← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 157

Sashe 23

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafasasshen ruwan zafi Salame ta taho dashi a bokiti tayi daurin kirji kamar mai niyar shiga wanka sai da tazo daidai bakin bahon da kayan Mairama suke ta sheka musu ruwan nan. Ledojin dole suka yi laushi sunyi tsamo tsamo babu dadin tabawa. Salati ta soma yi wai wucewa zata yi ta sirka ruwan wankanta don ta ga kamar famfon wurin yana diga an kawo ruwa. Mairama ci gaba tayi da diban ruwanta sai da ta ciko bokiti tana zuwa ta ajiye shi sannan ta cira hannu ta kwashe Salame da mari mai gigitarwa don tana kallon yadda komai ya faru.

Ihu ta kurma gidan da suke neman abin gani kuwa aka fara fitowa bawa ido abinci.

"Ni kika mara Mairama?"

Rai a bace Mairama tace "ko zaki rama ne?"

"Kan bala'i, billahillazi baki mari banza ba sai na rama"

"Gaki ga kumatun Adda Salame. Na gaji da wannan abubuwan da kika tsira tun kafin muyi aure har yanzu ana abu daya. Kece dukan min yara, yada min habaici da bakaken maganganu duk akan me? Me na tsare miki?"

"Dole kice haka mana tunda kin rabani da wanda nake so"

Yadikko na jin haka ta kora yaran gabadaya tace su shiga dakinta. Hajjo ba kunya ta bisu don jin ba'asi. Salame kasa karasa bayanin tayi don tasan ita ce da jin kunya. Tabarmar kunya ta nade da hauka wai Mairama tana yi mata gani gani saboda ta fara rike kudi.

Da daddare da Malamijo ya dawo Yadikko ta bashi shawarar ya raba musu daki mana.

"Babu wadda ta bani ko asi domin ginin gidan saboda haka idan zasu cinye kawunansu ne ma su cinye bai dameni ba. Wadda taji haushi ta kawo miji tayi aure"

"Idan bazaka rabasu ba ka taimaka ka zame musu uba na kwarai ka kawo karshen wannan rashin jituwa da yake tsakaninsu. Kafi kowa sanin cewa da ba haka suke ba"

Shu'umar dariya yayi kafin ya turo hularsa gaba ya bata amsa "ki kan bani mamaki wani lokacin kamar baki san zafin zawarci ba. Kodayake baki taba danawa bane amma cuta ce mai zaman kanta. Shiyasa kika ga suna harin junansu. Babu mai tayar min hankali ni dai"

Babu yadda ta iya haka ta tashi ta bar dakin nasa tana kara godewa Allah da bai bata haihuwa da Malamijo ba.

Mairama ta gama yiwa Karami shirin bacci ta goya shi tana jiran kanwarta ta kawo Radhiya da take wasa a wurinsu Salame ta shigo ta dawo daga zance da dan gayun saurayinta. Matashi ne ko auren fari baiyi ba. Baje ledar da ya bata ta tsire tayi a gefen katifarta da burin cusawa Mairama haushi. Abin dariya yadda take ci tana shuu da baki.

Tana ganin Radhiya ta sake bude ledar da kyau. Yarinya tace "Ummi nama"

Mairama ta dauko wata leda babba ta mikawa Na'ima kanwarta tace suje su raba sannan ta dauko wata 'yar madaidaiciya ta bude ta janyo hannun Radhiya ta bata cinyar gasasshiyar kaza. Sai yanzu take gode Allah da haka nan ta bawa Bature kudi ya siyo kajin nan guda uku. Ta dauki daya ta basu biyu su raba. 

Ai kuwa Salame ta shaka har wuya ta shiga fadin maganganu wai gara su suna kwance ake basu. Wahalallu kuwa sai sunyi da karfin jikinsu kafin su dandani zakin nama.

Shiru ma magana ce. Mairama bata ce mata komai ba haushi ya kamata tsiren ya fice mata a rai.

"Dazu nace kin rabani da masoyina baki tambayi ko waye ba bare ki bani hakuri"

"Indai Salisu ne nayi imanin bazai sakeki saboda ni ba. Allah kadai Yasan dalilin mutuwar aurenki sai kuma ku kanku"

Kallon cikin ido ta yiwa kanwar tata "Mairama, na rigaki ganin Zayyan kuma na rigaki fara...."

A harzuke Mairama ta tashi duk wani kulli na kanta yana kwancewa. Yanzun ta gama gano duk abubuwan da Salame tayi mata sunfi kama da kishi. Duk da mijin nata baya raye amma tana tsananin kishinsa itama.

"Ya isheni ba sai kin karasa ba, na fahimci da aurenki kike son nawa mijin. Idan abinda Salisu ya gano ya sakeki kenan sai ince Allah Ya dada karawa."

Daga haka bata koma cewa komai ba sai da ta tabbatar Salame tayi bacci ta sha kuka ta godewa Allah. Ta tabbatar Zayyan ya sani shiyasa shima baya son Salame saboda kada yaci amanarta. Sabuwar kewarsa ke ratsa duk wani sassa na jikinta tana inama yana nan tare da ita.

***********

Shekararsu biyu a gida Salame tayi aure. Kafin auren Mairama ta tuna cewa Salisu abokin Hadir ne a lokacin ta kwantar da kai wurin sau uku tana tambayar Salame kwatancen gidansu Salisu. Ita kuma ganin ta matsu tasan ko meye yana da mahimmanci shiyasa taki fada. Gashi baya zuwa garin don idan za'a kawo mata Halifa aiko drebansa yake likkafa ta kara ci gaba.

Bayan auren Salame ne Idris dan gidan Mal Kallamu abokin Malamijo ya sami aikin koyarwa a makarantar firamare ta gwamnati ta cikin Sumaila. Da yake suna shiri da Mairama kamar wasa ya gabatarwa Headmaster da ita akan ko 'yan aji daya ne ta samu ta rinka koyarwa. Shine ya amince aka yi mata cuku cuku sai gashi ta sami aikin a karkashin L.E.A. Kwalin karatun nata iyakarsa sakandire shiyasa bata wuce aji daya ba a koyarwar. Ita dai ko yaya ne hakan yayi mata don albashinta yana mata rana ga cinikin zobo da lamurje.

Haihuwar Salame daya aurenta ya sake mutuwa. Wannan karon lalaci da rainawa miji ya janyo mijin ya saketa. Duk abinda zai kawo mata sai ta karba a wulakance tace ba haka baban Halifa yake yi ba. Sai da ta kaishi makurar da yayi mata duka ya sakota.

To yanzu ma an sake dawowa gidan jiya. Dan da ta sake haifa shima babansa ya kaiwa yarsa. Ta dawo gida an sake komawa zaman zawarci ga rashin abinyi. Bakincikinta ya karu da yadda Mairama da yaranta suke rayuwa ta rufin asiri. Duka suna karatu a inda take koyarwa. 

Ta soma saka gilashi ne a lokacin da ta fara fama da matsanancin kaikayin ido da gani dishi-dishi. Ta sha wahalar idon sosai ta kuma kashe kudi.

**********

Sun dawo gida da Emzee ya shiga dakunan duka matan gidan su hudu don tuni Malamijo ya sake cike gurbi. Yadikko tana nan a matsayin uwargida Hajjo kuma ta biyu sai amare Hanne da Binta.

A gajiye take ta kwanta tana murna anyi hutu. Sallama taji anayi ana kwala mata kira ta tashi a zabure Salame tana kwalliya zata je wurin mamanta.

"Uwar yarinyar nan Alhihi take ko me kace Danmama?"

Danmama ya zumburo baki "Alheran amma Radhiya naji ana cewa. Ita ce ta mareni kuma Anti batayi komai ba saboda 'yarta ce"

"Allah gamu gareka" Mairama tace a ranta kafin ta fita tsakar gidan zuwa wurin matar.

"Hajiya kiyi hakuri rigima ce irin ta yara kuma tun a wurin an hukunta su"

Rai a bace tana nuna bayan Danmama ta ce "a hukuncin ne aka yi masa bulala biyar ita kuma biyu saboda son kai. Dama wane adalci kuke yi idan kuna koyarwa a makarantun da 'ya'yanku suke. Daga yau sai yau ki jawa 'yarki kunne. Idan ta sake taba min yaro bazan yarda ba"

Hakuri Mairama ta bata duk kunya ta isheta. Radhiya ba dai dauko magana ba. Idan anyi magana tace ita 'yar soja ce. Yadda take alfahari da aikin babanta sai ka rantse ta tashi tare dashi. Ko ina ta tsaya ma yanzu bata sani ba. Bari dai ta dawo yau mai rabasu sai Allah.

Ashe gidan Mal Kallamu ta bi Uncle Idris. Can taci abincinta a bangaren amaryar Idris din sannan ta fito suka hadu da Malamijo a kofar shiga. Harararta yayi kamar ya kwadeta jiya taje gonarsa ta sami wani sabon maikaci da yayi ta nuna masa wata tinkiya wai Malamijo ne ya aiko ta fada masa a yanka ya dau kai da kafa. Ana cikin fida yazo ya gani jikinsa na tsuma yayo kanta tace gani tayi ta kasa. Kunnenta ya damko tana ihu 

" 'Yar kundun uba ta ina kika ga ta kasa din?"

Ba yadda ya iya a dole jiya gidansa aka ci dafge kowa ya warwasa. Dakinsa ta bishi yana gwawiyar kashi tace "Malamijo ashe kaima kana son naman dai. Allah Yasa in ga wata ta kuma kasawa" da mafici ya biyota har yana tuntube.

Ita ce a gaba ta hango Umminta da Danmama da mamansa. A guje tayi niyar komawa Malamijo ya riko wuyan rigarta ya kaita gabansu.

"Mairama ki jawa 'yarki kunne idan ba haka ba wannan karon idan kunje hutun Sakkwato ki barta a can. Yarinya ce kamar aljana. Dubi kaninki nasa salihancin har haushi yake bani. Ke kadai kina mace kin tattaro duk halayen kiriniyar kin dorawa kanki"

Kallon da ta ga Mairama na yi mata tasan yau jiki zai fada shiyasa tana tura baki da magana ciki-ciki tace "to ba shine yake wakar wai Malamijo tsolon rake ba, rama maka fa nayi"

Jikin Malamijo da na uwar Danmama sai yayi sanyi. Danmama yayi wiki-wiki da idanu hakan ya tabbatar ba karya take ba. Babarsa kuwa ta talle masa keya tana cewa ya bashi hakuri. Yara kuwa sai dariya suke a hankali Malamijo yaji kunya ya shige daki. Kunnen Radhiya Mairama ta kama tace ta wuce daki. 

Da yamma ranar sai ga Alh Ado Indararo da kansa yazo bayan matarsa ta fada masa abinda Danmama yayi. Sun saba ciniki da Malamijo baya son kasuwar ta watse don yana dukan hancin Malamijo akan dabbobinsa sosai batare da shi ya sani ba.

Ya bashi hakuri ya nemi Mairama itama ta fito da babban mayafi ta gaishe shi. Kallon farko Alh Indararo ya fada kogin kauna baya ji baya gani. Tana komawa ciki baiyi kasa a gwiwa ba ya fadawa Malamijo bukatarsa. Zani ce ta tadda muje mu. Shima kwadayin kudin Alhajin yake yace ya bar masa wuka da nama.

A daren ya sanar da ita tayi tsalle ta dire tace bata da sauran aure a duniya. Sun fara rigimarsu bayan kwana biyu ta tattara ta tafi Sakkwato kamar yadda ta saba duk hutu suna zuwa suyi sati daya ko kwana goma.
Chapter 23 · 0% Book details