Sashe 25
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe idanu yayi yana sauraronta tana ta yi masa magana. Can ya soma jin fitsari, ya rasa yadda zaiyi tun yana kokarin rikewa har ya saki a kan katifar kamar kodayaushe yanzu ya zamewa kannensa wani karin nauyi.
Lura da danshin Zainab tayi ta mayar masa da hannunsa inda yake ta fita wurin Ummansa tana neman tsumma da ruwa.
"Fitsari yayi ko?" Umman tace tana jin babu dadi.
Murmushi Zainab tayi "eh Umma, yanzu zan gyara wurin"
"Barshi Zainab ki huta kinji. Idan kannensa sun shigo sai su gyara. Yanzu zaki ga daya daga cikinsu. Sun san yanayin nasa shiyasa basa yin nisa ake barin guda a kusa"
Kai ta dukar "danshi zai dame shi. Zan iya gyarawa"
Bata jira cewarta ba ta koma dakin. Yana nan inda ta barshi sai kansa da ya juya yana kallon sama sabanin dazu da yake kallonta. Wani kululun bakinciki yaji ya rufe shi a lokacin. Ya gama wahala ya dawo da ransa amma ya zama kaya irin haka. Zainab dinsa abar tattalinsa ita ce haduwarsu ta farko bayan watanni zata kare a gyaran fitsari. Kuka zuci ya rinka yi har ta gama mirgina shi ta sauya masa kaya sannan ta cire zanin gadon ta shimfida zanin goyon Ibrahim a gefe inda ta ja shi ya kwanta.
Zama ta kuma yi ta dora kansa a cinyarta "Hadir"
Bude idanu ya sake yi sai ya ga ta duku da kanta ta sumbaci lebensa. Zuciyarsa tayi nauyi matuka. Ga matar da yake so take son shi amma ko yatsanta bazai iya rikewa ba.
"Ka ga alamomi zamu fara koya yadda zan rinka ganewa idan kana bukatar wani abu"
Ido ya kifta don ya nuna mata ya fahimceta. Ta gyara zama tana yawo da yatsunta a kansa "idan kana son abinci ko ruwa sai ka juya kanka barin dama. Idan kuma bandaki kake son zuwa sai ka juya hagu. Ni kuma sai ince abinci ko ruwa idan dama ne. Sai ka kifta ido sau data shine eh, sau biyu kuma a'a"
Ta jima ko lokaci bata tunawa tace sai sun kwatanta. Ummansa da kanta ta dawo tace lallai tazo taci abinci. Ko da ta diba dakin nasa ta sulale ta koma taci. Shi sai su kunu ko koko ake bashi da ruwa. Asibitin da aka kaishi a Kano ne suka ce kada a bashi mai nauyi har sai ya soma sabawa da sabon yanayin jikinsa. Kudin da aka nema na gwaji da aikin da ake tunanin yi masa kuwa ko yana daukar albashi kila sai ya shekara biyar zai tara su. Aiki a lakarsa ta kashin baya ba karamin tsada bane dashi.
Da daddare ko keyarta basu gani ba a ciki. Hadir ya sake matsuwa cikin daren tana rungume dashi tana bacci haka ya saki fitsarin nan ya bata musu jiki saboda bashi da damar tashinta. Tana tashi da asuba gyaran wurin ta soma yi sannan ta goge masa nasa jikin tayi masa alwala.
Satinsu daya babanta ya koma. Zainab ita take yiwa Hadir komai banda zuwa bandaki saboda yayi mata nauyi. Wannan tana ganin yayi alamar take sanar da kaninsa.
Wata guda suka yi a haka babu wani cigaba kullum yana nan a yadda yake sai ma hawan jini da ya kama shi saboda yawan tunani. A wata na uku mahaifanta suka dawo dubiya. A lokacin ne kuma baban Hadir a gabansa da Ummansa da iyayen Zainab ya bijiro da maganar kashe aure.
Kofin kunun hannunta ne ya subuce bata sani ba kuma bata damu ba.
"Kashe auren wa kenan?" Babanta ya tambaye shi.
"Zainab da Hadir"
Zubewa tayi a kasa ta fashe da kuka "Umma kuyi hakuri idan wani abu nayi zan gyara."
"Ko daya Zainab. Wannan shawarar da wahala muka iya yanke ta. Zamanki da Hadir babu alfanu sai tarin wahala. Nasan kunyi mana halacci da kawaici amma in sha Allahu bazamu bari naku hakurin ya kare ba"
Kuka sosai Zainab ta saka tana ji suna cigaba da maganar tana ta magiya.
Shi kansa Hadir din hawaye yake fitarwa. Babansa ya sake bata hakuri "kina da kuruciyarki ta yaya zamu barki da mutumin da bazai iya yi miki komai ba sai zame miki nauyi. Abu na biyu Hadir ne karfinmu mu kanmu. Yana kwance yanzu mu ma rayuwar wahala take mana ta ina zamu ajiyeki? Yau da gobe sai Allah 'yata Zainab, watarana zaki bukaci fiye da Hadir amma aure yayi miki dabaibayi. Zaki so kulawa da kowacce mace take muradi a gidan aurenta. Sannan ko mu iyayensa zamu iya gajiyawa balle mata. Komai fa sai anyi masa hatta gyara kwanciya. Kudin aikinsa kuma bamu da yadda zamuyi mu taba hada rabinsa ma. Zuwana Sakkwato uku akan maganarsa sun ce babu kudi a barikin"
Zainab daga gaban wannan take zuwa gaban wancan tana kuka tana roko akan su barta da mijinta. Kwarai ta basu tausayi amma basa son nuna son kansu da rashin dattako. Hadir sai rufe ido kawai yayi zuciyarsa tana kuna sai da yaji mahaifinsa ya kira sunansa.
"Hadir, ina mai umartarka da ka sauwakewa Zainab kada mu zama masu daukan alhaki, ka amince"
"Kada ka sakeni, don Allah ku barni da aurena" Zainab ta fada cikin tashin hankali.
Kifta ido Hadir yayi babansa ya sake cewa " ka amince cewa kai Hadir ka yiwa Zainab matarka saki daya?"
Wannan karon ma ido ya sake kiftawa yana zubar da hawaye. Zainab yaji ta fado a jikinsa ta kankame shi tana kuka bata san ma me take yi ba "Wallahi ban saku ba, babu inda zani"
Mamanta da Umman Hadir kukan suke tayata saboda tausayi.
"Zainab kiyi hakuri"
"Ba fa zan je ko ina ba ai ba da bakinsa yayi sakin ba"
Babanta gani yayi abin yana daukan lokaci an kasa rarrashinta ya tashi ya mareta. Ta rike kunci baban Hadir yana cewa don me zai mareta "yaya take so muyi mata ne? Duk wani bayani anyi amma da gangan taki ganewa. Ki tashi maza ki hada kayanki yau dinnan ma zamu koma"
Karamin hauka Zainab tayi ranar har suka bar garin gashi ance ta bar Ibrahim saboda Hadir yaji saukin rabuwa da ita shima.
Sau biyu tana guduwa Kano bayan sun koma sai da babanta yayi mata kaca kaca karshe ya yi mata aure. Lokacin Hadir ya kusa shekara biyu a kwance. Ranar da aka kaita a ranar ta nuna mijin da wuka tace ko ya saketa ko ta kashe shi ta kashe kanta. Bai tsaya bata lokaci ba yayi mata saki ukun da ta bukata.
Iyayenta sunyi fushi sosai da ita ta koma wata iri ita kanta saboda tashin hankali. Sai da kyar ta samu suka hakura bayan an sake saka mata rana da wani ma'aikacin kamfanin man fetur a Port Harcourt. Wannan karon babanta yace idan ta sake kashe aurenta ko taje Kano bazai yafe mata ba. Mijin nata mutumin Sakkwato ne amma a can Port Harcourt din zasu zauna.
Ba don taso ba akayi auren. Mutumin mai suna Musa Waziri yana matukar son Zainab shiyasa baya fushi da ita. Yana da kudi shi ya canjawa iyayenta gida ya samarwa yayyenta maza biyu aiki a branch din gidan mansu suka samu rangwame daga kangin talaucin da suke ciki.
Ranar da ta tare tayi kuka kamar ranta zai fita. Gani take taci amanar Hadir shiyasa har shekaru suke tafiya tsakaninta da mijinta bata taba wata doguwar walwala ba. 'Ya'yansa 'yan mata biyu da ya rabu da mahaifiyarsu su kadai ne suke samun kulawarta. Wannan dalilin shi ya karawa Musa hakuri da ita da halinta na rashin son sa. Duka wani hakkinsa tana saukewa amma soyayya da fara'arta sai yayi watanni bai gani ba.
Hadir yana nan kwance sai gashi da suka samu kaninsa yake kaishi idan yayi ciniki a kasuwa kudi sun samu. Gashin yana taimaka masa wurin jin dadin jikinsa saboda yawan kwanciya. Magana ce dai da wuya yake iya hada kalma daya kwakkwara. Ibrahim yana girma ya gane waye Hadir a wurinsa a hankali ya gudu daga cikin gidan ya koma dakin mahaifinsa. Sannu a hankali indai ba yana makaranta ba komai na Hadir ya dawo gareshi. Idan aka kaishi hutu wurin Zainab baya iya sati biyu ya rinka cewa Abbansa kenan dole a mayar dashi da wuri.
A haka shekaru ke tafiya a haka rayuwar wannan iyalin ta wargaje gabadaya daga aikin soja. Miji ya koma kan wheelchair ga ciwon zuciya ya kama shi da gaske saboda yawan tunani. Uwa ta sake aure bisa dole amma zuciyarta tana ga tsohon mijinta sannan dansu ya taso a wata bahaguwar rayuwa bai san komai ba tunda ya fara wayo sai jinyar mahaifinsa.
A bangaren Hadir rashin iya magana ya nemi iyalin Zayyan yana damunsa sai ya kwana yana kuka idan ya tuna rasuwar aminin da ya dauka tamkar dan uwa. A irin lokutan ciwonsa ke tashi a kasa gane kansa. Zainab ma bata taba mantawa dasu ba amma kunyar nemansu take yi a yanzu bayan shekaru sun ja ta dan dawo cikin nutsuwarta. Bata san Zayyan ya rasu ba haka nan bata sani ba ko shima ya dawo kamar Hadir. Mami kuwa sunan garinsu kadai ta sani ta ina zata fara nemanta.
Babban abin dubawa shine komai na rayuwa duk yadda ka kai da matsuwa dashi sai Allah Ya nufeka da yinsa. Mukan kwadaitu da gabatar da wani abu mai girma a garemu amma sau tari sai wasu abubuwa suyi mana shamaki dasu. Yanayin rayuwa bai mantar da Zainab mutanen da suka yi zaman amana ba amma halin da ta tsinci kanta yasa damuwarta ta danne hangenta. Burinta daya ne a rayuwa...ta komawa Hadir!
**********
"Ni na kashe shi...ni nayi ajalin Zayyan..ina zan saka kaina? Hassana na kashewa Alheran mahaifi. Meyasa nima ban mutu ba?"
Kuka ne irin na mazan da suka ga tashin hankali muraran ba labari ba. Babban soja mai ji da jarumta shine yake zubar da hawaye kamar yaron goye.