← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 157

Sashe 146

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jakar kayan kwalliyarta ta dauko ta jeresu akan dressing mirror sannan ta shafa mai. Gaban showglass din taje ta bude ta shafa humrar masu daddadan kamshi tazo ta shiga fesa body spray. Gashi dama jikinta yasha dukhani dama cikin kamshin take. Tana durkushe gaban akwatin neman kayan sawa daga ita sai tawul taji an murda kofar dakin za'a shigo. Gabanta ya fadi da sauri taje ta danne kofar tana cewa waye cikin rawar murya.

Murmushi Awwab yayi saboda a haka ma ya iya gano hakikanin firgici da tsoro a muryarta.

"Schatzi masallaci zanje, na ajiye aby a falo ne kada ki gani ya baki tsoro baki san wanda ya kawo ba"

"To"

"Ba zaki bude naga fuskarki ba kafin na tafi?"

Shiru tayi tana kallon kanta yaushe ma zata yarda ta bude.

"Sai na dawo matsoraciya"

A hankali yaji tace "adawo lafiya"

Kasa kunne tayo taji karar rufe kofar gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya. A gurguje ta janyo wasu riga da skirt na wani yadi mai laushi ta gyara fuskarta da kwalliya madaidaiciya ta kuma fesa turare sannan ta saka wani zumbulelen hijab mai hannu har kasa shima ta bishi da turaren. Sallar isha tayi ta hada da shafa'i da wutiri. Bayan ta idar ta zauna addu'a akan sabuwar rayuwarta kafin ta shafa ta ake jin alamun an shigo sai dai yanzu kai tsaye ya bude kofar dakin ya tsaya yana kallonta a zaune kan abin sallah.

Shafawa tayi ba don ta gama ba sai dai kawai kallon da yake mata yayi yawa kuma yaki magana. Yana ganin tayi yunkurin tashi yace ta zauna. Abin sallah ya dauko a inda ta dauki wanda take kai ya shimfida a gabanta. Ta san sallar me zasuyi bata bukatar karin bayani ya ja su suka yi nafilar godiya ga Allah. Addu'a sosai yayi musu tana cewa amin a hankali ta kasa daga ido ta kalle shi.

Mikewarsa ne ya sanar da ita ya gama zai nade abin sallar ta karba da sauri amma har yanzu bata kallonsa. Shi burge shi take yi komai nata. Ta bayanta taji ya tsaya ya zuro hannayensa ya tayata ninke abin sallar. Faduwar gabanta ya sake tsananta lokacin da ya rungumeta a haka ya dora kansa a kadafarta yana mata magana a kunne.

"Dama kin ajiye wannan shirun bani da niyar chanja abinda nayi niyya yau ko da zip zaki saka a bakin"

"Hammana me kayi niyya?" tace jiki a mace.

"Good ashe da bakinki...idan na fito daga wanka zan fada miki, abinda na sani dai shine...." ya juyo da ita suna fuskantar juna tayi saurin runtse idanu. Matso da fuskarsa yayi saitin ta sosai "muna da alkawarin massage idan kin manta zan tuna miki"
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Bai jira cewarta ba ya saketa ya kama rigarsa zai cire. Da sauri ta bar dakin ta rufe masa kofa tana haki ita dai yau ta shiga dari. Awwab kuwa dariya yayi ya wuce yayi wanka shima yayi duk wani abu da ya saba na shiri bacci.

Tana zaune tsuru kamar wadda ta yiwa sarki karya ya bude kofar dakin ta dago kai da sauri suka hada ido. Kayan bacci ne a jikinsa na cotton riga mai gajeren hannu da dogon wando. Wannan kamshin da yake janta gareshi ta soma shaka ta lumshe ido a hankali. Kusa da ita ya zauna ya bude ledar kazar da take da zafi har yanzu sai kuma ya mike ya dauko robar maltina daya a fridge ya dawo.

"Cire hijabin kici abinci"

"Ni dashi zan ci"

"To babu laifi shi ma bazai hana ango abinda yayi niyya ba" yace yana kashe mata ido.

Turo baki tayi cikin shagwaba "ni wallahi tsoro kake bani Hammana. Me kayi niyya"

Mischieviously yayi murmushi "nothing...ahhh bude baki" ya mika mata naman.

Kasa karba tayi ta sunkuyar da kai. Ya kula dai yau da rigima a tare da ita sai ya dauko remote ya danna tunda an jona komai na tv din ya shiga neman channel din da zai bari a nilesat. MBC 2 ya kai ana wani film ya tambayeta ko tana son gani tace eh da sauri.

"Zan barki ki gani amma da sharadin zaki cire wannan hijab din muci naman nan if not yanzu zamu shige daki..."

Kafin ya kai karshe ta yiwa hijabin masauki akan wata kujerar yaji numfashinsa ya tsaya na yan dakiku saboda kyaun da tayi masa. Gashin ta ta kama ya zare ribon din ya zuba a bayanta da kafadu. Wannan lallen da tayi yasa kan yayi kyau sosai inda kalar ta fito ya zura yatsunsa a ciki yana rufe idanu.

"I love this Alheran" ya janyota kusa dashi sosai yana yamutsa mata gashin.

A gefen jikinsa ya rabata ya shiga bata naman yana ci shima. A haka suka koshi yace tayi zamanta ya kwashe komai zuwa kitchen. Sauran ya saka fridge ya wanko hannunsa ya dawo. Miko mata hannu yayi yana son ya taso ta kyabe fuska "ai ba'a gama film din ba"

"Brush kawai zamuyi mu dawo"

"To kaje ka fara yi kaine babba"

Dariya ta bashi wai nan wayo zata yi masa ya wuce dakin yayi ya dawo "saura ke"

"Kada ka kashe tv din Hammana yanzu film din ya fara kyau" tace tana tashi bayan bata fuskantar komai a ciki. Ko wuka za'a saka mata bata san me akeyi ba.

"Zama zanyi na gane miki inda kika tashi" ya zauna ta tafi.

Tana rufe kofa ya kashe tv din da fitila sannan ya shiga daki ya rufe kofa.

Ai tana jin motsin shigowarsa jiki ya soma rawa ta gama brush din ta kasa fitowa. Sai da tayi minti biyar ta yanke shawarar ce masa ita fa kallo zata yi kawai. Da kwarin gwiwa ta fito yana waya cikin harshen jamus yaki kallonta. Zaune yake akan gado ya mike kafafunsa ya jingina da pillow. Kofar dakin taje ta murda taji a rufe. Ta sami wuri ta tsaya tana jiran ya gama.

Sallamar mutumin yayi ya taso yana tahowa gabanta na kara faduwa. A tsakiyar dakin ya tsaya ya ware mata hannuwansa yana murmushi tare da yi mata nuni da ka. Babu yadda ta iya ta saki hannun kofar ta taka da sauri ta fada kan kirjinsa. Sun dauki kusan minti biyu a haka kowa da nasa tunanin da yake tattare da soyayyar dayan.

Da yatsunsa ya dago kyakyawar fuskarta a tausashe yace "Babyna guduna kike yi kuma?"

"Film din...." sai kuma tayi murmushi ta kasa karasawa.

"Kema kin san baki da gaskiya gashi kinyi shiru. Muje ni inyi miki tausar tunda kin kasa cika alkawari"

"Zanyi maka"

"Fara saka kayan bacci"

Akwatin nata ya bude babu ko daya na lefenta kuma suna Sakkwato za'a wuce dasu Abuja. Wardrobe ya bude inda ya zuba nasa kayan ya dauko mata t-shirt dinsa tana ta kamshi.

"In saka miki?" Yace yana dariya don yasan bazata yarda ba.

Harararsa tayi "da kayana zan kwanta"

"Schatzi" yace hannuwansa na jindadin yamutsa mata gashi ya rasa dalili ita kuwa da kyar take iya bude idanu saboda yadda take ji.

"Naam" ta amsa a raunane.

"Saka riga ko Ango yayi abinda yayi niyya"

Sakinta yayi ba don yaso ba tana ture turen baki ya fita daga dakin don ta shirya a tsanake. Cikin sauri take komai tana yi tana kallon kofa gashi key din ta waje yake. Rigar ko cinyarta bata gama rufewa ba. Tana fesa turare ya turo kofar jikinta ya soma rawa shi kuwa Awwab rufe kofar yayi ya jingina da bayanta tare da harde hannuwansa a kirji yana kallon Alheran a matsayin matarsa abar so da kaunarsa.

Turaren da ta dauka ta ajiye jikinta yayi matukar sanyi tana kallon gadon tana son zuwa ta kwanta ta rufe jikinta amma bata son yin kwakkwaran motsi a gabansa. Tahowa yayi gabanta yasa hannu a waist dinta ya matso da ita jikinsa da dayan hannun kuma turaren da ta ajiye ya dauka ya feshe mata jiki dashi sannan ya saka hannuwansa duka ta bayanta ya dagota jikinsa ya soma juyi da ita a dakin tuni ta kankame shi tana dariya.

"Please, please, pleeeeaaass ka ajiyeni" tace tana zagaye hannuwanta a wuyansa.

"Sai na cire miki wannan tsoron da yake hanaki sakewa"

"Zan sake....Chéri na sake ma.....Hammanaa"

Ajiyeta yayi a hankali tana jin kamar har yanzu juyin suke yi ta kankameshi tana sauke numfashi. Hannuwansa ta sake ji ta bayanta ya tura yatsunsa cikin gashinta da ya mayar abin wasa yana magana can kasan makoshi "na yafe miki tausar nan fa"

Zare jikinta take neman yi ta kasa saboda rikon da yayi mata a hankali tace "nagode"

Dago kanta yayi yana bin bakinta da kallo idanu a lumshe "gani nayi ko da tausa ko babu bazai hanani abinda nayi niyya ba"

Tsoron ya soma dawowa tace "Wai me kayi niyya ne?"

Wani irin kallo mai kashe jiki yake binta dashi yace "Spending the whole night loving you my baby. Ki taimaka ki bani dama saboda ko kinki bazai hana Awwab abinda yayi niyya ba, bani da hakuri indai akan sonki ne Alheran" kasa yayi da kansa ya soma kissing dinta tamkar ranar ya fara samun wannan damar. Radhiya bata iya sake komai ba sai abinda Awwab ya koya mata. Kamar yadda yace ya nuna mata soyayyar da bazata taba hadata da komai ba a rayuwarta. Bacci kuwa sai can cikin dare ya rungumeta tsam a jikinsa ta soma yinsa a wahale tana ajiyar zuciya hawaye har cikin bacci yana jin digarsu a kirjinsa.
Chapter 146 · 0% Book details