← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 157

Sashe 19

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan dadewar tasu ta dami matansu sosai. Kowacce dai tana kokarin daurewa ne don kada su rinka tadawa juna hankali. Amma a zahiri babu wadda bata kukan dare idan kewar mijinta da rashin sanin halin da suke ciki ya dameta.

Radhiya baki ya bude ba laifi don akwai surutu. Zaman da take yi dasu Zahra shi yake kara bude bakin. Ta dai fi likewa Awwab saboda yawo. Sai ya dauketa suyi ta karade barikin nan.

Yanzu ma 'yan takalmanta masu madauri aka sanya mata bayan an gama kitson tasa kuka ganin sun doshi gida "Ummi, Amma wawo" nufinta a kaita wurin Hamma su tafi yawo.

"Hajiyar gantali ni dai na gaji. Kiyi fatan daga islamiyya ya biyo sai ya kaiki wurin Mami"

Tana jin sunan Mami kuma kukan ya karkata tana kiranta. Tana ta bata baki yarinya taki shiru. Ba yadda ta iya dole ta kaita gidan. Mami tana cewa ta zauna tace gida zata tafi jikinta babu dadi. Radhiya harda yi mata bye bye tace idan Awwab ya dawo yazo ya karbar mata kaya don tasan yau ma ita kadai zata kwana Mami bazata bari a dawo da Radhiya ba.

Cikin dare bacci ya gagareta kamar yadda take ta fama 'yan kwanakin nan. Kullum cikin mafarkin Zayyan take, watarana ta tashi da kuka wani lokacin kuma idan mafarkin yayi dadi ta tashi da farinciki. Sai dai a can kasan zuciyarta tana fama da wani irin firgici wanda ta kasa gane dalilinsa. 

Envelop din da ya bar mata ranar tafiyarsa ta dauko ta shafa amma har yau taki budewa. Tsoron me ya rubuta take yi, karshe ma dai ta fadawa kanta idan ya dawo ya karanta mata da kansa.

Haka ta cinye daren a tunani baccin da kyar ya dauketa. Bayan tayi asuba ma komawa tayi abinta ta kwanta. Wurin tara na safe ta ji bugu kamar za'a balle mata kofa. Haka ta taso da hijab a baibai saboda sauri ta bude tayi karo da Christie. Itama makociyarsu ce tare da mijinta akayi tafiyar.

"Mama Radhiya e bi like say your sister don die ooo. She just knack her head for ground after one officer wey I no know come give her letter"

Cikinta ne ya murde da tsoro ta bi bayan Christie da gidanta yake kallon na Zainab.

Mata ta ga sun zagaye Zainab ga Ibrahim yana ta tsala ihu. Ashe a kansa ma ta fada bayan ta karanta takardar Allah Yasa akwai mata a wajen suka dauke shi.

Da kyar Mairama ta durkusa a gabanta tana rike mata hannu "Zainab menene?"

Takardar ta iya mika mata kawai. Mairama tana karantawa itan ma sai kuka da tausayin Hadir. Christie ta cewa ta shiga da Zainab gida tana zuwa. Hankali a tashe tana baza sauri ta tafi gidan Mami don ta fada mata. A can ta tarar da wani mummunan tashin hankalin.

Mami ke kuka sosai tana ta hada kaya ta jibge akwatuna biyu a falon tana ta watsa kayanta da na su Fauziyya a ciki.

Gabadaya yaran suna gefe kowa yayi tsit harda Radhiya da ta ga babu mai kula ta. Awwab bai san me ya faru ba amma ganin mahaifiyarsa na hawaye shima yake tayata.

Mami na ganin Mairama taje ta rungumeta ta sake fashewa da kuka "Ummin Awwab na shiga uku, ina zan sanya kaina"

Duk ta gama tsorata ta daure tace "addu'a zakiyi Mami ba kuka ba, komai yayi zafi maganinsa Allah. Me ya faru?"

"Daddy ne..." sai ta mika mata takardar ta karanta da kanta.

Hawaye ne ya cigaba da zuba a fuskokinsu Mami tace "Katsina zan tafi yanzu. Sai naje na ajiye yaran in sanar dasu sai mu wuce Legas din"

Suna haka Zainab ta shigo ta goya Ibrahim da har yanzu yake kukan faduwarsu ta dazu tana jijjiga goyon tana kuka. Mairama ce tayi mata bayanin me ya sami Major kuma. Su uku suka hada kai suna ta kuka abin tausayi.

Kusan a tare Mami da Zainab su ka fuskanci Mairama "Zayyan fa?"

Dammm taji gabanta ya yanke ya fadi ta juya a guje ga nauyin ciki ga kafarta da take yawan rikewa ta nufi gidanta. Tsoronta daya kada itama anzo sanar da ita halin da Zayyan yake ciki ba'a sameta ba. Bata tarar da kowa ba ta tsaya tana ta haki tana jin kamar za ta amayar da abinda yake cikinta a lokacin. Da jan kafa ta koma gidan Mami sun gama shiri ita da yaran.

"Zainab, Mairama...Allah kadai yasan ranar sake haduwarmu. Komai nawa ya danganta da samun saukin Daddy"

"Babu komai, Allah Ya basu lafiya baki daya."

"Amin" suka amsa sannan Zainab ta kara da cewa itama zata je ta sanar da nata iyayen ne domin a aika Kano gidansu Hadir. Sannan a san yadda za'ayi a dawo dashi gida.

Ji suke kamar daga ranar sun rabu kenan suka yi ta kuka sosai. Radhiya da kyar aka rabata da Awwab ta makale masa wuya tana ta ihun Amma.

***********

Gidan iyayenta Zainab ta wuce cikin kasa da awa guda ta isa. Bayan ta yiwa mahafinta bayani a take ya taso babban wan ta ya bashi kudin mota yace ya wuce Kano gidansu Hadir ya sanar dasu.

Zainab na kuka tace masa su yaushe zasu tafi Lagos din.

"Zainab kinfi kowa sanin halin da nake ciki. Kudin da na bawa yayanki wallahi harda na cefanmu na yau da gobe ne. Kasuwar babu kudi yanzu sai nayi huluna biyar ba'a sayi ko daya ba"

Shiru tayi wani hawayen yana sauko mata. Ita ta sani kuma bata boyewa iyayenta talakawa ne fitik. A Kano ma iyayen Hadir ba wasu masu karfi bane. Sai dai sun fi nata sosai. Albashin Hadir shine yake turawa gida kuma a haka yake yiwa iyayenta ihsani lokaci zuwa lokaci. Zuciyarta ta gama tsinkewa da wannan bakon lamari a gefe guda kukan Ibrahim yaki tsagaitawa.

Mahaifiyarta ta karbe shi tana ta juya shi da shafa jikinsa ashe ya sami gocewar kashi ne a hannu sakamakon faduwar da Zainab tayi a kansa. Babanta ya karbe shi ya tabbatar hakan ne yace ta tashi su tafi gidan dori.

"Wayyo Allahna Baba. Da me zanji?" Ta kara rushewa da kuka.

"Zainab kamar baki da ilimin Tauhidi? Ki fawwalawa Allah ki yawaita addu'a. Daga gidan dorin zan wuce wurin kawunki ko Allah zai sa yana da abinda zai ranta min ko ni kadai ne sai na wuce Ikkon. Kinsan babu yadda za'ayi na barki kije ke kadai baki san ko ina ba ga yaro babu lafiya"

Kai ta gyada kawai suka tafi gidan dorin aka gyara masa hannun. Ibrahim ya zama abin tausayi don ya jigata ba kadan ba. Suna dawowa sai zazzabi da amai ya sarke shi ko hannu baya iya motsawa da kyau. Zainab tayi kuka har taji babu dadi.A rana daya rayuwar wannan baiwar Allah ta juye gabadaya. Miji yana asibiti a wata uwa duniya, amma babu kudin zuwa gareshi. Babanta yace su jira yayanta da yaje Kano ya dawo. Idan iyayensa sun dauko shi sai ta tafi can ko da yaya zai samu ya biya mata kudin mota. Yini kuka, kwana kuka haka ranar ta kasance mata.

***********

Gidansu Mami unguwa daya ne da na su Major Mustapha. Iyayensu maza su biyar ne a gidansu. Baban Major ne na biyu nata kuma auta. Da suka tashi aure sai suka zauna a gidajen da katanga kadai ke raba su. 

Daga tasha bus ta hau zuwa unguwar tasu. Tana shiga layin ta hango babban wan iyayen nasu da suke kira Alh Baba. Yayi shigar mutumci da babbar riga da farin rawaninsa irin na malamai. Motarsa kirar Pigeout (pijo) zai shiga daya daga cikin yaransa zai kaishi unguwa ya hangota. Dakatawa yayi don ya tabbatar da wace ce saboda ita da Usainarta sai kayi musu farin sani kake iya tantance su.

Tana matsowa ya saki murmushi saboda daga yaranta ya ganeta masu kama da mahaifinsu "Mutanen Shehu saukar kenan?"

Daga ita har yaran sun durkusa da niyar gaishe shi kawai ta fashe da kuka. Yaran ya kalla yasan duk yadda akayi wani abu ya faru "Kai Muhammadu wuce ciki da kannenka" ya fadawa Awwab.

 "Ke kuma muje" ya nuna mata hanyar gidansu Major.

Awwab kamar ya bita ganin tun a gida suke ta kuka amma tarbiyarsu tasa ya bi umarnin kakan nasu. Ciki suka shiga matan gidan suna ta murna ana tambayarsu mamansu suka ce tana wurin Alh Baba.

Basu sami baban Major ba sai Iya mahaifiyarsa. Alh Baba ya tura aka kira ragowar kannensa sannan suka bukaci jin dalilin zuwanta tana kuka. Duk sun sani cewa ya tafi Liberia tunda yazo yayi musu sallama. Tana kuka ta sanar dasu abinda takardar da aka bata ta kunsa. Gidan sai kuka tamkar ance ya riga ya rasu.

Bayan dawowar mahaifin Major iyayen su kayi zaman shawara. An daidaita magana akan cewa Alh Karami baban Mami da kuma yayan Major Mustapha da suke uwa daya uwa daya su ne zasu tafi.

Mami ta kasa daurewa tana kuka, Alh Baba ya dubeta "kiyi hakuri Hassana. Su dinmu dauko shi zasuyi a dawo dashi gida yayi jinyar a kusa. Legas tayi mana nisa. Idan munje da yawa bamu san ina zamu kwana ba"

Ba haka taso ba ko kadan amma bata da yadda zata yi. Tana ji tana gani asubar fari suka kama hanya a motar Alh Baba.

**********

Kwanaki biyar kenan da samun sakon da ya tada hankula a Giginya army barrack. Mairama ta rame sosai a 'yan kwanakin. Radhiya ma bata samun kulawa yadda ya kamata saboda tun ranar da suka tafi fargaba tasa ta fara nakuda a tsattsaye tana daurewa.

Rayuwa take yi mara dadi. Babu miji kuma babu wadanda suka zame mata tamkar 'yan uwa na jini. Tarin fargaba ne ya cika zuciyarta da kokonto. Ta damu tasan halin da su Hadir suke ciki  ga kuma rashin sanin komai game da Zayyan ya sanya take jin kamar zata yi hauka.

A kwana na shida ciwo yaci karfinta ta daure taje ta buga kofar gidan Christie. Ita dinma duk zulumi da fargaba sun cinyeta tana ta ramewa. Tana ganin Mairama a haka tasan nakuda ce. Gida ta koma ta dauko zani ta saba Radhiya a baya sannan ta taimaka mata suka tafi asibitin sojojin inda take awo.
Chapter 19 · 0% Book details