← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 157

Sashe 151

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsakaninta da Allah tace "Ummi ai ta yafe nasu ya wuce. Emzee nake maka magana yanzu. He is so hurt yana ganin laifin Rahima a tunaninsa yaudararsa tayi taki fada masa wace mamanta"

Jinjina kai ya rinka yi "indai zaki yiwa Emzee wannan kukan ni kuma me zaki yi min idan na kamu da son wata aka rabamu?"

"Kace me?" Ta jefa masa tambayar idanunta sun wani kankance tana huci.

Dariya ya soma yi mata "cewa nayi fa...ke dai banyi magana ba"

"Ya dai fiye maka idan ba haka ba kuma yau babu bacci a dakin nan" ta juya masa keya.

Kwanto ta yayi jikinsa "wasa nake yi miki Schatzi don ki saki ranki. Ina jindadi idan naga 'yan uwa suna son juna domin Allah. Keep it up my baby amma fa kada kowa ya kamo matsayina"

Sunkuyar da kai tayi tana jin kunya "kowa matsayinsa daban...KAIMA.KA.SANI"

"Wanne ne matsayin Awwab?"

"The only man in my life"

Rungume ta yayi suna shakar kamshin juna daga baya ya tasheta daga kan gadon "muyi wanka idan nayi sallar magrib zan koma wurinsa muyi magana man-to-man. Amma ki sani tun wuri sai na rankwashe shi. Haka kawai ya janyo min dan janbakin da naci burin gogewa idan mun dawo ya bi hawaye ya gudu"

Da sauri ta tashi ba shiri ta koma ta zauna. Abu goma da ashirin ke damunta, dama jikin lallaba shi take ga kuma hawa rakumi da tayi dazu ta rinka jin kanta kamar akan kaya. Runtse idanu kawai take yi Awwab dama ya san matsalar yana mata sannu suka yi wanka ta gasa jiki sosai. Ana kiran magrib yace mata za'a kawo abinci takwas da rabi idan ta ci ta yi isha ta kwanta kafin ya dawo. Da kyar ta tsakuri abincin tana idar da sallah bacci mai nauyi ya kwasheta saboda irin gajiya da ciwon jikin da yayi mata rubdugu lokaci guda.

Tare da su Daada Awwab yayi sallah ya nemi Ibrahim ya kira masa Emzee. Dawowa yayi yace yana kwance kamar bashi da lafiya kuma yaki bari ya fada a cikin gidan.

"Kyale shi muje dakin"

Ibrahim sauri yake yaje wurin Zayyana bai shiga dakin ba. Awwab na shiga ya same shi ya hada kai da gwiwa zaune a kasa. Kusa dashi yaje ya zauna yayi irin zaman da yayi suna zaune kusan minti biyar sannan Emzee yace "yaya zanyi Hamma?"

Ya tabbatar dole zai ji daga bakin Radhiya kuma abinda ya kawo shi kenan.

"Rahima tana sonka?"

"A da ba! Ni yanzu ban ma san me ta daukeni ba" ya amsa cikin kunar rai.

"Bana jin wannan yarinyar mai nutsuwa da hankali ga karancin shekaru za ta iya amince maka saboda wani mugun nufi. Emzee open your heart and listen to its voice. Me kake so?"

Baiyi wani tunani ba yace "Rahima"

"Shekarun baya dangina sun rabani da Radhiya a tunaninsu sunyi domin karfafa zumunci sai gashi ya lalace fiye da zato da tsammanin kowa. Idan kana tunanin za ka gujewa Rahima saboda zumunci ne you are making a grave mistake. Emzee aurenka da ita shine abinda zai fi komai saurin gyara abinda yake tsakanin Ummi da yayarta."

Da sauri ya dago kai "Allah Hamma?"

"Talking from experience" yace da murmushi "da ace tun wancan lokacin na auri Ghazalatu da Radhiya zumuncin iyayenmu da yafi karfi iyaka mata suyi kishi a junansu. Amma da hakan bata samu ba sai da akayi shekara uku su ukun suna jin haushin juna ana rigima mara tushe. Babu wanda nake fadawa amma I hate myself da na zama dalilin faruwar hakan so if you can avoid it please do so"

A raunane Emzee yace "ina jin ni fa yanzu ta dena sona ta sami wani"

Awwab ya ce "So da wahala yake komawa ki. Kai dai kada kayi wasa da damarka at the same time ka tuna cewa kaima yaro ne ko karatu baka karasa ba. Zanfi so ka gama karatun ka fito da karfinka ka yaki zuciyar Rahima har sai ta amince maka."

"To yanzu dai in kyaleta?"

"Da zancen soyayya kam ka rabu da ita ka gama karatu itama ta gama secondary. Amma try your best ka tabbatar ka mamaye rayuwarta..."

Chuckling Emzee yayi yau fa yana daukar darasi sosai "how?"

"Kada ka bari wasu mazan su sami dama. Keep her close, babu zancen soyayya amma ka bata kulawar da ko wani yazo a bayan idonka zata rufe ido ta kore shi batare da ka sani ba ma"

Haba Emzee ya rike "Allah Sarki Addata, Hamma ka rinka yi mata a hankali kada son ka yayi mata yawa"

Keyarsa Awwab ya talle yana dariya "kai kace ita, iya tace kai ni mai bada shawarar kuma baku damu dani ba"

"Daga fadan gaskiya" ya turo baki.

"Ladan kukan da ka saka min mata ne...bari na koma na barta ita kadai karshenta ta kasa....."

Kofa Emzee ya bude masa da sauri "Allah Ya bamu alkhairi ba sai kace komai ba" ya kara da toshe kunnensa kada ya jiyowa kansa.

Awwab ya fita yana dariya sosai ya ce masa "ni dai ka daure ko P.O.P ne kayi sai mu aurar da kai....ga Rahima 'yar karama da ita har ta bani tausayi"

Kamar zaiyi kuka ya ce "wayyo Hamma ya na neman fassara ni"

"Me kaji nace? Daga cewa 'yar karama to ba karamar bace?" Ya kuma yin dariya.

"Wallahi zama da Adda ya fara nunawa a jikinka ni dai sai da safe" Emzee ya bata rai ya rakoshi waje.

Tare da su Yousuf suka tafi. Yana zuwa shima kwanciya yayi yana rungume da Radhiyansa. Washegari akayi gagarumar dinner da daddare inda ma'auratan suka yi shigar buzaye su da iyayensu. Da safe kuwa kowa ya kama gabansa. Yousuf da Arifah Hawaii suka wuce honeymoon daga can kuma zasu tafi France inda gidansa yake kusa da na iyayensa. 

Su Awwab ma a ranar da suka koma washegari bakwai na safe suka tashi zuwa Athens babban birnin Greece zasuyi kwana goma kafin ya koma aiki.

Duk wannan abu da akeyi babu wata alama ko kadan da Rahima ke nunawa ta damuwa sai dare yayi ta kwana tana kuka. Sabanin Halifa da yake namiji ita abin ya tsaya mata a rai fiye da kima. Da ciwo matuka ace mahaifiyarka ta cutar da wani, wanin ma kanwarta ta hanyar asiri har tayi shekaru goma babu ido. Ita nata daya ne yanzu baya bambance mata abubuwa amma yaya take ji bare wanda zai ga tsananin duhu na tsayin lokaci. Abu na biyu bai wuce mahaukacin so da tausayin Emzee da take yi ba. Ko kadan bata ganin laifinsa don ya kyamaceta. Uwa tafi karfin wasa. Ita ma bata guji Salame ba duk munin halinta ta yaya shi ba zai tsayawa tasa mahaifiyar ba..mace kamar Ummi mai kyauta da kyautatawa. Bayan dogon tunani da koke koke a boye ta yankewa kanta shawarar hakura dashi har abada. Emzee ba sa'an aurenta bane da kunya ta iya hada ido dashi bayan abinda Ummanta tayi musu. Sai yanzu ma take dada godiya ga Allah da ita ta samu a ido da wayar ba Radhiya ba. Da zasu barta ta koma Sumaila da tafi jindadi ma. A zahirin mu'amalarta da mutanen gidan duk karancin shekarunta ta iya daurewa ta nunawa Ummi bata da matsala. Har daki Ummin ta kirata akan maganar Emzee ta ce mata ko yana sonta bai taba fada ba. Shi kuma yana makaranta bare ya karyata.

Satinsu guda da gama biki har an kai Rahima sabuwar makarantarsu anyi sa'a sun barta a SS3 amma Daada yasa an dauko mata lesson teacher wuni suke suna karatu saboda ta ci WAEC tunda bata yi rejistar NECO ba kuma an riga an makara. Ummi ma ta soma zuwa Baze tana kuma samun kulawa sosai daga maigida ran gida Zayyan Tureta. Cikinta mai laulayi ne shiyasa daga makaranta sai daki saboda rashin son kamshin gidan.

A yau ana sauran kwanaki hudu su Radhiya su dawo Emzee yayi magana da Awwab wanda yace kada ya manta shawarar da ya bashi game da Rahima. Bayan sun gama hirarsu ne ya tura mata text.

Zaune take tana kokarin solving din wani aiki da lesson teacher din ya bata a physics text din ya shigo. Duk a zatonta irin na layin wayan nan ne shiyasa zuciyarta tayi wani irin bugu da ta ga sunan Emzee. Jikinta wata irin rawa ya kama yi ta bude da sauri.

(Kanwata kwana biyu boko ya boyeki. Ina fata babu wata matsala a sch din taku. All the best Rahima, Allah Ya bada sa'a. Yayanki)

Ta karanta wannan gajeren text yafi sau shurin masaki. Dama malamin nata ya tafi aikin ta zauna yi sai kuma ta kasa fahimtar komai dole ta tashi ta shiga ciki. Wayarta a hannu lokaci lokaci sai ta duba ta kuma karantawa duk da tana kwabar zuciyarta da take jinya har yanzu.

Da safe ma tana shirin tafiya makaranta wani text din ya kuma shigowa shima dai addu'a ce yake yi mata da fatan alkhairi. Baiwar Allah sai ta koma ruwa tsundum dan karfin halin nata ya guje mata. Haka dai akayi karatun ta dawo gida. Daga bakin kofa take jin muryar Salame tana cewa maiaikin nan gidan kanwarta ne ita bazata ci dan wake ba a dafa mata sabon abinci.

"Banda ta raina ni ai tasan yau zan taho amma shine da zata tafi makarantar bata bar muku sallahun dafa min komai ba sai danwake? Ko ki dauke shi ko na yanko masa tsinuwa dashi da hannun da ya tsumbula shi a ruwan zafi"

A kidime yarinyar tace "Ta fada mana zaki zo amma kinfi son danwake"

"Da kenan! Amma Yasin bazan zo Abuja inci danwake ba kamar wadda iyaye suka cewa jeki kya gani"

"Harda farfesun da salad din ma na kwashe?" Mai aikin ta tambaya a tsorace.

Salame ba kunya ta karbe tray din "kece bakiyi bayani ba, cha nake mai da yaji zaku bani."

Da gudu-gudu Rahima ta shigo ga takaici ga dariya ta fada jikinta.

"Umma?"

Salame ta washere baki kamar gonar auduga ta rungumota "Rahimata...."
Chapter 151 · 0% Book details