← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 157

Sashe 152

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah Sarki zuciya na wuya sai kawai ta soma kuka tana kankame a jikin mahaifiya mai dadi ko da kuwa ta buzuzu ce. Da kyar Salame ta samu Alh Indararo ya barta ta taho sai da tayi karyar zuwa zata yi suyi magana akan yaran da za ta basu. Malamijo kuwa cewa yayi indai tasan rigima ce za ta kawota Abuja bai yafe mata ba idan ta je. Damuwa ce fal a zuciyarta akan Rahima. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da yarinyar sosai. Daga baya ta fahimci dama can tana son abarta wasu abubuwan ta saka a gaba kawai.

Wannan kuka na Rahima ya tada mata hankali fiye da tunani ta kama hannunta zuwa dakin baki da yake kasa.

"Rahima wani abin kika sake ji nayi?" Ta tambayeta a tsorace tana fata yanzu kuma ba labarin ta taba son Zayyan Tureta bane ya fito.

Girgiza kai tayi hawayenta yana karuwa cikin rawar murya ta ce "Umma nace ki rinka yi min addu'a Allah Ya cire min Ya Emzee daga raina Umma ba kya yi...Umma ko sau daya kiyi min addu'a a rayuwata" ta durkushe a kasa tana matsanancin kuka.

"Ina miki addu'a duk sallah Rahimata, idan ban miki ba wa zanyiwa bayan duk abinda naja miki" Salame ji tayi ta tsani kanta tana Allah wadai da son zuciya. Ita bata girbe da hannunta ba 'yar da take jin kunya ita ce take mata dakon wahala. 

A wannan lokacin Mairama ta nufo dakin saboda an sanar da ita zuwan Salame. Nan ta jiyo kukan Rahima ta bude kofar da sauri sai ta ga sabanin abinda ta zata wato tana dukanta rungumeta tayi.

"To me yasa bana jin komai, kirjina kullum ciwo yake. Ki koma gida dani ina kunyar Ummi, ina kunyar Daada dasu Adda Radhiya"

Fuska sharbe da hawaye Salame take shafa bayan Rahima "kiyi hakuri zan roki Mairama na santa da hakuri za ta duba lamarinki tunda tana sonki"

Rahima sai girgiza kai take yi "a'a Umma bazan taba auren Ya Emzee ba ko...."

"Ya isa haka Rahima zo ki fita" Mairama ta yi mata tsawa cikin bacin rai "ina zaune da ke ina bibiyar me ya sameki ni kin kasa fada min saboda ni baki daukeni uwa ba?"

"Ba haka bane Ummi kiyi hakuri" tace tana dawowa kusa da ita tana wani irin kuka.

 Rungumeta Mairama tayi sannan ta ce "Karami ya taba cewa yana sonki?"

Kai ta daga kawai jiki na rawa. Wannan wane irin so ne mai cin ruhi da ba za ta iya hakura kamar yadda take son yi ba.

Cikin kulawa ta sassauta muryarta "indai ni na haifi Zayyan in sha Allahu sai kin amsa sunan matarsa tunda shi ya fara nemanki"

"Ummi a'a" tace saboda sanin da tayi cewa yanzu baya sonta.

Salame ta galla mata harara ga hawaye har yanzu "ke kaniyarki, ku ji min yarinya ana baki kina kin karba"

Mairama murmushi tayi sannan ta ce "Kina so muyi fada ne?"

"A'a"

"To kada na sake jin zancen me ya hadani da Addata a bakinki ko na 'yan uwanki sai na saba muku. Babu ruwanku tare kuka ganmu. Karami kuma ki tattara shi ki zuba a kwandon shara ki fuskanci karatunki sai ya nemeki da kansa. Akwai wani namiji da ya isa ya ja wa RAHIMATA aji ne" ta kalli Salame da jin baki taji me zata ce.

"Na fada miki Mairama ba dai hakuri ba ke dai barta da zuciya kamar kuturwa" cewar Salame tana fyace hanci da mayafinta.

Rahima tayi murmushi ta ce "kai Umma"

Mairama tayi 'yar dariya ta ce "Kin dai ga yadda nake hakuri da ita ku ma sai kuyi ta yi. Kiyi wanka ki ci abinci. Yau ranar zuwan malamin islamiyyar ne ko na lesson?"

"Lesson ne"

"Kici ki kwanta zan kira shi nace ya bari sai gobe....idan na sake ganin hawayenki akan wata damuwar da ba taki ba ni da ke ne"

Fita Mairama tayi Salame ta bi bayanta da sassarfa. Kamar ba ta ji ta ba sai da ta shiga dakinta itama ta shigo kawai ta durkusa a gabanta tana  kuka. Itama Mairaman kuka ta saka tana tsaye Salame na durkushe tana yinsa mai cin rai da zuciya abin tausayi.

Lallai duniya mai yayi duniya juyi juyi yau ita Salame Ali ita ce durkushe a gaban Mairama Ali tana kuka irin wannan "Ki gafarceni Mairama wallahi ban kyauta ba, soyayya ba hauka bace ni ban san me yake damuna ba ko tunanin me nake har na rinka yi miki irin wannan diban albarka. Da gaskiyar mijinki hassada na dorawa zuciyata gashi ina nan jiya e-yau. Don Allah ko bayan raina Mairama ki aurawa Karama Rahima ko ta sami saukin cutarwar da nayi mata. Kinga ni ce da laifin amma ita ke da wahala banda haka ina ita ina wata soyayya mai zafi haka..."

"Adda ki tashi ki zauna muyi magana"

"Idan kinga na zauna to yafe min kika yi"

"Ke fa kika ce mun wuce wannan matakin tun a Nijar" inji Mairama

"Lokacin ma wasa ne nake yi mutum baya wasa da rokon gafara." Salame ta sake kwantar da kai.

"Komai ya wuce a wurina, dama can ke kika jawo muna zaman zamanmu kika canja hali. Allah Ya kara mana hadin kai"

Wani kallo mai cike da girmamawa da mutuntawa take yiwa kanwarta. Idan tana da sauran shakku na cewa Mairama tayi mata fintinkau a komai ya kau a yanzu. Za ta iya rantsewa cewa idan ita ce Mairama sai ta baro mata rashin mutumci kwando kwando kafin ta hakura. Halinsu ba daya ba haka nan zuciyarsu da bambanci. Kila shiyasa ita ta kare a kasa marainiyar wayonta ta haye ta barta.

"Nagode, nagode, nagode...amma nace ba, maganar Karami da Rahimata za ki sanar da maigidan naki da wuri ko" 

Dariya ta baiwa Mairama "Adda Salame kenan maganar aure ai babu ita?"

"Cewa zakiyi baki yafe min ba!" Salame ta saka sabon kuka.

Zaunar da ita Mairama tayi don ta gaji da tsayuwar ta soma magana a nutse "Adda daga Karami har Rahima yara ne masu karancin shekaru. Shi yanzu yana ashirin da biyu da watanni ita ko sha bakwai bata rufa ba haka ne?"

"Eh to amma auren wuri ba yafi ba ko don fitintinun zamani"

"Nima zanfi son haka amma shi da yake namiji bai gama karatu ba. Ita ma bana so a yanke mata ba hanzari muke yi ba. Wannan soyayyar da suke yiwa juna wuta-wuta kamar yaki harda kuruciyar da take cinsu su duka da kuma isharar Allah akanmu ni da ke. Mu barsu su kammala, su kara nutsuwa su sake hankali sai mu ga abinda Allah zaiyi. Kada kiyi min mummunar fassara duk duniya babu matan da Karami zai kawo min a matsayin suruka nayi farinciki sama da Rahima ko Zayyana saboda su ne 'ya'yana. To Alhamdulillahi ba tare da wata dabara daga garemu ba sun daidaita kansu. Mu kara hakuri kadan wannan hayakin ya sauka hankali ya game jikinsu musamman shi namiji da ragamar gida za ta hau kansa"

Kallonta Salame take cike da sha'awa tana murmushi "lallai boko ya ratsaki Mairama ji yadda kike fito da bayani mai ma'ana da kuma hangen nesa. Hakan yayi min wallahi dama burina ni dai in hada zuri'a dake duk tsiya ko albarkacin jikoki sai kin yafe min" ta kare da murmushi.

Sai da Mairama ta dara don tasan tsokanarta take yi "zan yiwa Rahiman bayani da kaina ba rabasu zanyi ba amma a maida kai wurin karatu. Babban tashin hankalinta kuma kinsan akan yadda kike yi ma ta ne ina rokon arziki ki gyara ko zamu ji dadi"

Dofana mazaunanta tayi a kusa da kanwarta sai ta ga bata kyareta ba sannan ta saki jiki "Mun riga mun shirya da ita fa...zancen gaskiya ma ina ganin laifinku a yadda na canza ke da Malamijo"

"Da muka yi me?"

"Tunda abin nan yake ta faruwa da kun sani kun karbo min taimako ko da na ruqiya ne don jikina yana bani me yiwuwa shafar jinnu ke damuna"

Mairama ta kwashe da dariya "idan jinnu basu shafeki ba ai wannan annakiyar kazantar za ta shafeki. Adda ji hakoranki don Allah koraye babu kyaun gani. Na san da wuya idan Alh Indararo yana iya kusantar wannan bakin naki"

Salame ta rike haba "su Mairama babu ranar girma, kada dai kice min kuna nan kun daddangwalar bakunan juna ke da mijinki"

Dariyar da Mairama tayi ta jima rabonta da irinta "wai dangwalar baki...to naji ko ma me kike kiranshi ku ba kwa yi ne?"

"Allah Ya agajeni ni ko magana yake min kaina baya matsowa kusa da bakinsa mai dan uban wari"

"Wai Kura ce za ta ce da Kare maye, ke ma me zai kawo shi gaban naki. Ina ku ka baro brush da makilin?"

"Tabbb..mu sami na kai wa bakin salati dai shine magana." Tashi tayi tana murza hannuwa "yanzu dai tunda hankalinki ya kwanata Salame ta dawo gareki a taimaka a bani abinci"

"Au ni kadai ce hankalina ya kwanta? Shikenan jeki abinki kowa yayi ta kansa"

"Daga wasa sai ki hade rai kamar zawo" Salame ta ce tana murmushi. Babu abinda zai faranta mata yanzu kuma sama da ganin ko yaya ita da Mairama sun fahimci juna.

Wata dariyar Mairama tayi kawai tana cewa ta kula kazanta ta sami mazauni a tattare da yayarta.

Abinci Salame taje taci ita kuma Mairama tayi wanka ta sauko kasan. Salame dai kasa sakin jiki tayi duk yadda ta so saboda wani girma da kwarjini da Mairama ta kara a idonta. Masu aiki take gani su na rawar jikin cika umarninta kuma ba wai don ita din ta kasance mai tsanantawa ba. Ko kadan, tsabar iya mu'amala da nuna musu cewa su da ita abu guda ne ya janyo hakan. Nasiha da jan kunnen da ta yiwa Rahima ya sake ninninka girmanta a idon Salame. Cikin hikima da sanin ya kamata take nuna mata ta ajiye komai tayi karatu. Ga mamakin Salame har ji tayi tana cewa,

"Karami ba autan maza bane kada ki bari tun ba ku daidaita ba ya san cewa kina son shi haka. Kuma kada ki sakawa zuciyarki lallai sai shi, rayuwa bata da tabbas, kiyi kokarin inganta rayuwarki da ta iyayenki da kuruciyarki"
Chapter 152 · 0% Book details