← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 157

Sashe 144

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata irin kunya ta rufeta wai ita ke da ciki. Dazu da safe Mama ta kaita asibitin an tabbatar mata wata biyu ne. Da yatsu tayi masa alama Zayyan harda hawaye "kinga ikon Allah da yadda Yake gwada karfin mulkinSa ga wanda Yaso a lokacin da Yaso. Ina sonki Mairama Allah Yayi miki albarka Yasa ki zama matata har aljanna"

"Amin Sojana...ba ka jiye min haihuwq ga 'ya a gidan miji"

"Itama ta haihu nan da wata tara nake fata. Arziki ne ni dai nagode"

"Nima ai nagode"

"To muje mu kwana kafin na fara jin rubewar panadol din nima" yaja hannunta suka kwanta kamar kodayaushe aka bude sabon babin tsohowar soyayyar da kullum suke aikin sabunta ta.

Da safe da yawa cikin bakin sun tafi musamman na Kano. Na Sakkwato kuwa sun jira su koma tare the next day. Zahra da Fauziyya ko keyarsa babu sai a ranar tafiyar. Awwab yazo yayiwa Radhiya sallama tare da saka mata kudi a jakarta ko za ta bukaci wani abu saboda shi da su Mami Katsina zasu wuce. Ummi, Mama da Tante ne zasu Sakkwaton.

Can ma gagarumin taro aka hadawa 'yar Zayyan don sunyi bajinta sosai 'yan uwansa. Anyi komai an gama lafiya. A ranar 'yan daukar amarya suka zo da ga Katsina da akwatunan lefensu guda takwas da kit. Awwab yayi kokari matuka abu kadan ne ba shi ya saka ba.

 Duk wannan bidiri da akeyi Ghazalatu suna can wani karamin hotel da Nura yana angwancewa. Tayi kuka tayi bala'in ta koma rarrashi duk ya toshe kunmuwansa. Cewa yayi sai ranar da za'a kai amarya Katsina zasu koma lokacin an gama share gidansu domin can zasu wuce. Tana kuka ta kira Mummy Gambo wadda tace mata umarnin Alh Baba ne tayi hakuri ta zauna gidan mijinta da kansa yayi alkawarin idan Nura ya sake tabata zai dauki mummunan mataki a kansa. Ba sa son da kuruciyarta a fara kirga mata aure. Ba haka taso ba amma dolenta ta hakura ko don gudun kada jiki yayi tsami.

Cikin wata hadaddiyar laffaya Mama ta shirya Radhiya aka fara shirin tafiya Katsina da matar Awwab. Ummi dai ba binsu zata yi ba daga nan Zayyan zai zo su wuce Nijar. Har yanzu bata bari kowa ya gane tana da ciki. Dauriya take sosai shiyasa Mama tayi ta kawo mata abin da zai sassauta mata tashin zuciya a boye. An fito tafiya da amarya idanunta a bushe saboda har yanzu ita fa bata ganin an kaita kenan tunda tasan zasu je Nijar sannan a koma Abuja. Abinda ta sakawa ranta kawai wani bikin zasu je a Katsina. An fito tafiya bakwai da mintuna Jume da Gwaggo Ladi sunyi mata nasiha zasu tafi da  iyayenta mata yayyen Zayyan da matan su Badaru ga wasu cikin cousins dinta sai su Yadikko masu komawa Sumaila yayin da Hajjo da wasu yau din zasu tafi Katsina.

Takalmin Radhiya me madauri ne ta durkusa tana daurawa wata tsohuwa tayi zaton kuka take yi tace " 'yar nan sai hakuri ki dena kuka haka kowace mace haka aka yi mata kema da sannu zaki saba"

Dagowa Radhiya tayi innocently tace "Iya ba kuka nake ba takalmina nake daurawa"

(wadda ta tsargu da ita nake.....)

Ummi na gefensu tsabar kunyar da taji bata san lokacin da ta durma mata wani uban dundu ba sai da ta kuma durkusawa cikin fada tace "kuka kike mana, ba na hanaki karya ba shine zaki kalli idanun Iya kice mata ba kuka kike ba"

Iya wadda ta kasance 'yar uwar Mal. Muhammadu ta kalli idanun Radhiya sosai "ai kuwa kamar ba kukan take ba Mairama"

"Kuka nake mana Iya baki gani bane kawai...ni ku rikeni na fasa tafiya" Radhiya ta soma yi musu hargowa ana rikota tana komawa ta rungume Ummi. Tsabar takaici ta rasa me zata yiwa yarinyar nan ta huce. Wannan runguma a bainan nasi salon ace basu da kunya.

Fada Ummi ta soma yi mata matar Rayyanu tace "haba Mairama ki rike yarinyar nan taji dumin uwa mana sai ki hauta da fada kamar baki san ciwon rabuwa da gida ba"

Mama ta gimtse dariya tace "kinsan wani idan abu yayi masa yawa kukan ma kasawa yake...tun da muka tashi asuba take sharar kwalla"

Ummi kamar ta hadiyi zuciya da Jume ta fito ga mutane suna ta cewa wai sun basu tausayi wannan uwa da 'ya akwai shakuwa sosai a tsakaninsu. Duk yadda take jin kunyar 'yar fari kuma a gidan surukai Sakkwatawan nan babu ruwansu suke cewa ta shiga daki ta kwantarwa da 'yarta hankali.

Suna shiga Ummi ta juyo a fusace Radhiya ta kwashe da dariya sannan ta nutsu tace "Ummi Allah Ya kara miki lafiya wallahi bani da kamarki duk duniya"

Hawaye ne ya saukowa Ummi ba shiri ta kai mata rankwashi ta goce. Da kanta ta rungumo Radhiyan tana murmushi zuciyarta na sake cika da farinciki "Allah Yayi miki albarka Ya baku zaman lafiya. Banda kiriniya kinga dai aure ba abin wasa bane kuma kin girma"

Tana makale a jikin mahaifiyarta take amsa mata. Gudun kada a leko ta tasata a gaba suka fito aka sakata a mota. Canter guda aka cika shake sosai da kayan gara gari guda kamar masu shirin bude kanti.

Gidan Alh Baba aka kaita inda duka kakanin da matayensu suke zaune suna jiransu. Yau dai wanda baisan Alheran Radhiyan Awwab ba ya ganewa idanunsa. Wasu ma sai tausayin Awwab din ya kamasu yadda Alh Baba ya hana wannan auren da farko. Zukekiyar bafillatana mai jinin buzaye irin wannan har ita ake yiwa yanga. Motocin da suka kawota dama akwai na sojojin da suka biyosu domin kariya kowa yasan ta wuce ajin raini ita da danginta. Yarinya an kawota da gararta abin kwatance sai son barka.

Zahra ce ta shigar da ita falon kanta a rufe ba ta iya dago kai ba amma jikinta ya bata Awwab yana ciki saboda wani fitinannen kamshin turaren da yake amfani dashi yanzu. A gefen kakarsu Maman Biyu aka zaunar da ita Alh Baba yace "dawo kusa da mijinki jikata"

A sanyaye ta tashi Zahra ta ja ta kusa dashi ta zauna a darare ita kuma ta fita. Nasiha tsofaffin nan suka rinka yi musu baka jin komai sai sheshshekar kukan Radhiya da gaske fadan yana shigarta. Da yake ta baza laffayar a kasan inda ta zauna ta karkashi Awwab ya zura hannu ya kamo nata sai da ta zabura amma yaki saki yana matsawa a hankali. Kukan nata ne ya tsagaita Baba Karami yace a wuce da ita gida su samu su huta. 

Uwargidan Alh Baba ce ta fito da ita aka damkata hannun iyaye mata suka wuce gidan Daddy. Dangi ne ko ta ina ga su Hajjo ma sun iso. Ana neman uwar amarya Mama ta fito ta rike hannun Radhiya har dakin Mami suna tare da 'yan uwanta ana hira kamar wani abu bai hadasu ba.

Bayan gaishe gaishe da tambayar hanya Mama ta kama hannuwan Radhiya dake zaune a kasa har yanzu bata bar kuka ba jikinta yayi sanyi ta dora a tafin hannun Mami na dama sannan ta kawo na hagun ta dora a kai ya zama na Radhiya ke tsakiya.

Muryarta babu alamun wasa tace "Mami ga amanar 'yata...."

Mami ta harareta "meye haka Zainab, Radhiya 'yata ce kada kiyi min haka"

Girgiza kai Mama tayi harda 'yar kwallarta "Mami ki barni nima na aurar da 'ya yadda kowa yake yi. Alheran dai a tafukan hannunki ta fado duniya kece kika karbi haihuwarta. Ko da aure ko babu ke uwa ce ga tsatson Mairama da Zayyan. A madadin babansu Hadir ina mai baki amanarta. Kinsan halinta babu wani abu sabo a wurinki. Idan tayi kuskure kinfi kowa sanin ta yadda zaki tsawatar ki sakata a hanya. Na baki amana ne ba don bazaki iya ba sai don taji da kunnenta cewa yanzu da da ba daya bane. Da can 'yarki ce yanzu kuwa jininki ta koma. Ke kuma Radhiya daga yau kin girma saboda haka duk abinda na fada miki a gida ki fara aiki dashi domin ibada kika zo yi"

Zantukan Mama Zainab ya taba Radhiya da Mami suka rungume juna suna kuka. Yadda suka yi ya taba matan dake dakin sosai suna kara girmama wannan kyakkyawan zumunci na mutanen nan.

Mami da kanta ta kama kai Radhiya dakin da Fauziyya suke tana fita kuwa suka fara zolayarta sai dai babu bakin ramawa an kashe mata jiki gabadaya. Bayan sunyi sallar la'asar anci abinci Mama ta hada 'yan uwanta da wasu kannen Mairama suka fito suka zaga kofar baya bangaren Awwab da yake jikin gidan amma kofarsa daga barin hagu ake shiga. Da can dan karamin falo ne da daki sai toilet. Amma ana gab da daura auren Daddy ya fadada masa wurin aka kara girman falon sannan akayi kitchen. Sun saba kowa a garinsu yake zuwa sallah. To haka yake son ta kasance ga tilon dan nasa. Sai kuma ya ga gidan nasu babu yara Zayyana kanta ba dadewa za'a aurar da ita ya zama daga shi sai Mami. Shine yayi wannan gyaran yada idan anzo Awwab ba sai ya nemi wurin ajiye iyali ba ko kuma su rinka rabe rabe a cikin gidan. Lokacin da ya fadawa Baba Hadir yayi wannan gyaran alfarma Hadir din ya roke shi akan cewa kada ya bari Zayyan ya sani haka kuma matansu sun boyewa Mairama. Komai da ya kamata a saka a cikin gidan nan Baba Hadir da Mama Zainab ne suka yiwa 'yar tasu. Daki daya ne aka saka mata wani makeken royal bed mai kyau. Ba'a cika dakin da tarkace ba bayan kayan gadon sai wani irin show glass na gani da fada wanda yasha turarukan wuta na asalin da humra da wasu irin turaruka masu maiko. Labulayen dakin kansu abin kallo ne. Toilet din a cikin daki yake an chanza tiles, tray din wanda, toilet seat da sink gabadaya an zuba sababbi. Kayan cikinsa ma sun hadu kamar ba toilet ba anyi masa kyale kyalen zamani.
Chapter 144 · 0% Book details