← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 157

Sashe 51

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba wuya anci galaba a kanta. Bare kuma rarrashi daga Umminta sai tayi dan murmushi.

"Kyalesu ni na fasa tunda basa son tawa sallamar" ta basar a zuwan taba damu ba.

"Ke dai ki karba kafin ki zo da kanki na hana"

Sautin dariyar Radhiyan taji ta girgiza kai. Wannan yarinya sai addu'a. Radhiya na kira da taji ta shiga sai kuma kunya ta kamata ta mannawa Umminta wayar a kunne. Dauka Mami tayi tana fada mata inda suke yanzu.

"Tsakanin ke da Maman yara bansan wanda ya koyawa yarinyar nan shagwaba ba. Ba karamin abu kesa aji kukanta ba. Yanzu kuwa kukan gaske take min wai bakuyi sallama ba"

"Allah sarki Radhiyata, bata wayar mu gaisa"

Karba tayi ta gaisheta kamar ba ita ke kukan ba ta kuma gaisa da Zahra "ina su Adda Fauziyya?"

"Suna daya motar da Hamma ke ja. Yanzu zan fada mata ta kira ki"

Katse wayar tayi ta kira Fauziyyan ta fada mata. Ita kuma tana jiran Zahran ta turo mata nambar take fada musu wai Radhiya tayi kuka da bata gansu ba.

Motar sai ta koma hirarta da kewarta da suke yi. Ghazalatu haushi ya kamata kamar wadanda aka yiwa asiri kowa ya bude baki sunanta yake kira. Awwab tuki kawai yake yi kamar ruwa ya cinye shi. Matsananciyar damuwa ya shiga na son sanin dalilin kukan da kewarta da take ratsa shi ta ko ina. Yana ji suna hira da ita wannan ya karba ya bawa wannan amma bata yi cigiyarsa ba, shima bai nema ba tunda yana tuki ne.

Daurewa kawai tayi bata neme shi ba duk a cikin fushin idan kowa baice a tasheta ba shi ya kamata yace. Ummin tana jin yadda muryarta ta sauya cikin jindadi ta gama wayar ta tashi ta tafi yin wanka.

Sun isa Kano shabiyun rana. Mama tayi musu abinci tace su ci kafin su wuce. Aka zubawa Awwab ya kalli plate din yaji gabadaya yunwarsa ta tafi. Cin abincinsa da Alheran a soron gidan Malamijo yake muradin maimaitawa. Kasa daurewa yayi ya fita ya bar Abdallah da su Ibrahim suna cin abinci. Mami da Mama kuma suna can suna tattauna yadda al'amarin aikin Hadir zai kasance. Cikin motar ya koma ya zauna a baya sannan ya kira Fauziyya yace ta turo masa nambar da zai kira su Ummi. Dariyar shakiyanci ta rinka yi masa ya fara fadan da bata sanshi dashi ba tayi saurin katse kiran ta tura masa.

Bugu biyu Ummi ta shafa wurin daukan kira ta kara a kunnenta. Muryar Awwab taji ta tambaye shi yaya hanya. Sun taba hira kadan kamar ta fuskanci me yake jira ta kwalawa Radhiya kira.

Bata tambayi ko waye ba ta karba "hello"

Shiru yayi yana jindadin amon sautin daddadar muryarta. Ita kuwa ta gaji da hello hello din tace "Ummi anki magana fa"

"Ko ta katse, duba zaki ga nambar Awwab ce ki sake kira. Mami tace ta saka nambar kowa"

Tashi tayi da gudu ta bar dakin, Ummi sai shiru taji ta koma inda suka kwana tana jin wani nauyi a ranta. A hankali tace "Hamma"
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Kukan ne har yanzu baki dena ba?" Yace a hankali yana jin farinciki na shigarsa saboda jin muryarta.

"Ni ba kuka nake ba"

"Shine daga tashinki kika soma damun mutane da waya ina jin ko wanka bakiyi ba"

"Ba kune ba sai kuka tafi bakuyi min sallama ba"

Siririyar dariya taji yayi "Silly girl. Cewa zakiyi nine na tafi banyi miki sallama ba ko ba haka kike son fada ba zaki basar?"

"Inji wa? Ni da munyi fada da kai"

"Ke abu baya wucewa a wurinki ne? Kuma ba na goge ba. Wai ma in tambayeki fushin na meye?"

Daburcewa tayi ta rasa me zata ce masa har ya sake maimaita tambayar "uhmm to ai zaka janyo mana ace yayanmu ne kai kuma kaje ana baka abu a baki"

"Ba ma ki da kunya, kema fa na baki har sau biyu"

"To ai ni kanwarka ce" tayi maganar da wasiwasin iya matsayin da take so daga gareshi kenan ko kuwa.

"Tunda dai bakya so na dena. Da Ghazalatu kadai zamu rinka yi"

Kit ta kashe wayar zuciyarta na tafarfasa. Ai sai yaje su karata ita dama meye ya dame ta dasu. 

Kallon wayar hannunsa yayi yana tambayar kansa meye tsakaninsa sa Alheran. Ta wuce kanwa shi kansa ya sani amincewa ta rage. Lokaci yayi da zai dena yaudarar kansa don bazai iya ba. Bashi da karfin zuciyar jurewa. Kallo daya yayi mata ranar da ya fara ganinta a gidan Mama aka kwance duk wani notin jikinsa. Sake kiranta yayi wayar na hannunta dama tana nadamar kashewar da tayi kada yaki sake kira.

"Ke da na hana tashi idan muna magana shine kike katse min waya."

Baki a kumbure tana fushi tace "kayi hakuri"

"Bakin naki zan like tunda baya son yi min magana bashi da amfani"

"Ashe rabon wani ma zai nemi nasa ya rasa ne" tace tana dariya da tayi tunanin abinda ta taba son yiwa Gwaggonta Salame wata rana da taji ta zagi Umminta. Wurin Hanne taje lokacin tana auren Malamijo da niyar karbar super glue ta saka mata a kunu tayi rashin sa'a ya kare.

Jin kansa yake cikin nishadi yace "Ki gwada ki gani idan Ghazalatu bata zane min ke ba"

" 'Yar soja ce fa Hamma ko ka manta ne"

"Na dai ce bazaki yi sojan nan ba kuma kin yarda"

Bata sanin tana shagwaba sai maganarta ta fito kamar yanzu da tace "to gaskiya ka dena cewa bakina bashi da amfani"

Fuskarta kawai yake haskowa tana magana. A kasalance yace "fada min amfaninsa guda daya sai na kyale shi"

"Shan sweet in rage maka" tace da sauri ta dora hannu akan labbanta ta rufe bakin tana jin matsananciyar kunyar kalamanta. A karo na biyu ta sake katse kiran tare da kashe wayar. Kan katifar ta hau tana shure-shuren kafafu kamar zata yi kuka tana mai kunyar maganar da tayi da yanayin da tayita cikin wata irin siga mai tsayawa a rai.

Wani irin dumi yake ji yana ratsa shi tun daga tsakiyar kansa har kafa. Ya runtse idanunsa yana hangota cikin zuciyarsa. Abin takaici bashi da hotonta ko daya a wayarsa. Bazai iya sati biyu bai ganta ba shiyasa ya fara neman abinda zai fake dashi ya koma Sumaila cikin kwanaki kadan.

**********

Mal Aminu yayi bakinciki mara misaltuwa da jin yadda Maikudi ya yi da dukiyar marayu bayan Captain Onomza ya fadawa Major.

Gidan Zayyan na Kano yana nan tsahon shekaru ya zuba 'yan haya a cikinsa. Kudin da ya rinka aikowa da kudin hayar dasu ya tamfatsa katon gida mai bene a nan Sakkwaton a cikin wata sabuwar unguwa da yanzu ta fara cika. Bai kuma yi jayayya ba saboda dukan da yaci ya fada musu cewa yan uwan Zayyan na Nijar sun dauka iyalinsa duka sun rasu kamar yadda ya fada musu. Mal Aminu jikin girma bazai iya doguwar tafiya ba amma ya baiwa Major cikakken sunan gidan da zai nema da garin da suke.

Harka ta zamani da kwarewa Major ya bayar da cigiyarsu ta hanyar amfani da sojoji ta bangaren Captain Onomza. Zasu koma Katsina su bayar da sati daya ko biyu idan babu wata nasara da kansa zai je Nijar din nemansu. Ko a haka baya jin ya biya Zayyan fansar ransa.

**********

Kwana biyar da komawarsu Awwab Katsina. Kullum zai kira Ummi ke dauka Radhiya ta kirkiri wani abin da zai hanata karba. To ta karba tace me. Ta barshi da muguwar kewa ya gaza yin abin kirkin da yayi niyya wato zagayen gidajen 'yan uwa. A rana duk inda yayi biyu ko uku sai yace ya gaji. Sai dai fa duk dare suna tare da Ghazalatu wanda hira da ita ke debe masa kewar Alheran kadan. Yana takaicin yadda baya iya sake mata kamar da kuma hirar ma yana yi ne don kada ya wulakanta ta. Abin yazo ya fara damunsa ga tunanin Radhiya da rashin jin muryarta. Mafita ya nemawa kansa zuciyarsa kuma tayi na'am da shawarar.

Major yayi musu bayanin yadda ake ciki Ummi har kuka sai da tayi. Saboda abin duniya Maikudi ya kasheta ita da 'ya'yanta da bakinsa ya rabasu da danginsu. 

Su Malamijo kuwa sauki ya samu daga shi har amarensa. Yau gidan an tashi da kukan Asabe tayi rantsuwar ko ana ha maza ha mata sai Malamijo ya saketa don bazata yarda ya kasheta da ciwo ba. Fafur taki karbar girki ita takarda take jira shi kuma yace bai gama cin sadakinsa da kudin da ya kashe na aurenta ba. Rigima taki ci taki cinyewa duk jama'ar gida yanzu sun san lalurar da ta kwantar musu da uba.

Nene tana gogawa Radhiya maganin makeron da ta karbo wanda a cikin sati kan har ya fara hadewa yayi baki ta hanata fita kallon rigimar da take son taje ta yi. Kunkuninta ta gama da zumbure zumbure ta hakura.

"Ni kuwa tun zuwanku Radhiya kinje gidan Gwaggonki Salame?"

"Gaskiya kada kice inje Nene bazan iya zuwa ba"

"Akan wane dalili"

"Ita da ko Malamijo bata zo ta duba ba sai nice zani?"

"Wannan kuma tsakaninsu ne. Ina ruwanki ko ke kika haifa masa ita?"

Ranta dai bai son zuwa ta soma jan hanci Nene ta dungure mata kai "me tayi miki kike gudunta rigimanatu"

Duk wani abu da zata iya tunawa da Salame ta taba yi musu ta rinka daukowa kawai saboda neman dalili. Karshe tace "kuma harda aurewa Ummi baban Danmama. Ai da na sani Ummina zai aura don ma dai bana so kawai kuma ana ta cewa an kusa biki fa sai Ummi ta makance ita kuma Gwaggon ya aureta."
Chapter 51 · 0% Book details