← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 157

Sashe 127

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wayyo Ummi kinsan bana iya cin abinci da sassafe" yace yana kallon Daada yana neman agaji.

Daure fuska tayi "baka isa ba kuwa, ina fitowa kitchen na hadu da Rahima a falo ina jin ma ruwa ta fito sha idonta alamun bacci bai isheta ba amma ta karbi girkin tayi kuma kace na mayar"

Karba yayi da sauri bai gama jin me take cewa ba ya soma ci yana murmushi. Rankwashi ta sakar masa tana zaune akan kujerar da Zayyan ya tashi ya koma bayanta ya tsaya. Kuma ya hana Emzee tashi ya dauko masa wata. Ya kusa cinyewa suna ta masa tsiyar dama da yunwar Ibrahim ya shigo. Kafin yayi parking Zayyan ya duku kansa tsakanin Ummi da Emzee.

"Jama'a wai ni yaushe zaku koya min mota ne? Da kunya fa ace Zayyan Tureta bai iya dan murza sitiyarin nan da kowa keyi ba"

Me kuwa zasu yi banda dariya shi kuwa ya cukule yana cewa a motar Emzee zai koya yadda zaiji dadin bubbugeta kuma bazai ba da kudin gyara ba.

Ibrahim yana karasowa bayan ya gaishesu ya karbe fork din hannun Emzee wai zaici. Emzee ya damke hannun ya hana shi.

"Yanzu ko loma daya bazan samu ba?"

A daidai kunnensa Emzee yace "Idan ka dawo Zayyana ta dafa maka"

Yana jin haka ya gane wace ta dafa ya tasa Emzee a gaba karshe a tsaye ya karasa ci yana ta juya baya Daada da Ummi suna cewa da mai kwadayi da mai rowa. Cikin sauri sauri su ka bar gidan Ibrahim ya ajiye shi ya dawo. A hanya ya turawa Rahima text yana godiya da girkin da tayi masa da rokon kada ta bar gidan sai ya dawo.

A ranar ne kuma Aishatou kawar Tante ta iso za ta fara gyaran amarya Alheran Radhiya. Tante Nasara tace mata ta tabbata ta fito mata da 'yarta ta yadda ko ita kanta Radhiyan idan ta kalli mudubi sai tace bata gane kanta ba. Sai da Ummi taci dariya tace to ayi mata wankan inji mana daga nan.

Ba bata lokaci suna gama baccin gajiyarsu da kwana biyu aka fara gyara ciki da waje. Baki kuma kowa ya kama gabansa su Salame duka sun koma Sumaila na Nijar da Sakkwato suma sun tafi.

**********

Wayar gaggawa Daddy ya samu daga Katsina da daddare Alh Baba yana son ganinsa tare da iyalinsa. An tabbatar masa kowa yana lafiya sai shi Alhajin ne ma da yake ta fama da ciwon suga. 

Washegari kuwa ya hada kan iyalinsa su ka tafi. Dama kuma a ranar Bilal yaso tafiya da Fauziyya idan an fara bikin sai ta dawo. 

Awwab sallamarsa da Radhiya da ga nesa-nesa akayi. Tun ranar da akayi taron nan da suna waya yace mata akwai sauran rawar da za ta yi masa. Wani mugun kida kamar zai tsaga mata waya ya tura mata yace tun wuri ta koya suna sake haduwa zata yi masa. Shikenan take gudunsa duk da yayi ta magiyar cewa wasa yake yi. Ana fara gyaran jiki Aishatou tace shima mijin sai ana masa rowar ganinta domin a haka ne idan sun hadu zai fi ganin kyaun da tayi. Haka yayi ta korafinsa da mita ya hakura tunda ya fuskanci da gaske maigyaran jikin da Tante Nasara suke. Zamu hadu kawai yake cewa Radhiya don sai ya fanshe wannan punishment din na babu gaira babu dalili an hana shi ganin matarsa.

Mota uku su ka yi ranar da zasu tafi. Daddy da Mami a motarsa dreba na jansu. Sai Awwab da ya dauko Zahra, Raji da Zayyana. Mota ta uku kuwa Fauziyya ce da Bilal ana tuki ana shan soyayya wai kara'i take yi saboda laulayi ya sa ka ta a gaba kwana biyu yanzu kuwa anyi lafiya.

Wani masallaci su ka tsaya sallah irin na matafiya kafin su shiga Kaduna Zayyana ta tsaya sakawa Jawad takalminsa su Daddy Haroun su ka shigo wurin. Mummy Gambo, Ghazalatu da kanwarta suna shiga masallacin su ka ga su Mami suna sallah. Su din ma sallar suka yi an idar sai yiwa juna kallon kallo saboda abinda ake cewa ta ciki na ciki. Ko kadan sun kasa sakewa da juna ayi hira yadda aka saba. Ba su Mamin ba, ba kuma ga yaran nasu ba. Nama da lemuka Awwab ya siyo ya kira Zayyana tazo ta karbar musu. Ghazalatu na can gefe da kanwarta Fauziyya ta fara yunkurin jawosu jiki.

"Kuzo muci abinci"

"Mun koshi" Ghazalatu tace a kunyace saboda nauyinsu da take ji idan ta tuna duk abinda ya faru saboda ita ne.

Basu sake cewa komai ba amma cin abincin baya yi musu dadi saboda ga 'yan uwansu a gefe. Su kuma saboda sunce sun koshi babu damar zuwa su sayi wani.

Mummy Gambo sai ta rasa yadda za ta yiwa Mami magana saboda kunyar kowa yanzu yasan bayan sun gama yi mata tijara ga yadda auren ya kare. Mami kuwa sai ta yi kamar bata lura da yadda ta takura ba ita da yaran tana cin abincinta hankali a kwance. A zuci tausayin Gambo take ji sai dai dole ne ta nuna mata kuskurenta. Can da abin ya ishi Mummy Gambo gashi Daddy Haroun ya tsaya suna magana da Daddy wadda duka akan yanayin sabanin iyalansu ne ta dan matso kadan kusa da Mami.

"Ina ta zuba ido ko zaki gayyacemu taron da kuka yi na dawowar uhmmm baban yarinyar nan amaryar Awwab sai muka ji shiru"

"Banyi zaton zaki so zuwa bane" Mami tace kai tsaye.

Mummy Gambo dama neman kofar magana kawai take yi amma ba ta zargin yayarta don ba ta gayyacesu ba "Mami...hmmm...Mami kiyi hakuri akan duka abubuwan da suka faru"

Zahra na jin haka ba ta jira Mami tayi magana ba yace duka su tashi su bar wurin don ta san maganar ta manya ce. Ghazalatu har ta soma hawaye. Mami ta kalli kanwarta tana tuna irin batancin da suka yi mata har gida.

"Ki bar maganar nan mu karasa Katsina nan ba muhallinta bane"

"Naji amma kice kin hakura don Allah" Mummy Gambo ta fada a raunane tana kara tsanar abubuwan da tayi.

"Na yafe amma a bar zancen haka."

Gaba Mami tayi da sauri don kada ta soma hawaye a wurin suka tafi kowa ya shiga mota. A jere suke tafiya har Katsina gidan Alh Baba. Anyi abinci sosai na tarbar bakin gidajen guda biyu. Sai da su ka yi sallar la'asar aka ci abinci sannan Alh Baba ya kira kannensa, Ummansu Mami sai kuma Mami, Hussaina da Gambo kowacce da mijinta da kuma 'ya'yan da abin ya shafa wato Awwab, Ghazalatu da Nura. Ba tare da bata lokaci ba Alh Baba ya soma magana.

"Maman Biyu gani da 'ya'yanki da kowa a wurin nan kamar yadda nayi miki alkawari zanyi kokarin yi musu sulhu." Kallonsu yayi daya bayan daya  "Hassana, Hussaina da ke Gambo mun taba zama daku shekara uku da suka wuce akan auren Muhammad da Ghazalatu. A wancan lokacin nawa idon ne ya fara rufewa da son ganin kamar yadda da yawa cikin 'ya'yanmu su ka auri juna su ma jikokin suyi haka. A zatona zumunci zan karawa karfi ashe ruguza shi nake yi. Kuma sai akayi rashin sa'a zumuncin na 'ya'yan mutum daya na bata. Maman Biyu kiyi hakuri"

Mami da kannenta kowa sai sharar kwalla yake yi saboda ganin Ummansu tana kuka. Tayi bakin kokarinta ta shiryasu abu ya faskara shiyasa ta kawowa Alh Baba kukanta kuma bata ji nauyin fada masa gaskiya ba kai tsaye ta dora masa laifin bata zumuncin 'ya'yanta.

Alh Baba ya koma ga su Awwab "Muhammad da kai zan fara. Kai da kanwarka kun hada kai bisa rashin sanin mahaifinka har ya nema maka wani auren. Tabbas ka fini gaskiya a lokacin da ka nemi hada mata biyu domin fitar da mahaifinka kunya."

A hankali Awwab ya daga kai ya kalli Alhajin ya mayar da kansa kasa yana saurarensa lokacin da ya koma kan Nura yayi masa kaca-kaca akan irin tozarcin da ya yiwa Ghazalatu.

"Wannan abu duk mun sanya son kai a ciki karshe bamu ji dadi ba. Gambo kin biyewa 'yarki tace bata son kishiya...."

Awwab na jin zancen ya koma kan iyaye ya kalli Nura da yake tsananin jin haushi da Ghazalatu wadda tamkar a zare allura babu wata soyayya da ta rage masa a zuciya game da ita sai ta 'yan uwantaka da tausayin halin da ta fada a gidan miji.

"Ku tashi mu fita"

"Ban gama ba dreban sama ku koma ku zauna" cewar Alh Baba.

"Alhaji zamu dawo tunda na ga maganar yanzu ba tamu bace" karamar tsawa ya dakawa Nura dama ya girme shi "kai tashi mana"

Da sauri ya mike su ka fita su ukun. Alh Baba da sauran kakanin sun yabawa Mami wurin tarbiyantar da 'ya'yanta gashi har yasan su tashi saboda iyayensu za'ayiwa fada.

Fada, nasiha da jan kunne sosai Alh Baba ya yiwa su Mami musamman Hussaina da ya dorawa alhakin ingiza wutar rikici tsakanin Mami da Gambo. 

"Abinda akayi ta rigimar dominsa gashi sai da ya faru..." Baba Karami yake cewa dasu "munje mun karbawa Muhammad auren yarinyar nan Radhiya. Ku kuma da kuke ta tada jijiyar wuya gashi gayyar ta watse. Kunyiwa yaranku auren huce haushi sun kare da hadaku fada da juna"

Hussaina tafi kowa jin kunya ga ishrar da take gani a wurin Hany har yanzu bata da lafiya dangin saurayin kuma sunki amincewa.

"Nasan hakkinku ne yake bibiyata Hassana da Gambo ku yafe min don Allah"

Ummansu ma kukan take yi a dole su ka rinka cewa sun yafewa juna. Iyayensu albarka suka saka musu sannan aka sake kiran su Awwab. Baban Biyu yace yana bukatar daidaituwar zumuncinsu ko me zaije ya dawo tsakanin iyaye daga yau bai yarda su juyawa juna baya ba. Sun tashi zukata wasai. Daddy ne yayi saura da iyayensa yake fada musu irin alkhairin da Zayyan yayi masa da duk wanda ya rabe shi.
Chapter 127 · 0% Book details