← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 157

Sashe 137

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata irin fargaba taji a take ta dago kai ta kalle shi sai ta ga yayi gaba abinsa yana yiwa mutan gidan sallama kamar bai san da zamanta a wurin ba.  Idanunta suka cicciko da kwala tana mamakin wannan abu. Yaki daukar wayarta tun jiya yau kuma ya ganta ya share. To ko dai yana fushi ne saboda Ummansu ta daki yayarsa ta tambayi kanta. Babu mai jinta bare ya bata amsa haka ta fito a sabule ta bi bayansu.

Tun kafin ta karaso wurin motar Awwab ya fito ya dora hannu a jikin kofar bangaren da yake yana kallon yadda Radhiya take tafiya tana dan cije lebenta na kasa. Gashi wurin da mutane dole ya daure ta karaso.

Gaba Emzee ya tafi zai shiga Awwab ya hade fuska cikin wasa yace "haba inlaw koma baya ka barni naji ya kwanan iyali"

Murmushi Emzee yayi Radhiya na dariya idanunsu suna cikin na juna Rahima tayi murmushi ta shiga baya. Ga tsananin mamakinta wata muguwar harara Emzee ya doka mata yana ganin kawai da gangan tazo masa shiyasa taki fada masa wace babarta.

"Hamma bari kawai zamu taho a kasa ga Halifa can na hango ya fito"

"Wasa nake fa shigo mu tafi kada mu bar Daada da jiranmu"

Ai baya jin yana kaunar zama inuwa daya da Rahima. Ayatul kursiyyu ya shiga karantawa yana son idan ma wani abu aka yi masa Allah Ya bashi lafiya. Ko da yaji, wannan soyayya da yake mata daga haduwarsu a ranar ko baccin kirki bai iya yi ba sai aikin tunaninta. 

"Ina biye daku dama babu nisa fa" yace kawai ya taka ya riski Halifa. Awwab ya ja motar tare da kamo hannun Radhiya ya rike gam. Ba magana suke yi ba sai dai kallon da suke yiwa juna kawai mai cike da shauki. Rahima bata kula da abinda yake faruwa a gaban ba saboda tashin hankalin da take ciki. Me ya sami Emzee kamar bai san ta ba.

Suna zuwa gidan ta sauka daga motar ta shige ciki. Awwab ya dago hannu ya shafa fuskar Radhiya ta lumshe idanu. Jinginar da ita ya yi kokarin yi yana cewa "bayanki bazai sage ba kin zauna kinyi gaba Schatzi"

Da sauri ta dago jin zai hada bayanta da kujerar tare da yin kara cikin wani irin sautin wahala "aashhh Chèri da zafi"

 Gabadaya Awwab ya rude "mu gani" yace yana shirin kwanto da ita jikinsa ta matsa da sauri tana rufe idanu.

"Silly girl" ya ja hancinta "ashe ciwon ba na gaske bane tunda bai hanaki jin kunya ba"

Kyabe fuska tayi kamar me shirin kuka "Hammana ina kayan dubiya?"

"Bayan kin fada min kika yi sai a wurin Mami naji."

"To kuma sai ka taho hannu na dukan cinya" 

Kai ya girgiza yana dariya "wata maganar idan kika yi sai ta tuna min wata yarinya da na hadu da ita shekara uku da suka wuce a falon Mama mai kwalkwalin kai"

Shan kunu tayi tana kumbure kumbure "sai na fadawa Daada kana tsokanata"

Dariya yake mata ta cukule fuska "baki san yadda hoton kan yarinyar ya zauna min bane a kaina"

"Kaga bana so"

"Idan baki so a bani janbaki na shanye ki gani idan zan sake tsokanarki" ya kare da lumshe idanu yana budesu a kanta.

Kunya duk ta kamata shi kuwa kamar ya cusata a zuciyarsa kawai yake ji saboda yadda komai nata yake burge shi. Hira suke yi a nutse yana ta tsokanarta daga baya ya kare da bata shawarar a matsayinta na babba kada ta bari ko kadan su Rahima su ga wani chanji daga garesu. A irin wannan lokacin ne mutum yake kwasar lada domin ya rama sharri da alkhairi. Sosai take jindadin shawarar tasa kafin daga baya su gangara kan shirin dinner din da za ta daki Abuja nan da kwanaki.

Halifa da Emzee basu dade ba suka isa gidan inda suka shiga dakin da iyayen nasu da kakanni suke. Emzee yana kallon Umminsa ya hango Rahima a jikinta Ummin kamar tayi kuka tana kallon fuskarta.

"Ni dai ko asibiti zan kaita ne a Kano wannan idon yayi kwanciyar jini" tace tana juya fuskar Rahiman yadda su Innawuro zasu gani.

Kirjin Emzee yayi wata irin dokawa saboda yadda fuskar Rahimansa ta koma...Rahimansu dai ya gyarawa kansa da sauri tare da saurin barin wurin. Yana tafe fuskar tana masa yawo a ka cike da tashin hankali. Ba zato yaji ance "Karami"

Juyawa yayi yana kallon Salame tayi wani iri. Fuskar Rahima ya tuna yaji ransa ya baci amma albarkacin Ummi sai ya gaisheta. Kasa boye mamakinta tayi saboda tasan bata kyauta musu ba amma yaran suna da ladabi duk da fitinarsu da ake gani musamman Radhiya.

"Uhmmm dama...nace...dama...uhmm"

"In tafi ne?"

"Cewa nayi ko za ka kira min su Radhiya da Halifa"

"Radhiya ko Rahima?"

"Radhiyan dai" kunyar ganin Rahima take ji sosai kuwa.

Wayarta ya kira sannan ya tafi kiran Halifa wanda tun a hanya yake bashi hakuri yace kada ya damu magana ta gama wucewa.

Radhiya da Halifa sunje sun sameta sai ta rasa abin fada sai da Halifa yace zai tafi ta iya hada kalmar hakuri ta baiwa Radhiya. Murmushi kawai tayi tace babu komai saboda yadda bata sakewa a gabanta. Bayan tafiyarta ne ta dan sassauta murya tace da Halifa

"Me kanwarka take cewa game dani?"

"Me zata ce kuwa Umma banda kuka"

Shiru tayi na rashin sanin abin yi kafin daga baya tace "wai fuskarta ta kumbura?"

Shi gabadaya ya kosa da tsayuwar ma "bari na kirawo miki ita ki gani"

"Dawo Halifa" tace tana yafito shi da hannu bai tsaya ba sai da yaje kofar dakin da suke.

"Rahima kizo inji Umma"

Duk wanda yake wurin ya ga firgicin da ya bayyana a fuskarta ta kankame Mairama sosai har ta soma kwalla.

"Tashi kije Rahima" Nene ta umarceta.

Tamkar wadda kwai ya fashewa haka ta mike tana kallon Ummi ko zata ce mata ta zauna sai ta ga tayi mata alamar taje. A tsorace take sosai ta fito ta bi bayan Halifa. Tana zuwa daga nesa ta zube a kasa ta gaisheta. Salame ta amsa yau babu wannan hura hancin.

"Dama jiranki nake yi mu tafi"

A kidime tace "ina?"

Murmushi Salame tayi wai nan ita gyara za ta yi "muje gidana kiyi min kunshi saboda Kamun gobe. Amma ki fara dauko kayan da zaki saka goben sai mu shiryo daga can"

Abinka da rashin sabo Rahima sai jin abin tayi bambarakwai ta kasa cewa komai sai faduwar gaba. Halifa take kallo tana neman agaji.

"Umma ita za ta yiwa Radhiya kunshi fa ko?"

"Eh da su Anti Laila" ta ce cikin sauri.

Salame ta fuskanci akwai tsoronta a tattare da Rahima to amma so take ta gyara ya kamata su bata dama.

"Nima ina nan din zan jira ki sai ku fara da wuri saboda yau nice da girki." Ta murmusa hakoran nan masu gansa kuka suka bayyana "yau sai ki tayani muyi girkin tare"

Qut...Rahima ta hadiyi yawu Halifa ya kalleta ya danne dariya saboda yasan karshen takura da tashin hankali tana cikinsa. Salame ta bar wurin batare da Rahiman ta amsa ba can kasan zuciyarta tana jin wani iri game da yadda idon yarinyar ya koma.

Yarfe hannuwa Rahima ta shiga yi tana kallon Halifa "yaya zanyi?"

Tausayinta yaji a ransa yana murnar shi namiji ne don gaskiya bai hango yadda zai iya kwana da ita ba da shine Rahima. Babu wata sakewa ko shakuwar uwa da 'ya kawai sai ku kwanta kusa da juna. 

Kiranta taji Radhiya tayi bayan tafiyar su Emzee suna wurin Ummi tace a kira wata mai lallen Rahima babu wanda zata yiwa saboda idonta. Radhiya dama a yatsu kawai zata yi saboda dai kada ace amarya ba kunshi. Gidan ya soma kaurewa da hayaniya Ummi ta fadawa Rahima ta tafi gidansu ta hado duk wani abu mai mahimmanci musamman takardun makaranta da ita zasu koma gabadaya. 

"Ummi gabadaya kika ce?" Ta kasa boye farincikinta. Tana son Mairama tsakani da Allah saboda a dangin mahaifiya babu inda ta ga soyayya da kulawa kamar a wurinta. Bayan la'asar kuwa ta sulale ta fice a soro ta hadu da Salame "yauwa dama ke nake jira muje" ta nuna mata kofa.

A tsorace tace mata kaya zata debo a gida. Salame ko a jikinta tace idan ta dauko ta taho gidanta gobe sai suyi sammakon fitowa.

Yau Rahima an shiga tsaka mai wuya. Yanzu idan ta rufeta da duka tana cikin bacci fa.

"Naji ance jibi zaku wuce ne kinga zai kyautu mu kwana muna hira tunda zamu jima bamu hadu ba"

Jiki a sanyaye tace to tayi hanyar gidansu. Baffanta da Iya basu ji dadin ganin yadda idonta yayi ba ta hada 'yan kayanta masu kyau ta fada masa inda zata kwana. Nan yayi tsalle ya dire yace ba dashi ba babu inda zata je. Iya ce tace ya kyaleta tunda babu mai rabata da mahaifiyata. Ba don taso ba haka taje gidan. Kanenta na binta da ido shekeke Salame ta daka musu tsawa tace bazasu gaishe da yayarsu ba.

 Rahima da yaran a tare suka firgice Salame ina ma ta kula sai fada take wai basu da tarbiyya basu san girman na gaba dasu ba. Murhu ta hada ta dawo ta kirata wai ta tayata tankade. Tare suka yi girkin tana ta dararewa saboda kada jikinta ya gaya mata.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Tare suka yi girkin amma Rahima ce karfin aikin. Yaran gidan sai binta suke da kallo ita dai kanta na kasa har suka kammala. Baffanta ne ya kira Ummi ya sanar da ita inda zata kwana kada suji shiru. Addu'a ta rinka yi Allah Yasa kada wani abu mara dadi ya biyo baya. 

Lura Salame tayi da yadda Rahima take tsakurar abincinta. Tuwon masara ne da miyar karkashi sai tashin daddawa take yi ga sukunbiya an saka saboda ita. A cikin kwanon silva ta zubawa Rahima ta kwarara miyar a kai. 

Sai da ta gama lashe hannunta ta bi irin abin miyar nan da ya kan makale a tsakanin hakora da harshe tana sakato shi sai ji kake tana tsk-tskk da baki ta kora da ruwan rijiya sannan ta tabe baki.
Chapter 137 · 0% Book details