← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 157

Sashe 56

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zayyan yana ganin haka yayi kukan kura ya kwace jikinsa daga wadancan biyun ya fada kan wancan. Abinda yaje dauka yayi sa'ar samu wato bindigar da take aljihun wandonsa ta baya. Baiyi wata wata ba ya saita kansa ya sakar masa harsashi. Wadancan suna daga inda suke suna kokarin harbe shi da bindiga yayin da ogan nasu yayi wani irin ihu saboda kaninsa ne Zayyan ya kashe ya sake saita mutane biyun da suka fi kusa dashi suma ya harbesu yana daga durkushe. A take wurin ya hade sai sautin harbi kake ji amma karfin ruwa ya bawa Zayyan damar kubcewa. Ya sadakar dama yau mutuwarsa tazo amma bai hakura da harbin ba sai da ya sake kara mutum biyu sannan aka same shi a hannun da yake harbin dashi. Dole ya saki bindigar kafin ya farga wannan ogan nasu ya kafta masa bindiga a tsakar kansa ya fadi a wurin sumamme.

Wani irin abu yake ji kamar ruwa yana zuba a fuskarsa amma kuma a shake yake. Yayi ta yunkurin bude idanu amma ya kasa sai wani irin abu kamar an like idanun suna ta radadi. Duk wani tunaninsa ya tsaya cak kwakwalwar ta cushe. Sai bayan wani lokaci yana cikin wannan yanayi na shakewa da ruwa ya soma turjiya ya gane kafafunsa daure suke a jikin wani abu sannan hannuwansa ma an daure su ta baya. Hannun da aka harba dama tamkar ba a jikinsa yake ba saboda kumburi da ciwo. A kokarinsa na mikewa tsaye ne ya gane cewa akan kujera yake a zaune. An daure kafafunsa da jikin kujerar hagu da dama. Hannuwansa kuma suna daure ne ta baya harde da juna. A takaice ma tsumma ne aka dora akan fuskarsa ana kwarara masa ruwa wani ya rike kan ta bayansa.

Sai da suka tabbatar ya azabtu iyakar azabtuwa aka cire tsumman. Tari ya rinka yi a wahale ruwa na fita ta baki ta hanci. Idanunsa sun juye ya kasa tantance a ina yake ga rashin wadatar haske a dakin.

Hargagin mutane yaji aka bude kofar hasken rana kwal ta mamaye dakin.  Wasu mutane ne suka shigo kai tsaye wurinsa suka nufa. Bayan sunyi magana da yare ne suka koma turanci aka tambaye shi mutum nawa ne a sansaninsu da sauran. Sojoji nawa ne Nigeria ta turo domin kwantar da tarzoma kuma a ina da ina suka kafa sansani. Idan ma zai iya magana bazai fada musu ba saboda duka jikinsa hatta bakinsa da hakora suka cire jiya da suka dauko shi ciwo suke yi. Dukansa suka fara yi saboda yaki yin magana sai yaji muryar wani shima a wahale yake yace suyi hakuri ya sami lafiya sai ya basu amsar da suke nema.

Marinsa wani yayi suka ce yayi musu shiru. Sai da suka sake yiwa Zayyan ligi-ligi sannan suka yasar dashi a kasa suka tafi. Mutanen wasu tsageru ne cikin 'yan tada kayar baya da gwambatin kasar ke nema ruwa a jallo. Su kuma suna son dakile taimakon da kasarsu take samu na jajirtattun sojoji musamman daga kasarmu mai albarka Nigeria. Shiyasa suke yi musu dabaru suna kashesu suna kama na kamawa domin neman bayanai. Har yanzu dai babu nasara domin sojojin sun dauki amanar kasarsu jini da tsoka. Idan suka kasa samun abinda suke so sai su kashe mutum.

Bayan fitarsu dayan mutumin da yake dakin ya janyo shi da kyar zuwa wani dan lungu. Tsohuwar katifa ce a wurin da 'yan tarkacen asibiti. Kwantar da Zayyan yayi akan katifar ya farke hannun rigarsa da ya kumbura. Ga dukkan alamu bullet din da ya same shi yana ciki ga uban kumburi fitar dashi zaiyi wahala. Shi kanshi mutumin wahala ta zuge shi duk ya rame.

Wata siririyar wuka ya dauko ya kunna lighter da take ajiye a gefe ya rinka saka tsinin wukar a cikin wutar na dan lokaci ya dauki zafi sannan ya mika masa wani tsohon yagwalgwalallen filo ko riga babu.

"Put it in your mouth"

"Wwwwhat?" Ya fada idanunsa akan filon da babu kyaun gani. Bai rufe bakinsa ba mutumin nan ya tura masa filon lokaci guda kuma ya danna wukar cikin hannunsa saitin inda yake iya ganin alamun bullet din ya shiga. A maimakon kara Zayyan cizo ya kaiwa filon har hakoransa suka kusa hadewa ta ciki don azaba. Juyi biyu mutumin yayi da wukar sai ga bullet ya fado kasa.

Zayyan yayi gumi ba kadan ba idanunsa sunyi jazur sai jijiyoyin kansa da suka mike. Kwanciya yayi mutumin yana masa sannu. Babu bakin amsa sai kai yake gyadawa. Daga wannan lokacin bai kara sanin me ya faru ba sai farkawa yayi yana jin kamar ana dukan wani ga dare. A take ya wartsake ganin mutumin da ya taimaka masa ne ake yiwa dukan kawo wuka. Mantawa yayi da ciwon jikinsa ya tashi a fusace yayi kansu. Ransa ya kara baci ne da ya fahimci dalilin taimakonsa da mutumin yayi ne ake masa haka. Dukan ya koma su biyo ake yiwa amma Zayyan bai hakura ya janye jikinsa ba. Sai da suka gaji don kansu suka fita aka barsu a kasa kowanne jiki yayi laushi.

"Allah Ya isanmu tunda kunfi karfinmu....ashhh bakina" hannu ya dora daga gefen kumatunsa bangaren da hakoran suka zuba. Wahalalliyar dariya wancan mutumin yayi daga inda yake. Zayyan ya dinke fuska don ya jigata sosai yace "baka daku bane kake dariya, ni yanzu suka sake dawowa suman karya zanyi"

Dagowa mutumin yayi da kyar Zayyan sai ya koma turanci "are you okay?"

Dariya mutumin ya sake yi sai abin ya dan bashi tsoro ya ja jikinshi kadan ba dai mai matsalar kwakwalwa bane ko.

"Duk wannan dukan da muka sha ka sani dariyar dole" kallon mamaki Zayyan yayi masa yana jingina bayansa da bango ya dora da cewa "ina kallonka nayi tunanin kaima bahaushe ne"

"Kaima dan Nigeria ne?"

"Soja kamarka" yace da muryarsa da take a kausashe kamar wanda ya tashi daga bacci ko aka shake masa wuya.

Zama Zayyan ya gyara yana kallon mutumin sosai. Wannan zai girmewa Major Mustapha sai dai rashin khaki a jikinsa yasa a haka bazai iya gane mukaminsa ba.

"Lt Zayyan Muhammad Tureta, Giginya Army Barrack Sokoto"

"Colonel Nasiruddeen Aliyu, Bukavu Army Barrack Kano"

Soja ya ga ubangidansa, da ciwon hannun nasa haka Zayyan ya yunkura ya mike yana dafa bango ya dan kame jikinsa yayi masa salute.

Kai Col. Nasiruddeen ya kada yana dariya "baka daku bane shiyasa kake iya tashi, ni yanzu suka dawo cewa zanyi mace ne ni da kayan maza"

Ga wahala ga ciwo Zayyan sai da ya bushe da dariya. Sun dan zauna shiru kafin Col. Nasiruddeen ya soma bashi labarin dalilin zuwansa wurin.

Col. Nasiruddeen Aliyu mutumin karamar hukumar Wase ne ta jihar Plateau. Likita ne na sojoji wanda yake kwararren consultant a asibitin sojoji na Bukavu barrack a Kano inda yake base dinsa. Rabon wannan wahalar da kansa ya nemi a sanya sunansa cikin masu tahowa Liberia saboda burinsa na taimakawa sojojinsu. Sai aka shi turo a matsayin Cheif Medical Officer tare da wasu mutum uku su ma duka sojojin ne kuma likitoci. A lissafinsa yayi a kalla wata biyar tare da mutanen nan. Watarana sun sami rahoton rigima tsakanin sojojin kasar da abokan rikicin nasu inda mutane da yawa suka jikkata ana bukatar likitoci domin taimakon gaggawa. Shi da sauran da suke sansani guda inda yake a matsayin wurin kula da masu rauni suka dunguma da kayan kula da marasa lafiya da magunguna. Rabin tafiyar suka yi kamar yadda aka shammaci su Zayyan su ma haka aka yi musu. Bayan musayar harsashi an kashe mutum biyu cikinsu sauran kuma aka kadasu aka tafi dasu. Akan idanunsa saboda sun san shine babba a cikinsu aka rinka kashe na kasa dashi don sunki bada bayanan da ake bukata. Akwai takardu a jikinsa na bayanin sojoji masu tahowa, ranar isowarsu da ma adadin makamai, abinci da magunguna da zasu taho dashi. Tsoron kada a cutar dasu ya sanya ya fakaice su ya dunkule takardar ya cusa a bakinsa ya hadiya farat daya. Stapler din da take jiki wadda aka mannesu tare ita ce a lokacin hadiyar yana ji tana kartar masa wuya har ta wuce. Bai fahimci mugun rauni tayi masa ba sai da aka zo yi masa tambaya yana bude baki sai jini ya rinka zubowa ga uban radadi daga cikin wuyan nasa. Ya sha wahala sosai karshe muryarsa ta koma haka bayan wani lokaci. Babu ko mutum daya saura cikin abokan tafiyarsa duka an azabtar dasu an kashe. Shi kuma sun mayar dashi likitansu. Abubuwan da ya gani da idanunsa mutanen suna yiwa bayin Allah ba kadan bane, jiran amfaninsa ya kare kawai yake yi shima su kashe shi.

Zayyan ya tausaya masa shima ya fada masa yadda ya fado hannunsu. Ranar hirar da suka yi kenan kafin wahala ta sa suyi baccin dole. 

Wurin da suke ba cikin daji bane hasali ma a cikin gari ne mutanen suka samu wani tsohon gini da rigima ta kori masu shi suke dabdalarsu a ciki. Tsaron da suke masa yasa har yanzu ba'a gano suna zuwa wurin ba. Sanyin asuba ne ya farkar da Zayyan ya tashi ya ga Col Nasiruddeen shima ya farka. Gefe yaja jikinsa ya bubbugi kasa ya dawo.

"Rabona da sallah tun la'asar ta ranar da muka fito"

"A haka zaka yi sallar babu alwala ko tsarki?"

"Akwai ruwa ne a kusa?" Zayyan ya tambayeshi yana leka lungunan gidan.

"A'a sai dan wanda suke kawo min tare da abinci. Idan yana da yawa dashi nake yin alwalar nayi sallolin da suka samu"

Murmushi Zayyan yayi masa "shiyasa Allah Ya hore mana taimama domin saukakawa a inda ruwa yayi karanci."

Col. Nasiruddeen bai nuna girman kai ba ya bari Zayyan ya koya masa. A zaune duka suka yi sallah jiki ya kara tsami. Zayyan ya dade yana yi saboda yasan wanda suke kansa da yawa. Addu'a yake ta yi Allah Ya tseratar dasu, Yasa su Hadir sun tsira kuma Ya maida shi ga iyalinsa.
Chapter 56 · 0% Book details