← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 157

Sashe 39

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motsi Radhiya ta soma yi dankwalin yana neman faduwa aka yi sa'a ya zauna. Ita dai Zainab a tsorace take kada ta tashi a hagu su rasa inda zasuyi da ita.

"Ina Ibrahim da Zayyan karami?" Yayi tambayar har ransa yana fatan Allah Yasa ba wannan na kwancen da ya kasa tantance waye ba za'a kira da daya daga cikinsu. 

"Sun fita cikin gari amma nasan suna hanya"

Iska ya furzar yana fadada murmushinsa "da gaske? Huhhh Alhamdulillah"

Zainab sai tayi tunanin yana murna ne don tace suna hanya. Sake kallon Radhiya yayi shi dai hankalinsa gaskiya bai kwanta da ita ba. Kamar ta san tunanin da yake a kanta kuwa tayi mika ta tashi zaune. Dankwalin ya zamo daidai lokacin da ta sauke idanu akan fuskarshi. Shi ma ita din yake kallo daga sama har kasa don ya tabbatar da jinsinta sai dai fuskarta ta tsaya masa har ya kasa magana. Kai a lailaye ga fuskarta harda janbaki. A hankali idanunsa suka fara saukowa daga fuskar a kokarin kure mata kallo sai ya tsaya cak a wuyanta ya kasa karasawa yana jin wani yanayi da bai saba ba a jikinsa. A hankali ya furtawa kansa "mace ce".

Tsuke baki Radhiya tayi tana jin ba don Innawuro ce tayi mata askin nan ba wallahi da abinda zata fara yi idan ta koma rugar Barkindo shine ta sauke mata nata gashin. Waye wannan da ya cika mata ido ta kasa sakin baki a gabansa ya gane mata sirrinta. Motsa bakin ta sake yi ko ihu ne ta kwarma musu amma ta kasa. Kumatunta na dama da yake lotsawa idan tayi yunkurin magana shine ya sake daukar hankalin Awwab ya kuma kallonta da kyau.

"Kaddai? Nooo it can't be." Ya nanatawa kansa da sauri. Girgiza kai yayi shi kadai gamo da Radhiya yana nema tafiya da nutsuwa da tunaninsa.

Su Fauziyya da suka taho yi masa barka da zuwa kowacce tayi shiru kamar ta hadiyi kota suna jiran su ga me Radhiya za tayi. Dankwali dai gashi nan amma rabin kai a bude yake. Hannunta ta dora a ka taji iya ina ne a bude. Tana ji ta janyo dankwalin a hankali ta tashi bata ce komai ba ta bar falon.

Karar kofa suka ji da karfi wadda ta gwara saboda bacin rai.  Zainab ta girgiza kai su Zayyana jiki yayi lakwas. Awwab yana lura da yadda suka sauya su duka ya daure yace "Alheran?" Da sigar tambaya yana tsananta addu'a kada ace wannan ce da ta tashi yanzu.

Kamar jiransa suke suka bushe da dariya gabadayansu. Alheran din da yaci burin gani har ya kasa zaman Katsina ce. Babu wanda ya tsammaci zuwansa Kano a yau ana tunanin zai zauna ya huta amma doki ya hana. Ghazalatu har fushi tayi ya bata hakuri da alkawarin zai dawo washegari. Kin zama tayi a gidan yayi mata shiru da yawa ta tafi gidan Alh Baba wurin kakarta.

"Ita ce ta shige ciki yanzu" Zainab ta bashi amsa da dan murmushinta.

Da ba don da kanta ta amsa masa ba zai ce ko wani salon tsokana ne kuma suke yi masa don ansan yadda ya damu da ita kuma ya matsu ya sake haduwa da ita.

Da hannu ya nuna hanyar da ta bi ya marairaice fuska "wannan din?"

Basu dena dariyar ba kuwa Zainab tace "yau idan kuka shiga hannunta ko kafata bazaku gani ba"

Rige rigen bashi labarin Radhiya suka shiga yi kowa tana fadin nata. Awwab bai san lokacin da ya saki murmushi ba wato bata chanja ba kenan daga sanin da yayi mata. Shiru kusan minti ashirin bata dawo ba abinda bata saba ba. Hadir yana ta kallon kofa Zainab ta fahimce shi tace su dubo mata ita.

"Mama gaskiya ki tura Zayyana ita ce karama"

"Wani sabon abu ne kuka koya a aikeku ku tsaya zaben mai zuwa?" Awwab yace yana dan bata rai.

"Radhiyan ce ai Hamma" 

"Come on tashi ki karawo min ita Zayyana"

Tana zumbura baki ta shiga kofar hanyar dakunan. Tun kafin ta karasa take jin shesshekar kuka. Da dan gudu tayi sauri ta bude kofar dakin. Radhiya ta gani kwance akan abin sallah tana kuka fuskarta har tayi ja.

"Uhmm Adda Radhiya kizo inji Hamma Awwab"

Zumbur ta tashi zaune Zayyana ta dan ja baya kadan ta share kamar bata gani ba, cikin yanayin damuwa tace "shi wannan na falon shine Hamma Awwab din?"

"Eh"

"Kunci amanata! babu wanda yace min zai zo kuma aka ki tashina daga falo da zai shigo" Radhiya tace tana sake fashewa da kuka. Yanzu da wane ido zata kalli mutumin da taci burin haduwa dashi saboda irin labaran da ake bata. Ance mata sun shaku da tana karama kuma yana sonta sosai. Ashe ma ya zama dan gayu irin haka kamar likita amma aka bari ya ga askinta.

Zayyana komawa tayi tana jin tausayin Radhiya. Ko ita ce da kwalkwal bazata so ace kowa ya gani ba.

"Ina take?"

"Kuka take yi Mama"

Da 'yar damuwa a fuskarta tace "Yanzu dai Awwab duk kaine ka janyo wannan rigima da ka ga kanta, yau ban san yadda zamuyi ba"

"Ni kuma me nayi daga zuwana" Su Zahra ya tsare da idanuwa "me yasa baku tasheta ta rufe kan ba?"

Kusa dashi Zayyana ta zauna "haka tace wai munci amanarta da bamu tasheta ba ma"

Samun kansa yayi da rashin jindadi, ba haka ya tsara haduwarsu ba. Garin yaya ma aka yi mata aski irin haka don Allah? Sallamar Ibrahim da Zayyan ita ta katse tunaninsa. Zaratan samari ne dake ganiyar tashinsu.

"Kunga Hammana" suka ji Zayyana ta fada tana murmushi ta nuna shi.

"Naki ko namu?" Ibrahim yace yana mika masa hannu.

"Da gani kaine Ibrahim, sau biyu Zayyana tana kawo min kararka. Baka san ba'a tsokanar autar Daddy ba?" Awwab yace cikin sakin fuska.

"To kace ta dena shagwaba ko muma mu fara ko Emzee, mu dinma duka autoci ne"

Kalmar tasa ta karshe ta sanyasu dariya. Awwab ya kalli Emzee yaron is very calm sai murmushi da yake yi kawai. Ji yayi ya burge shi, a fuska ya tuna masa da babansa Zayyan sosai amma wannan Zayyan din da gani ba mai hayaniya bane. Hannu ya mika masa suka gaisa Emzee yana dari-dari ba kamar Ibrahim mai saurin sakewa da sabo ba.

"Dama kai nake jira taimaka ka fito min da yayarka wadannan duk matsorata ne" ya nuna su Fauziyya.

"Kin fitowa tayi?" Ibrahim yace da mamaki "kullum fa zancenta idan ka dawo zata dena kula kowa a gidannan"

" 'Yan cin amana sun saka mana ido ya muka iya yau sunci amanarmu" Awwab yace yana aron kalmar da Zayyana tace tayi amfani da ita.

Ibrahim yace "Mama me suka yi mata?" 

Zayyana ce ta bashi labari kafin Zainab ta soma magana. 

"Anci amana gaskiya, bari na koma cikin gari na kwana don ga dukkan alamu yau mutanen gidan nan zasu kwana da balotelli"

Emzee ya daki kafadar Ibrahim suna dariya kafin ya nufi dakin. Tana nan zaune hanci ya kumbura, idanu sun kankance sunyi ja saboda kukan da tasha. An cuceta da aka aske mata kai. Da an bar mata na zaman falon da ta roka ko babu komai zai rufa mata asiri yau.

"Adda kizo inji Hamma Awwab"

"Ni fa gida zan tafi"

Daure fuska ta ga yayi "ke babu dama ranki ya baci sai kice zaki je gida? Idan Ummi taji abinda kike yi a gidannan zata ji dadi ne? Kowa na tsoron bata miki rai kina jin dadi kamar abin kirki"

Mamakinsa ta soma yi. Emzee din da babu ruwansa ko me tace ta zauna shine yake mata fada. Jan hanci tayi "to ba kaina suka bari ya gani ba"

"Ance iska kika je sha, kina da wannan kan da kike boyewa ki rasa wurin shan iska sai falo. Yanzu da Kawu Zakari ne ya zo fa?"

"Bakinka ya sari danyen kashi, wannan ai mugun fata ne." tace tana harararsa ta tuna wanda ya dan gani a gidan Baffa Gide.

"Tunda Allah Ya rufa miki asiri ba shi din bane ba sai kawai ki basar ba irin a zuwan baki ma san me ya faru ba. Da nine ke fa wallahi da magagin baccin karya zan bar falon"

Sauran hawayen ta goge da bayan hannunta tana dariya harda kyakyatawa "shege Emzee ka iya bada shawara Yasin"

"Shine zaki zageni to" ya harareta yadda take masa.

Dan ture shi tayi bayan ta daure kanta da dankwali ta saka hijab "wasa ne dalla" ita ce a gaba yana bayanta. Sai da suka zo bakin kofar ta kasa fita tana jin kunya. Emzee na zuwa ya turata ta soma turjewa amma da ta ga kowa ita yake kallo sai ta dake yadda yace mata ta basar.

Duk da kumburin fuskarta bai hana Awwab sake gano kamannin wannan Alheran din mai askakken kai da 'yar karamar kanwarsa mai rigima ba. Ta girma amma tana nan da dan jikinta don tafi karfin a kirata ramammiya sannan baza'a ce ta shiga sahun lukutaye kai tsaye ba. Radhiya a dire take ta ciko ta ko ina. Da kadan ta dara Zayyana a tsayi ita da ake yiwa kallon doguwa saboda tsayin kafa. 

Yayin da Awwab ke kokarin hada ido da ita, ita kuma su Zahra ta kalla tana ta kokarin kada ta kalle shi. Tunda Emzee yace ta basar to fa basarwar zata yi.

"Shine baku tasheni nayi sallah da wuri ba Adda Zahra"

"Naga baccin naki yayi dadi ne"

Sai ta maida hankalinta ga Ibrahim "ka fadawa Umma ina gaisheta?"

"Tace kafin ku koma kije kiyi mata kwana biyu"

"Mama gobe zaki sa ya rakani?"

"Sai dai jibi Radhiya. Gobe asibiti zan kaiki ko har kin manta?" Asibiti za ta kaita saboda makeron da yaki barin gashinta yayi abin kirki.

Awwab sai binta yake da ido tana ta jan mutane da hira banda shi kamar ma baya wurin. Sai da Zainab tace "wai baki ga Awwab bane?"

Radhiya ta wani bude baki da idanu irin mamakin nan "laahhhh Mama yaushe yazo? Hamma, oyoyo"
Chapter 39 · 0% Book details