← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 157

Sashe 55

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima Major yayi wannan tunanin to amma yanayin aikin Awwab din anya auren mata biyu lokaci guda zai haifar musu da da mai ido kuwa? Kansa yaji ya soma sara masa yayi sallama da Daddy Haroun ya shige mota domin tafiya gida.

A hanyar ma dai tunani yake ta yi yana neman mafitar da ta dace. Iyayensu idan ya koma garesu ma bai san me zai ce dasu ba kamar yadda bai san me zai ce da iyayen Radhiya ba.

Gajeren tsaki yaja a lokacin da ya dauko waya ya fara laluben nambar Awwab. Gara dai yaji ta bakinsa kafin yasan me ya kamata yayi kuma.

**********

Ayuba yana zaune gaban Ummi Mairama ya gama yi mata addu'a yana tofawa idanun yace "Adda Mairama anya ba sihiri bane wannan makantar? Ciwon kan nan da kike ji tun jiya sai nake ganin kamar addu'armu ce take ci."

"Allah Yasa Ayuba, amma ni kuwa waye ya tsaneni haka da zai yi min asiri?"

Roba biyu ya yiwa tofin ayoyin tsari da neman sauki ya kuma tofa mata a kan fuskarta sannan ya tashi zai fita.

"Ka turo min yarinyar nan bana jin ko abinci ta baiwa Awwab sai suru....suruuuu" wani irin haske ne wal ya shiga cikin idonta ga alamun mutum tana gani sai wani matsanancin ciwon kai kamar an kwada mata guduma. Rike kan tayi da hannuwanta biyu sosai tana ji kamar zai fadi.

"Ayuba....wayyo Allah kaina Ayuba"

Da sauri ya dawo gabanta ya durkusa sai dai ciwon da take ji yayi tsananin da ya sumar da ita. Ayuba ya hanzarta fita yana kiran su Yadikko a lokacin Radhiya da Awwab suke tahowa dakin zai bawa Ummin wayar da ya siyo taki karba suka ga ana tururuwar shiga dakin ana cewa Mairama ta suma. A guje Radhiya ta shiga ta samu ana shafawa Umminta ruwa a fuska amma ko motsi bata yi. Kuka ta saka Awwab yace su fito da ita zai je ya matso da mota kofar gidan. Shima a kidime yake musamman ganin irin kukan da Alheran dinsa take yi.

Ayuba yana ganin haka yace su kyale masa ita su matsa gefe. Radhiya dai babu inda zata je sai ma kan Ummin da ta dora akan cinyarta. Da alwalarsa dama ya dauko littafi mai tsarki ya bude suratul Baqara ya soma karantawa yana yi ya umarci Radhiya ta rinka shafa mata ruwan tofin nan. Atishawa tayi mai karfi a hankali ta soma bude idanuwanta wanda suka sauka akan fuskar 'Yar Soja Alheran 'yarta da Zayyan. Murmushi tayi ta daga hannu ta shafa fuskar Radhiyan wadda bata gane me yake faruwa ba sai da taji tace.

"Ashe ma na fiki kyau"

Tana kuka tana dariya tace "Ummi kina ganina? Me nake yi yanzu?" Ta murguda bakinta gefe yayin da Awwab ya dawo ganin me ya hanasu fitowa.

"Hmmm bakin tsiwar kenan ake murguda min"

Wata wawiyar runguma Radhiya ta kai mata tana murna. Kowa a dakin sai san barka. Ayuba kuwa cewa yake kuyi ta kabbara yau ko waye ya yiwa Adda Mairama asirin nan Allah Ya dandana masa abinda taji.

"Malam da kanka?" Inji daya daga cikin amaren da za'ayi bikinsu nan da 'yan kwanaki.

"To na janye...mu godewa Allah da wannan ni'ima da Yayi mana. Da kaina zanje wurin Malamijo a gona nayi masa albishir"

Dariya suka yi Ummi tana binsu daidai da taimakon murya tana ganesu. Kyakkyawan matsashin da ta gani a jikin kofa yana murmushi fuskarsa mai cike da annuri ta yafito da hannu.

"Haka Awwab dina ya koma"

Hannunta ya kama ya rike gam ya kalleta ya kalli Radhiya da nata bakin itama yaki rufuwa. Wayar Ummin tasu ta dauka cikin hanzari ta kira Emzee ta fada masa wannan daddadan albishir.

"Ki taimaka ki rufe fuskarki da zani sai na dawo ta ganmu tare" yace yana fita daga dakinsu zuwa falo ya fadawa Mama Zainab.

"Sorry yaro ni ta fara gani"

"Bata wayar"

Ummi na karba ya soma rokon ta rufe ido ta bar ganin mutane haka sai ya dawo. Dariya dan nata ya bata. Sun gaisa da Zainab tace zata turo su a yau don bata jin Karami zai iya bacci.

Awwab ma Mami ya fara kira ya fada mata sannan ya kira Major da yake hanyar komawa gida daga gidan Alh Baba.

"Ina ka shiga ina ta kira tun dazu?"

Hakuri ya fara bashi sannan ya fada masa abin alkhairin da ya faru "ina isowa na kiraka nima"

"Na gani ina tare da Alh Baba ne."

Murnar budewar idanun Mairama ta hana shi tambayarsa meye tsakaninsa da Ghazalatu. Zai jira shi ya dawo din sai suyi magana. Sai dai ciwon kan da take ji wanda da alamun haske ne yayi mata yawa ya fara addabarta. Awwab yace gara a kaita asibiti ko akwai abinda zasu bata.

Shi ya kaisu asibitin suka bata magunguna aka koma gida. Hudu har gota Ummi tace yayi hakuri da tafiyar sai da safe. Abinci aka kai masa tsakar gida wurin Malamijo sai ga Radhiya ta tazo tace ciwon kan na Ummi ya sake tashi ko bude ido ta kasa. 

"Ko dai babban asibiti zaku kaita. Dama can fa tana da lalurar idanun kafin wannan makantar" cewar Nene Marka.

Rabon ayi komai da Awwab yazo Sumaila a ranar. Nene, Ummi da Radhiya ya dauka suka nufi Kano domin a samu ta ga babban likitan ido.

**********

Maza ne manya manya majiya karfi masu kirar da kai tsaye zata razana mutum su biyu aka budewa kofar karfen da mukulli ne kadai zai iya budeta saboda tsananin karfinta. Mutum hudu suka tarar a ciki kowa da katifarsa a jikin bango. Uku hira suke a junansu cikin wani yare yayin da cikon na hudun yake zaune ya tankwashe kafafunsa akan katifar yana tunani.

Dogon mutum wankan tarwada wanda kallo daya zai sa ka gane wahala ce ta kara masa shekaru ba don ya kai hakan ba a zahiri. Kana iya ganin furfura kadan a cikakken bakin gashinsa. Dukkan wata cikakkiyar kamala ta mutumin kirki ta tabbata a fuskarsa. Sai dai zuciyarsa wadda kuncin rayuwa ya yiwa dabaibayi tasa baka ganin walwalarsa.

Wanda yafi girma cikin mutanen yana zuwa da izgilanci yaje ya take katifar da kafa daya yana karkada masa yatsa a gaban fuskarsa.

"Tashi nan nake son na rinka kwanciya"

Dayan na bayanshi yana dariya a nan din ma sai sun gwada rashin mutumci irin wanda yayi musu sanadin fadowa wannan gida.

Maza ukun da hira suna ganin abinda ake yi masa suka taso suna nade hannuwan riga "idan kana da matsala a dakin nan ka nemi daya daga cikinmu amma ba'a taba 3810"

"Ku kiyaye Boss dina baya son raini fa"

Dayan da suka shigo tare yace musu yana zaro idanu.

"Alamu sun nuna kun shigo prison da zafin kai, sai dai ko zaku gwada hali kada ku taba shiga harkar OUR ZAYYAN. Muna jurewa komai banda bacin ransa"

Basu daddara ba dayan ya daga hannu zai mari Lt Zayyan Muhammad Tureta mai lambar prison 3810 wadannan maza uku suka far musu fada ya kaure a tsakaninsu. Yana nan zaune inda yake har gandirobobi suka shigo rabasu.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: TUNA BAYA

"Daga hannuwanka ka dora a bayan kanka" akace daga bayansa da gurbataccen turanci.

Ruwa, iska hade da hayakin wutar da take ci sakamakon tashin bom din wurin yasa ganinsa yayi rauni amma duk da haka ya fahimci ba mutum daya bane a wurin. A kalla sun kai su takwas ko sama da haka kowannensu yana nuna shi da bindiga. Hankalinsa ne yayi mummunan tashi da ya tuna cewa muddin aka harbe shi dole zai daga kafarsa daga kan wannan land mine din. Yana dagawa kuwa banda wadannan mutanen harda Major da Hadir a cikin wadanda zasu iya rasa rayukansu. Dole ne ya kara musu lokacin yin nisa da wurin kafin mine din ya tashi. 

"Kuyi hakuri ko me kuke bukata daga gareni zanyi muku amma kada ku harbe ni. Akwai landmine a kasan kafata"

Dariya suka kwashe da ita tamkar basu fahimci nasa turancin ba. Bai hakura ba ya cigaba da cewa su taimaki kansu suyi nesa dashi kada su mutu tare don bai san karfin abinda ya taka ba.

"Get down" wani gabjeje yace masa fuskarsa babu digon imani a cikinta. 

Zayyan ya sake cewa akwai bomb a kasan kafarsa. Mutumin a fusace ya matso gabansa ya daga kasan bindigarsa wurin fadin ya maka masa a gefen fuska. Wani mahaukacin zafi, radadi da zugi yaji a take turame biyu cikin hakoransa suka fita ya furzar dasu tare da jini. Duk da haka kafarsa yake kokarin dannewa a kasan kada ya tayar da bomb din 'yan uwansa basuyi nisa ba. Idanunsa suna kan hanyar da Hadir ya bi.

Mutumin ya bi wurin da kallo ya yiwa wani nuni da ka. Sai gashi a gaban idon Zayyan mutumin ya cizge irin abin kasan mulmullalan bomb dinnan ya dage ya jefa shi hanyar da suka bi din. Wannan shine bomb din da Major da Hadir suka ji wanda karfinsa yayi sanadiyar fadawarsu kwazazzabon da firgici yasa Hadir bai kula dashi ba.

Mutum biyu suka zo suka damki Zayyan wanda ya saki ihu sosai sakamakon tashin bomb din yana mai cike da tsoron ko ya shafe su. Zuciya ce ta debe shi ya tuna irin ta'asar da suka yiwa gabadaya rundunar da suka taho wurin da niyyar taimako. Mutane biyun ya sakalawa hannuwansa a wuyansu ya daga kafar da niyar dukansu su mutu tare akan sai sun tafi ya mutu shi kadai. Ko babu komai ya sadaukar da rayuwarsa ya rage mugun iri. Runtse ido yayi yana jiran yaji ya tashi sai dai maimakon kararsa sai sautin dariyar muguntarsu yaji. Wani cikinsu ne ya taho daga shi sai dogon wando da singeletin da ba lallai a gane ainihin kalarta saboda mugun datti yazo ya durkusa a gabansa ya ciro abin da suka binne a wurare daban daban masu yawa domin danawa mutane tarko. Duk wanda yayi tunanin landmine ne yaki dauke kafarsa ya zama nama a wurinsu inda zasu fito daga mabuyarsu su kama shi su azabtar domin neman bayanai.
Chapter 55 · 0% Book details