← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 157

Sashe 97

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuskarsa sai tayi kalar tausayi ya kalli Ummi yana girgiza kai "ina tsoron fada in saka babarku kuka". Kasa daurewa yayi da ya kyalla ido ya kuma ganin Zayyan a zaune " 'Yar soja mai kamar mahaifinku matar nan tana son yi min cune. Dadin abin ma dai tsakanina dashi sai alheri har muka rabu muna mutunta juna"

Dariyar kowa a take ta fito fili Zayyan ya matso ya sake kama hannuwan.Malamijo da yake shirin sandare masa saboda tsoro "nine dai Zayyan ban mutu ba"

"Minal hubsi wal haba isi....tuf, tuf" ya mike tsaye jiki na tsuma amma a dole dauriya zaiyi yana tofe tofe "kakana malami ne har ya mutu kuma sunansa naci har wata fatal..."

Ummi gani tayi abin ya soma yawa baban nata yasa yara suna dariya ta tashi ta riko hannunsa suka zauna kusa da Zayyan.

"Malamijo Allah Yayi da ransa ashe rufe shi akayi a kurkuku a can kasar da suka je yaki."

"Ki bari dan Manzo"

"Taba shi kaji wallahi shine"

Ali gadanga Malamijo ikon Allah sai kuka yana shasshafa jikin Zayyan. 

"Allah Qadiran Ala Mayyasha'u. Zayyanu kana nan dama?"

Zaman jajantawa akayi ya kira Na'e da bata sanshi ba a wurinta yake jin Yadikko ta fita. Sun dan taba hira aka tafi yin sallah Mairama ta fada masa Kano zasu wuce a bar masa yaran. Bai fada mata komai game da Hajiyayye ba sai iya wanda idonta ya gani. Dan sauran mutumcinsa yaji yana son karewa a idanunta. Idan sun tafi zai fadawa su Radhiya ko da ja a kasa su fitar masa da ita da yaranta. Kuma a nemo masa shanunsa kafin jininsa ya karasa hawa.

**********

Kyakyawar matashiya ce irin wadda ake kira black beauty durkushe a gaban Salame tana sauraron fadan da take yi mata tana share kwalla da kasan hijabinta.

Salame ta zama tamkar wata almajira a yankwane duk ta tsufa fiye da shekarunta hakora sun soma yin wani layin kore kore daga sama ta kankance idanu tana surfa mata masifa har wani yawu ne yake kumfa kumfa daga gefen bakin.

"Banza jinin matsiyata. Dangin ubanki kaf basu da farcen susa sai kwala kwalan idanu kamar mujiya. Yanzu Rahima banda baki daukeni a bakin komai ba in aika miki cewa bani da lafiya amma kizo min gida hannu na dukan cinya"

Muryarta har ta dashe saboda kuka a tsakar dakin da ko arzikin leda babu ga kannenta 'ya'yan Alh Indararo sai murguda mata baki suke yi da masu gwalo tace "Umma wall..."

Hannu ta kai ta mangareta "rufe min baki zaki fara sakin karya yadda ubanki yake yi. Kina sana'ar yin kunshi amma 'yar kazar nan ko ki dan kullo kudin ki bani domin saka albarka ya gagara. Kinfi ganewa ki bawa matsiyacin babanki ya ciyar da matarsa da 'ya'ya ni da na tsugunna na haifeki ko oho"

Maman Danmama ce ta dago yagaggen labulen dakin ta leko "ke kuwa Salame ki bar yarinyar nan haka mana. Tun shigowarta kin sakata a gaba da bala'i kamar  baki san ciwon haihuwarta ba"

Cike da masifa ta dago "ki dai zuba ruwa a kasa ki sha kawai saboda farinciki. To dai duk tsiya tafi Danmama da yake karen mota a tasha"
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: ***********

Tsattsaye suke maza da mata a kofar dakin a aibitin likitoci suna ciki suna aikin kokarin ceto rayuwar yarinyar da ke ciki.

Daga can gefe Hussaina ce take kuka wiwi jikinta duk jini tana sambatun kada autarta ta mutu. Duk cikin yaranta kowa ya shaidi yadda take masifar son auta Hany. Yarinya ce kyakkyawa mai mugun shiga rai. Bata da hayaniya ga kokari a makaranta. Hussaina duk inda ake hirar yara tamkar sauran shidan babu su zancen bai wuce Hany tayi kaza ko Hany tace kaza.

"Kiyi shiru mana Hussaina mu samu su fito aji halin da take ciki" Ummansu tayi mata tsawa.

Alh Baba da akayi komai a kan idonsa ya biyo su asibitin shima hakuri yake bawa Hussainar hankalinsa a mugun tashe. Saboda soyayya yarinya ta sanya reza ta tsinke jijiyoyin hannunta wai gara ta mutu da a rabata da wanda take so. Wannan wane irin zamani ne rikirkitacce haka.

Lokaci ya shude kafin likitan ya fito yace anyi nasarar tsayar da jinin amma fa wanda ta zubar da yawa ana bukatar a kara mata ko leda daya ne zuwa biyu. Hannu na rawa Hussaina ta kira Nura. Blood group dinsa daya da Hany tace maza maza yazo a debi jininsa.

"Kawai ki nemi wani" taji ya bata amsa ga alama ma cikin maye yake don a datse maganar ke fita.

"Nura ni kake fadawa haka? Kanwarka fa nace"

"Tare fa aka gwadamu kuma kema irin naki ne ki bata mana" ya kashe wayarsa ya fada gado rigijib. Kwance a kasa Ghazalatu ce rike da cikinta bayan yayi mata mugun duka. Da rarrafe ta soma tafiya domin ta bar dakin sai ta gano ashe jini ne yake naso a duk inda ta bi ga azababben ciwon ciki ya murdeta. Lallabawa tayi zuwa dakinta ta kira Mummy Gambo ta fashe mata da kuka.

"Sai da nace bazan dawo ba Mummy gashi nan zai kasheni"

Hannu ta kai ta tabo Daddy Haroun ta saka wayar a speaker hankalinta a tashe saboda yadda take jin muryar Ghazalatun.

"Me ya sameki?"

"Mummy dukana yayi ga jini yana bin kafata kuma cikina...cikina..."

Kashe wayar tayi da sauri ta kira Hussaina wadda take kwance ana diban nata jinin. A zatonta Nura ne shiyasa ta matsawa Ummansu ta bata wayar sai dai tana karawa a kunne ta jiyo masifar Gambo hatta Umman tana ji.

"Hussaina ki rubuta ki ajiye sai nasa an daure Nura in ga uban me kuke takama dashi. Yarinyata ba jaka bace da zai rinka dora mata hannu duk lokacin da ta raya masa. Dama kuma na fadawa Alh Baba idan ya kuma dukanta ya daki aurensa"

Muryarta ta zama weak sosai tace "Gambo muna asibiti da Hany ki bari..."

"Bazan bar komai ba. Ki tura a dauko min yarinya a kaita asibiti tace jini yana bin kafarta"

Yunkurin tashi tayi Umma tace ta kwanta ta fita ta sanar da Alh Baba wanda ya hana a fadawa mijin Hussaina da Baban biyu komai sai yadda ta kaya. Dan tsohon sai ya kara shiga firgici ba yadda ya iya haka ya kira Baban Biyu ya sanar dashi. Yana gida a zatonsa Umma tana gidan Alh Baban ne ashe kuma suna asibiti. Kanin su Mami ya nema Allah Yasa ya dawo gida dayake bashi da nisa daga gidan iyayen nasa yazo suka fara tafiya gidan Nura. Bugun duniya Kawu Mas'ud yayi a dan karamin gate din gidan ba'a bude ba. Ya shiga kiran Ghazalatu tana can bata san inda kanta yake ba sai da Baban Biyu yace ya zai kira wasu cikin 'yan uwa su taru a balle kofar sai ga Nura cikin maye ya bude gate din.

"Wane dan...."

Naushi yaji ya sauka a bakinsa da hanci zaiyi magana hasken fitilu ya nuna masa fuskar kakansa da kuma kanin babarsa wanda ya sauke masa naushin kafin ya bangaje shi ya shiga ciki. Kofa biyu ya bude yana leke ya sami dakin da Ghazalatu take kwance a kasa. Da sauri ya ciccibota don ma wahala ta sake zugeta bata da nauyi ya fito ya sakata a bayan mota. Nura yana tsaye ya yi ribas suka bar wurin bai iya motsi ba. 

Asibitin da aka kwantar da Hany suka kaita tunda nan Alh Baba yace su samesu. Ana zuwa Ghazalatu tayi bari na 'yan biyu. Umma kuka ta zauna tana yi sosai kamar yadda Hussaina duniya tayi mata zafi.

"Kinji dadi Hussaina, ga ribar shiga tsakanin Gambo da Hassana kin gani zahiri ko. Itama Gambon da shegiyar kafiya da kin jin magana zata zo ta ga nata sakamakon na dora son zuciya akan komai."

"Umma kada kice haka" Hussaina tace a raunane.

"Matsa min ni na wuce"

Umma ta fita tana share hawaye. A wajen inda motar Kawu Mas'ud take ta sami Alh Baba da Baban Biyu. Ranta yana kuna yau ta manta da surukuta da girman Alh Baba ta soma magana.

"Kun tuna lokacin da Awwab da iyayensa suke rokon a barshi ya auri Ghazalatu da daya yarinyar abokin Mustapha ko? Ku ka kekashe kasa kuka nuna naku, naku ne dan kowa bai isa ba. To yau gashi Hannatu tana son yaron da iyayensa sun rantse sai dai ya auri 'yar uwarsa kuma su danginsu basu zama da kishiya"

"Fatima!" Baban Biyu ya daga murya da niyar yi mata fada.

Kukanta ne ya tsananta tace "Ko me zaka ce sai dai ka jira na gama fadin nawa. Saboda wannan akidar ta auren dangi da ba farilla ba kun raba min kan 'ya'yana. Dukansu yanzu daga masu goyon bayan Hassana sai 'yan bayan Gambo. Hussaina kam dama ita ta sayawa kanta koma me ya sami nata yaran saboda kofar da kuka bude musu tun farko. Ni dai baku yi min adalci ba wallahi". Bayan motar ta bude ta shige "kaini gida Mas'ud" ta umarci dan nata.

Alh Baba da Baban Biyu aka rasa me cewa komai. Yanzu yake bawa kaninsa labarin abinda ya kaisu da zuwa asibiti. Hussaina ta damu da halin da Hany ta shiga saboda dangin saurayin nata sunki yarda ayi auren shine ta tsefe ido ta tafi gidan Alh Baba tana rokon ya sanya baki tunda kakan yaron abokinsa ne. Fadan da ya soma yi mata ne akan soyayyar ya sake jagula komai ta fita ta yanka hannunta. A take Hussaina ta kira mahaifiyarta tana kuka shine ta taho gidan suka wuce asibitin tare.

"Yanzu ita Hussaina ba kwari gareta ba ga jinyar mutum biyu. Na rasa yadda zanyi da rigimar nan. Nura bashi da hankali dole muyi wani abu"

"Ko baka ce ba wannan wajibi ne. Tunda Fatima ta ajiye kawaicin tayi magana kasan an kure hakurinta."

Umma na zuwa gida ta kira Mami ta fada mata abinda ke faruwa tana kuka. Hankalin Mami a tashe ta sanar da Daddy. Suna haka Daddy Haroun ya kira shi wai Gambo babu lafiya jininta ya hau suna asibiti.

Mami ta leka daki wurin Fauziyya, ita kadai ta rage a gidan ta fada mata zasu fita zuwa asibiti.
Chapter 97 · 0% Book details