← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 157

Sashe 148

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan gado ya fada sai lokacin ta kula ya chanja komai amma kunya ta hana tambayarsa ina ya ajiye wadanda ya cire.

"Kunyar fita nake yi kada a gane" ya tashi yana tafiya a gefenta "tayani dubawa tafiyata bata chanza ba ko"

Bubbuga kafa ta soma yi "Hammana bana so"

"Ba fa dake nake ba, nima bana so a gane ne kinsan manyan nan..."

Daga murya tayi cike da shagwaba ta ce "HAMMAAAA"

Yana kyakyata dariya ya fita. Kwandon abincin ya gani ya dauko ya dora a kan centre table sannan daga inda yake ya fada mata ta tabbatar ta ci kafin ya dawo.

Shiryawa tayi cikin wani hadadden lace tayi daurin da ya bayyana gashinta da tayi packing ta sako shi tsakiyar daurin sannan ta gaban ma ta ja dankwalin ya danyi baya. Fuskarta tasha kwalliya tayi kyau sosai. Sauri tayi ta gama saka awarwaron da ta dauko kalar kayan sannan ta fito falo ta dan karkade kura duk da babu. Turaren wuta ta saka a ko ina kamshi kuwa ya soma tashi kana tahowa bangaren za ka ji.

Fridge ta bude babu komai na kayan abinci sai ruwa da lemo kala kala. Da yake ana sanyi tunda suka zo Katsinan sau daya aka dauke wuta shima bata dade ba aka dawo da ita. Abincin da aka kawo ta bude, doya ce da aka soya da kwai a flask daya sai bread da farfesun kaza ya ji kayan kamshi. Ga kayan tea da ruwan zafi a flask. Kitchen ta kai ta ajiye don bata jin za ta iya cin komai duk yunwar da take fama da ita kuwa sai Hammanta ya dawo. 

Awwab kuwa da gaske sai da Bilal yayi da gaske su ka shiga falon Mami inda iyaye da kakanni ke zaune. Ana ta tsokanarsa sai su Bilal ke ramawa shi kam baki ya mutu Schatzi kadai yake tunani. Da su ka gama fita suka yi zuwa wurin Radhiya an gama saka kayayyakinsu a motocin da zasu bi.

Duk kunya ta isheta gashi babu su Rahima an barta ita kadai da manya kowa da abinda ya ke kara mata na nasiha. Kafin su fita Awwab ya dawo ya shiga daki sai gashi da envelop guda biyu. Daya ya bawa Hajjo dayan kuma ya baiwa Gwaggonta Mubaraka kowa su raba da abokan tafiyarsu. Shi kadai ya rakasu ta biyosu zuwa bakin kofar net din suna cewa ta koma ba sai ta fito ba.

Tunda Awwab ya shigo suka ci abinci tare suke makale da juna sallah kadai ke fitar dashi. Shagwaba kala kala yana gani tana kuma burge shi sai nan nan yake da ita kamar kwai. A haka ma baya samun yadda yake so sosai saboda kunyarsa da tayi mata yawa. Abincin rana ma kawo musu akayi daga ciki wannan karon Rahima ce ta kawo Awwab ya karba. Su Zahra da Fauziyya suka kafa naci kamar bala'i sai sun je wurin Radhiya.

 Mama tace "gulmammu wace acikinku bata ga wannan daren ba eyye. Zaku je ganin kwaf ku gani ko ta sauya tafiya ko..."

Mami sai da tayi dariya don ba karamar kunya suka ji ba har Fauziyyan kuwa. Zahra kamar ta kifa don sauri ta fice daga falon kafin a karasa barota. Mama kuwa sun kunnata bata iya yin shiru ba ta cigaba da sababi.

Kafin magariba ragowar tawagar Malamijo sun iso gidan saboda tafiya Nijar da safe. Salame ce akan gaba ko zama bata yi ba wai sai ta ga dakin amarya. Sakin baki tayi tana kallon kayan kudi sai da Mama taje da kanta ta yo waje da ita wai da bandaki zata shiga ta rage mara tayi alwala ko tunanin cewa bandakin daya ne kuma a cikin dakin baccinsu bata yi ba.

Sai da suka shiga ciki ne ta ga Halifa tare da Emzee da Ibrahim. Duka su ukun sun gaisheta babu yabo babu fallasa sai dai yanayin fuskar Emzee ya tsaya mata a rai fiye da zato da tsammaninta. Ganin Rahima ne ya mantar da ita komai abin mamaki ga ita kanta Rahiman Salame wani mugun tattali take yi mata kamar ta maidata ciki. Tunda Malamijo ya kirata yayi mata tas akan mutuwar idon Rahima tasha kuka kamar ba gobe. 

Ba komai ya tsaya mata a kahon zuciya ba irin yawaitar lokutan da Rahima ke durkusawa a gabanta tana rokon idan laifi tayi mata ta taimaka ta yafe mata. Yarinyar bata da matsala kuma bata santa ba. Burinta daya a duniya ta ga mahaifiyarta ta sakar mata fuska ta kaunaceta kamar kowa. Ita da ta iya zuwa wurin boka ta makanta Mairama da asiri yau an wayi gari 'yar cikinta ta gamu da lalurar da indai wani abu ya sake samun dayan idon mai lafiya to ta makance kenan fa. Tana ganin abubuwa amma ba ta iya rarrabesu. Ranar duk wani guntun rashin mutumci ma nemansa tayi ta rasa. Fatanta bai wuce ta kyautatawa Rahima ba ko ta yafe mata cikin sauki. Ga Halifa fuskarsa kullum a hade idan ya ganta musamman bayan matsalar idon kanwarsa. Baccin kirki kasawa tayi da ta duba hagu da dama sai kaji tana ina Rahimata?

A bangaren su Ummi ranar su ma suka wuce Nijar da Daada. Duk wani boyonta kallo daya Mammee tayi mata ta ja ta uwar daki tana murmushi.

"Mairama ciki gareki ko?" Tace da hausarta mara fita sosai.

Ummi taji kunya sai sunkuyar da kai kasa take. Mammee kuwa tsabar murna ta fito tana shelantawa. Ummi ta rufe kanta a daki ta kasa fita saboda yadda 'yan uwa suke ta murnar wannan rantsatssen rabo. Zayyan yayi ta dariya yace maganinta kenan tunda ta damu a boye gashi anyi mata mai gabadaya. Cikin 'yan uwansa mata harda mai tambayarta wata nawa ne saboda a fara shiri. Ta ga gata muraran don ko cikin fari ne a jikinta karshen abinda zasuyi mata kenan.

**********

Da daddare bayan sun gama dinner Radhiya tana wanke kayan da suka yi amfani dashi bata ji shigowar Awwab ba sai hannuwansa da suka bullo ta gefe da gefen cikinta ya riko plate din da take daurayewa suna yi tare. Jikinta tuni ya fara rawa saboda hatta soso sai ya sarke yatsunsu sun wanke abu tare dashi.

Kiss taji a wuyanta ta kusa sakin glass  cup din da suka gama daurayewa ya ce "hankali baby"

"Ai kaine"

"Ni sarkin laifi me kuma nayi"

Tsuke bakinta tayi ya cigaba da abinda yake yi yana birkita mata lissafi. A daddafe aka gama ta rufe ido kawai ta kwanto da kanta kan kirjinsa sosai na dan lokaci sai kuma ta juyo suna kallon juna "Chèri muje na hada maka kayan tafiya gobe"

"Kin hada naki ne?"

"Suna cikin akwatin da Zayyana ta kawo min dazu da ta kawo abincin dare"

Dakin su ka koma ya dauko wani akwati mai taya hudu daga kasa irin wanda duk nauyinsa mai ja baya ji saboda a tsaye yake rectangular. Na biyun karshen ya dauko ya nuna mata kayan da zaiyi amfani dasu ta fito dasu za ta zuba sai gani tayi ya zazzage nata kayan akan gado.

"Hammana ya ka juye kayan ko basu shiryu bane?"

A akwatin da take zuba nasa ya shiga jerawa "babu amfanin mu tafi da bags daban daban ne"

"Idan ba masaukinmu daya ba fa?"

Janyota yayi suka fada kan gadon yana zagaye fuskarta "nasa Yousuf ya kama mana hotel na kwana biyun da zamuyi"

Ai sai ta kasa hadiyar yawu don fargaba "duk kowa yana nan sai mu tafi hotel?"

"Yes...ta kare min Schatzi kema kin sani" ya cigaba da zana fuskarta da yatsansa "idan da nayi hakuri yanzu bazan iya ba...KEMA.KIN.SANI" ya fadesu dalla dalla kafin ya shiga nuna mata soyayyar da ko rabi rabin abinda ke ransa bai sauke mata ba.

Kayan da basu karasa hadawa ba kenan su da akwati daya da himilin kayansu dake zube a gefe suka kwana a kan gadon. Tun asuba da suka yi wanka ta karasa hada musu kayan ta gyara dakin ta wanke toilet. Basu bar komai a waje ba bedsheet din ma cirewa tayi ta dinke ta turasu cikin ledar da yake ciki da kyar saboda gudun kura.

Motoci harda wanda babu budget dasu mutane sun bi su Nijar ganin kwai da kwarkwata. Kamar kullum karamcin mutanen yana bawa Radhiya mamaki. Kudi ne dasu iyaye da kakanni amma akwai tarbiya da tsagwaron hadin kai a zuri'ar Alh Ghousman Agali. Gidan Alh Sidi Radhiya ta shiga saboda ance Umminta tana nan ta fada dakin da aka nuna mata da murnarta nan ta sami Emzee suna rigima da Mammee tana tura masa nonon rakumi ya damtse bakinsa yaki karba. Kan Ummi ta fada da murnarta Mammee ta sakarwa Emzee robar nonon ta tashi tana fada.

"Alheran yaushe zaki girma ne ni Aghaisha"

Turo baki tayi tana nanikar Ummin "me kuma nayi miki daga shigowata?"

"Dagata kada ki kassara min jika, maimakon ki tayamu tattalinta sai ki tsaya shirme?"

Ina kasa ta bude Mairama ta binne kanta. Emzee ya dago fuskarsa da nono ya watso masa ya kalleta sai wani nauyi ya bakunce shi ya dukar da kai. Radhiya kuwa ihun murna ta saki bilhakki ta sake rumgume Ummin tana murna.

"Wayyo ni, wayyo Umminmu Allah Yasa mace zaki haifa me kama dani" tace tana dariya.

Emzee ya kalli yadda take yi ya kalli Umminsu da kunyar da ta lullubeta sai ya tashi kawai yaja hannunta "Hamma Awwab yana kiranki muje na rakaki"

Zame hannunta tayi "kai Emzee yaushe kuka hadu?" Ta juya zata kuma zama "Ummi wane watttttt" keyyyy haka Emzee yayi waje da ita yaja kofar ya rufe.

Mammee tayi dariya tare da goge 'yar kwalla "sannu da kokari Mairama nasan irin halin Alheran. Haka yayata take kusan komai nata ta dauko. Zama da kishiya ne yasa tayi sanyi amma ko shi Mal. Muhammadu ai yayi fama da kiriniya tun farkon haduwarsu har auren."

Murmushi Ummi tayi tana sauraron labarin uwarmijinta da bata taba gani ba sai a hoto.

Wani falo Emzee ya kai Radhiya ya girgiza kai "ni da kin sani ni na fara fitowa yadda zan iya zaneki son rai. Sam baki kula da kunyar da Ummi take ji ba kike ta takurata da tambaya"

"Ayya Emzee ban gani ba bari naje na bata hakuri" tace innocently.
Chapter 148 · 0% Book details