← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 157

Sashe 63

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakura tayi bata matsa masa ba saboda tana ganin akwai abinda bai dace ta matsa sai ta sani ba musamman idan danginsu ya shafa. Fatanta bai wuce kada ya kasance matsala aka samu game da neman Radhiya da yayi ba tunda Fauziyya tace Mummy din taje sunyi fada da Mami. Wannan damuwar ita ce ta karfafa mata gwiwar son zuwa Katsinan a washegari. Daren ranar suka yi waya da Zainab suna airport zasu tashi. Ummi tayi ta jero addu'o'i suna fatan Allah Yasa ayi komai cikin nasara Baba Hadir ya dawo musu da kafafunsa.

Washegari kuwa bayan daurin aure Ummi suka shirya tafiya Katsina ba zata sami kai amaren ba. Babu irin tunanin da bata yi ba a matsayin dalilin da zaisa 'yan uwan Mami su zo gidanta suyi fada da ita da ya wuce kin amincewa ace ko auren Ghazalatu ba'ayi ba Daddy ya newa Awwab wani auren shi kuma ya karba.

Emzee ne a gaba Radhiya da Ummi a baya. Ba wata hira suke yi sosai ba. Ummi da Awwab tunanin me zasu tarar a can ke damunsu. Radhiya kuma shirun da ta ga yayi tun jiya bai sake nemanta ba shine yasa itama ta kama nata bakin.

**********

Sallah Ummi ta idar ta kasa taba komai cikin kayan abincin da aka ajiye mata. Tunda idanunta suka bude sai yau suka hadu. A waya Mami ta nuna tsananin farinciki ta tayata murna amma yau da suka hadu abu na farko da ta fara gani a fuskarta shine damuwa. A haka ma Mami tana ta kokarin boyewa ne. Taji dadin dai ganin Mamin tayi kyau haka ma su Zahra. Sai dai kaifin tunaninta yasa tasha jinin jikinta da wuri. Yaran da iyayensu duka suna tattare da wani abu na rashin jindadi a zukatansu.

"Ummin Awwab har yanzu baki tashi kinci abincin ba? Ko na zuba miki da kaina ne?" Mami ta fada lokacin da take shigowa dakin rike da katunan daurin aurensu Zahra da aka aiko daga gidan Alh Baba.

"Gajiya ce take tambayata Mami"

"Ga kuma wata da zata tarar miki ke kadai tunda Zainab bata nan"

Ummi ta mike tsaye tana ninke sallayar "dadin abin Maman Ghazalatu da Anti Hussaina suna nan sai muyi tare"

A take yanayin fuskar Mamin ya sauya wanda shi Ummin ke nema don ta tabbatar da cewa lallai akwai wata a kasa. Mami sai ta chanja akalar zancen ta dauko hirar mutanen Nijar. 

A bangaren 'yan matan ma Radhiya ce kadai a daki. Zayyana tana falo tare da Emzee yana cin abinci tana zuba surutu da labarin shirin biki da take yi. Fauziyya kuma tana can wurin Awwab tana yi masa bayanin abinda taji kuma ta gani a jiya suka rutsa Zahra akan sai ta fadi waye take so tana ta kuka.

A hasale yace "shirunki bashi da wani amfani da zai mana"

"Kamar yadda fadar ma bata da amfani. Hamma na riga na hakura ba shikenan ba"

"Zahra please ki fada mana" Fauziyya tace idanunta suna taruwar kwalla.

"Let us help you Zahra" Awwab ya sassauta muryarsa yana kallon kanwar tasa.

"Raji ne" tace da muryar da kuka ya sauya ta.

"Raji Abdulwahab?" Awwab yace mamaki na bayyana a fuskarsa. Abokinsa ne duk da cewa Raji din ya dan girme masa. A zuwa masallaci sallar juma'a da suka mayar al'adar gidansu a zaman Germany suka hadu da iyalin Ayodeji Abdulwahab mahaifin Raji. Wani abin dadi shine limami a community din da suka hada nasu na musulmai a wurin 'yan kasashe daban daban. Tasu tazo daya da Raji babban dan Limamin wanda yake aiki a kamfanin Benz. Yana yawan zuwa gidansu ashe Zahra yake so babu wanda ya sani.

Kai ta gyade ta kuma fashe musu da kuka "nasan babu mai yarda na aure shi saboda bayerabe ne shiyasa na kasa fada da wuri. Daga baya Mami ta sani kuma lokacin tayi alkawarin fadawa Daddy su yiwa Alh Baba magana sai kawai muka ji zancen Fawaz. Wallahi Hamma Raji har kwanciya yayi a asibiti"

Kukanta yana taba masa zuciya fiye da zato da tsammani. Shi kam Allah bai dora masa kabilanci ba musamman ga dan uwansa musulmi a duk inda yake. Sai dai a yadda ya fuskanci akidar su Alh Baba son kansu da yasa suka dagewa auren zumunci kadai babbar matsala ce balle kuma ace wani yaren daban.

"Daddy yayi miki magana ne jiya bayan Mami ta fada?"

"Yayi min da daddare. Baiji dadi ba da bamu fada masa da wuri ba gashi lokaci ya kure. Hamma yaya zanyi? Shekaranjiya da Munirat ta kirani kuka take yi wai bashi da lafiya har yanzu"

Tana kuka ne Fauziyya ma na tayata aka bar Awwab da aikin rarrashi. Kamar ance Mami ta leka su ta gansu a wannan yanayi ta kuma ji karshen maganganun nasu. Kwalla ce ta cika mata idanu ta koma batare da ta bari sun ganta ba. Rayuwar 'ya'yanta duka ta shiga wani yanayi. Fauziyya ce kadai take tunanin kila sun hada kai ita da Bilal ta kula ya ma fi Fawaz zuwa dama. Abin dai duka kadaran kadahan babu wani karsashi ko doki a bangaren amaren da angwaye.

Wurin Ummi ta koma suna dan taba hirar Zainab taji sallamar babar Fawaz matar cousin dinta saboda ta bangaren namiji suka hadu. A harzuke ta shigo gidan ranta yayi masifar baci ita da Mummy Gambo. Zayyana da take falo da Emzee aka dakawa tsawar ina mahaifiyarta ta ruga daki ta kirawota.

Mami na ganinsu tasan ba lafiya ba ta dai daure tana cewa su zauna mana.

"Ba zama nazo yi ba Hassana" Haj Azumi tace cikin kaushin murya "ni zaki wulakanta har kike ikirarin 'yarki bata son Fawaz? To wallahi ki jika abarki ki sha indai ni na haife shi ko ana muzuru ana shaho a dangin nan naku Fawaz bazai auri Zahra ba. Ke wallahi bari kiji in fada miki ko aurena ne zai mutu sai dai ayita ta kare"

Mami ta daga kai ta kalli Gambo tana mamakin wai kanwarta da suka fito ciki daya ce take ingiza wannan rigima. Ummi bata fito daga daki ba amma tana jin komai. Haka ma su Awwab dake daki ya hana kannensa fitowa saboda a ganinsa hakan bai kamata ba. Radhiya kuwa tsurewa tayi ita kadai a daki tana jin ana wannan daga murya. Ita fadan ba shine ya dameta ba kamar cewa da matar take yi danta bazai auri Adda Zahra ba. Me yayi zafi haka za'a raba masoya?

"Haj Azumi ki zauna muyi magana don Allah. Gidan nan da baki ga yara"

"Baki? Ke suka dama bakin. Idan 'yan biki ne suka fara zuwa gara su ji su tattara su koma inda suka fito. Aure ne nace a bawa Zahra da ta tashi a kasar waje tafi karfin dana wanda take so. Shi kuwa zan baku mamaki muna nan tare daku mata biyu zan aura masa a rana daya wanda suka fi taki komai da komai"

"Gambo kinga abinda kika jawo ko?" Mami tace muryarta na fallasa yadda abin yake mata ciwo.

"Sai kiji idan da dadi, ni ba tawa 'yar kike neman hanawa nata farincikin ba. Ko bikinsu ba'ayi ba kunje kun nema masa auren wata saboda tsabar son burgewa ace kuna da zumunci. To amma banda abinki zumunci ya wuce ka fara yi da jininka. Mutanen nan 'yan kauye n....."

Wani lafiyayyen mari Mami ta saukewa Mummy Gambo idanunta jajir kamar garwashi. Gidan gabadaya shiru yayi Ummi ta kasa daurewa duk da ta soma hawaye ta fito. Awwab ma fitowar yayi bayan ya gama waya da Daddy ya sanar dashi rigimar da ake yi.

"Gambo ki kiyayeni wallahi. Ba tsoronki nake ji ba sannan baki fi karfina ba. Ki fice min daga gida kafin mu kaiga abinda rayuka zasu fi haka baci"

"Ni kika mara Hassana saboda wasu can bare da kika hadu dasu rana tsaka?" Mummy tace hawaye na neman zubo mata.

Ummi lokacin ta fito zuciyarta ta gama karaya ace saboda ita ko 'ya'yanta ake wannan rigima "Mami don Allah kuyi hakuri"

"Au dama kina ciki? Kun lallabo a cigaba da cusa masa 'ya don ya aura"

Awwab zaiyi magana aka kira shi. Zuciyarsa har suya take saboda bacin rai amma ya tabbatar idan yayi wani abu na rashin da'a ga matan da suke da matsayin iyaye a gareshi ba karamin fushi Mami zata yi ba ko da kuwa yayi haka ne domin rama mata. Sunan Alh Baba ya gani sai da yasha jinin jikinsa.

"Muhammad da kai da kannenka da iyayenka dake cikin gidan nan kuzo gabadaya yanzu ina jiranku"

Sai da ya dan rissina ya amsa masa sannan ya fada musu sakonsa. Haj Azumi da Mummy suka fita suna ta masifa. Mami ta kalli Ummi kunyar baiwar Allahn nan ta sa ko idonta ta kasa kallo. Murmushi Ummi tayi ta saki fuska.

"In sha Allahu komai zai daidaita"

"Kiyi hakuri Mairama ban so kika tarar da wannan rigimar ba"

"Haba Mami waye bai san ire iren wadannan matsalolin na dangi ba? Kuje ku dawo Allah Ya kawo mana mafita"

Daki Mami ta wuce ta sako hijabi ta fito. Fauziyya da Zahra harda Zayyana su ma kowacce da lullubinta. Ta kalli Zayyana tace mata ta zauna kiran bai shafeta ba. Dama a firgice take saboda haka bata ji komai ba sai murna da aka hanata zuwa. Suna fita Mairama ta dubi Emzee.

"Ina yayarka?"

"Tana dakinmu Ummi" Zayyana ta bata amsa. 

"Turo min ita dakin Mami ku zauna a nan ke da Karami."

Hawaye ne sharbe a fuskar Radhiya lokacin da ta shiga dakin ta fada jikin Umminta tana kuka sosai. Taji komai kuma ta fahimta. Duk da bata ga fuskokinsu ba amma ta gane akwai maman Ghazalatu kuma bata so ta auri Awwab. Ita kuwa wani irin mugun sonsa ma take ji yanzu bata fatan giftawar abinda zai iya raba su. Bata ki ba ko mata uku za'a aura masa a danginsu indai itama zata sami gurbi a zuciyarsa da gidansa.

"Alheran"

Faduwar gaba taji saboda bazata iya tuna yaushe ne taji sunanta ya fito daga bakin mahaifiyarta ba.

"Na'am"

"Kina son Awwab ne?"

Da ka ta amsa sababbin hawaye na gudu akan kumatunta.
Chapter 63 · 0% Book details