← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 157

Sashe 98

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daren ranar basuyi kwanan kwanciyar hankali ba. Mummy Gambo ta tayar da hankalinta saboda bata san halin da Ghazalatu take ciki ba. Can kuma Hussaina da daya daga cikin 'ya'yan Alh Baba mata ne zasu kwana da Hany da Ghazalatu.

Garin Allah na wayewa sai haramar tafiya Katsina. Mami bazata bisu ba saboda Fauziyya dake fama da laulayi ga yaro sannan mijinta baya gari. Daddy ne yayi musu kara suka tafi tare. Al'amura dai basuyi dadi ba haduwar Hussaina da Gambo tamkar ba ciki daya suka fito ba. Sai da Umma tayi kuka sannan kowacce ta shiga hankalinta. 'Ya'yan dai da suke yi dominsu sune yau suka hadasu fada. Umma kuwa tace hakkin Hassana ne ya kamasu. Shekara uku sun dauki gaba ta babu gaira babu dalili akan abinda idan kowa ya ajiye son zuciya zasu daidaita shi cikin lumana. 

Gabadayansu sun fahimci kuskuren abinda suka yiwa Mami akan auren Awwab tunda kowacce ta gani a kwaryarta. Ita Hussaina yanzu 'yarta ce a matsayin Radhiya na da kuma dangin mijin masu bala'in kudi ne saboda haka ana yi musu kallon masu kwadayi. Mummy Gambo da take ganin 'yarta tafi karfin zama da kishiya ta kare a gidan mashayi mai duka. Banda bari sai tayi jinyar jikinta da ya doku. Daddy Haroun ma dai cewa yayi a raba auren saboda ko waya Nura baiyi ba bare yazo dubiya.

Bayan dogon zama da mayar da maganganu Alh Baba yace da mijin Hussaina ya umarci dansa da sauwakewa Ghazalatu kafin sauran zumuncin iyayensu ya karasa lalacewa. Sai dai Nura ya kafe bazai saketa ba. Hakuri yayi ta badawa akan cewa yana sonta kuma bazai kuma shan kayan maye ba. Mummy Gambo ta tafi da ita Abuja suna jira idan ya gama haukan a cewarsu zai kawo takardar.

***********

Rugar Barkindo da Gaya wurin Nene da su Ummi ke da niyar zuwa sai waya suka yi musu suna bada hakuri da zarar ya gama da wurin aiki zasu zo. Innawuro tace babu komai dama yanzu ai zama bai ganshi ba. Radhiya suka tsaya dauka kawai Emzee da Ibrahim aka ce su biyo motar haya saboda motar tayi musu kadan. Kafin su tafi Malamijo yace da Ummi idan ta sami sarari ta dawo zasu yi taro na 'yan uwa. Abin yayi mata dadi kuwa sosai yadda baban nata ya sauya.

 Hajjo ce dai take wahalar dashi yanzu taki yarda ta koma sai yawon ban hakuri yake yi. Gidan kajinsa ko ashirin ba'a samu ba duka sun mace da cutar murar tsuntsaye. Ayuba ne ya kwantar masa da hankali akan cewa yaci sa'a ba shi kanshi aka dauke ba saboda kin fitar da hakkin Allah na zakka. Duk lokacin da yayi masa magana a shekarun baya Malamijo sai yasa a kamo kaji uku ko biyu yace ayi miya zakka ce ya fitar.

***********

Abin farinciki da murna ashe kiran da aka yiwa Zayyan kira ne na alkhairi. An tabbatar masa da sabon mukaminsa na Major General sannan kuma gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar Nigerian Army su ka yi masa kyaututtuka na bajinta. Da farko dai an bashi dankareren gida a unguwar Maitama nan cikin Abuja da masu gadi kananan sojoji. Gida na gani na fada ginin zamani wanda bai taba tsammanin akwai irinsa ba bare ace zai mallake shi. Sai kuma motoci guda uku banda daya da take mazaunin official car tare da drebansa. Basu tsaya a nan ba aka hada masa da cheque wanda ganinsa ya sanya shi fitar da hawaye a matsayin compensation. Ina zai kai wannan kudin yake ta tunani. Ranar shi da iyalinsa sun ga soyayya daga wurin 'yan uwa da abokan arziki. Daddy da Baba Hadir sunfi kowa murna babu kyashi babu hassada. Zayyan ya cancanci fiye da wannan ma. Taron karramawa kamar yadda aka yi masa bayani tun farko za'a yishi ne daya ga watan junairun sabuwar shekara abinda bai kai watanni biyu ba. Shi kuma nasa taron da kudurin da yake dashi na wannan ranar sai washegari biyu ga wata.

A cikin satin su Ummi suka yi parking din dan abinda ba'a rasa ba domin sabon gidan babu abinda babu cikin manyan kayan bukata na gida. Abinda baiyi musu ba ko babu sai su canja. Ranar Juma'a suka tashi Ummi tayi kuka tamkar bazata sake ganin Mami da Mama ba. Suna yi tana yi mazansu na bada hakuri. 

"Meye abin kuka bayan ko minti ashirin bana jin zakuyi a hanya kafin ku ga juna" cewar Daddy.

Mami tace "Mun saba fa tafiyar kafa ce kullum muna tare"

"To ai sai kuyi hakuri kowa ta koyi zaman kula da mijinta ku dena yawo"

Ummi da Mama kunya ta kamasu saboda shi ba mai yawan surutu bane. A haka dai suka tare Baba Hadir ya baiwa Zayyan shawarar cewa ana iya yiwa Ummi tranafer ta karasa karatunta a Nile ko Baze University da suke a nan tunda babu amfanin ace tana karatu a Kano shi yana Abuja.

"Ko zaka kara aure ne?" Ya tsokane shi.

"Yi hakuri kada taji yau ta hanani tuwon dare"

"Kafin a koma hutu sai mu nemi bayanin yadda ake yin transfer din"

Littafin da ya rubuta masa Zayyan ya kalla ya dan bata rai "wai da gaske haka zamu rinka hira Hadir bazaka kokarta kana magana ba?"

"Wwwahhalla" Baba Hadir ya bashi amsa.

"Duk da haka ka daure don Allah. Idan ba bude baki kayi muna zantawa ba gani zan rinka yi kamar ban hadu da Hadir ba har yau"

Alkawari yayi masa cewa zai cigaba da kokari. Cikin motocin da aka bawa Zayyan wadda tafi kyan ya bawa Ummi aka hadata da dreba. Daya kuma ya bawa Ibrahim mukullin "kai da dan uwanka. Nasan ba gari daya kuke karatu ba saboda haka tana nan sai kunzo hutu babu mai tafiya da mota makaranta" 

A hakan ma sun gode matuka iyayensu suka tayasu murna. Da yake gidan bene ne babba akwai dakuna shiyasa guda biyu da suke kusa da juna a kasa aka bawa Ibrahim din daya Emzee daya. Radhiya tana murnar zata gyara daya a sama Ummi tace kada ma ta batawa kanta lokaci aurar da ita zasuyi daki na Zayyana ne.

Mama ta bata rai "ya haka ne kun kwashe yaran duka?"

"Wadda taji haushi ta sake haihuwa" Ummi tace tana satar kallon Mami.

"Cigaba da yi min fata kizo ku haihu rana daya da Radhiya muga tsiya"

Ai gaban Ummi sai da ya fadi tana ta cewa ba amin ba Mama da Mami suna dariya wai sun ga honeymoon din kamar bazai kare bane sai ta sauka. Kunya sosai taji kuwa ta ja bakinta ta tsuke.

Duk wani shiri da ya kamata ayi domin fara aikin da ya dawo da Radhiya Baban Arifah ne kan gaba. Abinda take shirin yi ya kayatar dashi matuka inda ya dauko mata hayar kwararren cameraman aka hadata dashi. Arifah kuma ta zabi zuwa a matsayin wadda zata yi co-ordinating komai saboda ya tafi bisa tsari tamkar shirin film ba kara zube ba. Da connection din Excellency ya samu aka nemo masa wasu cikin makotansu Zayyan wadanda mazansu suka rasu a Liberia dasu zata fara.

Yau litinin suka gama shiri zasu tafi Kwara state can karamar hukuma Moro. Suna airport kafin jirgin ya sauka Radhiya ta matsa gefe suna hira da Awwab. Rigima take yi masa tun jiya wai ya dawo.

"Schatzi saura kadan fa na gama. Ko baccin kirki bana yi saboda saurin da nake yi na dawo wurinki."

"Ya za ka dena bacci sosai salon kaje kayi mistake a kara maka kwanaki ko"

"Ya Allah, yanzu yaya kike so ayi?"

"Ka rinka bacci, cin abinci akan lokaci da tunanin ina nan ina kuka saboda ba ka nan"

Tamkar yasa hannu ya daukota ta cikin wayar haka yake ji "Do you miss me that much?"

"Every second Hammana" ta amsa masa da murmushi.

"Ki kula min da kanki okay, banda kula likitoci kuma."

Dariya tayi mai sauti yana jinta har ransa "yanzu ko asibiti idan ba dole ba ai bazani ba saboda ta kare min"

Shima dariyar ta bashi. Yana so yaji tace ta kare mata dinnan cikin shagwaba "I love you Alheran"

Kalmar da har yau take yi mata wuyar maida masa a kunnensa kenan. Nauyi take ji sosai sai dai ta kare da me too. Tun yana korafi har ya hakura.

"Chèri ka turo min hotonka amma yanzu zaka dauka please kafin mu tashi"

"Ba yadda na iya dake" yace sannan ya katse kiran. Shi ba ma'abocin daukar kansa a hoto bane sai dole yanzu ma abokin aikinsa ya bawa ya dauke shi ya tura mata. Bayan kamar minti biyar ta turo masa wani. Daukar kanta tayi tayi kyau sosai dimple dinnan ya fito ta hada da nasa a photo college wani frame mai kyau. Akan hotonsa ta rubuta Alheran Schatzi a nata kuma Awwab Chèri. Sun tafi zasuyi boarding ta sake kiransa.

"Ka saka shi wallpaper dinka. Idan ka dawo zan duba. Yanzu zamu shiga kayi mana addu'a. Yaya Arifah tana gaisheka"

"Whoa, ki dan tsaya mana in amsa kowanne kafi ki cigaba"

"To ai yanzu zamu tashi"

"Allah Ya tsare Yasa kiyi ki gama a sa'a kuma Ya sa mana albarka a ciki. Ki gaishe da Arifah"

"Amin" tayi ta cewa har aka bada umarnin a kashe waya tana masa hira sannan ta kashe.

Arifah ta kalleta tana murmushi "ba fa zaki rigani aure ba duk wannan lovey dovey din naku sai na riga"

"Nima zan fi so babban yayan nawa kada yazo bikina yana gwauro"

Dariya suka yi tare kafin su dora hirar Yousuf da Awwab. Magana dai tsakaninsa da Arifah ta kankama don yace ta fada a gida zai zo wurinta amma da maganar aure so gara a sani tun wuri. Tante ma sai da ta kira Radhiya ta dan yi mata tambayoyi game da Arifan sun gamsu ana jiran komawarsa Nigeria su karasa daidaitawa.
Chapter 98 · 0% Book details