← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 157

Sashe 81

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka kece da dariya. Wannan ko kadan baiyi kama da wanda Gwamnan nasu zai saurara nan kusa ba saboda ayyuka da suka sha kansa 'yan kwanakin nan. Sannan kuma ai ba haka nan ake ganinsa ba, akwai matakai da ake bi.

Bai hakura ba yace "yana gida yanzu ko office?"

"Yana office"

"Nagode"

Gefe ya koma abinsa ya tsaya a jikin katangar gidan. Da sauri cikin masu gadin mai kayan sojoji yazo yace ya bar wurin. Gaba ya kara amma duk inda yayi sai ace ya matsa wai ba wurin tsayuwa bane. Chibuzor baiyi zuciya ba don biyan bukata yafi dogon buri. Ainihin titin da ake yin kwanar dama a kansa a shigo titin gidan gwamnatin yaje ya sami inuwar wani gida da filawoyinsa suka hauro ta saman katanga ya tsaya. A nan ya wuni ko ruwa bai matsa ya saya ba saboda tsoron kada ya rasa abinda yake nema.

Gajiya, yunwa da shigowar sanyi wanda baya yiwa  mutane da sauki a garin na Jos sune suka sarke shi amma da yake mutum ne mai juriya da amana bai gajiya ba. Tunawa kawai yake yi da shekarun Zayyan a prison dinnan yana ji a ransa da yana da hali ko sakan daya bazai bari ya sake yi ba.

Tara da rabi na dare sai ga jiniyar motocin gwamna sun taho a sukwane. Ko kallon titin da zai tsallaka baiyi ba ya bi zugar motocin nan a guje yana harin ta tsakiyar wadda yafi tsammanin ita ce gwamnan ke ciki.

"Zayyan Tureta is alive"

"Zayyan Tureta is alive"

"Lt. Zayyan Tureta"

"Liberia prison"

Wadannan kalmomin ya rinka maimaitawa yana bin motocin yaki sauraron ihun da sojoji suke yi masa.

His Excellency Nasiruddeen yana bayam mota tsabar gajiya har soma gyangyadi yaji kalmar TURETA da LIBERIA. Firgigit ya bude idanu ya soma cewa "stop da car" cikin gaggawa. Dreban sai da ya tsorata amma shi da PA sun kula kamar ba a hayyacinsa yake ba duk ya rude shiyasa ya danna trafikato zuwa barin dama sauran motocin bayan suka tsattsaya suma. Yau babu batun jiran a bude masa kofa da kansa ya bude don sauri ya kusa faduwa saboda babbar rigarsa da ta harde shi. Wurin da sojoji masu tsaronsa suka danne Chibuzor a kasa ya isa yana yi musu tsawar su daga shi. Kowa darewa yayi gefe da suka ga ya durkusa ya tayar da Chibuzor zaune. Cikin harshen turanci yace masa

"Me kace?"

Jikinsa babu kwari sosai ya dago kai yana kallonsa "kaine Col. Nasiruddeen Aliyu?"

"Nine, nine" ya rinka nanatawa yana gyada kai.

Yana jin wata kakkarfar ajiyar zuciya da yaron ya saki don bazai fi sa'an Awwab ba.

"Sir, Lieutenant ZAYYAN MUHAMMAD TURETA..."

"Ina jinka, Tureta nawa kake nufi? Wa ya aikoka? Daga ina kake?" Ya rinka jero tambayoyin yana jijjiga shi.

"Liberia prison, the Lieutenant is waiting"

Hularsa ya tuge bai sani ba saboda yadda ya tashi tsaye da sauri "Lieutenant Zayyan fa kace"

"1993 Liberia Peace Keeping Troop"

Zuciyarsa bugawa ta rinka yi da sauri da sauri yana tsoron kada ya gaskata maganar mutumin ya tashi yaji ashe mafarki yake yi.

"Daga ina kake?"

"Liberia Prison"

"Innalillahibwa inna ilaihi raji'un" yace gumi na karyo masa "Zayyan yana da rai dama?"

"Yace akwai Hadir ko shima yana da rai?"

Hannuwansa Excellency ya riko ya tayar dashi tsaye "nasan Hadir, nasan Mustapha, nasan matarsa da 'ya'yansa kowa yana nan"

"Ahghhhh" Chibuzor yace da kyar saboda murdewar da cikinsa yayi ga dukan da ya soma sha.

Excellency da kansa ya tallabo shi a jikinsa ya ja shi zuwa motarsa jama'arsa suna kallonsa da mamaki. Wani ne yayi karfin halin cewa

"Your Excellency kawo shi mu saka shi a motarmu"

"Noooo muje kawai" ya amsa yana kankame Chibuzor a jikinsa.  Da suka isa daidai kofar shiga cikin gidan ma da kyar ya bari aka shigar masa dashi ciki. Kansa ya kulle so yake yaji gamsasshen bayani. Matarsa da Arifah a ranar suka tafi Abuja daga shi sai ma'aikata. Abinci yasa aka kawo masa yana zaune yana jiran ya gama ci ya kara yi masa bayani. Shima a nasa bangaren baya jin zai iya yin komai sai ya sauke wannan nauyin.

"Sunana Chibuzor Kalu"

"Ci abinci tukunna sai muyi magana" ya fada batare da maganar ta kai zuci ba.

"Bazan iya ba..."

Cikakken labari ya samu daga wurin wannan yaro tun daga rabuwar Zayyan dasu Hadir zuwa yanzu. Sai ga His Excellency the Executive governor of Plateau state yana zubar da hawaye. Shekaru daidai-daidai har ashirin da biyu rabon Zayyan da iyalinsa. Kurkukun ce ta fado masa yaji wani kunci yana sauka a ransa. Garin yaya bai taba tunanin komawa su duba wurare ko za'a same shi ba? To amma a gaban idonsa aka yi masa harbi guda biyu ya fadi kamar matacce.

Wayarsa ya zaro wadda mutane kakilan suke da layin ga gumi duk ya jika tafin hannunsa saboda girgiza da yayi ya soma neman sunan Major Mustapha. Bai kai ga dannawa ba ya kwabi kansa. Bincike ya kamata ya fara yi ya tabbatar ba wai ya tayar musu da hankali bisa abinda bashi da tabbacinsa ba.

**********

Kwanansu Radhiya biyu da zuwa kuma gobe Tante da Yousuf suke sa ran tafiya Nijar. Jiya da Ummi tace suje gidan Daddy Haroun kafin lokacin fitar tasu dreban Major ya kawo rahoton wahalar mai da aka fara tun daren jiya shima bai sami labari da wuri ba. Yawancin masu ababen hawa kowa yana kan layin mai ko kuma ka daure ka saya wurin 'yan bumburutu idan kana da hali. Awwab na ji yace idan sun fita sai suyi full tank a wurin nasu. Raji ya nemi fassarar bayani a wurin Zahra da ta kawo masa dankadafinsa Femi ta fada masa da turanci. Sai cewa yayi wai yana son yayi experiencing bin layin mai irin wannan. Shi da kanwarsa a Germany aka haifesu kuma bai taba katarin samun wannan matsalar ba a duk zuwansa Nigeria.

"Raji ba fa wurin shakatawa bane, nima ban taba bi ba amma nasan labarinsa. Wahala ce kawai harda fada wani lokacin"

"To ba sai mu kafa tarihi ba" cewar Yousuf da yake jin hausa sosai kasancewar babansa ba yarensu daya da Nasara ba. Hausar Nijar suke yi mai kamanceceniya da Sakkwatanci.

"Gaskiya ba dani ba" Awwab ya fada zai gudu daga falon saboda ya ga zasu jajibo masa wahala baiji ba bai gani ba.

Magana har wurin Daddy saboda Raji ya matsa wai yau daya dai su dana. Ba don yaso ba aka ce ya tuna bakinsu ne ya karramasu da abinda suke so. Sai da suka yi la'asar suka bar gidan. Raji yasa Zahra ta hada masa 'yar jaka da irin pillon nan na matafiya a jirgi na kafada, abin rufa, touch light da 'yan kayan ciye ciye. Awwab da baya son zuwa sai gashi yana dariyar mugunta. Wai shi nan Raji hango abin yake kamar wani picnic ko camping. Yousuf ma da nasa shirin suka shige mota Awwab ya bi bayan dreban da daya motar.

Sa'arsu daya yau tun safe garin dama da hazo da sanyi sanyi ba kamar jiya da suka iso ba. Amma fa abu tun ana dariya sai gasu sunyi kicin kicin da fuska zukata sun matso kusa. Layin mai ma ana alfarma. Ga rigimar cin layi da dai sauran abubuwa marasa dadi da kan biyo bayan zama a layin mai. Layi har dare ko tafiya suka ce zasu yi yadda wurin ya cushe da wahala su sami hanya ta dadin rai. Haka suka zauna dare ya gabato sauraye suka ce salamu alaikum sanyin da zai koresu bai kankama ba gara suma suyi full tank. Dukkansu jikinsu ya fada musu kuwa. Ba su suka koma gida ba sai hudun dare. Zahra da Ummi ne kadai ido biyu. Take taken Raji na makalewa Zahra yana ta korafin wahalar da yasha yasa Awwab bin Yousuf bangaren Ummi yana girgiza kai. Zahra na ta zillewa amma yaki barinta. Awwab na jin yana cewa da a gida suke wanka yake so ta taimaka masa yayi ya dauki kayan bukatarsa ya fita. Baya son ganin abinda zai dame shi yazo yana jin kunya shi da kanwarsa su zama surukan juna. Gara ya basu wuri ko yaya ne ta kula da mijinta. Radhiya ce ta fado masa a rai lokacin da yake kwanciya a kan bargon da ya jefa a kan kafet din dakin Emzee ya buga tsaki shi kadai yana ayyana wai ta cuce shi da yanzu shima...kwafa yayi kawai ya kwanta.

"Kasan babu dadi ko? Ka dawo nan gadon zai ishemu" Yousuf yace da ya jiyo tsakin.

"Its okay mantuwa nayi mai mahimmanci, kaji ina tsaki ko" a rayuwarsa babu abinda yake masa wahala kamar kwanciya kusa da mutane. Sai yayi ta ganin kamar zai takura musu kuma shima baya son tasu takurar.

Karamar dariya yaji Yousuf yayi yana cewa "Raji yayi mana wayo. Mun sha wahala tare wato shi mai mata ya gudu"

"Kai me kake jira" Awwab ya tambayeshi cikin duhun dakin yana fata kada yace abu guda suke so. Yinin yau kadai Yousuf din ya kwanta masa akwai ilimi amma a wani kamfani yake aiki ba likita bane. Ko me yasa jiya yaji Mama tace likita?

"Da dai na fara shiri amma na kula kamar bazai yiwu ba." Yanayin maganarsa zaka san abin baiyi masa dadi ba sai dai a rayuwarsa bai yarda da cusa kai inda ba'a nemansa ba. Yana son Radhiya kuma kanwa ce gareshi har kullum amma jiya shi kadai yasan me ya gani suna yi da sunan cin abinci. 

"Allah Ya musanya maka da mafi alkhairi"

"Amin, amma meyasa nake ji kamar kasan da wa nake?" Ya kuma yin dariya.

Wayancewa yayi shima yana dariyar 

"Ban sani ba fa...kawai fatan alkhairi nake maka" 

"Sai ka tayani nema tunda kasan irin wadda nake so"

Abin rufa Awwab yaja ya rufe kansa yana dariya lokacin da Yousuf yace kuma idan ya cigaba da jan rai zai ji ana biki a Nijar. Yasan so yake ya nuna masa ya gano wa yake so, shi kuma sai yaji kunya kada ya nuna abinda zai iya sosa ran Yousuf din. Da kyar suka yi sallar asuba jam'i su biyu don sai da aka idar Awwab ya iya farkawa saboda gajiyar da suka tara.

***********
Chapter 81 · 0% Book details