← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 157

Sashe 17

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Soye idanu tayi don bazata yarda a hanata zuwa ba. Ta nuna musu akwai makota da take son yiwa sallama irinsu Christie wadda bata kara gani ba tun lokacin da tace zata je yi mata girki. 

Mal Aminu yace "Ka barta taje Maikudi. Daga nan ma sai mu bincika muji ko akwai wani abu da zasu bawa iyalin mamatan. Mu bari jikinta ya kara kwari ko nan da kwana biyu ne" 

Ransa baya so saboda ya kula tunda ta dage sai taje akwai dukiya dankare a gidan da bai taba zuwa ko kofarsa ba. 

"Ina mukullin a bani na rike saboda 'yan barka da gaisuwa kada wata ta dafe"

"Maikudi kenan, ko ma wacece ba sai dai muce Allah Ya bada sa'a ba. Sata a gidan soja, gidan sojan ma a cikin bariki kamar mutum ya tashi da burin karar kwana" Gwaggo Ladi ta gwaba masa magana.

Bai sake magana ba su ka tafi gida. Jume tasa matan su Badaru gyarawa Mairama dakin Innar Zayyan. Tana shiga ta tuna ranar sunan Radhiya da hotunan da suka yi da Zayyan da Awwab a ciki. Idanunta da basa rabo da hawaye suka fara abinda ya zame musu jiki yanzu. 

Jume da kanta tazo tace mata ta shirya ta fito zata yi mata wankan jego. Jariri kuma Gwaggo Ladi ta dauka tayi masa wanka irin wanda bai samu ba tun ranar haihuwarsa saboda kasancewarsu a asibiti.

**********

"Ya muke ta bin lungu ne yaro? Nayi zaton a irin unguwannin nan da suke malale da titi gidan yake" 

Rayyanu ya kalli Malamijo ya sake daure zuciyarsa a karo na barkatai ya bashi amsa akan irin wadannan tambayoyin da yake ta yi masa.

"Gidan iyayenmu ne a nan unguwar. Zayyanu a cikin bariki ya zauna da iyalinsa"

Malamijo sai murmushi "Auhooo ko da naji. Ca nake a nan Mairaman tawa ta zauna ne"

Su hudu ne a ayarin tafiyar banda Rayyanu suka biyo motar haya. Nene Marka, Malamijo, Hajjo da kuma Salisu. Gidan yanzu Yadikko da Hajjo ne kawai a gidan, ya saki Dije da Inno yana shirin karo wata. Tun a tashar Kano ana cewa a kawo kudin mota Malamijo ya shiga tarin karya, daga baya ma sai yayi gaba yana dukan kirji sai da ya hango Salisu ya biya musu kudin motar su duka sannan ya dawo yana cewa kwarewa yayi.

"Sai ji nayi wani abu siririt ya wuce min ta makoshi. Kwarewa babu dadi, ammm nawa ne kudin motar ne?"

Nene tasan dalilin tafiyar tasa sai kawai ta dauke kai. Hajjo ce ta fada an biya yayi wata barazanar zura hannu a aljihu zai dauko kudin ya bawa shi. Sal da Salisu yace ya bari duk daga ne.

Iyaye da dangi duk lalacewarsu sunfi ace baka da kowa. Sallamar Malamijo kawai Mairama taji ta sa kuka sosai. Kuka ne na ganin babban gatan da ya rage mata duk fadin duniyar nan. Shine bango abin jingina a gareta wanda take sa ran idan tayi kukan rashin miji zai rarrasheta yace ta barwa Allah komai. Idan tayi kukan rayuwar marayunta zai yi mata alkawarin matsawar yana numfashi 'ya'yanta bazasu tagayyara ba.

Jikin Nene Marka ta zube suna kuka tare. Malamijo ya tausayawa Mairama sosai ya mika hannu ya dauki Radhiya. Zayyan wanda duka gidan an rasa mai kiran sunansa har Maikudi kuwa saboda tuna musu da marigayi da yake yi matar Badaru ta kwanto daga bayanta ta mikawa Hajjo.

"Iko sai mai shi, Malamijo dubi yaron nan don Ma'aiki."

Radhiya tana gefensa ya karbi jaririn yana kare masa kallo. Salisu yazo ya karbe shi shima ya ga kama sosai da mahaifinsa.

"Allah Ya raya mana kai karamin soja

"

Mazan sun koma waje inda ake zuwa yi musu ta'aziyya matan kuma suna daga ciki. Sai dare ne Mal Aminu ya sanar da Malamijo za'a kwaso kayan Mairama sai su tafi da ita.

"A'a a bar yarinya a gidan mijinta. Idan akwai wata dukiya da bazata iya juyawa ba ni sai na tafi da ita ba wani abu."

Maikudi yayi saurin cewa "dukiyar marayu zata fi dadi a hannun dangin uba. Saboda haka gobe zamuje ayi duk yadda za'ayi ne. Gida kuma ba nasu bane na bariki ne. Tunda ya rasu dole ne su tashi komai dadewa"

A hankali zantukan nasu suka fara neman komawa rigima. Maikudi da Malamijo kowa ya nuna zalamarsa a fili. Shiyasa kowa cikinsu yake ganin dole ya tsaya akan dukiyar da basu da tabbacin akwaita.

Shabiyun rana kuwa washegari suka isa kofar gidan da ya kasance na Mairama da Zayyan kwanaki kadan da suka wuce. Ta kalli gidan Zainab a rufe har yanzu. Tana son sanin halin da suke ciki da mazansu amma yanzu babu hali sai komai ya daidaita a nata bangaren. Gidan Christie ma a rufe yake. Bayan ta bude nata gidan sun shiga da yayyen Zayyan mata da kuma Hajjo sai ga wasu cikin abokan zamansu na kusa. Gaisuwar mijinta suka yi mata da barkar Zayyan karami. Ta tambayi ina Christie wata ta bata amsa da cewa ranar da ta haihu Christie tazo tayi mata girki kuma ta farfadawa makota haihuwar. Ta koma daidai lokacin da Mairama ta suma. A nan take jin duka sojojin sun rasu ciki kuwa harda mijinta. Bata iya shiga ba ta koma gida bayan ta sauke musu Radhiya. Shine aka sami wani da ya san gidansu Zayyan aka fada musu. Ita kuma Christie ta tafi garinsu ta fadi mutuwar har yanzu bata dawo ba.

Duka matan abin tausayi musamman wadanda mazansu suka tafi a bayan su Zayyan. Suna cike da tsoro da fargabar me zai je ya dawo.

Wasunsu sun saka hannu wurin tattare kayan kitchen da na falon Mairama ana hade komai wuri guda ana fitarwa. Cikin dakin ta shiga zuciyarta tayi matukar rauni. Shikenan daga yau duk wasu memories da suka gina da Zayyan a gidan nan cikin wannan dakin sai dai zu dawo mata a tunani. Kukanta Hajjo ta jiyo ta shiga dakin da sauri.

"Haba Mairama ashe bazaki sakawa zuciyarki salama ba? Ni ko kadan ban so aka ce wai azo kwasar kaya da wuri kamar ana korarki ba. Su dakata ki sami nutsuwar zuciya sun ki"

Mairama ta bude wani akwai ta dauko envelop din da Zayyan ya bata hannu na rawa ta saka a jakar hannunta sannan aka fara hada kayan gidan.

Malamijo yana waje yaki shiga ba don kunya ba sai don bakinciki. Shi kadai a ransa yake nanata an yaudareshi aka ce masa Zayyan soja ne. To yaji sojan ne amma ba wani mai mukami bane ashe. Ji dai wannan akurki da ya ajiye masa 'yarsa ya raya a zuciyarsa. Kuma ashe ma ba nasa bane. To duka kudaden da yake masa alheri dasu a ina yake samowa? Faduwar gaba yaji da ya tuna indai fa babu wani abin kirki da ya bari komai na Mairama da 'ya'yan wuyansa zai dawo. Hodijan inji mutanensa, aradun Allah bazai iya karawa kansa nauyi ba. Yanzu fa yara goma sha bakwai gareshi. Salame ce kadai a gidan miji tunda dai Zayyan ya rasu. Gata ta tunda tayi aure ta ari rigar rashin mutumci ta saka.Tsaki yaja sai hankalinsa ya koma ciki inda yake jiyo muryar Maikudi.

"Kai wannan takadirin yaro da gani zaiyi mugunta. Me kuma yake nema a cikin mata?"

Shiga yayi da Salisu ya sami Maikudi yana fada "ki fito min da duk wani kudi ko takardun abubuwa masu mahimmanci na Zayyan. Dukiyar magada sai da saka ido. Ba wai da ka zaki dauke komai ki rike ba"

Salisu ya riko hannunsa "kaga Mal Maikudi duk abin nan ba na rigima bane. Mairama ba jahila bace da zata ci dukiyar mamaci. Sai dai fa ina so ka sani duk danginku babu mai gadon Zayyan sai Mairama da 'ya'yanta"

Kamar zai kaiwa Salisu duka ya soma fada "ni nasan ba banza ba kuka taho kwanku da kwarkwata. Ashe da manufarku. To babu wanda ya isa yayi sama da fadi da dukiyar magada muddin ina raye"

Mairama dai sai kuka. Malamijo ya zakalkale yana ta zubar musu da daraja a gaban 'yan uwan Zayyan. Idan Maikudi yayi shi za'a ce da sauran kuruciya. Shi kuwa yana mahaifinta ga jikoki har uku amma har yau bai fasa halinsa ba. 

Mal Aminu da kawunsu Zayyan sun shigo sun  same su ana ta mayar da magana. Sam Mal Aminu baiji dadi ba. Ga Mairama sai ajiyar zuciya kawai take yi.

"Daga can ofishin nasu nake an kaini har wurin wani babba cikinsu a nan munyi magana. A takaice dai muna da yawa da muka rasa 'yan uwa a wurin nan. Amma yace muyi hakuri ba'a turo komai daga gwamnatin tarayya ba da zasu sallami iyalan sojojin ko kuma masu rauni"

"Ikon Allah, yanzu ace mutum ya rasa rayuwarsa a bakin aikinku amma babu sallama ga iyalansa da maraici ya kama su?" Cewar Salisu

"Don ma baka je wurin bane. Mutanen da yawa wallahi. Sun ce kuma sojojin da aka rasa suna da yawa ba wai na nan bane kadai. Kuma wai gwamnati bata da kudi amma zasu neme mu idan an sami wani abin"

"Wannan ai zancen banza ne, bata da kudin take kashe mana 'yan uwa? Ni bazan hakura ba. Wannan magana kuma bazan bari ta mutu a nan ba." Maikudi yace yana tashi tsaye "idan ma an fada ne don a sa jikina yayi sanyi kada na tsayawa marayun nan wallahi sai naje" ya zubawa Mal Aminu idanu.

Murmushi yayi kawai yace motar daukan kayan tazo. Kawunsu ne ma ya rinka yi masa fadan baya son rashin kunya. To amma da yake duka talakawa ne maganarsu bata wani tasiri a wurinsa.

 Abu kamar wasa Mairama da tazo barikin nan a matsayin amarya kasa da shekara biyu wai har anyi zaman an gama. Mijinta abin kaunarta ya tafi ya barta a hannun wadanda basu damu da halin da take ciki ba, kawunansu kawai suka sani.
Chapter 17 · 0% Book details