awwab ne ya bashi amsa "jiya sai da tasa na na juya gado da shirin falo gabadaya muna neman maganin da ya rube. Kuma ni bana jin komai wallahi ita kadai take ji"
Dariya sosai Daada yake yi Ummi ta bar wurin da sauri don kunya tana ji yana cewa "wannan warin bazaka taba jinsa ba Awwab. Ke kuma sai hakuri yanzu kika fara ji amma ku je asibiti kiyi musu complain. Ina jin likita kika hadiya"
Ta zaro ido "likita kuma Daada?"
Ummi na jinsu ta dawo da sauri saboda ba karamin aikin Zayyan bane sakin baki a gaban suruki shiyasa tace yazo wayarsa na ringing. Ita kadai ta dawo daga baya suka yi sallama Awwab ya wuce asibiti da ita duk da tana cewa babu inda yake maga ciwo sai warin maganin. Gwajin ciki suka yi mata tana dashi har na sati tara.
Murna a wurin Awwab ba sai an fada ba. Auren nasu shekara guda da watanni kadan ga Arifah tana nan da Nasrin dinta wadda sunan Tante taci aka juya mata shi.
Tare suke kula da cikin yana ta girma har yayi wata bakwai. Laulayi gareta kamar Ummi shiyasa idan zai koma aiki sai dai Zayyana ta dawo gidan ko Rahima.
Ranar wata asabar tafiya ta kama Daada zuwa Asaba aiki shi da wasu a karkashin jagorancinsa. Convoy din motoci biyar suka yi ciki Emzee da yake ta fushin kasa samun kan Rahima yace zai raka shi. Basu taba tafiya daga shi sai dan nasa ba saboda haka wannan ta basu damar yin hira sosai irin ta uba da da. Zayyan yasan komai game da lamarin Rahima ya rinka bashi shawarar yadda zaiyi ya shawo kanta su daidaita.
Sun wuce wani kauye da kadan su ka kula motoci da yawa suna dawowa a guje wasu ma da ribas suke tafiya. Nan da nan yaransa su ka fara kiransa suna tambayarsa ko su ma su juya.
"Are you crazy?" Ya dakawa mai tambayar tsawa "civilians su gudu muma mu gudu to waye zai kai taimako idan ana bukararsa"
Kai tsaye ya bada umarnanin kada a tsaya. Kowa yana sanye da kayan sojoji tunda official tafiya ce banda Emzee dan rakiya. Suna karasowa motoci suka gani guda shida da 'yan fashi su ka kama sun kashe titin ta daya bangaren babu mai karasowa ga harbi suna yi kamar hauka sun kashe drebobi uku masu kokarin guduwa. Ganin motocin sojoji ga su suna dirowa da shirinsu yasa ogansu kiran wadansu ashe mugun yawa garesu.
Tashin hankali ne muraran mutanen da suka biyo hanyar suka tsinci kawunansu a ciki. Baka jin komai sai tashin harsashi da kukan mutane. Abin ya wuce zatonsu dan karamin kauyen da yake gefen wurin shima sun yiwa mutanensa mummunar barna saboda rashin basu mafaka.
Jikin Emzee a take ya fara rawa yau gashi a filin daga na gaske. Major General Zayyan tuni ya fito daga mota a sukwane babu wani tsoro ko fargaba yana bada umarnin duk wanda su ka kama zaiyi gardama su harbe shi a inda zai raunata shi sannan su tabbatar anyi saving mutanen wurin.
Bindiga kirar AK47 ya dauko ya damki hannun Emzee ya bashi cikin rawar hannu ya saketa a kasa ga sautin harbi da kukan mata daga wannan kauye ya yawaita.
Dauko bindigar Zayyan yayi ya ratayata a hannunsa kamar yadda ya rataya wadda zaiyi amfani da ita ya rike fuskar Emzee a tafukan hannunsa.
"MUHAMMAD" ya kira shi da murya ta umarni babu wasa ko rangwame saboda dan cikinsa ne "this is why you became a soldier Lieutenant. You live and die for your country. Wancan kukan da akeyi da firgici aikinka ne ka tsayar dashi ka tseratar da mutanen nan"
Jiki na rawa ya gyada kai yana jin kunnuwansa na neman toshewa saboda bala'i.
Bindigar Zayyan ya sake mika masa yana jin wani karfin gwiwa su ka fara hawa dan tudun da zai karasa dasu kauyen Zayyan yana ta bada umarnin a kwashe tseratar da mutanen da aka kamawa motoci su bar wurin. Saboda wutar da aka bude 'yan fashin da yawansu sun buya ne a bayan gidaje suna harbin kan mai uwa da wabi.
Sai da suka gama hawa tare da wasu sojojin Zayyan ya rike hannun Emzee idanunsa suka dan kada na dakika kadan "ka taimaka min na maidawa Mairama danta cikin aminci...Allah Ya tsare min kai"
Bai jira komai ba ya kusa kai tsakanin katangar wani gida da na kusa dashi inda ya fi jin harbin ya soma sakarwa 'yan fashin nan harsashi. Emzee tuni ya nemi tsoro ya rasa sai aikin neman lada ya bautawa kasarsa. Harbi suke yi ba kakkautawa sai da suka tabbatar sun kora 'yan fashin suka soma dauko mutanen da suka jikkata a wurin suna dawo dasu bakin titi bayan kiran waya domin a kawo musu agaji.
Duk sunyi futu futu dasu a tunaninsu sun gama Emzee ya jiyo kukan mace daga wani gida. Kutsa kai yayi ya hadu da mata mai tsohon ciki a durkushe tana murkususu. Fita yayi da sauri ya kira Zayyan dake rike da wani tsoho. Wani sojan ne ya karasa da tsohon shi kuma ya bi bayan Emzee. Suna shiga gidan aka rufe kofa 'yan fashin nan su hudu su ka sakawa matar bindiga sannan aka umarci Zayyan ya fadawa yaransa kowa ya bar wurin saboda tsaron rayukansu suka yi garkuwa da su.
Tsananin tashin hankali sun shige shi domin matar gidan tana cikin mawuyacin hali. Zayyan bashi da zabi saboda rayuwar matar da dansa ya bada wannan umarni. Yaransa sun so yin gardama sai yayi musu bayani cikin lauya zance wanda su kadai sojoji ke ganewa akan cewa zasu iya hauro katangar gidan amma su bada lokaci.
Cikin wadanda suka sami tserewa nan da nan labari ya bazu cewa 'yan fashi sun tare hanyar Asaba sunyi garkuwa da wasu sojoji. Yadda labari ke gudu a social media kafin a farga Ibrahim da ke Kano ya sami labarin. Hankalinsa a tashe saboda dazun nan suke chatting da Emzee sai ya ji shi shiru. Baba Hadir ya kira ya tambaya yace baiji labari ba. Shi da Daddy su ka shiga neman layukan Zayyan da Emzee shiru. Headquarter su ka je neman ba'asi amma aka so boye musu. Sau kuma ga 'yan jaridu da gidajen tv zancen kenan dai akeyi. Daddy da Baba Hadir basu bar wurin ba har dare sai da Baban Arifah ya zo sannan aka saki rahoto cewa lallai an sami distress call daga hanyar Asaba sojoji na neman taimako an kama shugabansu Major Gen. Tureta da dansa.
Kan kace meye wannan zance ya zaha lumgu da sakon Nigeria ga masu mu'amala da social media ko sauraron labarai. Fadin tashin hankalin da Mairama ta shiga ma bazai yiwu ba. Tayi kuka har hawaye ya kafe a idanunta. Ga da ga miji ko shekara biyu baiyi da dawowa gareta ba. Duk wannan tashin hankalin kuma ga Radhiya can a labour room da ga jin zancen nakudar dole ta kama ta. Ga Nasr yana wani irin kuka na fitar hankali Mairama ta rasa inda zata tsoma ranta. Tana goye dashi suna asibiti tare da su Mami saboda an hanata zama ita kadai tana fama da tunani.
A can kauyen da sojojin su ka haura gidan cikin dare basu ga kowa ba. Ashe karbe abin maganar Zayyan suka yi aka fasa sannan su ka tafi dasu cikin dajin wai bazasu barsu ba sai sun tabbatar cewa sun tsira. Ana wannan tafiya ga mai ciki ciwo yaci karfinta a wahale tace haihuwa ce suna tsare a wani kango.
"Ku taimaka min" tace cikin tsananin azaba.
"Daada taimaka mata ni zan rinka lekawa in shammacesu mu gudu" Emzee yace ko kallon matar baya son yi saboda tsoro.
Duk da rashin wadatar haske Zayyan harararsa yayi "kai ya kamata ka taimaka mata saboda idonka yafi nawa gani girma ya kamani"
"Laahhh Daada tun ina yaro aka ce na gado ciwon idon Ummi" yace yana matsawa baya.
Zayyan bai ga abinda zai sa shi ganin haihuwa ba don gara a cigaba da fafatawa a wurinsa.
Dakewa yayi yace "Lieutenant this is a command ka taimaka mata. Ba don chanjin zamani ba nasan cewa haihuwa a lokacinmu da naku da bambamci da ni zanyi komai" ya hadiyi yawu mai daci.
"A BEG MAKE UNA HELP ME"(don Allah ku taimaka min) matar tace tana ciccije lebe ga 'yan fashin suna daka tsawar tayi musu shiru ko su harbe ta. Emzee na jin haka ya duka a gaban matar nan daga shi sai hasken farin wata yayi abinda bai taba zato ko tsammani ba. Ashe aikin soja ya wuce duk yadda ake tunaninsa. Yau shine da karbar haihuwa abinda ko a tv bai taba yarda ya kalla ba. Yana gabanta tana nishi tana fada masa ya duba ko kai ya fito.
Muryar mahaifinsa yaji ya dafa kafadarsa "Make me proud my son." Ya tashi yayi waje batare da sauraron kiran da Emzee yake yi masa ba.
Tashi yayi zai bi babansa matar tayi wani nishi iya karfinta sai ga da yana neman faduwa dole ya tare ya rike mata shi. Wuka ta dauko a gefen rigarta ta bashi ya yanke cibiya tace masa tun da mutanen suka fara harbi ta boye wukar domin tsaron kanta ashe zata yi musu amfani.