Sashe 135
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jiki na tsuma numfashinta sai ka rantse fita zaiyi saboda tsananin kidima ta fito ko takalmi babu sai mayafi tayi gaba suna biye da ita. Motocin da ta gani ne suka sa ta hadiyar wani yawu mai mugun daci sannan aka nuna mata kofar gidansu ta shiga a darare.
Zayyan yana mota ya hango shigarta ya kada kai. Mace da kimarta da komai ta zabi wulakanta kanta kamar wata mara daraja. Babu abinda yake tunzura zuciyarsa kamar makantar masa da mata na shekara goma. Fitowa yayi daga motar sanye da kayansa na sojoji yayi matukar kyau sai dai fuskar nan babu alamun wasa ko kankani kai baka ce Zayyan bane. A hade take tamkar hadari mai shirin zubar da ruwa. Cikin wani irin taku da dogayen kafafunsa yake tafiya da sassarfa yaransa suna kamewa suna sara masa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya da ya shiga soron gidan yana fatan bukata ta biya domin idan Salame ta sake gangancin taba masa iyali bayan zamansu na yau to ko Mairama bazata sami labarinta ba sai yasa an gama koya mata hankali. Wasu mutanen basa gane yaren laluma da bi a hankali. Magana tafi shigarsu da tasiri idan su ka ji an taba lafiyar jikinsu.
Katuwar tsakar gidan gabadaya iyayensu ne. Malamijo, Yadikko da Hajjo sauran amaren nasa yace kowacce ta zauna a daki. Gefe ga Innawuro da Nene Marka sai Ta Madina. Mairama da Mama Zainab suna daki. Can daya barin kuma Alh Indararo ne da Baffan Rahima.
Kusan tafiyar yaji Zayyan yayi da Salame tana labe a bayan kofa ta kasa karasa shiga tsakar gidan. Takun da taji daga bayanta da hadadden kamshi mai tafiya da hankalin duk wanda ya shaka su ne suka sa ta farga ta juya baya. Ai tana hada idanu dashi kallon da yayi mata sai ji tayi fitsarin da take makalewa yana diga. Zayyan kuma ya dauke kai kamar bai ganta ba ya taho fuuu shine ta shiga kamar wadda aka koro.
Babu wanda cikinsa bai yamutsa ba da Zayyan ya shigo duk da cewar da yawansu sun sanshi amma babu wanda yayi masa wannan sanin ta fuskar sojoji. Escort dinsa na bayansa sauran suna waje ya nufi gaban Malamijo. Mal Ali Gidado sai ji yayi hantar cikinsa na kadawa kamar ba surikinsa bane. Yanzu yaron nan idan allurar sojansa ta tashi ya manta da matsayinsa a gareshi yace zai hada dashi a kulle ai ya shiga uku. Wani tunani ne ya darsu a zuciyarsa ya kara tsorata wato tunanin ko Mairama ta fada masa yadda baya ciyar da ita da yaranta sosai lokacin da ta dawo gidan. Dan sakin fuska yayi ya gaishe shi sannan yace ina Innar Salame.
Ta Madina jiki na rawa taja jiki ta fara yin hanyar kofa za ta gudu Hajjo tace "ga ta can a bayanka...Ta Madina ana magana"
Idanunta su ka soma kadawa ta dafe kirji "banda abinki Hajjo idan da kara ai Yadikko zaki nuna matsayin Innarta. Ni dai haihuwar Salame kawai nayi amma komai nata da tarbiyarta a hannun Yadikko suke. Yau ko wani abu tayi ba daidai ba tarbiyar Yadikko ce da Malamijo"
Yadikko ta zaro idanu ganin kowa ita yake kallo "daga abin arziki kuma sai kice nice na haifeta. Irin wannan tunda ya nemi ainihin mahaifiyar nasan cewa akwai dalili."
Shi dai Malamijo gumi ne ya cika masa tafin hannu ya kalli Salame ta firirice gabadayanta a ta manne da bango.
Zayyan ya sake daure fuska yana kallonta sannan yace "Malamijo ina son ganinka da mahaifiyarta muyi magana"
Kan kace kwabo su Hajjo da sauran kowa ya bace sun shige dakunansu. Alh Indararo ma da Baffan Rahima cewa suka yi zasu jira a soro su ka tafi. Ta Madina ba don taso ba aka bude musu wani dan daki suka shiga ita da Malamijo. Zayyan zai bi bayansu ya kalli Salame ya daka mata wata razananniyar tsawa da ta kadawa hatta Mairama da ke daki ciki "zaki zo ki shige ko sai...."
Bai rufe baki ba ta shige dakin itama ta sami jikin bango ta kuma rabewa sannan Zayyan ya shigo ya zauna.
"Salame" taji ya ambaci sunanta da wata irin kakkaurar murya. Jinin jikinta ya sake tsinkewa bakinta kamar ansa kwado ta kasa budewa ta amsa.
Ta Madina kuwa ta kai mata duka "ke dallah bude baki ki amsa kina ji ana kiranki"
"Barta dai so take ta nunawa sojoji iyakarsu" cewar Malamijo a hasale.
Kai ta dago a hankali su ka hada ido da Zayyan sai ji tayi har abada bata fatan sake kallon wadannan idanuwan masu tsorata mutane su kada masa zuciya da hanta. Sunkuyar da kanta tayi tana kallon kasa.
Gyara zamansa yayi ya dan rankwafo kansa "naji labarin duka abubuwan da kika yi tun daga tafiyata zuwa jiya da yamma."
Gumi take yi sosai tsoro iyaka tana ji kuma tayi imanin idan sun nemi tafiya da ita babu mai hanasu. Yadda ake bada labarin rashin imanin sojoji itama yanzu haka zasu je su rinka azabtar da ita? Muryar Zayyan ce ta katse mata tunani.
"A jiya da aka fada min abubuwan da kika yi babu abinda yazo raina sama da son kulleki a dena jin duriyarki har abada...." kallonta yayi na abinda baifi sakan goma ba ya kula hankalinta yana gareshi kamar yadda yake so "...sai dai kinci darajar haihuwa Salame. 'Ya'yanki daidai har bakwai idan na rufeki ko kadan banyi musu adalci ba musamman kananan. Yanzu ina so a gaban mahaifanki ki fada min me Mairama tayi miki wanda ya janyo faruwar wadannan abubuwa"
Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta ya daga murya "ba dake nake ba?"
Zabura tayi ta sake yin baya "uhmm, uhmmm"
"Kin zama bebeya ne ko me?" Ya sake yi mata tsawa.
"Uhmmm babu komai" tace da kyar iyayenta suna kallonta cike da haushi.
"To ni bari na fada miki me ya hadaku. Shekaru ashirin da hudu da suka wuce nazo gidan nan tadi wurin kanwarki kika kawo min wasikar tayin soyayya, anyi haka ko ba'ayi ba?"
"Anyi" tace da sauri.
"A lokacin na amsa miki ko nayi wani abu da zai nuna miki cewa ni Zayyan ina da fuska biyu ta ha'inci in nemi kanwa in nemi yayarta?"
Girgiza kai ta soma yi a hankali tana tuna yadda ya yayyaga wasikar ya watsar.
"Salame nasan cewa soyayya babu ruwanta da dacewa ko akasin haka. Amma ance wai ana barin halal ko don kunya. Kanwarki wadda bata da zance sai naki kuma kema a yadda na fahimta wancan lokacin kina sonta ita ce kike son manemin aurenta. A tunani na ke mai iya hakuri ce ki bar mata ko da ina sonki balle tun farko ita na nema. A matsayinki na musulma tun lokacin ya kamata ki karbi kaddara ki rungumi kyautar da Allah Yayi miki ta Salisu. Ko kinsan cewa Zainab matar Hadir nine na fara nemanta? Ni na nemi kwatancen gidansu duk da ba wata muguwar soyayya naji ta kamani a lokacin haduwarmu ba amma kinsan indai saurayi ya nemi gidansu budurwa ko yaya ya ga abinda yake so ne. Amma abin mamaki ranar da Hadir yaje gidansu da zummar fada mata ni bazan samu damar cika alkawarin zuwa ba su ka kamu da son juna. Tun daga wannan ranar har rana irin ta yau ban taba sake yiwa Zainab kallon da ya wuce kanwata matar dan uwana ba."
Malamijo da Ta Madina sai jinjina kai suke yi yayin da Salame tayi shiru kawai tana sauraron maganganunsa.
"Ko da kina sona to ba da zuciya daya bane hasali ma nafi danganta abinda kika yi da hassadar kanwarki. Kun rayu kece 'yar gata saboda kina samun kulawar mahaifiya ita kuma babu uwa babu dangin uwa. A kullum Mairama ce a kasanki ki bata saura tayi miki godiya. Lokaci daya kinga abinda kike so shi kuma ya karkata gareta shikenan kika juya waccan soyayya da kike yi mata zuwa kiyayyar da hassada ta zama musabbabinta. Kin manta cewa kowane bawa da irin rayuwar da Allah Ya tsara masa. Wallahi Salame tunda kika ga baki aureni ba ki sani cewa bazaki taba iya rayuwar da Mairama tayi ba. Duka duka ba don rabon haihuwa ba zaman har na wata nawa muka yi a karkashin inuwa guda? Mun rabu da kuruciya batare da mun mori komai a zamantakewarmu ba mun sake haduwa farin gashi na wahala da zuwan shekaru ya zo gareni. Matata da na bari da kuruciya na dawo ta koma babbar mace. Kinsan yadda muke ji kasancewar shekarun da ya kamata mu zauna mu fuskanci juna sun kare bama tare. Duka duka Salame shekara nawa kuma ya rage mana da zamu sake maimaitawa a doron kasa? Na tafi na bar yarinya ko tafiya bata yi na dawo watanni kadan ga aurenta. Cikin da bansan meye a ciki ba na dawo na sami katon saurayi yana shirin zama soja. Salame zaki iya wannan rayuwar da Mairama tayi cikin kunci, kewa da makanta ga marayu a gabanta???"
Damm taji zuciyarta ta buga sai ga hawaye daga sama yana sintiri akan kumatunta.
Ta Madina ma kuka take yi Malamijo ya sake jin kunyar abinda yayi a baya. Kuncin da ya baro a baya ne ya tuna shi ma Zayyan din yasa yatsansa ya kore hawayen da ya taru a gefen idanunsa.