Sashe 85
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nasan akwai dan sauran kananun abubuwa da suka rage kamar cike-ciken takardu da sake daukar biodata dinka. Da kuma daukar statement din Rtd Major Mustapha da Rtd Lt Hadir. Amma duk da haka ina da tabbacin cewa a karshen komai da zamu iya gamawa a cikin sati guda kaine zaka fito da nasara kamar yadda muke tsammani."
Kansa ya sunkuyar kawai, emotions kala kala suna kai kawo a zuciyarsa. Mutumin ya sake kallonsa yace "kana da ra'ayin cigaba da bautawa kasarmu ko kafi son yin retire? Wannan tambaya ce da ya kamata nayi maka idan an kare komai..." ya dakata yana dariya "but I realy can't wait naji amsarka"
Zayyan ya kalli mutanen nan daya bayan daya. Dukkaninsu a shekaru sun girme masa amma kayan jikinsu sune suka fi komai fito da cikarsu a matsayin zaratan sojoji irin wadanda kasa take tinkaho dasu.
"With all due respect Sir, I remain a soldier"
Gyada kai suke yi in approval. Shugaban ya kallesu sannan ya dafa kafadar Zayyan yace "Although unofficial amma bazan iya tafiya gida ba batare da na gabatar muku da precious mutum kamar wannan ba. GENERALS, I GIVE YOU A HERO LIKE NO OTHER...MAJOR GENERAL ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"
Gaisawa suka sake yi dashi sannan shugaban ya sake cewa Zayyan "strictly unofficial" wato yana nufin yayi shiru har sai sun gama. Doki ne kawai ya debe shi da yadda Zayyan din ya burge shi.
Bude musu kofa akayi daga waje aka kaishi wani babban hall sanyin AC na ratsa ko ina. Chibuzor yana ta gyangyadi, Awwab na kallon agogo. Shi kuwa Excellency kamar ba dare ba amsa waya yake ta yi ta 'yan uwansa 'yan siyasa da suke akan kayar zabe mai zuwa.
Basu sha wahalar shawo kan Zayyan akan ya hakura gobe zasu kaishi gida ba saboda shima ya san yanzu dare yayi da yawa kada ya firgita iyalin nasa.
Kalle kallen garin yake kamar ba cikin duniyar da ya sani ba har suka isa gidan gwamnatin Plateau din. Maman Arifah tasan maigidan nata zai zo da baki amma bata san ko su waye ba. Dawowa cikin dare da baki kuwa ba sabon abu bane ga 'yan siyasa irinsa bare ma saboda harka da kamfen. Dakunan da za'a basu a gyare ga abinci sai da Zayyan fa yaci alwashin wallahi shi da abinci sai na matarsa. Awwab out of solidarity sai yaki ci shi ma. Chibuzor ne kawai yaci bacci ya kwashe shi. Awwab da Zayyan kuwa sabuwar hira suka bude idanunsu sun soye. Hirar dai game da iyalinsa ne shiyasa Awwab ya rinka kaucewa wasu abubuwan saboda yana gudun tayar masa da hankali daga dawowarsa. Ai bazai so jin kalubalen da suka fuskanta su duka gidajen uku ba kafin komai ya daidaita yanzu. Zayyan tuni ya fahimce shi. Dama can yana da saurin karantar mutane shiyasa ya hakura aka mayar da hirar ta Alheran. Ai kuwa baiyi danasani ba don ya sha dariya sosai.
Bayan sallar asuba Excellency ya kawo musu kayan sakawa da kansa. Duka kayansa ne dai sun yiwa duka su ukun har Chibuzor yawa.
"Ko nasa a dinko maka kaya kafin muzo tafiya anjima?"
"Na fuskanci kamar da gayya kake son ja min lokaci. Wane irin dinki kuma ana zaune kalau."
"Kasan Allah bazaka je wurin Maman Alheran a haka ba. Infact mai aski za'a dauko yazo ya aske maka wannan kasumbar a gyara fuska sannan kayi wanka. Ko so kake su rinka mafarkinka idan kaje a haka?"
"Baka tausayi na ne ko? To askin ma bazanyi ba" Zayyan ya koma ya zauna ya bata rai.
Excellency yace idan ta kama ya danne shi zai danne shi ne ayi askin kuma a kulle shi a bandaki yayi wanka.
Awwab yana kallonsu yana dariyar yadda suke wannan rigima. Rtd Col Nasiruddeen tamkar babban wa yake ga Zayyan. Ya dauke shi kamar kaninsa da suka fito ciki daya. Sarai ya fahimci yana kewar iyalinsa amma ko yaki ko yaso bazai barshi yaje garesu a mummunar kama ba.
"Kai Awwab kalli babanka da kyau banda aski me ya kamata ayi masa" yace a commanding voice.
Shima bai tsira ba sai da ya sami guzurin harara daga Daadaa. Ya daga kai yace "da dai zamu samu a gyara harda farce"
"Kai Awwab haka zaka yi min?" Yace da muryar ban tausayi.
Excellency bai saurare shi ba ya kira PA dinsa ya fada masa abubuwan da yake bukata saboda yana so yau Zayyan yayi sallar azahar a cikin iyalinsa. Harkar kudi sai da kudi. Karfe goma na safiyar laraba an siyowa Zayyan kaya readymade shadda da yaduka kala goma da takalma. Shima wai kawai don ya zabi wanda zai saka ne. An dauko mutum biyu daga wani sanannen wurin aski na zama masu shegen tsada kamar idan anyi askin baza'a kuma yi ba. Suna zuwa suka fara aiki. Mutum daya yana askin dayan kuwa dakalalliyar kafa da faratan Zayyan ya tasarma da gyara. Bakinsa bude yana ta al'ajabi wai ace zamani ya kai harda masu gyaran kaushi.
Ana wannan aikin Awwab ya samu ya kebe kansa ya kira Mama. Cikin rawar jiki ta dauka a can kuryar dakinta duk da cewa ma babu kowa a bangaren nata sai Ibrahim da Emzee suna nasu dakin.
"Awwab yaya" tace cikin tashin hankali. Jiya da kyar ta iya bacci tana ta juye juye ga fargabar kada ta kira taji mummunan labari ko wani yaji.
"Mama na turo miki sako ta whatsapp. Ki duba zan sake kiranki" yace yana karamar dariya.
Ita ta fara kashe wayar don sauri ta duba whatsapp dinta. Alamun Awwab ya turo mata hoto ta gani. Hannu na rawa ta bude. Bata san lokacin da ta saki wayarta ta fadi a kasa ba ganin hotonsa da mutumin da babu tantama aminin mijinta ne.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zayyan...." dukawa tayi ta dauki wayar ta sake kunnawa daidai da kiran Awwab ya shigo.
Kuka kawai ta fashe dashi "Awwab kuna ina?"
"Zamu taho daga gidan baban Arifah tare muke. A nan gida zamuyi azahar in sha Allahu. Sai dai tun jiya yaki cin komai wai sai yazo gida zaici na Ummi"
Dariya tayi ga hawaye a idanunta "Zayyan kenan, yaushe Mairama zata iya girki idan ta ganshi. Amma kada ka damu abincinta zai ci in sha Allah. Sai kun iso"
Mayafi ta yafa ta fita zuwa gidan Ummi. Baby Zayyan yana can a bayanta tun da tayi masa wanka. Tayi mamakin fitowar Maman saboda sun hanata yin komai ita da Mami.
"Jikin ne Zainab?" Ta tambaya da kulawa.
Jiya tsabar damuwa kasa komai tayi sai tsananin fargaba. Da aka dameta da tambaya tace zazzabi ne da ciwon kai suke damunta. Karshe dai Mami tace a dage taron sunan da ya kamata suyi a jibi sai wani satin ta kara samun sauki. A ganinsu cikar da gidan yake yi ne ya hanata hutawa. 'Yan uwa masu tahowa a yau kenan duka ta dakatar dasu da kanta. Bata san me zai faru ba amma bata da wani kuzarin yi taron suna wanda su Ummi ne suka takura sai anyi.
"Na ware sosai. Gajiya nayi na fito, kina da garin masara kiyi min tuwo? Miyar kukar rannan kinsan ta min dadi sosai"
"Kinyi sa'a akwai saura kuwa."
Fauziyya na wurin tace bari ta yi Mama tayi saurin cewa akwai fruits a bangarenta ko zasuyi fruitsalad kada su lalace. Radhiya taje ta kira suyi tare duk tayi laushi saboda rashin wayar Awwab da shareta da ya rinka yi kwana biyu. Ta ma kudurta a ranta ta dena basarwa idan ma dalilin haka ya janyo ya dena kulata.
Ummi bata kawo komai ba taje ta jika busasshen kifinta da ruwan zafi ta bara ta wanke shi tas. Bata rabo da jajjage ba bata lokaci ta hada wake, naman sa da kifin nan ta soma dafawa tare da daddawa da gishiri bayan ta kara albasa da kayan kamshinta da Innawuro take hada mata garin tafarnuwa, citta, kaninfari da masoro. Maggi sai miya ta dauko dahuwa. Girkin baifi na mutum uku zata yi ba yadda zai ishi Mama har dumame. Tana yi suna taba hira Mama sai ta kalleta ta kawar da kai ta share kwalla. Mairama komai nata da nutsuwa take yinsa gwanin sha'awa.
Sabon flask da ba'a taba budewa ba Mama tasa Radhiya da suke aikin fruitsalad ta kawo mata ta zuba tuwon da ta kukkulle a leda.
"Yau kice da Baba Hadir za'a ci tuwon nan"
"Ko daya ki boye min a dakinki sai anjima zan zo naci" Mama tace tana mikewa.
"A daki kuma? A kawo miki mana"
"Ke dai ajiye min ko a nan ne kada a taba. Da zaki taimaka min da wannan shayin naki mai kayan kamshi da kin gama min komai"
Ummi ta girgiza kai "anya baki kunso wani ba? Wannan abu kamar me yaron ciki"
"Rufan asiri ina fama da kaina. Zainabu tayi sanyi in fada miki. Idan ba gani nayi ya fara takawa da kafarsa ba ko kallon babansu na dena yi"
Me Ummi zata yi kuwa banda dariyar mugunta. Allah Sarki Mama an ga haza. Dakinta suka koma da hira da dabara Mama tasa ta kuma gyara shi duk da ma Radhiya ta gyara da safe ta wanke toilet. Amma Mama tace wai ana sanyin nan da yakunno kai gadan gadan ina ita ina bedsheet single. Ta fito da mai hade da duvet ta shimfida mana. A take Ummi ta fara zargin wani abu amma duk iya tunaninta ta kasa. Wani mai masifar kyau da laushi tsarabar da Radhiya tayi musu su uku zuwanta na karshe kafin wannan ta shimfida.
Tana gamawa Daadaa wato baby Zayyan ya farka. Yana cinyar Mama dama da zata gyara gadon. Shigewa tayi tana wanka zuciyarta na tunanin manufar Mama. Gabanta ne ya fadi da tayi tunanin ko shammatarta akayi ne aka daura mata aure? Idan ba haka ba meye na sa ta a gaba ta gyara daki. Hmmm zasu sha mamaki kuwa idan aka nemi turo wani cikin rayuwar da bazata taba sake irinta ba tunda ta rasa Sojanta.
**********