← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 157

Sashe 131

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarsa ce ta subuce daga hannunsa batare da ya sani ba yaji kansa yayi mugun sarawa. Hawaye sosai Muhammad Zayyan Tureta ya soma yi a garin yaya Rahima ta cuce shi haka? Meyasa bata taba fada masa ba? Shiryawa suka yi ita da babarta ko kuwa shima asirin aka yi masa tunda ta saba? Ko kuwa ta turota ne domin ta sake bakantawa mahaifiyarsa saboda tsanar da tayi mata?

Duka wadannan tambayoyin basu rage daidai da cikin cokali na soyayyar da yake yiwa Rahima ba sai dai wani irin zafi da yake ji a zuciyarsa domin ko sonta zai kashe shi bazai taba auren irin Salame ba.

"Why Rahima???" Ya durkushe a kasa yana kuka kamar karamin yaro. [7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Cikin Salame kullewa yayi da ta ji muryar Mairama. Yau ko ba'a fada ba ta sani cewa kashinta ya bushe ta kure kanwarta ta. Radhiya kuwa da sauri ta iso bakin kofar dakin idanu sunyi ja sun kankance.

Ummi na ganinta a haka taji hankalinta ya sake tashi yau 'yar kunyar ma babu ta janyota jikinta za ta dubata ta saki siririyar kara saboda bayanta da aka taba.

Ai kuwa da sauri Ummi ta zaro idanu ta juya Radhiyan ta dage rigarta. Ga farar fata ga gyaran da take sha jiki yayi mugun laushi shiyasa wayar tayi mata wani dogon layi da yake tsartuwar jini daga tsakiya. Ruwan bala'i da masifa yau sun tarar wa Mairama ta kama hannun Radhiya ta hada da ba Rahima.

"Kama kanwarki kuje Lucas yana mota ya kaiku MHC"

Mama kallo daya ta yi a kofar dakin ta hango Salame kamar kaya jibge a kasa tayi saurin jan hannun Rahima saboda duk lalacewa baza su so ta ga mahaifiyarta a wannan halin ba. Da taimakonta suka kama Rahiman saboda ta fi Radhiya jin jiki suka fice. Itama bata son ayi a gabanta gara yau dai suyita ta kare a gaban mahaifinsu.

Dama jiran fitarsu Ummi take yi tausayin Rahima ya dakatar da ita. Dakin ta banka kai ciki a fusace Salame ta mike da kyar.

Cike da bacin rai da masifa Ummi tace "zuwa nayi mu saukewa juna iskokan dake kanmu Salame saboda na dade da fuskantar cewa kanki yana da matsala"

Wai saboda karfin hali tana kallon kowa a tsaye ta kumburo baki "saboda na daki 'yar gwal shine kuka yo min taron dangi..." waje tayi sai ta tsaya turus gani ashe harda Malamijo da Nene, ga su Yadikko da Hajjo. A zatonta Mairama ce kadai da Baffan Rahima da ta gano tare da Alh Indararo shima tana jin ramawa tasa 'yar yazo yi. Bude baki tayi za ta sake yin magana Malamijo ya kai mata wani wawan marin da bazaka taba kawowa a ranka dan hannunsa zai iya ba. Hannu ne na tsohon kashi ya sake bata a kumatun hagu. Wasawasa sai da yayi mata yafi biyar wani tukukin bakinciki yasa ta kasa kuka. 

"Ke mahaukaciyar ina ce Salame? Na fuskanci burinki bakincikinki ya kaini lahira to amma baki isa ba. Ko Amiru da yake yawon jagaliya bai samin bakincikin da kike kunsa min ba"

"Duk wannan abin akan Radhiya ne saboda ita kuna kaunar uwarta tunda babanta yana da kudi ko"

"Rufewa mutane baki mutuniyar banza" cewar Nene tana jin kamar ta maketa. 

Jan bakinta tayi ta tsuke kowa a tsakar gidan ita yake yiwa kallon da take fassara shi da tsana.

Mairama ta dubi iyayen nasu "Malamijo yau gani ga ka ga kuma babbar 'yarka. Ban san me nayi mata ba tsayin shekarun nan tun farkon aurenmu amma wallahi na gaji. Daga yau sai yau idan ta kuskura ta sake taba min yara zan dauki matakin da mu duka nan sai ran kowa in yayi dubu ya baci." Ta mayar da idanu ga Salame "Wai da nake ta taraki ki sani ba tsoro bane kawai ina yi ne da sa ran wata rana zaki ajiye makaman yakinki mu zauna lafiya. Amma tunda kince ba haka ba mu zuba nida ke shege ka fasa. Duk wani zafin rai da kike takama dashi kin kwana da sanin Mairama tana da dubunsa a ajiye"

"Kinga malama ni dai ba da niya na taba Radhiya ba. Rahima zan daka ta tare wayar ta sauka a bayanta ko ba haka ba?" Ta tambayi iska tunda babu mai bata amsa jikinta yana kadawa kada a cigaba da maganar nan allura ta tono garma.

Malamijo zaiyi magana Mairama ta riga shi "assha 'yar uwa, kada kiyi tunanin dukan Alheran kadai ya kawoni ko daya. Gobe kafin wannan lokacin zaki baiwa ubanta bayanin dalilin dukan masa 'ya, kuma kada ki manta matar aure ce ban san me zai faru ba idan mijinta ya ji. Wannan diban albarka da kike yiwa Rahima kadai ya isheni. Don ta ni kin dade baki yi min rashin mutumci ba. Ranar da duk na gaji na fyatoki ba ganuwa zakiyi ba"

Dariyar Alh Indararo ce ta katse Mairama "wai ke nan duk masifar akan dukan da tayiwa Rahima ne dama? To ni tunda na auri Salame ban taba ganin yarinyar nan ta shigo gidan nan ta fita babu kwalla a idonta ba. Wannan kuma kadan ne cikin abubuwan da tayi miki"

"Me kake nufi Alhaji? Wai me kika dauki Rahima ne Salame?" Baffan Rahima ya tambaye shi a zatonsa ta yiwa 'yar tasa abinda yafi wanda ya gani "yanzu ashe alkhairi zai iya zama sharri, sharrin ma ka rasa wanda zaka yiwa sai dan cikinka. Kudine dubu dari da 'yan kai Rahima ta kawo tace min a Habuja tayi lalle ta samu. Shine aka raba kudin ni talatin itama uwar aka ce ta kawo mata talatin sauran kuwa zamu fara yi mata tanadin aure. Shikenan daga zuwanta ta dawo min gida da fuska a kumbure" ya kare zuciyarsa a karye saboda shi ba ma'abocin fada bane. Mutum ne mai kyaun hali da matukar hakuri. Kaddararsa daya bata wuce soyayyar Salame da tayi masa mugun kamu ba ashe rabon haihuwa ne yasa ya aureta.

Maganganunsa ba karamin shigar Salame tayi ba sai lokacin ta sake kallon ledar da Rahimar ta yar saboda marukan da ta sha. Kenan Mairama sake bawa Rahima wani kudin tayi a madadin wanda ta karbe? Wani abu taji yana neman danne mata zuciya sai dai bata yi nisa ba ta tsinkayi muryar Alh Indararo yana cewa "wanda bashi da kashin arziki ko a cikin rijiyar kudi zaka tsoma shi bazai taba yi ba. Nan ta dawo da kudi dubu dari tana yi mana burga wai 'yarta ta fara sana'a. Ci banza ci hofi bana jin akwai sauransu yanzu ma."

Kallon banza Mairama ta watsa mata saboda da gani babu abin tsinta a jikin Salame bayan tsiya tsagwaronta. Juyawa tayi da zummar fita daga gidan Alh Indararo ya ga idan yayi shiru ai wasa ya kare bayan ko rabin tanadin da ya yiwa Salame na bakinciki bai idar ba. Fada sosai Malamijo da su Nene suke yiwa Salame shi kuwa yayi saurin tsayar da ita.

"Mairama ince ko kina da masaniyar cewa duk wannan rashin hankalin da Salame take yi miki tana yi ne saboda son mijinki da take yi"

Cak Mairama ta tsaya ta juyo a hankali ta koma gaban Salame ta rike hannayenta duka biyu ta soma yi mata fada tamkar 'yar cikinta "da gaske baki da hankali ne Adda? Ta yaya za'ayi ki bari duniya tasan cewa kina son mijin kanwarki? A lokacin da ake zaton babansu Karami ya rasu babu kunya kika dubi idanuna ina zaman kunci da zafin rabuwa kika fada min kinso shi na hakura ban taba daga zancen ba. Adda Salame a lokacin har tausayinki na ji saboda soyayya bata taba yiwa mutum uzuri sai nake ganin ba laifinki bane." Hawaye ne mai zafi ya ke fito mata saboda rashin sanin wace irin mutum yayarta ta zama "idan kika kuskura kika bari su Halifa suka san wannan abin nayi miki rantsuwa abinda ya rage na kimarki da darajar uwa a zukatansu sai ya tsiyaye ya bi rariya."

Baki na rawa Salame ta iya hada kalmomin "sharri...sharri ne. Sharri yake min"

Tsawa Malamijo ya daka mata "Ki rufe min baki shashashar banza wadda bata san ciwon kanta ba...ko kinsan ko sati biyu bamu rufa ba da nasa Halifa ya hadani da babansa kuma ya tabbatar min dalilinsa na sakinki kenan. Har yaushe zaki cigaba da karar da rayuwarki akan hangen ta wani"

Mairama gani tayi idan ta cigaba da tsayuwa ba mamaki a kwashi Salame a baro saboda ji take yau da ita ce ta haifeta sai tayi mata dukan kawo wuka ko za'ayi sa'a kanta ya dawo daidai.

Abinda Nene Marka take ta gudun fitowarsa Alh Indararo yace "ke kuwa wace irin zuciya gareki Mairama? Ta so mijinki kin sani baki dauki mataki ba sannan ta makanta ki tsahon shekaru shima duk taci bulus kenan? To idan ke kin hakura ni bazan yafe ha'incin da tayi min ba na asirin aurenta ba tare da son raina ba"

Suman tsaye Mairama tayi jikinta yana bari kamar wadda aka kwara wa ruwan sanyi wani irin kallo take yiwa Salame ita kuwa sai girgiza kai take yi tana hawaye tare da yarfe hannuwa. Bata taba jin tsoron batawa wani mahaluki rai ba sai yau da take jin ta tsani kanta saboda sabanin kallon tsana ko fushi sai ta ga kallon tausayi sosai Mairama take yi mata. Idanu Mairama ta rufe hawaye suka zubo tasa bayan hannunta share sannan tayi murmushin kafi kuka ciwo. Muryarta tayi mugun sanyi ta dafa kafadar Salame tace
Chapter 131 · 0% Book details